Showing 18001 words to 21000 words out of 25545 words
Chapter 7 - WALIJAAM BOOK 3 COMPELET Hausa Novels By Maman Teddy .pdf
,taje ta Auri mutumin kirki ba irin
ka ba...ka kuma san inda xaka nufa da yar ka ,don batazo duniya bane tayi maka bauta.mugu
ka axabtar masu da yarinya ka jefa rayuwarta cikin garari ,kasa kowa na Aisha ya kita ya gujeta
duk saboda wannan diyar taka . Don haka yau sai ka rabu mun da Aisha ta auri na kirki ,kai
kuma sai ka koma ka Auri Wacce kuka haifi Zahra , da kuka saba iskancin ku akan hanya da titi
da ita ka dace ba diyar mutumci ba. Cije labban sa Anwar yayi idon shi ya kada yu jah kaman
wanda aka masa bishara da musiba. Daddy nayi laifi kayi hakuri don Allah ,bana tsammanin iya
rayuwa da wata mace da ba Aisha ba". Wacce kake magana ma Salaman ta rasu ,kayi hakuri
daddy ka gafarce ni ,Wlh Aisha dani ta dace ,bata dace da kowa ba bayanniii....wani dauke shi
da marin Alhaji Jalingo ya karayi da sai da wurin ya amsa. Hankalin Su ammie da hajiya Kaka
yayi matukar tashi ,sun san zafi irin na Mahaifin Anwar kwarai . Marin da Daddy yayi masa yasa
zubewa gaban Daddy da kokarin masa magiya . Yi mun shiru Anwar bana son jin ko wacce irin
magana daga bakin ka!!.
Abu daya nake jira takardan sakin Aisha ,na baka daga ynxu xuwa dare ,idan ba haka ba wlh
xakaga yanda xamuyi dakai. Yana fadin haka Ya juya fuuuu yana kokarin ficewa daga Falon.
Dakata!!! Suka tsinkayi muryar Hajiya Kaka daga sama tana cewa hadi da daga hannun ta .
Cak Alh.Jalingo yajah ya tsaya. Mikewa Hajiya Yalwa tayi tana matso kwallahn da dariya ya
kusa su6cemun. Haba Jalingo Kar ka zama iri na mana ,da ban baimawa mutum uzuri ,bansan
kaddara ba ,komai yazo dai dai da Raaayina shi nakeyi . Kabar yaro da yarinya suyi xaman
auren su ,laifi anwar ya riga da ya aikata sai dai muyi masa fatan shiriya. Sannan kuma ragowar
zance tsakanin sa ne da matar sa ,indai ta yafe masa shiknnn ni da kaina na roke ka don Allah
ka yafe mawa Anwaru na ..kuma ina mai baku hakuri akan abubuwan da nayi maku a lokacin
da hankali na ya gushe ,musamman ke Aisha". Ina rokonki kiyi hakuri ki zauna da jika na ,nasan
nida shi duka munyi maki laifi ,amma ko badon ni dashi ba ,ko don wannan yarinya da kika rike
ta tun tana tsumma.
Kuka sosai Shatu keyi bata ta6a tsammanin wai zataga Mahaifin Lil a rayuwa ba ,ta riga da ta
cire mawa zuciyarta zato ku tsammani . Sai kuma gashi kwatsam wai Anwar mijin da take tare
dashi shine mahaifin lil zahra. Kuka take ta rasa ne meye?? Na bakin cikin halin Anwar di ne,ko
na jin dadi kasancewan shi mahaifi wurin Lil zahran?.
Ji tayi an dafata kamin Ammie tace Aisha kiyi hakuri nima na rokeki badon d'ana ba don ni
kadai da lil zahra. Cike da sanyayyar muryar ta dake saka duk wani tsaurarrar zuciya sanyaya
tace " Ammie bakomai ni baimun komai ba ,lil ce xai nema gafarar ta...in kuma dani ciki tom na
yafe masa. Ta karake mgnn cikin kuka. Rungumeta Ammie tayi tsam a jikin ta hadi da dan
babbuga bayan ta a hankali tana mata mgn cikin muryar rarrashi . Tsagaitawa Shatu tayi da
kukan ,nan Ammie ta juyo tana kallon Hajiya kaka da ta sanya hannu tana dago anwar hadi da
mikar dashi tsaye. Humm danni Mmkin ta Ammie tayi ,don ta lura Hajiya Kaka baaka cin
galabarta sai akan na jikin ta ,akwai ta da son nata . Hajiya nima indai Aisha xata iya hakri akan
abunda Anwar yayi mai xai hana Daddyn Anwar dake kanki kuyi hakuri Dr Haula ta dawo gidan
mjjin ta.
