Showing 30001 words to 31939 words out of 31939 words
Chapter 11 - BAKAR TAFIYA BY MEENAT A YANDOMA.pdf
Maman Jafar itama kallonshi take da mamaki ta furta Abdallah.........
Juwar dayaji tana ɗibarshi ce tasashi yayi saurin zamewa ƙasa tare dayin zaman ƴan bori.
Hindu kuwa wasu hawaye ne taji sun wanke mata fuska, wai yau i ta ce take ganin Abdallah,
anya kuwa ba mafarki takeba.
Jafar ganin mahaifiyarshi yasa yayi yunƙurin tashi.
Ganin haka ummansu tayi saurin ƙarasowa wurinshi cike da farin ciki marar misaltuwa.
Alhaji Abdallah hawaayen fuskarshi ya sharce, ga wani gumi daya tsatstsafo mashi ta ko ina
ajikinshi.
Kallon Jafar yayi yaƙara tabbatarwa tabbas yanzu yaƙara ganin kamarsu da husaininshi.
Abdallah tashi yayi ya isa gabansu Hindatu tare da zaunawa amma bakinshi ya kasa furta koda
kalma ɗayace.
"Umma! Dama kinsan Mahaifin Salma?, koɗan uwankune."?
Ya ƙarashe maganar ya mai ƙara fuskantar Mahaifiyarshi.
"Ɗana ne kai, Jafar tunda na haɗa ido dakai jikina yabani kai ɗin jinina ne, Jafar Ashe kaine
ɗan, ɗan uwana Husaini daya bata, babu inda ban bancika ba domin ganin nasamuko amma
abin yaci tura ban gankuba."
Alhaji Abdallah ya ƙarasa magana muryarshi a matuƙar karye.
Hawayen dake fuskarta ta share ta ɗora da faɗar.
"Tun bayan rasuwar iyayenku, Husaini yashiga wani mawuyacin hali, saiya zaunar dani yayita
yimani wasu maganganu masu kama da wasiyya, ana cikin haka Allah ya nufeshi da 6acewa
inda haryau bamu ganshiba."
Kukan da taji yana naiman ƙwace matane yasata yin shiru.
"Mahaifanmu mu biyu suka haifa taƙwaye, muntashi muna matuƙar ƙaunar junanmu, har
mahaifanmu suka rasu lokacinne kuma Husaini ya bata, na nemeku lungu da saƙo amma ko
labarinku bansamuba, kullum cikin yima iyayenmu addu'a nike da Husaini har izuwa yau da
Allah Ya bayyana mani ku."
Jafar ji yayi anya ba mafarki yake ba, ace wai yau shine gashi ga yayan mahaifinshi, Allah mai
yadda yaso, yana ƙara roƙon Allah ya bayyana mahaifinshi aduk halinda yake ciki.
Salma wata gagarumar kunyace ta ƙara rufeta, wai yau ace wanda ta gama wulaƙantawa ashe
yayantane, yanzu ta ƙara tabbatarwa ɗan adam ba abin wulaƙantawa bane, wata sabuwar
nadama taji tana ƙara shigarta.
Mahaifiyar Habib da Alhaji Abdallah gaisuwar yaushe gamo suka hauyi ciki da farin ciki da
ƙaunar juna.
Sallamar Habib dasukaji ta maido hankalinsu ga ƙofar.
Basma tunda taga Habib wani farin cikin marar misaltuwa ya ziyarci zuciyarta, ashe tanada
rabon ganin mijinta farincikinta, tana ƙara miƙa godiyarta ga Allah.
Bayabo ba fallasa bayan gaisawarsu da ƴan ɗakin ya dubi Basma yana mata ya jiki.
Ba ƙaramin mamakin Habib Basma tayiba, ya matuƙar chanza mata sai wani shareta yake ga
wani haske da yayi da wata ƙiba da yayi abinshi.
Haƙuri ta hau bashi tana kuka ya yafe mata tayi nadama, ko kallonta baiyi ba ya furta naji
kanshi na sunkiye yana kallon screen ɗin wayarshi.
Tamkar Alhaji Abdallah zai maida su Hindu da Habib ciki haka ya riƙa nuna masu soyayyah.
Batare da sanin su Hindu ba Alhaji Habib yaje yasamu wasu malamai yayi masu fatawar ɗan
uwanshi da yayi shekara ishirin da bacewa yabar mata shin zai iya auren matar da ya bari.?
Bayan gama tattaunawarsu sun yimashi fatawa iya iliminda Allah ya hore mashin cewar zai iya
aurenta.
Farin ciki marar misaltuwa yaji acikin zuciyarshi, domin shidai harga Allah yanada gurin auren
Hindatu kodan ya taimaka mata, bai da gurin ganinta cikin wahalar rayuwa.
Ba ƙaramin artabu yayi da Hindatu ba kafinta amince da auren.
Sai da suka shafe wata huɗu a asibiti lokacin kowanensu ya samu lafiya yayi ƙiba abinshi.
