Showing 15001 words to 18000 words out of 31939 words

Chapter 6 - BAKAR TAFIYA BY MEENAT A YANDOMA.pdf

rayukanmu."
Tk ya ƙarashe maganar yana ƙara riƙe hannun Jafar kamar za'a kwace mashi shi

( Niko nace Tk ina ɗagin kan? Ko ka sauko tun yanzu.)

"Amma abinda nike gani naga mun fara hango alamu kamar a kwai kogi nan gabanmu in muka
buɗe saimu faɗa ruwan, abinda nasani dodanni basu san ruwa mu bari sai muna gaf da ida isa
wurin sai muhaɗa ƙarfi mu buɗe ƙofar nan."

Sun yi na'am da wannan shawarar ta Jafar, suna gani sun doshi gefen ruwan suka fara koƙarin
tserewa.

Da ƙyar da ji6in goshi suka samu ƙofar ta ɗan buɗe yadda mutum zai iya fitowa daga cikin kejin.

Da ɗai ɗaya suka riƙa dirowa suna ficewa a guje, Mandiyace ƙarshen fitowa tana dirowa Dodan
daya ɗauko kejin yaji kamar kejin ya rage nauyi.

Kejin daya gani a buɗe duk sun fice ya sanyashi wata irin kuwwa da sai da dajin yayi amsa
Amo!.

Jin wannan ƙarar ya sanya sauran Dodannin rugowa domin sun fahimci naman da suka kamo
ya sun tsere,agujsuka bi bayansu Jafar suna gudu suna daka wani irin tsalle tamkar ƙwaɗanni.

Gani irin azababben gudun da Dodannin keyi suna ƙoƙarin iskosu yasa su Jafar ƙara ƙaimi
suna ƙoƙarin isa ga wannan kogi.

Sunyi nasarar isowa
Tk ya fara isowa wani irin birki ya ja ya tsaya ganin irin zurfin da ke akwai kafin ka isa zuwa
ciikin kogin, Jamcy na isowa batare da ta luraba ta banka Tk sukayi ƙasa, suma sauran baya
suka mara masu.

Dodannin na isowa basu iske kowa ba, ganin haka ya sanya suka fasheda wani irin kuka daya
sanya wurin amsa kuwwa.

Abinda ya basu mamaki kuma ya tsorata su shine ganin ƙasan ruwan haske fayau tamkar ba
dareba.

Iyakar ƙarfinsu suke iyo amma abinda suka lura shine duk ƙokarin da suke suna nan tsaye a
wurin da suka faɗo, wannan al'amari ya matuƙar ɗaga masu hankali.

Ga iskar da suka shaƙo ta kusa karewa.

Lokaci ɗaya ruwan ya fara wani irin motsi tamkar wani abu ya fao cikinshi.

Duk ƙoƙarin da suke amma a banza, sai da Jafar ya fara karanto addu'a cikin zuciyarshi sannan
suka ga kamar an saki jijiyoyin jikinsu sun fara wuce wurin.

Tamkar an wulloshi haka suka tsinci Nura gabarsu kamanninshi su sauya yakoma Horror
idanunshi babu ƙwayar baƙi sunyi fari tas!.

Kafin suyi wsni yunƙuri ya warci Mandiya yayi ƙasan ruwan da ita.........

__________________________
"Allahumma ajirnifiy musibati wa'aklifini khairan minha."
Biba ta ƙarashe Addu'ar yayin da taga ƙofar na rufewa.

Tsaye suke ido ya raina fata, kowa ka kalla zaka hango tsananin firgici atattare dashi.

Ko ƙwaƙwƙwaran motsi bakaji kogon yayi tsit!

Jin motsi bayansu yadawo dasu daga duniyar tunanin da suka lula.

Kulu da Nas su suka farayin gaba sai Biba Rabson da Salma suka take masu baya.

Tunda suka fara tafiya basu haɗu da komi ba sai yana da ta dabaibaye ilahirin kogon sai sun
sanya hannu sun ɗebeta sannan suke samu su wuce.

Abinda suka lura kogon wata irin doguwar hanya gareshi tunda suka fara bi har yanzu basu zo
ƙarshenta ba.

Wani irin daddaɗan ƙamshin abinci hanci nansu suka fara shaƙo masu.

"Wow! Nas kaji abinda hancina ya jiyo mani?."

