Showing 9001 words to 12000 words out of 31939 words
suka samu Mandiya ta farka daga sumewar da tayi.
Tana tashi ta riƙa ƙwala ihu tana gasu nan gasunan zasu kasheni.
Saida Jafar ya dage mata da addu'a sannan ta dawo dai_dai.
Shawara suka yanke bazasu ƙara zaunawa wuri ɗaya ba sai dai in dare yayi su yada zango su
kwana su ci gaba da tafiya in gari ya waye.
Tafiya suke baji ba gani ga yunwar da ta addabesu da ƙishirwa.
Sunyi tafiya mai nisa suka iso wani wuri mai yalwar bishiyoyi masu suffar dodanni, wasu sun
rankwafa kamar zasu faɗi ga jikinsu babu ganye ko ɗaya, wasu kuma Suffar mutumce tsaye ya
buɗe baki yana dariya,wata bishiyar in kayi mata kallo ɗaya bazaka kuma kallonta ba.
Tunda suka shigo wurin suka sha jinin jikinsu, ba su Basma kaɗai ba hatta Jafar sai da
zuciyarshi ta buga ganin yanayin wurin, sai dai shi bai fiddo tsoranshi ba a fili, sa6anin su
Basma ita da Mandiya da suka maƙale juna suna bin bayan Jafar.
Busassun ganyayen dake baje wurin suka riƙabi ta saman su suna takawa domin su fita daga
wannan sarƙakiya.
Takun da suke da sauri yasanya duk busashshen ganyen da suka taka yake bada wata ƙara
rumutss!
A hankali wata iska ta fara kaɗawa ganyayen wurin suka fara tashi sama.
Lokaci ɗaya wata guguwa ta turniƙe wurin, dale su Jafar suka duƙa tare da rufe idanunsu.
A hankali iskar ta fara lafawa, buɗe idanunsu sukayi dan ganin mike faruwa.
Bishiyoyin wurin suka gani da wasu jajayen idanun tamkar garwashin wuta, sun buɗe bakunan
su suna wata irin dariya mai kama da kukan jarirai.
Tsoron da ya kamasu bai hanasu miƙewa su falfala da azababben guduba.
Duk bishiyar da suka gitta ƙoƙari take ta kawo masu Chafka.
Gudu suke ba ƙaƙƙautawa, suna ƙoƙarin tsira da rayuwarsu.
Wata bishiya ce tayi nasarar sanya jijiyarta ta chafko ƙafar Basma dake gudu.
Ihu take janyo ta bishiyar keyi da ƙarfi jikinta na karcewa da ganyayyakin dake ƙasa.
Ganin halin da Basma ke ciki ya sanya su jafar juyowa domin kawo mata agaji.
Gudu suke suna binta bishiyar na ƙara janta.
Jafar ne yayi nasarar danƙo sauyar bishiyar.
Ƙoƙarin kufcewa sauyar keyi amma ta kasa saboda ruƙon da yayi mata.
Da ƙyar da addu'ar dake bakinshi yayi nasarar karya sauyar.
Bata damu da ciwokan dake jikinta ba tana samu ya kwanceta ta miƙe sukaci gaba da
gudu........
__________________
Garba da kamanninshi suka gama rikiɗewa jikinshi yayi fari fat, idanunshi baƙin ciki ya bace sun
koma farare tas, ga farautanshi sun ƙara tsawo, duk ya zama abun tsoro.
Wasu yawu Salma da Rabson suka haɗiye atare kutt!.
Biba tunda tayi mashi kallo ɗaya tashiga karanto duk wata addu'a da ta zo mata.
Kafin su ankara Garba yayo kukan kura ya turmushe Rabson yana kokawar kai mashi cizo.
Wato wani bala'in inka ganshi tsoro barinka yake ka hau ƙoƙarin ceton rayuwarka.
Rabson ƙoƙarin yakice Garba yakeyi bakinshi na karanto addu'o'in da ya koya tunlokacin da
Kaka ta sanyashi islamiyyah.
Inya fara karanto kul a'uzu kafin ya ida ya kamo Walfajir, ita ma ya saki, ya kamo
Wata,ranar Rabson har addu'ar shiga kewaye (Toilet) sai da yayi.