Shiru Hajiya Kaka tayi kamin tace " mijin ta ko mijin ku. Zan yafe mawa Hjy Haulatu ,amma sai
idan an maida Auran ki dana Mahaifin Anwar. Ko a yau aka maida tom ni me sauki ne ya maido
da Hjy Haula.
Nisaawa su duka sukayi lokaci daya wani farin ciki ya lull6e duk wani mahaluki da ya kasance a
wannan wuri. A hankali Hjy kaka takai hannun ta tana riko Na ammie hadi da cewa " baxaki
koma kasar kiba ,sai da Auren ki da tsohon mijinki ,yanxu xamu tafi gidana....acan xaayi komai.
Ita kuma Hjy Haulatu ta dawo gidan ta.
Murmushi su duka suka saka ,harda shatu da diyana ,su duka suka bi bayan Hjy Kaka. Harda
mom Abbas ,mama kan tana dauke da lil suka fito. Shikan shi Alh jalungo yaji dadin wannan
magana ta Hjy da Ammie ,wanda ayau da yammaci ya dau aniyar ganin yagyara komai na
iyalun nashi da zaman lafyar su ta dore.
Mmn Abbas gidan ta ta wuce ,yyn da Abbas ya zauna da Anwar yana ta masa fada da nasiha
akan ya zauna lafiya da Shatun ,ya kuma rike masa ita da amana. Wannan maganan tasa yasa
Anwar yayi masa dariya suna hade hannun su wuri daya. Da misalin karfe biyar ne ta yamma
Dady ya umarci Anwar ya fada masa inda yakai Dr Haula ,wanda anan yake fada,masa. Da
kanshi Daddy yaje ya dawo da matar sa dakin ta ,hadi da fadi mata duk abun da ya faru a falon
bayan gushewan ta . Sosai tayi kuka ta nadama hadi da jinjina hali da karamci irin na Ammie.
Bayan sallar magriba ne da yammacinnan aka mai da Auren Ammie da Daddy. Wanda farin ciki
wurin Hajiya Yalwa baa mgna. Haka wurin shima kanshi Anwar din. A wannan dare Daddy yaso
ammie ta koma gidan shi dake cirdiya road ,amma hajiya kaka tace sai goben ranan.
Anwar kam sai rara gyefe yake yana so yace Shatu tazo su yafi gida ,amma ya kasa ,don ya
lura har a lokacin da sauran fushi da damuwa a zuciyarta... Don bata yarda su hada ido. Ko
kallon ta yake sai ta nuna bama tasan yana yi ba. Sai ta kawar masa da kai gyefe. Hajiya Kaka
ce ta lura da hakan ,wanda ita kam Ammie tuni ta lura da yanayin nasu ,amma sai ta doje don
tafison mace ta kwace hakkin ta. Hajiya kaka ni xan tafi gida ,sai da safe. Oahhh to Anwar
Aisha shirya kibi mijin ki ku tafi ko?? Badon Shatun taso ba ta mike tana daukar mayafin ta hadi
da daukar karamar handbag din ta. Cike da danne wani abu tace Hajiya Ammie mu tashi lfy. Lil
xaki zauna tare da Mom Diyana ko?? Shatu tayi mgnn tana kallon lil dake jikin diyana ,dan narai
narai tayi da ido kamin tace " Mom". Diyana ce tace " Zaki zauna dani??. Murmushi Shatu tayi
tana kara fadin zaki zauna da Mom Diyana?. Daga kai kurum Lil tayi. Kamun su duka suyi
murmushi tana bin bayan Anwar da tun da yaji Hjy kaka tace ta tashi ya bar falon don yasan
dole xata taho.
*********
Fuska babu yabo babu fallasa ta shiga moton ta taddashi zaune yana xaman jirar isowan ta .
