Showing 3001 words to 6000 words out of 31939 words
Jafar, Garba kisa, audu gwarama sai nura shila, su zasu shiga gidan su duba masu.
Ƙofar gidan kulle take gam, da ƙyar suka samu suka buɗeta, wata irin k’urace ta ke fitowa daga
gidan dole suka ja da baya sai da ƙurar ta gama ficewa sannan Jafar yai bisimillah suka kutsa
kai cikin gidan.
Duhu ne sosai gidan ko tafin hannunka baka gani, sai lokacin Jafar ya tuna da wayarshi, fiddota
yayi amma abun mamaki kwata_kwata babu network gurin ko alamun shi babu.
Touchligh ya kunna, tuni haske ya gauraye wurin, wani irin gidane mai wani irin fasali, inda suke
tsaye wani tangamemen falo ne mai ɗauke da gadaje uku gefe daya kuma kujerune aduk da
katakai akayi su, sai wasu ɗakuna biyu dake kulle, in ka matsa bayan kujerun wurin dafa
abincine shima da katakai aka ƙera wurin, amma duk yana ta lullube kayan gidan da kuma
ƙura,idanunsu ne suka hasko masu wani hoto amma ƙura ta lullubeshi, matsawa mukayi a
hankali Jafar yayi bisimillah tare da goge ƙurar,Hoton Turawane ya bayyana mata da miji da
kuma ɗiyarsu, sunyi dariya aka ɗauki hoton su, sunyi matuƙar kyau.
Kansu kullewa yayi, suna ma kawunansu tambayar miya kawo turawa acikin dajin nan har
sukayi gida?, lallai al amarin nan akwai ban tsoro.
Ƙofofin ɗakin suka buɗe da tagogin take haske ya bayyana duk da lokacin duhun magriba ya
fara.
Sun duba ko ina amma basuga wani abu na cutarwa ba.
Ɗakunan nan biyune kaɗai basu buɗeba.
Fitowa sukayi suka umarci abokan tafiyarsu dasu shigo daga ciki.
Bayan shigarsu ne kowa ya naimi wuri ya zauna yana jimamin halin da suke ciki.
Jafar ne yayi gyaran murya ya fara magana.
"Ƴan uwana ya kamata mutashi mu gabatar da sallolin dake kanmu, nasan da wuya musamu
ruwa a hanlin da muke ciki yanzu amma abinda yafi shine muyi taimama kawai zai fi mana."
Basma da Biba, Mandiya tare sukayi sallah, ƙiri_ƙiri Salma taƙiyin sallar cewa tayi ita gobe in an
samu ruwa ta haɗa tayi.
Garba kisa da yaranshi kuwa sai dai shiriyar, domin tabarsu kusa fiddo daga cikin aljihun wando
da ahana suka hau hura hayaƙinsu.
Dare yayi nan ido ya raina fata, kowa ka kalla zakaga tsantsar tashin hankali atare dashi.
Bayan sun kakkabe ƙurar da yana kowa ya fara neman inda zai kwanta, Mandiya,Basma,Biba
da Salma gado ɗaya suka kwanta, inda Salma tayita tsoki wai ita bazata haɗa jiki da su ba nan
Mandiya ta taso mata kamar zasu bigi juna, sai da Garba yace duk wadda ta ƙara masu
hayaniya zasu fiddata daga ɗakin sai dai ta kwana wajen.
Nan Salma tayi zuciya ta sauko ƙasa ta baza ɗan figaggen gyalenta ta kwanta sama.
Bayan kowa ya kwanta wasu sunyi addu'a wasu kuma ko uho.
Cikin bacci Salma taji kamar ana lasar mata ƙafa, afirgi ce ta buɗe idanunta ta sauke su kan
wata irin ƙatuwar mage baƙaƙirin bakinta wasu zara_zaran haƙora jini na ɗiga daga bakinta ga
wasu irin idanu manya_manya masu ban tsoro, wata mahaukaciyar ƙara ta ƙwala da tayi
sanadiyyar farkawar kowa daga bacci daya ɗauke su.
Ganin irin halittar magen ba matan kaɗai ba har mazan sai da hantar cikinsu ta kaɗa.
Garba kisane yayi ƙarfin halin shaƙe wuyan magen.