Allah ya dubi Rabson ya bashi sa'ar wurgar da Garba ya kwasa a guje su Salma suka take
mashi baya.
Miƙewa Garba yayi yabi bayansu da azababben gudu suka ƙara nausawa cikin jejin.
*COMMENT* ✅
*SHARE*✅
*MEEN@RT...✍*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: *BAƘAR TAFIYA*
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE *
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI
RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA
ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN,
ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
♀️♀️♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI
NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
*WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN
ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA*
*MASOYA INA MAI BADA HAƘURI BISAGA JINA DA KUKA YI KWANA BIYU SHURU, HAKAN
YA FARUNE BISA GA MATSALAR NEPA DA MUKA SAMU, AMMA YANZU KOMI YA
DAI_DAITA, INA GODIYA MASU TURO MANI SAƘONNIN DA KIRANA DAMA WAƊANDA
BASU SAMU DAMABA INA MATUƘAR GODIYA,ALLAH YABAR ZUMUNCHI* ___________________
*PAGE 12_13*
.......Gudu suke iyakar ƙarfin su, domin ceton rayuwarsu.
Basu ankara ba suka gansu gaban wani kogo, basu tsaya 6ata lokaci ba suka kutsa kai cikin
kogon.
Cirko_cirko sukayi suna mai da numfashi saboda gudun da suka sha.
Sai lokacin suka lura da inda suke,
"Mun shiga ukku minike gani nan?, ina muka kawo kanmu."
Salma ta faɗa tana nuna masu ƙwarangwal ɗin mutane birjik wurin.
Kogon ko ina ka kai dubanka ƙwarangwal ɗin mutane ne birjik ga yana duk ta mamaye wurin.
Ido suka fara rarrabawa suna ƙara bin wurin da kallo.
"Kada tsintar kammu a wannan ya tada mana hankali, mutsaya mu naimi mafita mu dage da
addu'a,kada mu kuskura mu rabu da junan mu."
Biba ta faɗa tana binsu Rabson da kallo.
"Eh haka ya kamata mu riƙa tafiya tare da junanmu, kada muyi kuskuren rabuwa da ƴan
uwanmu."
Salma ta faɗa muryar ta na kyarma tana ƙara shigewa jikin Biba.
"Muje mu naimi abinci nidai jina nike cikina kamar an hura wuta."
Rabson ya miƙe tare da yin gaba.
Bayanshi suka bi tare da nausawa ciki kogon.
Tunda suka fara tafiya Basu gamu da komi ba sai ƙasusuwan mutane da yanar da ta tare
hanyar sai sun ɗebe ta da hannunsu suke samun hanyar wucewa.
Tirjiya suka ja ganin
Mutum tsaye.
Salma cikin in iyna ta furta da..da..daddyy.....
____________________
Sunyi gudu har sun galabaita.
Tsayawa sukayi ganin sun baro wurin duhuwar, sun bullo wani wuri mai yawan kwazazzabai
ruwa na wucewa a hankali ta ƙasansu.
Yanayin wurin gwanin ban sha'awa.
Nan suka tsaya suka gabatar da sallolin da ake binsu.
Cikin ruwan da ke wucewa suka shiga suka ci gaba da tafiya, suna jan ƙafafu a hankali.
Jafar ne gaba sai su Basma a bayanshi.
Mandiya ji tayi kamar an tsunkule ta a ƙafa, a zabure ta yi tsalle ta ruƙunƙume Basma tana.
"Nashi ga ukku na lalace miye ya cijeni a ƙafa?, wayyo uwar daba da magajiya Allah ya
tsinemaku albarka, duk ku kuka jefani ciki halinda nike ciki."
"Ke ki sakini ya kike ƙoƙarin kayar dani, dake zaniji ko da yunwar dake ɗawainiya dani."
Basma ta yakice Mandiya ajikinta.
"Ya isa! Ku fahimci halinda muke ciki, ku daina yawan hayaniya kuna ɗaga muryoyinku hakan
zai iya janyo mana wata matsalar."
Cigaba da tafiya sukayi.
Tim! Sukaji ƙarar faɗuwar Mandiya cikin ruwan.
Janta ake ba ƙaƙƙautawa ana gwarata da dowatsun wurin.
Ganin wanda ke janta ya sanya su haɗiye wani yawun tashin hankali.