Shiru shiru akayi babu maicewa dan uwan sa ci kanka . Kamin kusan mintuna biyu da shigowan
ta Anwar ya kalle ta yana cewa " Ina lil zahra take ?. Kaman baxata basa amsa ba don sai da ta
mulmulu ta buashi iska sannan tace " Anan zata kwana da ammie". Humm sauke ajiyar zuciya
yayi kamin yayi mata kurrr da lumsassun idon shi. Ko ba ace masa ba yasan da akwai rigima a
kasan zuciyarta. Aisha!! Ya kira sunan ta da wani irin sanyin murya da bai ta6a kirar ta dashi
ba. Wani iri taji a jinin jikin ta. Hakan yasata dago da dara daran idanun ta tana kallon nashi. Kin
chanja mun alokaci daya". Yayi mgnan yana kasheta da makirarrun idon sa. Kaman bata gane
inda xancen sa ya dosa ba tace " ban gane ba. Shin ka manta dama yanda muka taho nan
daga zaria zuwa Bauchi??.
Huuuuuu hura iskar bakin sa yayi yana dora hannun shi bisa Sitiyari ,kamin kaman wanda aka
yi masa albishir da mutuwa yace " kiyi hakuri kar ki samun damuwa don Allah ". Idan kika nuna
kina fushi dani baxan iya driving ba ,sai dai nayi komai cikin ganganci. Kiyi hakuri sorrryyyyy
plzzzzz ya karke maganan da kasa da muryar shi can kasan makoshi wanda it kanta da kyar
take iya jiyoshi . Dago idon ta tayi nan idon ta ya sauka akan nashi ya gauraya...wani irin zarrrrrr
taji nan tayi saurin kauda idon nata ,ya koma kaman ba Hamma Anwar din ta da ta sani ba
,mutum mai bakar zuciya ,idan ya tsaya a abu babu mai hanashi , amma ayau kaman bashi ne
ba ,yana kwantar mata da muryar kaman xai mata sijjada. Kwayar idon shi ta kalla kadai yasa
ta gasgata dukkan maganganun sa. Babu daya da ya tsallake. Taga damuwa sosai a kwayar
idon sa.
Kwantar da kanta tayi jikin kujerar tana magana da cewa " Hamma Bacci xanyi". Oh..ohk Sorryy
bari ynxu xamu tafi. Yy mgnan cike da rawar murya kaman wanda ta shanye shi...yana kai
hannu hadi da kwantar mata da kujerar yanda xataji dadin kwanciya. Duk idon ta na lumshe
yake mata kuma bata bude su ba ,haka fuskan ta na nan yanda yake....tana ji yafara driving
yana barin farfajiyan gidan Hajiya Kaka".
*_BUZHUWA EMPHIREí ½í°ªí ½í°ª_*
_Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa damu a cikin wannan taskar tamu ta buxuwa
Empire ,sannun mu da shigowa hallarar mu ta buzayeí ½í°ª . Ina kuke matan Aure masu fuskan
tar kalubalen gidan Auren mu ,dan gane da mazajen mu...?? Ina yammata marasa farin
jinií ½í²ƒí ½í²ƒ ,ga Buzhuawa emphire ta taho maku da sabon sirrika ,da yake abun sirrine sirrikar
mallaka dana farin jinin yammata..akan sassaukar farashi duka mallaka da farin jini munayin shi
akan 5k ne kacal. Idan na farin jini ne daya 3k,muna kuma bada sirrin mallakan akwai na 2k da
3k. Ga masu bukata xasuna iya tuntuban wannan number 08081202932 / 09062466409 ...siyan
na gariii....??? Sai kun taho taskar buzhuwa xakisha mamaki da yardan Allah da annabin
rahma._
_Mallaka ta hanyar kwai_
_Mallaka ta hanyar madara_
_Mallaka ta hanyar yan shila sauyi_
_Mallaka ta hanyar Yaseen_
_Mallaka ta hanyar kayar Aduwa_
_Mallaka ta suratul Arrahaman_
_Mallaka ta hanyar nonon shanu_
_Mallaka ta hayar fatiha umul qur'an_
_Da dai sauran su...Mata iyayen kowa sai kunzo ,BUZHUWA EMPIRE na maraba da kowa da
kowa...._
_*Wasu na zuwa ma BUZHUWA akan maganan Suna so su abasu sirrin mallaka ,wasu na farin
jini ,akan cewan su da kansu xasuyi ,a fada masu kudin su biya...Ki sani Buzhuwa xata baki
mallaka dana farin jini ,amma abun da bakisani ba shine ,indai wani yy amfani dashi ba kyeba
,to baxaiyi ba...ita abun nata sirri ne tadabam. Ita da hannun ta take baki sirri indai kk baima
wani baxaiyi ba . Kar ku manta muna da ajent a koina , ga kadan daga numbobin ajent na
buzhuwa wanda zakuna iya samun mallaka a hannun su ,da kuma sauran karin bayani
