Showing 18001 words to 21000 words out of 31939 words

Chapter 7 - BAKAR TAFIYA BY MEENAT A YANDOMA.pdf

wuyanta suka yo aguje.

Jamcy ta yagi rigarta ta ɗaure mata raunin Jafar ya tofa mata addu'o'in suna mata sannu.


Basu ɗauki lokaci ba Jamcy ta kamo Basma suka bar wurin saboda ganin abinda ya faru.
(Ni nace Su Jamcy ina aka baro faɗan ko harkun sauko Hanya mai haɗin zumuntar dole)

Tafiya suke batare da sanin inda suke nufa ba.

Ga wata ƙishirwa da ta addabesu kamar su zube.

Wata inuwa suka samu domin su huta saboda zafin ranar da ake zubawa.


Tunaninsu ɗaya shine imna zasu sami abinda zasu ci dazai Gusar masu ƙishin da suke ji.

Ƙarar faɗuwar wani Abu sukaji a bayansu, Suna juyawa sukaga bishiyar kwakwa ce gasunan
sun nuna manya sun Zubo ƙasa birjik.

Kallon_kallo suke an rasa wazai je ya kwaso masu suci.


Jafar ne yayi ƙarfin hali yayi addu'a ya duƙa ya fara tsinta yana tarawa.


Sai da ya tsinto masu mai yawa ya fara fasawa sukayi Basmala suna shanye ruwan ciki.

Sai da suka gama shanye ruwan sannan suka fara cin kwakwar.

Sunci sun ƙoshi lokaci ɗaya sukaji wani irin bacci na ɗibarsu, kwanciya sukayi domin su huta
Jafar yayi Basmala tare da kwanciya.

Tunkafin baccin ya ida ɗaukarsu sukaji iska mai ƙarfi tana iso inda suke, kafin su ankara wata
irin guguwa mai matuƙar ƙarfi ta kwashesu tayi sama dasu......

_____________________________
...............Abinda suka gani shi yakusa sanadiyyar datsewar numfashinsu.


Tsintar kansu sukayi a saman wani ƙaton tsauni wanda ƙasanshi ya kasance wasu irin
itatuwane masu tsawo naban mamaki, itatuwan sune zaka kama ganyayensu masu tsananin
faɗi da ƙauri da suka rufe saman tsaunin In kana da sa'a ka isa ƙasan tsanin da rayuwarka.




Gashi duk iyakar hangensu sun duba amma basuga Wata hanyaba saidai wannan.

Tafiya sukaji tamkar irinta ƙwaro in ya doso inda kake.

Amatuƙar firgice suka juyo danganema idanunsu mike faru.


Wasu irin ƙwarine masu kama da gizogizo.


Idanunsu jajur tamkar garwashin wuta, ga jikinsu duk wani irin gashi abun kwanin ban bantsoro.



Wani yawu suka haɗe atare ƙuutt!, Salma da Rabson tuni suka rungume juna suna salallami
kamar basu bane suka gama gwabza faɗa ɗazu.


Ƙwari gudu suke suna ƙoƙarin isowa wurinsu Biba, ganin haka ya sanya su Biba ja da baya har
suka iso ƙarshen ramin, ganin basuda wata mafita lokaci ɗaya tamkar sun haɗa baku suduka
suka daka tsalle sukayi ƙasan ramin.


Ganin haka ƙwarin suka mara masu baya.

Saman ganye ɗaya suka faɗa su dukan su suna rarraba ido da tsananin mamakin wannan
wane irin ganyen bishiyane?.


Basu ankara ba sukaji dirowar ƙwarin saman ganyen.


Suna son miƙewa amma tsoron in suka tashi tsaye tabbas sil6in ganyen zai kayar dasu.


Rabson da dai yaga bashakka in suka tsaya mutuwa zasuyi, wuf! Yayi ya miƙe "Ku miƙe muyi ta
kanmu, bashakka in muka tsaya ƙwarin can zasu zuƙe jinin jikinmu abanza."