Nura shila suka gani kamanninshi sun sauya jikinshi yayi fari sol ya koma suffar horror yana jan
ƙafar Mandiya.
Ihu take tana kiran sunayensu, su taimaka mata.
Nura nasarar ida janyo Mandiya yayi, ya dasa mata haƙoranshi a ƙafa.
Wata irin kururuwa tayi jin azababben cizon da Nura yayi mata a ƙafa.
Ganin halinda Mandiya ke ciki ya sanya Jafar da Basma fidda tsoron da ke cikin ransu, Basma
ta kamo hannuwanta tana janyota tana kuka.
wani dutsi Jafar ya ɗauka ya bugama Nura a tsakiyar baya.
Wata ƙara ya ƙwala da tayi sanadiyyar sanya wurin amsa kuwwa, tsuntsayen dake wurin suka
yi sama.
Hannun Mandiya Basma ta kama suka yi cikin dajin da azababben gudu.
Nura ganin su Basma sun Tsere mashi ya ya sanyashi bin bayansu shima.........
____________________
"Daddy kai nike gani ko idanu nane ke yi mani gizo?."
"Nine Salma, Mahaifiyarki ta sanar dani abinda ya faru shiyasa na biyo bayanki nazo in fitar
dake daga jejin nan, Zo muje kinji Mamana."
"Aa Salma kada ki yarda dashi, wsnnan ba Mahaifinki bane, yaudara ce kawai."
Biba ta faɗa tare da kamo hannun Salma tana ƙoƙarin hanata ida isa wurin Babanta.
"Dallah malama rabu dani, dan kinga ba mahaifinki bane yazo tafiya dake shiyasa kike ƙoƙarin
hanani isa gareshi, ninasan dama zai zo da bataliyar sojoji ya fitar dani daga wannan jejin ."
Fizge hannunta tayi tare da rugawa ta rungume daddyn ta.
Wata Mahaukaciyar dariya taji an barke da ita, wadda ta haddasama Kogon girgiza.
Tuni su Rabson da Audu gwarama suka haɗe wuri ɗaya suna sallallami.
Biba baiwar Allah idanunta ta rufe taci gaba da kwararo duk addu'ar da tazo bakinta.
Salma jin Daddyn ta da ta rungume ne ke wannan dariyar ya sanya ta ɗagowa a matuƙar
tsorace.
Ja tayi da baya ganin ya chanza suffa ya koma wannan tsohuwar da ta mara lokacin da zata
shiga mota.
Cikin kakkausar murya tsohuwar ta fara magana.
"Ina kuma zakije ɗiyata?, ko har kin manta marin da kikayi mani?, bai kamata kiji tsoro tun
yanzu ba."
Zubewa Salma tayi bisa guiyoyinta ta fara ba tsohuwar haƙuri.
Ƙara tun tsurewa da dariya tayi."Dole ki ɗauki hukuncin abinda kika aikata kigane wulaƙanci ba
abu bane mai kyau."
Hannu ɗaya tasa ta suri Salma ta buga da ƙasa kanta ya bugu da wani icce take goshinta ya
haye yayi suntum, jini yaci gaba da zuwa.
Hayaƙi Aljanar ta koma ta shiga jikin Kwarangwal ɗin dake wurin take suka fara motsi suna
miƙewa.
Salma miƙewa tayi da ƙyar ga zafin da goshinta ke mata ga lebenta daya haye yayi suntum ga
hannunta da ta faɗa samanshi yana mata azababben raɗaɗi.
Ganin kwarangwal ɗin sunyo kansu, yasa suka fara ja da baya tsabar firgici kasa gudu sukayi.
Rabson cikin daga murya yace.
"Kuna gani ana naiman hallaka mu amma kunyi tsaye sororo, toni nayi gaba saikun taho."
Zabgawa yayi da gudu ko waiwayowa bayayi.
Suna gani yayi gaba suka take mashi baya.
Kwarangwal ɗin suka bi bayansu a guje.
Gudu suke suna waiwayen kwarangwal ɗin.
Sunyi nasarar fita daga cikin kogon sukaci gaba da gudu.
Turjiya suka yi ganin wani wawakeken tsauni da suka tsinci kansu samanshi,ƙasan tsaunin
ruwane ke gudu.