"Nima shinike jiyowa masoyiya."

Sauri suka riƙayi tamkar zasu tashi sama, turus! Suka ja wani birki yawunsu na tsinkewa.

Abinci ne aƙasa cikin filattai jere reras!, shinkafa damiya hada naman kaji zuƙu_zuƙu.

Rabson wani yawu ya haɗiye ƙut! Tare da lasar la66anshi.

"Kada kuci abincin nan, wani tarko ne aka haɗa mana, kuyi tunani."
Biba ta ƙarashe maganar tana riƙo hannun Kulu dake ƙoƙarin bin Nas daya kusa isa ga abincin.

"Malama sakar mani hannu, ke in bakici muki ƙyalemu muje muci iya cin mu."
Ta fizge hannuta tayi gaba.

Salma gallama Rabson harara tayi.
"To jikan ƴan lasau, kaje kaci naga tun ɗazu sai lasar baki kake kamar sabon kamu."

"Hhh! Haba my Salmaty na hanaki yawan magana fa, kinga yadda kike komawa bakinki har
hawa yake kamar tsohuwa zata kira tukur."
Ya ƙarashe maganar yana cigaba da dariyarshi.

"Bani da lokacinka marar aikinyi kawai mtsw!."

"Niko nike da aikinyi, in zauna inta kallon bakinki yadda yayi suntum ɗin nan in kina magana
tamkar yadda kikasan bakin aku haka kike komawa."

Iya ƙuluwa Salma ta gama ƙulewa da rainin wayon Rabson, a fusace tayo kanshi tamkar zata
kai mashi bugu.

Ihu Kulu ta fasa wanda ya jawo hankalinsu Biba.

Abincin da suka fara ɗiba ne ya koma tsutsotsi Nas da ya kai abincin cikinshi tuni ya baje ƙasa
ko motsi bai yi.

Ihu take tana girgiza Nas Amma babu alamar zai tashi.

Biba ta matso tahau tofa mashi addu'o'i a hankali ya fara buɗe idanunshi, wata mahaukaciyar
ƙasa da sukaji tasanya shi ida miƙewa tsaye.


Tsutsotsin ne suke haɗewa wuri ɗaya suna zama ƙatuwar tsutsa mai hannuwa bila adadin.

Salma da Rabson wuri ɗaya suka haɗe tana ihun kiran sunan dadyn ta shikuma yana kiran
Wayyo Kaka wayyo bunsurunleee....




Kuyi haƙuri da wannan, banijin dadi alƙawarin danayi makune yasa naƙoƙarta nayi
wannan.






*COMMENT*✅
*SHARE*✅












*MEEN@RT...✍*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: *BAƘAR TAFIYA*

( *HORROR STORY* )

*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*️


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*SALONSHI NA DABAN NE *

*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI
RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA
ABBANA*


*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN,
ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*

‍♀️‍♀️‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI
NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*


*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON
BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH
YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA
MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA
BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.*


_______________________
*PAGE 20_21*

............ganin anjanye Mandiya yasan ya su Jafar tsananin ruɗuwa suka ƙara himma wurin yin
iyo.


Da ƙyar suka samu suka ƙaraso ga6ar ruwan.

Kowa ka kalla fuskarshi cikin firgice take da tsananin tashin hankali.

Basma tunda suka fito take zazzaga uban aman ruwa, saboda ruwan da ta shaƙa.

Aman da takeyi kamar zata amayo ƴan hanjinta.

Jamcy kuka kawai take tana tashiga ukku lokacin mutuwarta yayi, da ta sani da bata fito ganin
kwaf ba.
Tk bai hanata yin kukan ba dominshima a halinda suke ciki inda zaiyi kukan zai fijin sauƙin
abinda Yakeji cikin zuciyarshi.

Sun ɗan jima awurin suna jimamin abinda ya faru da Mandiya.

Ɗunguma sukayi sukabar wurin suna tafiya da ƙyar jikinsu babu kuzari.

Jamcy faɗuwa tayi ta tare da fashewa da kuka.
"Wayyo masoyi, Mutuwa zaniyi bani iya tafiya, ga yunwa nikeji, dan Allah koɗan naman kifi kayo
iyo cikin ruwan nan ka gasa mani inci , ni bazan iya cigaba da tafiyaba."
Taci gaba da kukanta.

Galala suka yi suna kallonta.