"Kai kam bakada tunani arayuwar, yanzu in bayaga kanada tunani irin na bunsurunka ta ina
zamu gudu bakaga ƙasa rami bane?."
Salma ta ida maganar tana aikoma Rabson da kallon raini.


"Hhh, sai shegen surutu kamar aku, ja'ira mai zubin muciya baki kamar na agwagwa, nan
gabafa nine mijinki kuma Oga awurinki kisan irin maganar da zaki riƙa furta mani."
Ya ƙarashe maganar yana dariyar mugunta dan yasan ya gama tunzura Salma.

Ashar ta mulmula ta dura mashi tana Allah ya tsareta da auren faƙiri talaka irinshi.


Biba da taga faɗan nasu bamai ƙarewa bane tsalle ta daka tayi ƙasan ramin.

Bayanta suka bi suma, saman ganyayyaki suka riƙa faɗawa kafinsu ida isa saman wani ganyen
sul6i ya kwashesu sunyi ƙasa, haka aka riƙa tilli_tilli dasu.


Masu ihu nayi masu addu'a nayi.

Rabson daya bugu kanshi ya fara juyawa idanunshi suka fara hango mashi mutane suna
komawa bibbiyu.
"Ƙalu innalillahi, la'ilaha'illallahu, shikenan namakance nalalace wayyoh busurulle wayyoh kaka
uwata,Salma masoyiyi bibbiyu nike ganinku, lokacina yayi wayyon nazama makaho, yau Rabi'u
nike ba Rabson ba namakance nadaina gani shikenan nayi Expired Salma ko auren mukayi
saidai ki riƙa yimani jagora, inkuma namutu inkin koma gida kice ɗan busurulle Nabarma kakata
ta yanka ta cinama ta ƙoshi, wayyoh nazama makaho."

( Wuya ba daɗi, yaji wuya ya ɗauka makancewa yayi)

Duk da har yanzu gwarasu ake sunayin ƙasa masifar dake cin Salma saida ta tanka.
"Allah ya ida makantar da kai, bakinka yasari ɗanyen kashi, mai muguwar fata,kaga ɗan
bunsunru can inka mutu."
Bugata da akayi ta bugu da reshen wani icce ya sanyata yin shiru ta sume a take.

Sai da aka kawosu ƙarshen ramin suka faɗo tim! Batare da sanin inda kansu yake ba.

Wata guguwa mai masifar ƙarfi ta kwashesu tayi sararin samaniya dasu......



A haɗa da haƙuri Har yanzu kwance nike, ƙarfin hali yasa nai maku wannan.






**COMMENT* ✅
*SHARE*✅













*_MEEN@RT...✍_*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: *BAƘAR TAFIYA*

( *HORROR STORY* )

*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*️


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*SALONSHI NA DABAN NE *


*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI
RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA
ABBANA*


*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN,
ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*

‍♀️‍♀️‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI
NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*


*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON
BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH
YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA
MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA
BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.*

_____________________________
*PAGE 22_23*


..................Iskar lokaci ɗaya ta tsaya tamkar anyi ruwa an ɗauke.

Ganin waɗannan halittu ba ƙaramin dugunzuma hankalinsu Basma yayiba.

Jamcy da Basma tuni suka runƙunƙume juna jikinsu na mazari.

Wata mahaukaciyar dariya suka fashe da ida, wadda ta haddasama dajin. Girgiza.
"Kun ɗauka zaku iya guje mana ne,kunyi kuskure yanzu zaku girbi abinda kuka shuka ."

Asuƙwane suka yo kan su Jafar tamkar yunwatattun zakunan da suka shekara basuci abunci
ba.

Muggan makaman dake hannuwansu Suka fara kaima su Jafar hari da su.

Kowa kagani wurin takanshi yake yana ƙoƙarin ceton rayuwarshi.