Basu da wata mafita face su dira cikin ruwan nan.
Juyawa sukayi gani sukayi kwarangwal suna ƙara kusanto inda suke baki buɗe suna wata irin
kuwwa mai razanar da rihin bil adam.
Rabson cikin kyarmar murya yace dasu Audu.
"Nidai da in tsaya waɗan nan halinttun su kasheni a banza ƙara in faɗa ruwan nan."
Ƙafar wandonshi irin na gayun nan wanda ake kira Inna tayani cirewa ya duƙa ya nannaɗe ya
nufi ramin yana nayi gaba sai kun iso.
Tsalle yayi ya dira ƙasan ramin, suma sauran take mashi baya sukayi suka tsunduma ƙasan
ramin.
Lokacin da kwarangwal ɗin suka iso, har sun ɗira ƙasan.
Lokacin da suka dira cikin ruwan wani rin ruwane mai matuƙar yawa ga zurfi, iyo suka ci gaba
dayi amma babu alamun zasu kawo ƙarshen ruwan, gilmawar wani baƙin abu suka gani ya
wuce ta gabansu.
Tsananta yin iyon sukayi domin iskar da suka yi guzurinta ta kusa ƙaremasu.
Abun mamaki kowanensu cikin kwarewa yake iyo tamkar dama chan sun saba.
Rigar Audu akaja tareda yin ƙasan ruwan dashi, cikin kwarewa Rabson yayi saurin ruƙoshi yayo
sama dashi.
Da kyar suka iso bakin gabar ruwan kowanensu yana jan dogon numfashi.
Basu bar wurin ba nan suka gabatar da sallolin da ake binsu, zama sukayi suna hutawa, domin
a halin da suke ciki baza su iyacigaba da tafiya ba.
Jikin Audu ne ya ida zama green da baƙi, ga wasu iri jijiyoyi baƙaƙe da su ka bayyana a
fuskarshi.
Kamar an ɗauje shi anyi jifa dashi haka aka wullar dashi gefe ko numfashi babu a tare dashi.
Cikin firgici su Biba sukayi kanshi suka tsaya chirki_chirko.
A hankali kamanninshi suka fara sauyawa yana komawa Horror.
Ganin haka ya sanya su Biba ja da baya cikin tsananin tsoro.
Tamkar an harba kibiya daga cikin kwari haka Audu yayi wata alkafira ya dira gabansu
Rabson.......
*KU ƘARA DA HAƘURI, MATSALAR NEPA MUKA SAMU, AMMA YANZU ALHAMDULILLAH,
MASOYA INA GODIYA NAGA SAƘONNINKU DA KIRANA DA KUKA RIƘAYI KUJI LAFIYA, INA
MATUƘAR GODIYA ALLAH YA BARMU TARE*
*COMMENT ✅*
*SHARE ✅*
*MEEN@RT...✍*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: *BAƘAR TAFIYA*
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE *
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI
RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA
ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN,
ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
♀️♀️♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI
NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
*WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN
ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA*
*MASOYA INA MAI BADA HAƘURI BISAGA JINA DA KUKA YI KWANA BIYU SHURU, HAKAN
YA FARUNE BISA GA MATSALAR NEPA DA MUKA SAMU, AMMA YANZU KOMI YA
DAI_DAITA, INA GODIYA MASU TURO MANI SAƘONNIN DA KIRANA DAMA WAƊANDA
BASU SAMU DAMABA INA MATUƘAR GODIYA,ALLAH YABAR ZUMUNCHI* ___________________
*PAGE 14_15*
............Ganin sun tserema Nura yasan ya Mandiya faɗuwa ƙasa tana maida numfashi.
Dafe ƙafarta dake yi mata raɗaɗi tayi.
"Wayyoh ni Mandiya na bani na lalace, yanzu shikenan nima Horror zani zama."
Sauran maganar maƙalewa tayi saboda kukan da yaci ƙarfin ta.
Matsowa sukayi fuskokinsu da matuƙar tausayi suna mata sannu.
Ƙafar suka kallah, abin mamaki jinin dake zuba ya tsaya, wurin yayi wani irin green da baƙi.
Su kansu sun san nan da lokaci ƙanƙani itama zata zama Horror.