"Kuyi sauri ku buɗe mani ɗakin nan."
Jafar ne yayi saurin buɗe ɗakin, Garba ya fita da guda magen na hannunshi a shage.
Sai dai kash! Daya san abinda zai iske a wajen bazaiyi gigin fitaba.
Kan Magen ya riƙa bugawa da ƙasa amma ko gezau batayi ba sai ma hannunshi dayaji kamar
an daka mashi kaifaffar wuƙa, ihu ya ƙwala ya wurgar da magen yana duba hannun yaga ashe
cizone ta sakar mashi a hannu, take jini ya hau zuba ba ƙaƙƙautawa, nufar hanyar gidan yayi
zai shige, juyowar da zai yi yaga abinda ya kusa sanadiyyar tsayawar numfashin shi.
Magen nan ce ta rikiɗe ta koma wani basa muden Aljani jikinshi duk jini bakinshi wasu haƙora
ne zaƙo_zaƙo irin na zombie, juyawa Garba kisa yayi da nufin komawa gidan horror ɗin yayo
kanshi yana ƙoƙarin cizon Garba.
A tsorace Garba ya nufi ɗakin zai shige yana ihun su taimakeshi, ganin halin da suke ciki yasa
su buɗe ɗakin, yana gabda shigewa ɗakin aljanin na kamo ƙafarshi mutanen daki hannuwan
Garba suka kama domin ceton rayuwarshi, da kyar suka jawo Garba ɗakin suka maida ƙyaure
suka rufe.
Nura ne ya lura Garba ba alamun numfashi a tare dashi, "kai Oga fa yabar numfashi ku duba
ƙafarshi ga wani cizon nan ya ƙara samu."
Rigar jikin shi suka keta suka ɗaure mashi ciwon, suna yi mashi firfita.
"Yau ni Rabi'u nashiga uku na lalace, wayyo kakata ƙila shikenan mutuwa ke kirana ita ta raboni
da gida."
Kowa ka kalla a ɗakin hankalinshi a tashe yake, yana tunanin makomarsu.
A hankali Garba ya buɗe adanunshi da suka yi mashi nauyi, ya sauke su ga ƙafarshi dayaga an
ɗaure mashi.
Kwance wurin yayi sai dai abun mamaki ciwon ya warke sai dai wuri rauni yayi wani irin baƙi
wasu jijiyoyi sun fito sun miƙe har wajen cinyarshi, kamar yadda jini ke gudana haka wannan
baƙin abun ke gudana ajikin Garba kisa.
Sannu suka shiga yi mashi, baccin da basuyi ba kenan har gari ya waye.
Bayan sunyi sallah, nan suka shiga tunani abinda zasu samacikin su, kowa akayima maganar
yafito su tafi naiman abinda zasu sama cikinsu sai ya noƙe yaki fitowa.
Daga ƙarshe dai Jafar da Biba suka ce su zasu fita su nemo.
Tunda suka fara tafiya basu samu komi ba ko bishiyoyin da zasu ciri ƴa'ƴan suci basu samu ba.
Ƙorama suka iske ruwa na gudana , tsayawa suka yi suka sha ruwan suka ɗibar ma sauran
wanda zasu sha.
Sunyi tafiya kaɗan suka fara hango wata bishiyar kwaba a gabansu tsayawa sukayi.
"Kin ga dai tun ɗazu bamu samu komi ba duk yawo da mukasha, yanzu ni zani hau in tsinko ke
kiriƙa ɗaukewa."
Haka kuwa akayi sun ɗibi mai yawa suka nufi hanyar komawa wurin abokan tafiyarsu.
Kowa yayi murna da samun abinda zasu sa ga bakinsu banda Salma da ta ce ita tafi ƙarfin cin
gwaba, babu wanda ya matsa mata taci cikinta ne inma bataci ba.
Shawara suka yanke su ƙara kwana nan in Garba ya ji sauƙi sai su cigaba da tafiyar.
Dare yayi sosai kowa ka gani yasha jinin jikinshi yana tunanin abinda zai faru.
Garba tunda lamarin nan ya faru jikinshi ke rikiɗewa yana komawa baƙi, amma bai sanar da
kowa ba.