Basma kallon bakida hankali tayi mata cikin 6acin rai ta fara zazzaga bala'i.
"Ke yanzu in baccin kin maidamu marasa hankali da tunani irinki, gidan ubanwa zamu samu
maki irin waɗan nan kayan?, ko kitashi mutafi ko muyi gaba mubarki nan wurin."

Zagita aikoma Basma dashi cikin masifa dake cinta ta miƙe tayo kan Basma.
"Ke harkin gaya mani wannan maganar?, kinsan ko wacece Jamcy bala'i, nayayimi
kankazar_kazarki kaga tunkiya uwar tan6ele ke in banda gantali miya fiddoki kika baro mijinki
kika fito yawon gantali."

Tatss! Kakeji Basma ta ɗauke Jamcy da kyakykyawan mari, chakumar juna sukayi sukai faɗi
kowa tana naushin ƴar uwarta, an rasa mai raba faɗan sunyi tsaitsaye sunkasa koda furta
kalmar kudaina faɗan.

Ƙyalesu sukayi suka samu wuri suka zauna suka zuba masu ido.

Sun bugu sunjigata.
Jamcy da taji bugu fuskarta ta chanza kamanni samu tayi ta kubce daga hannun Basma takoma
gefe tana maida numfashi ta fara magana da ƙyar.
"Muguwa azzaluma, wannan ai zaluncine ace ana faɗa bazaki bari a huta ba sannan muci
gaba dan zalunci ,muguwa mai suffar agwagwa Allah ya isana ban yafe maki ba."

"Nikike kira mai suffar agwagwa?, kiƙara maimaita abinda kika faɗa yanzu in take maki kai in
maimaita maki bugun da yafi wannan 6allagaza mai zubin muciya."
Basma ta ƙarashe maganar tana huttai.

"Idan kun gama faɗan kutashi mucigaba da tafiya, nikam kunkusa daina ganina dan tsaf zani
rabu daku in raba tafiya daku."
Jafar ya ƙarashe maganar ranshi a 6ace.

Harararshi Jamcy tayi tana gunguni.

"Kai kuma maloho kayi sakaka kana kallo wannan matar tayi mani wannan bugun, wallahi zaka

gane in muka koma gida."


Tk banza yayi ya kyaleta kamar baijita ba, domin shi yanzu abinda ke damunshi taya zai
tseratar da rayuwar da daga wannan Baƙar tafiyar.

Sunyi tafiya mai ɗan nisa suka samu bishiyar ruman suka tsiga suka sha suka zauna suna
hutawa.

Motsin da sukaji alamun takun sawun mutum ya nufo inda suke yasanya su ɗago kawunansu.

A firgice suka miƙe tsaye suna kallo cikin matuƙar mamaki atare suka furta Rabson!.

Tsaye yake yana kallonsu yana murmushi.
"Nine zuwa nayi domin intafi daku wurin sauran abokan tafiyarmu, tunda kuka bace mana muke
yawon naimanku sai yanzu Allah yasa na ganku."

Cikin zaƙuwa Basma tayo wurinshi, "yauwa Mutumina Rabson ina su Salma da su Biba."

Jin an ambaci sunan Biba yasa Jafar matsowa domin yaji inda aka baro mashi abar ƙaunarshi.

"Suna chan suna jiranku, kuyi sauri mu ƙarasa wurinsu."

Ɗunguma sukayi suka mara mashi baya.

Sunyi tafiya maitsananin nisa har suka fara gajiya da sunce Rabson har yanzu bamu iso ba sai
yace masu ku ƙara haƙuri munkusa ƙarsawa.

Wani wuri suka iso mai matuƙar duhuwa ga yawan bishiyoyi ganyayen jikinsu duk sun zubo
ƙasa, ta cikin duhuwar suk riƙa ratsawa har suka iso wani bangare daya matuƙar basu mamaki.
Gani sukayi Rabson ya tsaya yaƙi gaba yaƙi baya.
"Rabson mun iso ko?." Basma ta faɗa tana ƙoƙarin shan gabanshi, dariyar daya tuntsire da i ta
ce tasanyasu ja da baya bashiri.
Suffarshi tariƙa rikiɗewa tana kasuwa kashi_kashi yana komawa wasu irin maridan Aljanu
hannuwansu ɗauke da muggan makamai tamkar waɗanda zasuje yaƙi.
Ga wata iriyar guguwa da ta turniƙe wurin........