08081202932 ko 09061466409.*_
[18/02, 11:20 AM] Maman Teddyí ¾í·¸: "Har suka isa gidan babu wanda ya kuma cema d'an
uwansa wani abu. Duk da Damuwar da Anwar ya shiga a wannan lokaci n da baison ganin
6acin rai na daga gareta. Itakam Shatu lumshe idon nata kurum tayi amma bawai don tana
baccin ko jin yin baccin kaman yanda ta fad'a masa ba. Tana ji yayi Horn mai gadin gidan ya
bude masa katafaren Gate din wannan kayataccen gidan nasa ,wanda Shatun bata ta6a shigar
shi ba sai a wannan karon shine na farko. Koda ya gyara tsayuwar moton nasa a haraban inda
aka tanada domun hakan ,tsayawa yayi yana kallon kyakykyawan fuskar ta ,wanda baya jin zai
iya tada ita daga baccin da a tunanin shi ya d'auke ta. Bude murfin moton yayi yana fita hadi da
zagayowa bangaren ta yana budewa. Saurin bude idon ta tayi tana masa wani irin kallo mai
dauke da fassarori ". Kamin bata ce dashi komai ba hakan shi ma ,tasa kafarta tana fitowa
,kallon sa tayi ,wanda a sanyaye ya sakar mata da murmushi kamin taji ya riko hannun ta yana
hade taffan hannun shi da nata yana nufan cikin gidan. Duk da dare ne ,amma gidan yatsaru
matuka yayi kyau na burgewa. Bin ko ina take da kallo a sace ba tare da tabari ya lura ba. A
zuciyan ta kuwa cewa take " Wow mashaallh. Ai wannan gidan yafi na Zaria kyau ". Shine ya
barni can ,anan kuma yana shirin saka amarya zabeena take kowa ne?? Uhmm Oho masa dai!!
A falon gidan ta tsinci kanta don batasan ya akayi har suka shigo nan ba ,tana can tana tunani
da kalle² ta koma kaman wata yar kauye. Hummm sauke numfashi tayi jin wani irin sanyayyar
kamshi da ya wadata falon na musamman. Ga yanda falon kyaunshi ya rudeta. Batasan lokacin
da ta saki murmushi ba ,tana bin ko ina da kallo. Wasu kayatattun Royals cushines aka yi ma
falon ado da ya kayata tsaruwan shi. Komai na falon da akayi decorate lemongreeen ne da
darkgreen mai duhuwa. Cotton center capet royal cushine duk wannan ne colour nasu....bin
royal din take da kallo wanda asalin royal ne ba emashiated one ba. Daga can gyefe guda
kuma wani hanya ce mai coridour da akayi masa Adon Glassdour tin daga farkon shi har karshe
a rufe yake amma kana hango komai na wurin ,wanda tsaruwan wurin sai ka za6i kasancewa
anan na tsawon hours ba tare da ka gajiya ba. Domu ko adon flawer akayi irin manyan nan
bida bi guda uku , gyefen kuma daga ciki wani window ne da akayi shi babba kusan rabin
bangon ...aka saka cotton trnsfrent one ,idan kuma ka leka wajen wannan window n garden ne
ta musamman me zaman kanshi . Wanda kayatiwan wannan wuri baa magana. Tsayawa na
fayyace maku tsaruwan wannan falon a yanxu bazai karuba. Tana can tana dube dube da idon
ta kaman me neman wani abun idon ta na akan Wani silver gloves dake a tsakiyar falon yana
walwali yana kuma fitar da haske mabanbanta red ,green , yellow ,bule , white da dai sauran
su..." Falon yayi maki ko kuwa da akwai wani abun da kikeso a chanja maki na dabam. Nasan
wannan shine best colour naki shiyasa nayi amfani da hakan wajen yi miki decoratin din falon
naki haka duk don naga farin cikin ki. Hhumm'uhumm tayi mgnan a kaasan makoshin ta wanda
sautin hakan ya fito kadan daga bakin ta ,tana dan ta6e masa baki kad'an tana jin lamarin nasa
kaman yana tsarata ne , Hamma kenan my colour ko her best coloured?". Amm ban gane ba
,wake nan? Yayi maganan yana kafeta da lumsassun idon sa ,wanda a takaice tace dashi " plz
Hamma ina ne nawa Dakin ? Tunda Allah dai yakawoni ko kaso ko kaki allah ya tsara nan ne
gidana ,ba gidan Wacce kaso ka saka ba. Tayi mgnan tana hade gira sama da kasa ,kawai jira
take ya nuna mata nata falon ta kara gaba ta barshi. Don taga harda up stairs daga gyefe a
cikin falon.
