Showing 24001 words to 27000 words out of 34797 words

Chapter 9 - KWARTON MANYA PART 3 by Maman Teddy .pdf

04 Nov 2025

791

É—an kwanakin nan har rama sukayi na
wahala da tashin hankali. Ana haka a satin aka kori Shema'u daga aikin nata , wanda wannan
yasa Hajiya Luba har suma tayi nan take gauuuuu....a dai asibiti ta farfaÉ—o tana kukan nadama
da baƙin ciki na rasa inda zasu nufa kuma!
******
Bayan Mom Salma ta amince da komawar Zainabu ga Habab ne , kwatsam a wannan dare
akayo ƙirar su daga Lagos zuwa KD duba ga wasu miyagun da suka fara addaban mutanen
Nigeria , wannan yasa akayi masu kirar gaggawa don ɓadda wannan ɓarakan". Da subahi
bayan fitowar sa masallaci yake sanar mawa Daddy , haÉ—i da sanar masa da tafiyar tasa kamin
gari yayi haske , duk da jirgi zai bi zuwa Kaduna". Nan Daddy sosai yayi masa Addu'a Allah ya
kaishi lafiya ya cimma abun da ya tafi nema". Gari bai gama Haske ba ya nufi Gidan Mom
Salma da fitowan ta kenan falo daga bedroom ta ganshi zaune cikin shigar sa ta kaki , komai
nasa a ready yake ,alamun tafiya ". Wani sanyi taji a ƙirjin ta ganin sa cikin shigar da tafi So tun
yana yaro take da burin ganin shi a hakan ,kuma gashi yanzu Allah ya cika mata burin ta ..
ɓangare ɗaya ne na kuma zuciyar ta ke mata fargaba da tambayan ina Habab zai tafi da
wannan sanyin safiyan??". Sojana kai ne da wannan safiyar lafiya dai ko? Ko kazo É—aukar Zee
ne ,don Nasan ka da naci da axuza. Murmushi Habab yayi yana gaishe da Mom da mata bark
da safy , kana yake sanar mata da tafiyar da ta taso masa ta gaggawa". Tsammmm Momy tayi
kana tace " To Allah ya dawo dakai lafy Habab ,kaje ka duba matan naka , ina tunanin ta koma
bacci gaskiya ,amma kaje ka duba ta". Murmushi yayi mawa Momy kana ya miƙe don ganin
Zainabu n da dama hakan yake buƙata". Koda ya shiga bedroom ɗin ta can tsakiyar gadon ya
hangota ta rufa da bargo da alamun tana jin daɗin baccin a wannan lokacin. Ƙarasawa yayi
yana takawa zuwa inda take kwance yana sa gwiwowin sa ƙasa. Hannun ta ya riƙe a hankali
yana matsa mata su ,ko zata buɗe idanun ta ,amma sai ajiyar zuciya ta sauke tana ƙara sauke
numfashi a hankali , murmushi yayi don ya lura baccin yayi mata nisa sosai...wannan yasa shi
kai bakin shi yana kissing É—in saman goshin ta , yana shafa fuskar ta ....kusan minti goma yana
a haka kamin ya miƙe da ga tsaye yana gyara mata abun rufa yana fitowa falon Momy don bai