__________________________
.......Ida haɗewa tsutsar tayi wuri ɗaya tana wata irin dariya mai haddasama kunnuwan bil adam
ɗaukewar jin su na wucin gadi.

Rabson da Salma haɗe suke suna kuka suna sambatu domin yau sun fidda rai da rayuwarsu,
Salma wani zazzafan fitsarine ya wanke mata ƙafafu batareda tasani ba.

Tsutsar dariyar datake ta tsagaita tafara magana cikin amon sauti tafara magana.
"Yaku waɗannan halittu masu tsananin taurin kai yau kwananku yazo ƙarshe kushirya baƙuntar
lahira."

Jin wannan jawabi ba ƙaramin tada hankalinsu Kulu da Nas tuni jikin Nas ya fara rawa tsabar
tashin hankali.

Tamkar maciji haka tsutsar tasulalo tayo kan Kulu da Nas.

Ihu suke suna naiman agajin abokan tafiyar su, amma ina suma ta kansu suke.

Tsalle tayi tadira jikin Kulu, ƙara Kulu ta fasa tana"Nawan kataimaka mani kacire mani ita, kayi
sauri wayyo nashiga ukku Nas kodai bakajin minike faɗa ne?."

Nas cikin muryar da ta gama karaya yafara magana tsoro ya gama baibayeshi.
"Aa Kulu na barki har abada kiyafe mani Allah yatsayar da mutuwarki ke kaɗai kinga tafiyata
kiyafe mani, in ana doyayyah alahira muyi a chan."
Ya ruga aguje yayi bayansu Rabson da suke ƙoƙarin guduwa bankesu yayi ya ƙwara kan Salma
dana Rabson yayi gaba.

Basuji zafin abinda Nas yayi masuba suka bi bayanshi.

Biba kowace addu'a tazo bakinta furta ta take tana naiman kariyar ubangijinta.

Kulu tariga ta yanke rai da tsira ta sadaƙar yau mutuwa zatayi.

Ganin halinda Kulu take cikigasu Nas sun gudu, wani ƙarfin hali taji yazo mata lokaci ɗaya ta
furta, "LA'ILAHA ILLAH ANTASUBUHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIM, ya Allah ka kawo
mana ɗauki, kafitar damu daga wannan bala'in ya Allah mundogara gareka ya Allah kakawo
mana mafita." Tashi tayi tanufi inda Kulu take ga wannan tsutsa ta kanannaɗe ilahirin jikinta, wani ƙarfe tagani
mai suffar wuƙa, ɗaukarshi tayi ta nufi inda Kulu take, shammatar tsutsar tayi ta luma mata
wannan ƙarfen ajiki bakinta ɗauke da addu'a take ta saki Kulu ta ƙwala wata irin ƙara, take
wurin ya6ule wani ruwa green mai kauri ya riƙa fita tamkar anbuɗe famfo, nan tagama bullayi ta
mutu.

Kamo hannun Kulu Biba tayi tana mata sannu, tashi tayi jikinta duk ya baci saboda faɗuwar da
tayi, lura Kulu tayi daga ita sai Biba da ƙyar tabuɗe baki tana tambayar ina sauran abokan
tafiyarsu.

"Yanzu dai ki miƙe musamu mafita daga nan."
Biba ta kamo hannunta.

Wata kunya ce takama Kulu da ta tuna da rashin kunyar da ta yima Biba ɗazu amma yanzu
gata itake taimakonta.

Lallai duniya kakiyayi wulaƙanta mutum bakasan ranar da zai maka wata rana ba, ɗan adam ba
abin wulaƙantawa bane duk yadda ka ganshi.

Abinda idanuwanta suka hasko mata ya kusa datse numfashinta na wucin gaɗi, jikinta kyarma
ya ɗauka tamkar mazari, hannunta yana kyarma ta ɗagoshi tana nunama Biba abinda
idanuwanta suka hasko mata.

Ruwan jikin wannan tsotsane ya dunƙule ya rarraba kashi_kashi yana wata irin kumbura tamkar
zai tashi sama, a hankali yake miƙewa tamkar yadda hayaƙi keyin sama yana miƙewa,wasu irin
halittu masu suffar ƙwarangwal saidai su basukai tsayin ƙwarangwalba gasu da ƙaton kai yatsun
hannuwansu kwara ukku rak!,idanuwansu jajur tamkar garwashin wuta jikinsu irin na
ƙwarangwal sak.

