Showing 24001 words to 25545 words out of 25545 words
Chapter 9 - WALIJAAM BOOK 3 COMPELET Hausa Novels By Maman Teddy .pdf
matan Aure y'ammata ku taho ga warakar ku tazo da alfarman annabin
S.A.W . Muna bada maganin mallakar aure da dai sauran su ,kuma muna da ajent namu a
kowani gari ,da yanken k'asashen dake kewaye na gida nigeriaí ½í²ƒí ½í²ƒ. Domun samun daman
karin bayani zaku iya tuntu6an wannan number 09061466409.
Alheri writers asso.í ½í³š
________________________
"Bayan tafiyar Anwar ne abun yafara dawo mawa Mahaifiyar tashi sabo , hankalin ta ya gagara
natsuwa ,wanda rasa wanda xata fada mawa halin da take ciki ne yasata sanar mawa Diyana a
ranan tarewan Ammie. Ita kanta Diya hankalin ta bakaramun tashi yayi ba ,ahaka tayi kaurewa
ba tare da ta bari Ammie ko wani ya fahimci damuwarta ba ,sai tufka take da warwara. Zaune ta
sa hannu biyu tayi ta gumi zuciyar Diyana da tunanin ta ya tafi akan yanda xatayi taga ta dawo
da Abbas k'asar sa ,ta kuma sama masa natsuwa ta hanyar kokarin mantar dashi komai . Kai
ina wannan ba shawara bace ba " baxai yiwuba wannan tace tana kauda kanta gyefe. Oh ni
Yalwa wannan wacce irin yarinyace kina zaune kina ta zuba shirmen surutai duk ke kadai??
Anya ba...Ba mene ba?? Kai hajiya kaka ,ni wannan tsohuwa da damu kike". Diyana tayi mgnan
tana mikewa daga tsaye. Eh dole innaga abun magana nayi ,ku bakwaso asan cikin ku kuyita
kunbi kunbiya ku kadai...aiko ma dai meye kike 6oyewa in yayi wari maji. Dariya Diyana tasa
hadi da kama baki tana cewa" Tofah Hajiya kaka kenan ,to ai ma bazai warin ba bare har kuji
din". Tana maganan ne hadi da nufar hanyar da xata bar falon. Ahaf kyayi ki gama komai xakuyi
a tafin hannu nake kallon ku. Hajiya kaka tayi maganan tana kai hannun ta zuwa saman plate
din kayan Marmarin dake gaban ta...tana cin Apple hankalinta sunan a kwance yake amma har
a lokacin mita take game da diyanan.
A wannan karon da kyer diyana ta cinye wata a nigeria , ta san yanda tayi ba tare da mom
Abbas ta sani ba da sauran iyayen ta ta nufi kasar malasia. Don duk hankalinta yaki kwanciya
tun da tajiyo labarin komai da ke tsakanin jaruman kuma taurarin uku. Anwar shatu Abbas
kenan.
Wanda Bayan isan ta Shatu kadai ta sanar mawa ,don itama hankalinta ya kwanta...duba ga
yanayin lafiyan ta a ynxu...
Sosai Shatu taji dadin albishir din da Diyana tayi mata na haduwa da Abbas da tayi ,kuma anan
take baima zuciyarta cewan Abbas yana dab da dawowa ,shima yafara sabon rayuwa cike da
farin ciki da walwala kaman yanda take ciki da nata mijin.
********
A hakan ne kwanaki ke shudewa zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da nuna soyayyar juna
tsakanin Anwar da Shatu abun sai dai muce mashaaallh....don wani kula yake bata na
musamman ,motsa kafan ta baison yaga tayi bare kuma ganun chanjin fuska daga gareta. Lil
zahra kuwa tuni ta cigaba da zuwa sabon school din da aka sakata tana babyclss ,wanda so da
kauna n da suke nuna mawa diyar tasu baa mgn. Hutu Anwar ya samu wanda a wannan
lokacin ne ya dauki iyalan nashi su duka suka nufi kasar egyft dangin Ammie...Kai tarba nuna
tattali soyayyar da wannan mutane suka nuna masu mai yawa ce. Don fahimtan da sukayi
shatu na dauke da juna biyu yaasa Yayar Ammie wato Bilqees hana su dawowa akan kari ,sai
da suka kwashi tsawon lokaci daganan. Suka wuce kasa mai tsarki kana suka dawo gida
nigeria. A wannan shekarar Abbas ya dawo kasar mu ta haihu ,tare ds taimakon diyana ,wanda
tayi nasarar afkawa soyayyar abbas alokacin da batayi tsammani ba ,abun da xata iya sani
shune tana matukar jin tausayin sa sanadin cutar Son da ya kamu dashi marar magani ,anan ne
tafara alkawarin ganin ta zame masa wannan maganin da xata bashi kulawa ta har abada.
A bangaren Abbas din ma hakan ya faru ,duk da dama akwai shakuwa tsakanin shi da Diyana
,amma a wannan lokaci sakonni ne yakeji na dabam a tare da ita. Wanda basu baimawa kansu
wahala wajen bayyana sirikan zukatan su ba. Koda iyaye suka fahimta bakaramun farin ciki
sukayi ba. Wanda aka sanya lokacin auren su a lokaci kalilan.