Soyayya mai ƙarfi ce ta ƙara shiga tsakanin Jafar da Biba har iyayensu suka fahimci abindake
faruwa, sunyi murna sosai domin ba wanda zai guji haɗa zuri'a da Jafar.
Oga Rabson ma yanzu Salma ta bada haɗin kai, soyayya suke sha ba kama hannun yaro.
A yau ne likita yayi alƙawari sallamar su saboda yaga sun warke yadda yake buƙata.
Sabo shi akema kuka ba mutuwaba.
Fuskokinsu yau suna cikin damuwa da kuma jimamin rabuwar da zasuyi.
Rabson hada hawaye na rabuwarsu da abokan tafiya.
Su Kuluma hada hawaye sukayi, ana kuka suka rabu da juna tare da yima juna fatan alkhairi.
Alhaji Abdallah bai yarda Hindu tashiga gidanshiba saida igiyoyin aurenshi akanta.
Bayan su huta Salma ke tambayar mahaifinta ina mahaifiyarta?, tunda aka kai su asibiti baga
tajeba.
Nan ya sanar da ita abinda ya faru.
Allah sarki ɗa da uwa sai Allah, kuka Salma ta riƙayi tana roƙon mahaifinta akan ya dawo da
mahaifiyarta.
Dakatar da ita yayi, ya sanar da ita shifa yanzu yayi aure ya auri Hindu.
Jafar da Salma sunji daɗin wannan al'amari, amma Salma tana addu'ar Allah ya huci zuciyar
mahaifinta ya maido mahaifiyarta.
Alhaji Abdallah da Hindu soyayyarsu sukeyi hankali kwace.
Su Hajiya Zaliha ana gida ana zawarci, Alhaji nan ya angwance.
Rabson tsabar murna da farin ciki yana Shiga gidan yayi wuf ya kwance bunsurulle ya ɗagashi
rama yana hajijiya dashi yana dariya yana murna.
Bunsurulle jin wannan jijjigashi da ake ya tabbatar mashi lallai Rabson yadawo, shima kuka ya
riƙayi.
"Yau ni naga lalata, Rabi'u daga dawowarka zaka dasa daga inda ka tsaya?, yanzu saika karya
busurun nan, kasaukoshi nace maka."
"Kaka kibarni yaushe rabonda in ganshi, bakiga yadda yake farin ciki ba shima."?
"Kaci gidanku nace! Maza saukeshi."
Yana saukeshi Bunsurulle ya manne mashi, duk inda yayi yana biye dashi.
( niko nace Rabson da Bunsurulle wannan ƙauna har ina)
Ba'a ɗauki lokaciba Alhaji Abdallah ya ɗauke kaka da Rabson ya basu wani haɗaɗɗen gida tare
da ɗaukar Rabson aiki a kamfaninshi na sarrafa shinkafa.
Murna da farin ciki ba'a magana wurin kaka da Rabson, Kaka ƙauye taje ta sanar da ƴan uwan
mahaifin Rabson sukaje naiman aure gidansu Salma.
Alhaji Abdallah ya karramasu inda yasa bikin wata ukku.
Abdallah bai manta da gidansu Biba ba, suma gida ya ƙyara masu ga kayan abinci daya loda
masu a store.
An haɗa bikin su Jafar danasu Rabson nan da watanni ukku.
Da ƙyar da ji6in goshi Hindu ta samu Alhaji ya yarda zai maido Hajiya Zaliha.
Tayi matuƙar mamaki data dawo ta iske gidan da wata mata.
Salma ta kwashe komi ta sanar da Mahaifiyarta.
Kuka Hajiya Zaliha ta riƙayi tana nadamar abinda ta aikata, tana zaman_zaman ta ita ɗaya a
gidan mijinta, yanzu gashi nan i ta ce hada kishiya, ta ɗauki ƙaddara tare da wata irin nadama
datayi, domin yanzu ta ɗauki darasin rayuwa.
Zaman lafiya suke tsakaninta da Hindu tare da girmama juna.
_________________________
Suna isa gida Basma ƙamshin wani daddaɗan abinci ne ya daki hancinta.
Abinda ya ɗaure mata kai bai wuce ita dai tasan Habib bai iya girki ba balle tace shi yake girkin.
Matashiyar budurwa da taga tafito da tsohon ciki tana tafiya a hankli, hannunta riƙe da Walid
daya sha wanka ansa mashi kaya masu kyau sai ƙamshi suke zubawa.
Gabantane ya yanke yafaɗi dafe ƙirji tayi tare faɗar.
"Yau ni Basma nashiga ukku! Minike gani haka?, Habib yaushe kazama ɗan iska ka aje mace
gida harda ciki dan kaga baninan."
Kallon bakida hankali Habib yayi mata.
"In kika sake bakin ki ya ƙara faɗar kalma ɗaya mara daɗi ga mamata zani shayar dake
mamaki, wannan da kike gani wallahi badan itaba da yanzu sunanki bazawara, ita taita
rarrashina harna yarda inci gaba da zama tare dake, dan haka ki shiga hankalinki."