Zaune yake ya sadda kanshi ƙasa kamar mai bacci, lura abokan tafiyar sukayi kamar Garba
yabar motsi, audu ne yayo kanshi da sauri dan ganin halinda yake ciki, ya isowa jikin Garba na
ida rikiɗewa ya koma green da baƙi.
Duƙawa audu yayi dan ganin mike faruwa da Garba.
Shak’arda Garba yayi ma audu gwarama yasanya ƴan ɗakin fara iface_iface ganin yadda
kaman nin Garba suka chanza.
Rabson guy tsabar firgici sulalewa ƙasa yayi ya sume.
Garba ya tsunshi da suka zama zaƙo_zaƙo ya dakama audu su a wuya ya wurgar dashi ya
bugu da bangon ɗakin ya faɗo ƙasa ba alamun numfashi atare dashi.
Garba juyawa yayi yai kan Salma da tayi mutuwar tsaye hada fitsarin dole yai wani irin kukan
kura wanda seda ilahirin dajin yayi amsa kuwwar da ’ya’yan cikin kowa suka kad’a.......
Sake kallon Salma yayi akaro na biyu yayin da y..........✍
♀️♀️♀️♀️♀️
*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅
*MEEN@RT...✍*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: *BAƘAR TAFIYA*
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE *
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI
RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA
ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN,
ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
♀️♀️♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI
NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
____________________
*PAGE 6_7*
......Tamkar yunwa taccen zaki haka Garba yayo kan Salma gadan_gadan, tsabar tsoro ko motsi
takasayi ta rufe ido tana sauraren mutuwar data nufota.
Ganin halin da ake ciki yasa Jafar yin kabbara ya ya ɗauki wani katako yayo kan Garba kisa
gadan_gadan, sai dai kafin ya iso Garba yayi nasarar shago Salma ya fara gama kanta da
bango, tsabar azaba nan take ta sume.
Ya isa isowa daf da Garba yayi kabbara da ƙarfi ya ƙwaɗama Garba katakon nan a tsakiyar kan
shi.
Take Garba yayi wata irin kururuwa ya faɗi ƙasa.
Salma gwara mata kai da bango ta sume batare da tasan mike faruwa ba.
Biba da ke labe bayan kujera tana addu'a tana hawaye gitowa tayi jin abun ya lafa, Ganin
Garba da tayi kwace ƙasa Kanshi jini na malala nan hankalinta ya ƙara tashi, abun mamaki jikin
Garba lokaci ɗaya yayi wani irin fari fat! Tamkar babu jini jikinshi ko ɗigo, kallon_kallo Biba da
Jafar suka hau yima juna.
"Biba yanzu ba lokacin kuka bane musamu mafita, ni fa gani nike mu haƙura da dajin nan mu
zauna cikin gidan nan kawai in Allah yayi zamu fita shi zai kawo mana ɗauki da kanshi, soboda
faɗar Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallam daya ce in annoba ta samu gari to naciki su
zauna a garinsu na waje kuma kar su shigo garin."
"Nima ina da wannan tunanin Amma yanzu abinda ya kamata mu samu abokan tafiyarmu su
farfaɗo sannan muyi gaggawar rabuwa da gawar nan, kaga fa yadda ta koma, ina tunanin
barinta tare damu kamar wani haɗari ne babba."
"Maganarki haka take, yanzu bara mu fara shafa masu ruwa su farfado mujita bakunan su."
Wurin Audu gwarama suka fara zuwa sunyi sa'a suna shafa mashi ruwa a fuska ya ja a jiyar
zuciya yana mai shafa wuyanshi dake mashi tsananin zafi, shi ma dai_dai in da Garba ya
yakusheshi wurin ya fara green da baƙi.
Sannu sula riƙa jero mashi yana amsawa.
Wurin Salma suka matsa ita ma tana nan kwance tamkar gawa.
Jafar dubar Biba yayi yana mata magana a hankali yadda in ba kusa kake dashi ba bazakaji
mitake fada ba.
"Biba Salma kinga mace ce bai kamata in tabata ba ke yaka mata ki fara duba inda Garba ya
buga mata kai ki kiyi addu'a nasan a firgice zata tashi saboda halin firgicin da ta shiga,sannan ki
shafa mata ruwa a fuska."