In suka kawoma mutum harida makaman hannunsu ya kauce ya samu wani icce take iccen
yake darewa gida biyu, in ƙasa ce makamin yasama sai dai kaga wurin yayi rami.

Basma da Jamcy wani Aljani yayo kansu da mugun nufi , sun riga sun sadakar yau kwanansu
ya ƙare jira kaiwai suke ya iso garesu.


Shurun da sukaji ta sanyasu buɗe idanunsu cikin kaɗuwa.


Ganin Jafar sukayi tsaye riƙe da wani abu mai kama sa sanda gefenshi gawawwakin Aljanun
nan yayi nasarar kashe wasu.

Cikin kakkausar murya ya fara magana.
"Yanzu ba lokacin tsoro bane, lokacine na tashi muyi fafutukar tseratar da rayukan mu ko mu
mutu ko muyi rai, dan haka ku kasance masu ruƙo da addu'a domin ta tasa nayi nasarar kashe
wasu daga cikin Aljanun nan dako taruwa mukayi bazamu iya yaƙarsu ba,amma saboda tasirin
addu'a gashinan Ubangiji yasa nayi masarar kashesu, dan haka kumiƙe kuceci rayuwarku ko
kuma kuyi asararta nan bada jimawaba."
Yana ƙarashe maganar yayi wurin sauran Maridan bakinshi ɗauke da kabbara.


Kafin Maridan su ankara Jafar yayi masu gagarumar 6annan domin dayayi kabbara yadaka
tsalle ya kaima tsakiyar bayan Aljani bugu saidai kaga yayi kururuwa ya zube ƙasa matacce.


Ganin irin illar da Jafar ke masu yasa mukayo kanshi da mugun nufin su raba kanshi da gangar
jikinshi.


Addu'a yaci gaba da kwararowa abakinshi yana mai dogaro ga ubangijin shi tare da naiman
ɗaukinshi.


Ƙarfin kabbarar da yake ta sanya Aljanun wasunsu yada makamai suna toshe kunnuwansu
domin ji suke tamkar ana zuba masu ruwan tafasashshiyayar darma a kunnuwansu, ganin haka

su Tk dake boye a mabanbantan wurare yin koyi dashi suna masu ɗaga murya tareda ƙwala
kabbara.


Damar da Jafar ya samu ga Aljanun ta sanyashi ƙara ƙaimi wurin ragargazar aljanun, cikin ikon
Allah yayi nasarar ƙararda Aljanun wasu kuma suka 6ace.

Iya jigatuwa Jafar ya jigata ga wata yanka da wani Aljani ya shammaceshi yayi mashi a hannu,
yana gama faɗan ya yanke jiki ya faɗi.


Tk ganin Jafar ya ƙarar da Aljanun ya sanyashi fitowa suka yo kan Jafar.

Duk iya ƙoƙarin su akan jafar da wani taimako da zasu bashi sunyi, ga hannunshi dake zubda
jini, Tk rigarshi ya yaga ya ɗaurema Jafar hannu yayi nasarar tsaida jinin, sunyi duk abubuwan
da suka san anayi ma wanda ya suma domin ya tashi amma abin yaci tura domin ba alamun zai
tashi.

Sunyi jigum_jigum suna tunanin halinda zasu shiga indai da gaske Jafar mutuwa yayi to
bashakka kashinsu ya bushe a tafiyar nan.

Sunan nan zaune jikinsu ya gama mutuwa, zuciyoyinsu sun sadaƙar lallai Jafar bazai tashiba,
ga duhun magriba daya farayi wurin ya ɗauki wani irin sanyi mai shiga ƙashi.


Hannunshi dake ɗaure yafara motsawa a hankali yana ƙoƙarin buɗe idanunshi bakinshi ɗauke
da addu'a.


Ganin haka yasa su Tk sukayo kanshi zuciyoyinsu cike da wani irin farin ciki marar misaltuwa.


Kamashi Tk yayi ya ida miƙewa zaune.