son tashin Zainabu n a yanda take jin daÉ—in baccin nata". Momy taso ya tsaya yayi breakfast
amma sai yace " Lokaci zai ƙure masa ,wannan yasa ta bin sa har wurin da yy parking tana
masa addu'oi ,kana ya fice daga gidan cike da farin cikin ganin yanda Komai na rayuwar sa ya
koma masa tamkar da baya cike da jin daÉ—i ya nufi airport. Ita ko Momy har ya fice ta kasa
komawa ,kawai sai jin ƙwallah tayi na bin kuncin ta , kewan Habab da tausayin sa suka rufe ta ,
falon ta juya tana komawa , don haÉ—a masu break fast ,tasan jiya Zainabu kwana tayi tana
zazzaɓi ,sai da ta taimaka mata da magunguna sannan taji dai dai , wannan yasata koda ta
farka da asuba tana sallah ta koma baccin ta....haka dai Momy tayi ta aikin ta ,tana murmushi
haÉ—i da cewa a zuciyar ta" Allah yasa abun da nake hasashe ya zama gaskiya".
*****
Tafiya sukeyi idon su rufe basa ko ganin gaban su...kashe mun ke zaiyi?? Ina bazai yiwu ba ,ga
tukwicin saki ga kuma shi yana shirin kashe mun ke Sobreen?? Tabbas sai na kaisa kotu ,kotun
ƙoliii kuwa, muje sobreen ,nemo mana keke mu hau yanxu zamu tafi kotun ƙoli....Ammin
Sobreen ke tafe tana sambatu na mahaukata , wanda nesa na hango Sobreen tana gudu haÉ—i
da ƙwala kirar sunan ta Ummma!! Amma ina gaba tayi tana shiga titi wannan abun hawa ya
kauce mata ,wancenn ya kauce mata". Isowan Sobreen yasata saurin jan hannun ta tana kauda
ita daga titin ,kana tace " Umma sati nawa da barin mu gidan Abba , muyi hakuri komai ya faru
damu mu muka jah mawa kanmu". Tayi maganan tana goge hawayen fuskar ta , da tayi baƙi
wannan farin fatan da ake ƙafulle dashi ya jeme ta lalace tamkar ba ita ba. Sobreen!! Taji an
kirata cike da mmki ta juya ganin su Shema'u da Hjy Luba suma a wulaƙance ". Kunya ne ya
kama Sobreen wanda yasata kasa haɗa ido da su sai sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana cigaba
da zuban hawaye". Mai ya sameta ??? Hjy Luba tayi maganan tana nufar inda Mahaifiyar
Sobreen take ta duƙa tana ta tsintar ledoji . Cike da Muryar kuka Sobreen take basu labarin
sakin da mahaifin ta yayi mawa Umman nata , da kuma dukan da yayi mata tamkar zai kashe ta
....wanda ruÉ—un rabuwar su yasata haukacewa...... Salati Hjy Luba tasa tana rushewa da kuka ,
wanda suna tsaka da hakan ne Suka ga Umman Sobreen ta razana tana jah baya da cewa " Ni
ne Alh nafi'u zai saki?? Bazai yiwu ba sai na kai sa kotun ƙoli tana maganan haɗi da fallawa da
gudu tana nufar titi , bin ta sukayi suna cewa " Taimako a kamata a riƙe , amma ina tuni ta shige
ma titin , wani babban moto ne yayo kan babban titin ,wanda jah baya su Hjy Luba sukayi suna
sakin wani gigitaccen ihu ganin moton yabi takan Umman Sobreen.... Sobreen kuwa ganin
hakan yasata zubewa wurin gwiwowin ta ƙasa tana tsaga ihu.... Mutane ne suka rufe wurin ciki
harda Alh nafi'u mahaifin ta da dama yake neman ta ta bashi Æ´ar sa . Da ita kenan masa wato
Sobreen ya ɗauki alƙawarin aura mawa koma waye koda kuturu ne".
[7/3, 16:01] Matar Doctor: *Littafin na kuÉ—i ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal
group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank
,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*

****
[7/3, 16:44] Matar Doctor: *Littafin na kuÉ—i ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal
group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank
,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*

Mutane kuwa daga masu kama kai sai masu ihu ganin irin daga dagan da Umman Sobreen tayi