"shiru yayi mata don sai a yanxu ya fahimci har a wannan lokacin kishi ne ke dawainiya da ita.
Yau Eishan Hamma Tana kishin sa kenan?...Means tana sona kenan. Yayi mgnan a zuciyar shi.
Yanda suke ba tare da ya cika mata hannun nata ba yafara tafiya tana binsa a haka taga sun
fara hayewa wannan upstairs din.
Fadin kayatuwar wannan wuri kam....humm abun dai sai wanda ya gani . Nuna mata wani kofa
yayi yana cewa " kinga nan ne bedrooom...bai gama rufe baki ba yaji ta raba hannun ta dana
shi tana shigewa hadi da fadin Gud night". Ta murda kofan tana wucewa ta barshi nan tsaye da
sakin baki yana kallon ta. Nashi bedroom din ya nufa don kimtsa kanshi. A zuciyar shi yana
tunanin lamarin Shatu ,a sarari ne ya furta anya kuwa xanbar Aisha ta cigaba da
karatu...Secondary din ma data kammala ya wadatar.
*********
Ita kuwa Shatu baayan ta gasa jikin ta da ruwan dumi ne ta shafe jikin ta da mayika masu
kamshi ,tana bin duk wani ga6a na jikin ta da turare mai sanyin kamshi. Wani lallausar sleep
drees ta dauka tana sanyawa ,wanda ya kasance gown ce iya gwiwa. Kame gashin ta tayi da
ribom. Tana nufo gadon ta don ta kwanta. Wani irin yuuu taji jiri na deban ta lokaci daya ,sai a
sannan ta tuna da yunwa don rabon ta da ta ci wani abu tun safe. Juyawa tayi tana saka
takalmin ta hadi da nufo falo. Tsayawa tayi tana tunanin me ma zatayi ,don batasan inda xata
nufa ba. Dinnig ta hanga daga can gyefe amma babu komai a saman table din. Cije lips tayi
tana dafe goshin ta ,idon ta ne ya sauka a karamin fridge din dake gyefen dinning area. Sauri
tayi tana nufa don jikin ta har rawa yake yi don yunwa. Lemu ta gani kala kala da sauran kayan
mukulashe hannun ta takai tana daukar wani lemu na strewberry tana kaiwa bakin ta don ko
tsayawa xama batayi ba ,ta hau shan lemun. Mikewa tayi tana nufan cushine din falon don tana
zama. Sam bata san lokacin da ta shanye lemun nan ba.
Jikin tane taji yana 6ari yana rawa kaman mazari ,kaman ynxu ne tama soma jin yunwan. Ga
uban zufa dake karyo mata. Idon ta sunan yana bude ne ,amma bata ganin gaban ta .
Mikewa tayi a hankali tana lalube ta nufi bedroom din ta hadi da shigewa..... Ita kawai neman
gado take ta kwanta ko taji saukin jikin ta ,don kanshi ganin dishi dishi takeyi . Fitowansa kenan
daga toilet yana tsane ruwan jikin shi yaga ta shigo masa bedroom ,kaman xai mata magana
kuma sai yayi mata shiru ,ganin yanda kaman baa hayyacin take ba. Inda yake ta tunkaro ba
tare da taji ko motsinsa ba....