Allah sarki Jafar duk halin tsananin da suke ciki zuciyarshi tana wurin Biba kullum cikin
tunaninta yake zuciyarshi tana hasko mashi hoton fuskar Biba.
Basma ta taimaka ma Mandiya sukaci gaba da tafiya har duhu ya farayi.
Ƙarƙashin wata itaciyar Kuka suka yada zango, daji Jafar ya shiga ya samo masu ƴa'ƴan
itanuwa sukaci.
Fuskokin su duk cikin tashin hankali suke, kowa da irin tunanin dake cikin zuciyarshi.
Motsin da sukajine ya sanya su dawowa daga duniyar tunanin da suke.
Tamkar walƙiya haka sukaga wani farin abu ya gilma ta gabansu.
Basma da Mandiya rirriƙe juna sukayi ido ya raina fata.
Miƙewa Jafar yayi a hankali cikin sanda ya dudduba ko ina amma bai ga komi ba.
Dawowa yayi ya zauna zociyarshi cike da tunane_tunane.
"Jafar ka duba sosai kuwa?, ni fa kamar fatalwa nagani wallahi baka gani ta gifta tanan."
Basma ta ƙarashe maganar tana ƙara dudduba wurin.
"Tabbas nima ita na gani, amma komiye mu dage da addu'a babu abinda yafi ƙarfin Allah."
A ɗarare suke jininsu kan akaifa.
Dare yayi dare bakajin motsin komi sai kuka tsuntsaye da wani irin gurnani da suka rasa gane
namiye.
Jafar gani yayi zaman zugum ɗin yayi yawa nan ya buƙaci jin miya fiddo da su daga gida.
Basma ta fara basu labarin abinda ya fito da ita, Jafar ya girgiza sosai dajin labarin yayi
mamakin yadda ta bijirema umarnin miji ta taho biki, wai kuma bikin ma na ƙawa.
Nan itama Mandiya ta fara bada labarinta kamar haka;
"Kamar yadda kujaji da farko nidai sunana Mandiya, garinmu ɗaya daku wato gefen Kai kazo,
na taso babu uwa babu uba, natsinci kaina a gidan karuwai hannun wata mata mai suna uwar
daba, tun da na taso banida kunya ko kaɗan ga taka mutane da bi ta saman duk wanda ya so
kawo mani raini, tun ina da shekara 20 uwar daba ta ɗorani a hanyar karuwanci, in da ni dana
tashi sai karuwanci na yayi zarra saboda rashin kunyata nayi suna duk inda kashiga indai gidan
karuwai ne to an san da zamana, abinda yayi sanadiyyar fitowata wannan tafiyar Magajiyar
karuwai tai ta kwaɗaita mani inzo garin kai kazo zani tara dukiya mai tarinn yawa, domin chan
karuwanci yafi tsada, kunji abinda ya fiddoni, har yanzu ina dana sanin fitowata da kasancewata
karuwa ina nadamar rayuwar da na tsinci kaina ciki."
Kukan dayaci ƙarfinta ya sanyata kasa ida maganar.
Sun tausaya mata halinda ta tsinci kanta.
Nan Jafar ya ƙara jan hankalinta Allah gafurun rahimun ne, ta tuba har cikin zuciyarta Allah
yana karbar tuban bawanshi madamar baizo gargara ba.
Nan shima Jafar Ya basu labarin abinda ya fito dashi gida, sun jajantama juna suna addu'ar
Allah ya fitar dasu a wannan jejin.
Tsit! Wurin yayi kowa da abinda yake tunani, Jafar yana gefensu ya takure wuri ɗaya yana
addu'a a zuciyarshi.
Dariya aka kece da ita wadda ta tilasta masu toshe kunnuwansu da duka hannayensu biyu.
"Hhh! Wane ganganci da ƙarar kwana yayi Sanadin kawoku cikin jejin nan, kamar yadda muka
rasa rayuwarmu muka koma fatalwa haka kuma zaku rasa taku rayuwar bazaku taba fita a jejin
nan ba."
Kawunansu suka ɗaga suna ƙarema halittar kallo, sanye take da farar riga da tayi face_face da
jini, ilahirin jikin ta farine sol idanuwanta babu ɗugon baƙi ko kaɗan ga dogayen hannuwa masu
ɗauke da farata