ta haÉ—e da kwalta , inalillahi wa'inna ilaihir raji'un shine kaÉ—ai abun da Hjy Luba ke cewa " ruÉ—u
iya ruÉ—u tashi ga a wannan rana .. Alh Nafi'u ne ya kama hannun Sobreen da take ihu kaman
ranta zai fita ,yana jefa ta a moto yana jahh haÉ—i da barin wurin , don ko a jikin sa ganin wannan
haɗari , cewa ma yake hakkin mahaifiyar sa ne , da ta raɓasu tsawon shekaru. Don haka can
zai kai Sobreen garin Adamawa ta koya mata tarbiya kaman sauran Æ´aÆ´an da ya saba gani.
Zainabu kuwa sam bata farka ba sai wuraren 9:00am ,wanda da addu'a a bakin ta ta miƙe ,
tana kirar sunan Habab , sai da idon ta yaƙara buɗe wa ne ta tabbatar da mafarki tayi". Dafe
ƙirjin ta tayi da yake harba mata da ƙarfi tana cewa " Meke shirin faruwa da Habab ?? Allah
kasa mafarki ne ba gaskiya bane . Kasa nufar toilet tayi sai kawai nufan falon tayi don ganin
Momy a wani hali take ciki don tasan jiya a kanta ta kwana". Cike da murmushi Momy take bin
Zainabu da kallo da tayi wani dama² tayi kyau ta murje sai ƙiban ta take mai sukuni da natsuwa.
Cike da harka Zainabu ta ke yin mata an tashi lfy? Kana ta nufi kitchen don taimaka mata aiki.
A'a Zainab koma kije ki huta , na kammala komai ai , yanxu ke nake jira ki shirya kizo kiyi
breakfast sai kisha maganin ki". Nisawa Zainabu tayi tana murmushi da mata sannu da aiki
,kana ta juya don ta watsa Ruwa ta sauya kayan jikin ta daga na barcin zuwa na zaman gida".
Cike da jin ƙaunar Zainabu n Mom Salma kebin ta da kallo , tabbas abun da take hasashe
hakan yake , juna biyun jikin ta na nan bai fita ba ,Allah kenan! Allah ya raba lafiya". Mom
Salma tayi maganan tana cigaba da shirya dirnng area n. Motsin Zainabu ne yasata ce mata "
Bismillah zauna dai da lura! To Momy". Zainabu tayi maganan tana zama a hankali duk jikin ta
nauyin shi take ji a kwana biyu sai tana rinƙa jin ba daɗi a harshen ta ,kome xata ci bata jin
daÉ—in shi....nan tafara break cike da gode mawa Mom Salma don iya girki da karamci ba baya
ba". Gaskiya Mom Komai yayi daÉ—i". Zainabu tayi magana tana dariya. Dariya itama Momy tayi
tana cewa " mashaallh to tun da Zee ta yaba saura ɗan ƙaƙƙwafi Habab! Ohhh!! Ɗazu fa Habab
yazo gidan nan kina bacci tfy aiki ya kamasa a yau É—in nan yanxu ma ina tunanin jirgin su ya
ɗaga gasky". Wani irin bugawa ƙirjin Zainabu yayi , wanda sakin cup ɗin tea tayi tana cewa "
Momy meyasa kika bar sa ya tafi?? Wallh tsoro nakeji nayi mafarki Momy ki kirasa ya dawo!!!.
Ganin Zainabu ta ruÉ—e lokaci É—aya yasa Mom Salma saurin dafata tana É—an bubbaga kafaÉ—an
ta da cewa " Shiiii... Ya isa ai zai dawo yace baifi 1 mount zaiyi ba , kuma mafarki Zainab ba
gaskiya bane ba kinji ,Allah zai dawo maki da Habab lafiya inshaallh". Nisawa Zainabu tayi ji
tayi komai ya fice mata a rai. A hankali ta ce " To Momy Allah yasa". Amin abun da Mom Salma
tace kenan tana cigaba da matsar mata da irish gaban ta.
****
Kwana uku da tafiyar Habab Daddy da Kanshi yazo bikon Mom Salma ,wanda iyaye sun shiga
cikin maganan sosai da Æ´an uwa da suke ta zuruntu garuruwa kuwa ,wannan yasa don dole
Mom Salma ta kuma amincewa , a satin a ka maida auren su da Daddy ,duk da ba wani taro
akayi ba,manya ne a dangi suka taru...a kuma ranan Mom Salma da Zainabu da baki yaƙi
rufuwa saboda farin ciki suka koma gidan Daddy. Da komai na gidan sai da aka sake , niko
nace sabon gwamnati kenan shi aka kafa". A ɓangaren Zainabu ke zaune ,kula da gata iri iri
take gani a wurin Momy da Daddy kowann su na ƙoƙarin ganin sun faran ta mata ,sun kawar
mata da dukkan wani damuwa . Wanda a yanxu kusan wata É—aya kenan da tafiyar Habab . A
yau ne Zainabu ta shirya don zuwa gidan Umman ta ,wanda a yanxu idan kaga Zainabu komai
na alamun masu É—auke da juna biyu ya bayyana mata , gashi bai fara girma ba ,amma ya sata
tayi kyau matuƙa ,duk da da hutu da kula irin na Mom Salma da take bata".