A hankali ta fara buɗe idanunta ta sauke su kan Biba dake tsugune kanta.
"Nashiga ukku ni Salma! Yanzu shikenan nima horror zani zama, wayyoh daddy na danabi
shawararka da yanzu ina gida zamana, yanzu gashi na kawo kai na ga halaka."
"Aa Salma Garba bai cijeki ba, ya dai bugaki da bango yayi sanadiyyar sumanki."
Tamkar wata ƙaramar yarinya haka Salma ta maƙale jikin Biba tana kuka, niko nacr salma
ina nuna isar da wulaƙanta muta ne da nuna masu ƙyama.
"Addu'a zakiyi ba kuka ba Salma, a wannan halin da muke ciki addu'a kaɗai ce magani, kuka
bazai amfane mu da komi ba."
Biba ta faɗa tana ɗora hannayenta a kafaɗar Salma.
Audu lura yayi da halin da Ogansu ke ciki.
Da gudu ya rugo ya rungume Garba yana mai fashewa da wani irin kuka, "Oga shikenan katafi
ka barmu cikin wannan halin, Oga ji nike dama nine na mutu na huta ba kai ba, haka muma
zamuyi ta mutuwa ana kashemu ɗaya bayan ɗaya, ina nadamar yin Baƙar tafiyar nan yanzu
nasan nayi bankwana da kakata." Kukan dayaci ƙarfinshi yasa maganarshi sarƙewa.
Jafar ya iso wurin Garba ya rabashi da gawar yana bashi haƙuri, addu'a ce kaɗai zata kawo
masu mafita.
Lura sukayi da abokan tafiyarsu babu Mandiya da Nura shila da Basma.
Sun bincike ko ina amma basu gansu ba.
Ɗakin farko sukayi shawarar buɗewa ko ciki suka buya.
Sai da suka haɗa ƙarfi wurin buɗe ɗakin, Ɗakine mai yalwar faɗi ba laifi, sai dai tsananin duhun
ɗakin ya hana ka ga mike ciki, motsin da suka jiyo ne ya sasu juyowa a razane, Nura shila da
Basma suka gani ƙarƙashin wani bencin katako sun boye ganin su yasa suke ƙoƙarin fitowa.
Bayan fitowarsu Biba ta fara magana, "Sanin haɗarin da muke ciki yasa daga yanzu ko wani
bala'i ya samu ɗan uwanmu kada wanda ya ƙara ƙoƙarin guduwa ya rabu da sauran."
Kowa yayi na'am da wannan shawarar
Ɗayan ɗakin suka buɗe, buɗewarshi tayi dai_dai da bugawar zuciyoyinsu kallon_kallo suka fara
yima juna, wannan ɗakin yasha banban da saura, saboda shi wani abun mamaki babu duhu
acikinshi, kayan wasane na yara birjik aciki, su kansu kayan wasan in ka kallesu sau ɗaya
bazaka ƙara ba saboda abin tsore, daga ɗiyar robar da aka cirema hannu ɗaya tana hawayen
jini sai wadda ta cire kanta ta riƙe a hannu tana murmushi haƙoranta duk jini, wadda tafi masifar
tada masu hankali wata ɗiyar babyce girmanta ya kai na jariri, zaune take jikinta jar riga ce
hanta gashi ya baje ta ko ina baka ganin ko fuskarta, ga wasu irin wuƙaƙe a hannunta duk jini
ya bata su, kallo ɗaya zakayi mata ka ɗauke kanka.
Wani yawu Rabson guy ya haɗiye ƙut! Da yayi sanadiyyar juyowar abokan tafiyarshi, sun naimi
Mandiya lungu da saƙo sun rasa, motsi suka jiyo bayan ƙyaure, ƙin leƙawa sukayi kowa jininshi
kan akai fa saboda tsoron dake ɗawainiya dasu.
Jafar ne yayi ƙarfin halin yawo ƙyauren, tsaye take tayi labo bayan ƙyauren jin an jawo ƙyaure
yasa ta fara junduma ihu, "wayyoni Mandiyar uwar daba yau nakawo kai na ga halaka, Magaji
kin cuce ni da kika bani shawarar zuwa garin Kaika zo! Ashe ajali ke kirana a wannan BAƘAR
TAFIYAR, nashiga ukku na balbalce."