Wata irin ƙuna taji zuciyarta nayi mata, wai yau i ta ce da kishiya, ita kam ta gama shiga ukku,
rayuwa ta koyar da ita darasinda harta mutu bazata manta ba.
Hannu tamiƙa da nufin ɗaukar Ɗanta Walid, tsalle yayi ya fashe da kuka tare da maƙalƙalewa
jikin Hanan yana magana cikin hausar da bai ida ƙwarewa ba.
"Wayyo Momy foyeni, wannan matar bani sonta kice kada ta ɗaukeni nidai."
Ya ƙarashe maganar yana ci gaba da kuka.
Basma jin abinda Ɗan cikinta ke faɗa jitayi ƙafafunta sun daina ɗaukarta sulalewa ƙasa tayi tare
dayin zaman ƴan bori ta saki wani marayan kuka.
Habib tsoki yayi tare da shigewa ɗakin Hanan.
Hannan bin bayanshi tayi takai walid ɗakin ta ajeshi itakuma ta fito.
Kuka Basma keyi tamkar ranta zai fita, i ta ce yau ɗan da ta haifa yake gudunta yama manta da
ita, wannan duk laifintane ita tajama kanta, kuka ta fashe dashi tare da ɗaga hannuwanta sama.
"Ya Allah ka yafe mani, Allah ni mai laifice a gareka na sa6ama mijina Allah ka yafe mani."
Kukan dayaci ƙarfintane ya sanyata yin kasa cigaba da addu'ar.
Kafaɗunta ta dafa
Cikin taushin murya ta fara mata magana.
"Kiyi haƙuri Basma, banshigo gidan nan ba dan in fiddaki ki kwantar da hankalinki, insha Allah
zani shawo kan mijinki, Walid kuma sai a hankali zai saba dake."
"Nagode maki Hanan Allah yayi maki albarka, Allah ya zaunar damu lafiya."
Hanan tasha wahala kafin Habib ya yarda ya yafema Basma, zaman lafiya suke a gidan nan
duk da a yanzu Habib ya yafison Hanan akan Basma, amma yana ƙoƙarin 6oyewa, sai dai har
yanzu Walid yaƙi yarda da Basma shicewa yake Hanan ce Momynshi.
Allah ya sauki Hanan lafiya, tahaifi tagwaye mace danamiji.
Basma anata rawar ƙafa kamar ita ta haihu kullum macen na wurinta, da hanan taga soyayyar
da take nunama babyn saita barmata ita.
Haka sukaci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
__________________________________
Su Nas iyayensu yanke shawarar haɗasu aure sukayi.
Ba'a ɗauki sati biyu ba aka ɗaura aure Jamcy da Tk, Kulu da Nas, sai dai muce Allah ya bada
zaman lafiya.
_____________________________________
Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya.
A yau jama'a da dama suka shaida ɗaurin auren Rabi'u Mukhtar da Salma Abdallah, tare da
Jafar Abdurrahman da Habiba Hashim.
Bayan anɗaura aure aka gayyaci malamai suka gabatar da wa'azi akan zaman takewar aure.
Kowace amarya an miƙata gidan mijinta.
Wani katafaren gida Alhaji Abdallah ya mallakama Jafar anan aka kai amarya Biba, sai dai
muce masha Allah kwatanta haɗuwar gidan 6ata lokacine, domin ya haɗu haɗuwa mara misali.
Rabson ma Cikin gidajen Alhaji Abdallah ya mallaka mashi wani haɗaɗɗen gida nan aka
mallakamashi suka tare shida amaryarshi.
Rabson bai manta da Bunsurulleba, wani wuri yaɗiba aka gyara ya kawo bunsurulle ya ɗaure
ya ɗauko mai kula dashi, rayuwa tayi daɗi arziƙi ya bunƙasa Rabson yanzu yake Rabson guy.
Bunsurulle ya girma ya koma kamar bijimin sa.
In Salma naso ta tsokani Rabson saitace ita fa tana ƙwaɗayin naman Bunsurulle, nan zai tubure
yace shifa shida bunsurulle mutu ka raba, nan zasu tuna da baya suci dariya abinsu.
Biba da Jafar rayuwa suke cikin jin daɗi da kwanciyar hankali, ga kuɗi sun zauna masu sai da
muce Alhamdulillah.
*END*
*TAMMAT BILHAMDULILLAH.*
_YAU MUN KAWO ƘARSHE WANNAN LABARI, KURAKUREN DANAYI ALLAH KA YAFE
MANI, ALLAH KASA MUYI AMFANI DA ABUBUWAN DAMUKAJI MASU AMFANI, ALLAH KA
GYARA KASATA KA ZAUNAR DA ITA LAFIYA, MU HAƊU A LABARI NAGABA MAI SUNA
RAZANI KADA KU BARI ABARKU BAYA DOMIN WANNAN LABARI AKWAI FAƊAKARWA
NISHA ƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA, KUDAI KADAKU BARI ABAKU LABARI._
*MEEN@RT...✍*
08133562798