Farin ciki da taje gidan ba'a magana wurin mutan gidan da su Abba ,bana har da Sama'ila anan
nan da ita ,wanda sosai taji daÉ—in hakan , Zainabu fah anyi hankali don har da tsaraba takai
mawa su Umma da sauran yaran gida. Anan take jin ashe Habab sai da yazo sukayi sallama
sannan ya wuce. Wurare n yammaci ta tattara tana komawa gidan Daddy. A falo ne take jin
kukan mutane da magiya na ban haƙuri ,wanda yasata kutsa kanta cikin sauri , idon ta ne ya
sauka akan Hjy Luba da Shema safiya dukan su a falon gaban daddyy ,gyefe guda kuma Mom
Salma ce itama fuskar ta É—auke da damuwa.........

*Littafin na kuɗi ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal group ₦300 Vip
group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,idan kuma kati ne
MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*
[7/4, 16:55] Matar Doctor: *Littafin na kuÉ—i ne Don Allah kar ki karanta indai baki biya ba, normal
group ₦300 Vip group₦500 Spc ₦1000 via 👉 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank
,idan kuma kati ne MTN zaku Turo ta wannan number 08081202932*

Jiki a sanyaye Zainabu ta isa tsakiyar falon tana zama gyefen Adda Raliya da itama ke share
ƙwallah ganin yanda Uwar tasu duk ta mozan ta ,duk da da halin ta amma kuma uwa uwace !
Zama Zainabu tayi a ƙasa a hankali tana jin yanda Safiya da Shema'u keba ma Alh Ahmadu
Haƙuri harda Hjy Luba , wanda cike da Muryar girma Alh Ahmadu ke cewa " Ya yafe masu Allah
shi yafe mana baki É—aya". Jin hakan yasa Su Hjy Luba juyowa ga Momy da Zainabu da kanta
ke a ƙasa suna bata haƙuri akan abubuwan da suka ai ƙata da yanda ta kori Momy da hannun
ta duk don kishi da masifa". Cike da nuna komai ya wuce suka ce Allah ya yafema na baki
É—aya". Wani irin Zainabu taji ganin wai Hjy Luba ce take yi masu sallama zata bar gidan ita da
su Safiya. , Wanda ganin hakan yasa Momy kallon Daddy tana cewa " Ya kuma zaka barsu su
tafi? Don Allah dai kayi haƙuri akan komai mu ɗauke shi muƙaddari dama rubuta ce ne Allah ya
tsara xaya faru. Maganganun Momy ne yayi tasiri a zuciyar Daddy , wanda sai da suka fita ne
yake ce mawa Adda Raliya ta kai su É—aya daga cikin gidajen sa na High low cost , ya bama Hjy
Luba har muddan rai , su Safiya su zauna can , har Allah ya basu bazajen aure ,idan kuma
auren nasu ya dai daita Alhmdullh". Ba Adda Raliya ce kaÉ—ai tayi godiya ba , har da Zainabu da
farin ciki yaki ɓoyiwu a fuskar ta , don ganin Hjy Luba a wannan hali ba ƙaramin ɗaga mata
hankali yayi ba". Godiya sukayi ta mawa Daddy har ya shige side É—in shi ,kana Adda Raliya ta
fice da sauri don sanar mawa su Hjy Luba da kyautar da karamcin da Daddy yayi mata... Momy
ne ta kalli Zainabu tana murmushi kana tace " Har kin dawo yasu umma?? Suna lafiya Momy
sunce a gaishe ki". Cike da jin daÉ—i Mom Salma tace " to mashaallh ina gdy. Tun daga nan shiru
ne ya biyo bayan su tsawon lokaci ,kamin Zainabu ta katse shirun da cewa " Momy wai don
Allah nayi maki wata tambaya ,Allah yasa bazai ɓata maki ba , don a kan rayuwar ki ne Momy
da na Habab!