Misalta halindasu Biba suka shiga bai misaltuwa, ga halittun sun fara miƙewa,Biba hannun Kulu
ta kamo suka bi bayansu Rabson aguje.

Sunyi rasarar riskarsu Rabson, "ya kunkashe tsutsar?."
Salma ta tambaya tana maida kallonta ga Biba.
"Ta mutu amma kuduba bayanmu wani sabon bala'in ke tunkaro mu."ta ƙarashe maganar tana
maida numfashi da ƙyar.

Hayaniyar da sukajiyo tasasu juyawa ganin abinda ke faruwa, halittun ne sun nufo inda suke
bakunansu buɗe.

Ganin haka yasasu bin wata wangamemiyar ƙofa dasuka gani tabi tacikin kogon.

Bawan Allah Rabson yana gudu wani dutse ya taɗe shi ya faɗi kasa warwas, da rarrafe yasamu
yana bin bayansu Alkah yabashi sa'a yayun ƙura yamiƙe tare dayi bayansu, ga waɗannan
halittu biye dasu bakunansu buɗe.







*COMMENT*✅
*SHARE*✅

*MEEN@RT...✍*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: *BAƘAR TAFIYA*

( *HORROR STORY* )

*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*️


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*SALONSHI NA DABAN NE *


*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI
RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA
ABBANA*


*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN,
ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*

‍♀️‍♀️‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI
NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*


*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON
BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH
YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA
MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA
BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.*


_kwana biyu kunjini shiru, hakan ya farune sanadiyyar rashin lafiya danayi, masoya na haƙiƙa
naga saƙonninku ina matuƙar godiya,Allah yabar zuminci_

___________________________
_dan Allah ku sanya auntynah cikin addu'a, yau kwana Ukku tana labour Allah ya sauketa
lafiya_


*PAGE 24_25*

..........A guje sukayo wurin Basma domin ceton rayuwarta.

Sunyi iya ƙoƙarinsu wurin fiddo Basma a cikin ruwan amma abun yaci tura, saboda ruƙon da
Mandiya tayi mata bana wasa ne.


Ƙarfi suka haɗa suka fizgota daga cikin ruwan.

Tare da Mandiya da ta yi mata mugun ruƙo suka fiddota.

Ganin yadda Mandiya ta koma yasa sauran abokan tafiyar ja da baya in banda Jafar da yake
naiman hanyar da zai taimaki Basma.


Tamkar yunwataccen zaki haka Mandiya tayi wurgi da Basma tayo kan Jafar gadan_gadan.

Da nufin cizonshi ta iso takamashi da kokawa sukayi ƙasa.

"A'uzubillah! Subhanallah!!."
Jafar ya furta ganin mace wadda ba muharramarshi ba ta ta6i jikinshi suna kokawa a ƙasa.

Tunyana kare kanshi daga muggan hare_hare da take kawo mashi harya fara mai da mata
martani.

Su Jamcy ba kata6us tsaye suke sun haɗe wuri ɗaya ita da Tk suna surutan da ko su basu san
mi suke faɗaba.

Ƙoƙarin yakiceta Jafar yayi ya wurgar da ita can gefe.

Abinda ya lura da waɗannan Horror ɗin basu taba mutuwa sai dai suyi doguwar suma inkayi
nasarar luma masu wani makami ta bayansu.

Dube_dube ya fara naiman inda suka yada itatuwanda suke kamun kifi da su.


Can nesa da inda suke ya hango su.

Da gudu ya nufi inda suke, yana gaf da ida isa yaji an warto ƙafarshi ba shiri yayi ƙasa.


Ganin Mandiya na ƙoƙarin kawo mashi hari ta kowace hanya ya sanyashi kai mata harbi da
ƙafafunshi cikin zuciyarshi yana karanto duk wata addu'a data zo mashi, yana ƙara ƙaimi wurin
isa ga iccen da yake ƙoƙarin kaiwa.

Yayi nasarar ɗauko icce inda yayi nasarar luma matashi a tsakiyar baya, wata firgitacciyar ƙara
ta kwala ta faɗa cikin ruwan ta 6ace 6at.

Wurin Basma dake kwance magashiyan dafe da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login