"Buɗe idonki ki gani mune fa abokan tafiyarki."
Jafar ya faɗa yana mai bata hanyar wucewa.
Idanu ta buɗe danjin muryar abokin tafiyarsu.
Shawara suka yanke suyima gawar Garba sallah su binneta.
Ruwan da ya rage masu suka yi alwallar dasu, sun gama sallar sun fara gina zasu binneshi
wani baƙin hayaƙi ya bayyana ya ja gawar Garba suka bace.
Nan fa suka ɗiba aguje suka koma gidan suka rufe masu kuka nayi masu addu'a nayi.
Basma kuka take tana sambato ita kaɗai, "Allah sarki masoyina kuma mijina habibina, dana bi
shawararka da yanzu ina gida amma haka na nace dole sai naje bikin ta gaban goshi, Allah ya
isa tsakanina dake ta gaban goshi ke kikai ta turani ina ma habib rashin mutumci, yanzu gashi
nan na baro ɗana mijina yana fUshi dani nasan mutuwa zaniyi."
Babu wanda ya rarrasheta koya bata hakuri domin kowa ta kanshi yake.
Nan suka faɗama sauran abokan tafiyarsu shawarar da suka yanke ta barin wannan gidan su
ƙara gaba, amma ba haka ya kamata suyi ba, kamata yayi su zauna suga yadda zata kasance.
Wasu sunyi na'am wasu kuma sun bada shawarar abar gidan, sun yanke shawarar zasu bar
gidan in gari ya waye.
Duhun dare ya fara kowa hankalinshi ya ƙara dugumzuma, kingin kwaibar da ta rage masu
suka raba suka fara sha, Salmar tun kafin azo kanta ta warci biyu ta faraci.
Dare yayi sosai dajin babu abinda kakeji sai kuka tsuntsaye da wani irin iska mai bada wani
firgitaccen sauti in ya haɗu da kukan tsuntsaye.
Mandiya, Basma, Biba da Salma yau gado ɗaya suka haye ba zancen nuna ƙyama yau Salma.
Mazan suma wuri ɗaya suka dunkule.
Bacci ma in kaga kana yin shi to baka shiga wani bala'in ba kokoma sai dai in bacci barawo ya
sace ka.
Duka ɗakin kowa manne yake da ɗan uwanshi,idosu biyu sun kasa bacci gudun abinda zai biyo
baya.
A hankali tagogin ɗakin (Window) suka fara buɗewa da kansu, jikake kit!_kit! Taga ta bude da
kanta, karar da sukaji ce ta maido hankalinsu ga abinda ke faruwa.
Dirowa sukayi daga gadon suka cibre wuri ɗaya jikinsu na kyarma, duk wannan halin da suke
ciki addu'a ce bakin Biba sabanin su Salma da suka fara kuka.
Ƙofofin na ida buɗewa wani farin hayaƙi ya fara shigowa yana dunƙulewa wuri ɗaya.
Yana gama haɗewa wuri ɗaya wata irin halitta Mai suffar kare ta bayyan, jikinta ko ina hannuwa
ne idonta guda ɗaya ne a tsakiyar goshi, ga bakinta wagege da haƙora masu matuƙar tsini.
Dariya halittar ta kece da ita wadda ta haddasa ma ɗakin girgiza.
"Kunyi kuskure bil adama masu taurin kai da gadara, yau kwananku ya ƙare, a sannu zaku
baƙunci lahira."
Jafar yayi ƙarfin halin fara magana.
"Ƙarya kike yake wannan la'anannar halitta, ke baki isa ki kashemu ba sai dai in kwanan mu ya
ƙare ubangiji ya rabuta zamu mutu yau, amma badai ke ba."
"Hahaha! Gaskiya wannan bil adam jarumtarka ta burgeni, amma kayi kuskuren faɗa da ƴar
tsito ƙaramar aljanu kuma shaiɗaniyar cikinsu, yanzu zani shanye jinin jikinka inyi
gunduwa_gunduwa da naman jikinka."
Tana rufe baki tayo kan Jafar da mugun nufi a cikin zuciyarta.
Abun mamaki kafin ta ida isa wurinshi sanadiyyar addu'ar da yake ya bace ma ganinta nan