Murmushi Mom Salma tayi kana tace " Haba É—iyata faÉ—i maganan ki mana ? . Gyara zama
Zainabu tayi tana kama hannayen ta kaman mai shirin bada labarin wani abu ,kana tace " Har
yau Habab bai san daliln barinki gidan Daddy ba , anai meki an rasa , kin rabu dashi da Daddy
,wanda ada baya akan su ki rabu da komai naki ƴan uwa ƙasar ki da kowa naki ,amma Momy

lokaci É—aya da rana tsaka aka neme ki aka rasa wai meyasa??? . Nisawa Mom Salma tayi tana
girgiza kai kurum na tana lumshe idon ta haÉ—i da buÉ—esu lokaci É—aya ta fara tuno da komai na
rayuwar ta da ya shuÉ—e". Zainab tabbas kaman yanda kikaji haka yake , Ni Asalinsa baturiya ce
ta england , wanda acan nayi rayuwata da ƴan uwa na , Alh Ahmadu yazo ƙasar akan
kasuwancin sa ne sanadin riƙon amanan sa yasa naji ya burgeni kuma har naso mu ƙulla
mu'amala da shi ,wanda da ga hakan har addinin iyayena na bari na zaɓi na zauna dashi na bar
ƙasa ta ,kuma iyayen shi basu taɓa nuna mun wani ƙiyayya ko hantara ba...sai dai ba mutaɓa
samun ƙyaƙyatawa r mu'amala da Ita ba. Kullum a cikin yada mun da maganganu da gori tana
kirana da tubabbbiya ,wanda hakan ke ɓata mun rai matuƙa , kullum ina hƙri don Ni macace
marar son hayaniya bare faɗa ,aranan dana bar gidan ban taɓa mantawa a yammacin ranan ne
Hjy Luba da ƙanwarta suka zo suka tsaya mun aka suka zageni zagin tijara da cin mutunci
wanda fushin zuciya yasani barin gidan , a daren ,wanda a washe gari na bar Nigeria na sauka
a ƙasar Japan na cigaba da rayuwata tsawon lokaci , duk da rayuwar bata mun daɗi kullum ina
cikin kewa na É—ana da halin da na bar sa ,ga kuma mijina Wanda sanadin shi na shiga addinin
Musulunci ,wanda zai kaini ga Allah da Manzon sa. A kullum ina hƙri da wannan rashin ashe
mahakurci mawadaci yau gashi na dawo ina zaune da ɗana da kuma mahaifin sa...ga ƙarin
sarika har ina gab da samun jika ta ƙare maganan tana sa dariya da gode mawa Allah. Cike da
kunya Zainabu ta rufe idon ta tana miƙewa haɗi da shiga ciki da sauri. Dariya Mom Salma keyi
sosai . Kana itama ta miƙe tana nufar ɓangaren Daddy"


Haka rayuwa yayi ta tafiya , kullum Zainabu na fama da lallaulayin ciki don sai da cikin ya fara
girma ne sannan take jin jikin ta , yanxu kusan 5 mount kenan , tun da Habab ya tafi Basu taɓa
waya ba ,kullum in ya kira wani abu zai gifta tsakanin su ,wanda shikenan Muryar natan da
baxaiji ba kenan , don bacci ne take yawon yin shi ,shi kuma duk idan yaji tana bacci sai yace
Mom ta rabu da ita basai an tashe ta ba. Tun Zainabu na nuna rashin damuwa ta , har tafara
tunani ita dai har ga Allah tsoro n aikin soja takeyi musamman irin nasu Habab É—in ... Zaune
take a falo cikin atampha brown tayi É—inkin doguwar riga ,don juna biyun jikin ta ya fito sosai duk
wani siffa ta mai cike ya bayyana mata , gaban ta dafaffan ƙwai ne a bowl da Mom Salma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login