Rugar surbajo kuwa idan Shatu taje yanda kasan su maida ta ciki don murna ,komai yafaru ya
wuce kaman baayi ba ,an ma manta dashi. Hardo ya auri yar uwar sa a wannan ruga itama
bafullatana ce yariga da ya hakura da shatun don yasan sama tayi ma yaro nesa. Anwar da
Shatu sun samu Dr salma kawar mahaifiyar lil zahra, sunje har gidan marayu don suji ko sun
san wani asali na mahaifiyar zahran amma basu samu komai na daga labarin taba. Hakan
yasa su hakura ,shatu takara kama Lil ta rungume tamkar yanda ta dauketa a da baya. Su teeema kam anga ala wadai ,don tun wannan tsahon shekarun babu mijin aure ,tuni ta fidda
ran ta ga Anwar ,tafara neman miji amma babu. Nikam mmn teddy nayi zaraf nace ta nufi wurin
jaruma BUZHUWA ,wanda da taimakin buzhuwa empire mijin aure ya tsaya anan fa duk wani
hali nata mara kyau ta gyara shi ta rungumi kaddarar ta.
Bangaren mahaifiyar zabeena kam da ita ma zabeenan ,wani yaron commissioner ne ya tsaya
mata ,anata iyayi da karya....Sai a ranan biki yace ya fasa ,wannan yasa Zabeena kamuwa da
heart attack...tun da aka kwantar da ita a asibiti tsawon lokaci tana nan rai ga hannun allah. A
wannn ciwon nata ne komai na mahaifiyar nata ya karka6e...ta dawo babu dukiyan da ake ka
fahari da shi . Suka dawo babu cin yau dana gobe sai anyi maula.
Daga karshe dai har gidan Dr haula taje ta roki yafiyarta ,tare da taimakon ta akan ciwon
zabeenan. Bataji komai ba sai tausaya mata da tayi ,anan ta bata makudan kudi akan lafiyan
Zabeena.
Bayan shekera shida ,komai na farin ciki ya wanzu a wannan ahali ,abubuwa da dama sun
shude farin ciki da walwala ya yawaita ,arxiki ya ninka na da baya. A wannan lokacinne Shatu ta
nada yaran ta uku...duk da Lil zahra.bayan lil ta haifi yara biyu mace dana miji yan tagwayen
ta.an sanya mawa macen sunan Hafsa Wato Hasile don sun yaba da Gwagwarmayan da
wahalan data sha a GIDAN KWARATA ,namijin kuma aka sanya masa sunan jarumin gidan
kwarata wato ALIYOU HAIDAR. Sai Diyana da Abbas da suke ta jero yaran su don a shekara
shida yaran su uku ,maxa biyu mace daya macen sun sanya mata sunan likitan su da ta amsa
haihuwar wannan tauraruwar wato DR MARYAM nasan baku manta da mairon ku ba ta
BAFULLATANAN RUGA.... Sadeeq kuwa Ya auri Yar kanwar mahaifin sa ce a kano shi kuma
yar sa daya ne yasaka mata sunan jaruman da tayi gwagwarmaya wato AHYAAN ,don yasan
rawar ganin da ta taka a SIYASATA.
TO ANAN NAKE CEWA ALHAMDULILLAH . Anan na kawo karshen wannan littafi nawa....
'kurakuren dake ciki allah ya yafe mun,abun da na rubuta dai dai allah kabamu ladan dakuma
damar aiki dashi . Inda kukaga kuskure don allah kuyi mun afuwa kunsan dan Adam ajixi ne
,nasan da yawan ku bazaku so na yanke labarin a nan ba ,amma hakan xaifi mana ne yanda
muka fara cikin nishadi mu gama a haka ,ina godiya kwarai da yanda kuka nuna mun soyayyar
ku a wannan littafi na WALJM ,ina fatan na gaba xan samu linkin linkin soyayyar ku ngd...taku
har kullum mai maku fatan alheri maman teddy
sai mun hadu a littafina na gaba mai suna......
*í ½íµŠï¸KWARTON MANYAí ½íµŠï¸*
_(Mr Perfectí ½íµŠï¸)_
FROM THE EXPIRIENCE WRITER OFí ½í±‡
BAFULLATANAN RUGA
ZUMA DA MADACI
SIYASATAH
GIDAN KWARATA
YAR WAYE
YAR MAULA
DIJAMA YAR FULANI
WALIJAAM
YAR AIKI
HABIBY DAIMAN
KAWALIYA TAH
BINTOTO da sauran su...
_Na kira sunan labarin da KWARTON MANYA ne badon komai don so nake na nunar da
makaranta wasu abubuwa dake kulull6e da jaama'a baki d'aya kuma yake kalubakantan mu ,da
bamu san dashi ba ,kuma duk yanda kuka ga labarin dama salon da yazo dashi kenan.
Hummm idan na zauna ina tunanin labarin kwarton manya wato MR PERFECT sai inji kaman
na dakata da yin ko wani littafi na kawo maku shi ,don lbrn ya dauko maku salo na dabam
,wanda ya kunshi abubuwa Na dabam , zamba! yaudara ,gadara izza ,butulci tare da tsantsan
madarar tare da zuman kanannadaddiyar soyayya ,wanda yake bansan me xan fassara shi
bama , ni kaina nakan kosa don naga na kawo maku wannan labari ,but any where ku kasan ce
dani uwar teddy a new book dina mai taken MR PERFECT wanda nayi masa lakani da
KWARTON MANYA!!
Inshaallh inda rai da lafiya xai fara zuwan maku ne a bayan sallah after ramadan da yardan
Allah. Zaku iya tmbyan wannan littafi wato mr perfect KWARTON MANYA da zarar yau ance
maki anfice sallah ,a kowani website youtube whatsaap facebook da dai sauran su...
Taku mai maku fatan alheri tare da nuna maku son so lillahi.....
Ayusha mohammed
Maman teddyí ¾í·¸
08081202932