Sannu suke ta keta kwararo mashi yana binsu da yawwa.


Sai da Jafar ya ida dawowa cikin hankalinshi sannan ya umarcesu dasu tashi suci gaba da
tafiya, domin zama bai gansu ba.


Tafiya suke ga duhu daya yayi tsayawa sukayi sukai taimama suka gabatar da sallolin da aka

biyo su.

Ƙara nausawa sukayi cikin jejin duk da yunwar da ta addabesu ga matsanancin sanyin da ake
zubawa hakan bai hanasu cigaba da tafiyaba.


Yada zango sukayi saboda baccin daya rinjayi idanuwansu.

Wurine mai yalwar ciyayi ko ina ka wurga idonka lullube yake da ciyawa tamkar cikin yanayin
damuna.

Kwantawa sujayi Jafar ya umarci kowanensu da yayi addu'ar kwanciya bacci kafin ya kwanta.


Bayan kwanciyarsu Jafar ya warware hannunshi domin ganin yadda raunin ya koma.


Abunda ya tada mashi hankali kuma ya bashi mamaki bai wuce ganin yayi wani irin rami tamkar
an yanke fatar wurin, addu'o'i yacigaba da kwararowa yana tofama raunin domin yasan babu
abinda ya gagari Allah.

Kowa yayi bacci wurin in banda Jafar da sai da yatofe jikinshi da addu'a ya kuma tofe inda suke
kwance ya kakka6e inda zai kwanta ya kwanta bakinshi ɗauke da Basmala.

Wurin yayi tsi! Bakajin motsin komi sai munsharin da Tk ke yi kamar wani bujimin sa.


A hankali wata irin iska mai kaɗawa cikin natsuwa ta gauraye wurin, ciyawar dake ƙasan wurin
a hankali ta fara kaɗawa rana motsawa, Bayyana sukayi cikin muguwar suffar mai tsananin ban
tsoro.


Rashin sani yafi dare duhu, domin dasu Jafar sun san inda suk kawo kawunansu da tuni tun bar
wurin.


Tsaye suke jikinsu baida maraba da jikin Fatalwa, gasu wasu irin dogaye fuskarnan tasu ba
kyangani idanunsu guda ukku jere reras basuda hanci sai wani irin bakuna tanan suke shaƙar
iska, fuskar su cike take da gashinda yayi nasarar lullu6e ilahirin fuskar,ga jikinsu sanye da
wasu fararen kaya da jini yayi nasarar mai dasu jajaye.
Cikin tsananin 6acin rai macen takawo hannu da nufin ta ɗauko Jafar ta tsotse jininshi, sai dai
mi, hannun na ida isa inda Jafar ke kwance taji wani irin zafi Kamar ta sanya hannunta cikin

Wuta, bashiri tayo baya tana mai yarfa hannunta da fatar wurin ta dare jini Ya fara zuba.


Ganin abinda ya samu matar ya Sanya mijin zura hannuwanshi biyu da nufin ya tattaro su Jafar
su duka ya hallakasu.


Abinda yaji yasanyashi ja da baya ga hannuwanshi dasuka fara ƙonewa.

Yaja matarshi suna mamakin abinda ya yi masu shamaki da kashe waɗan nan halittu, bacewa
sukayi zuciyoyinsu cike da ƙudirin ɗaukar fansa.

Kamar cikim bacci Jafar yaji hayaniya amma yana buɗe idonshi yaga babu kowa.


Addu'a ya ƙarayi tare da komawa ya kwanta.


Sanyin asubar daya ratsasu shine yayi nasarar farkawarsu daga bacci,buɗe raunin hannunshi
Jafar yayi, abun msmaki raunin nan ya warke tamkar bai ta6ajin ciwoba wurin, taimama sukayi
suka kabbara sallah bayan sun gama suka zauna suna tunanin inda zasu samu abinda zasu
sama bakinsu.
Gari na ida yin haske suka tafi naiman abinda zasuci.

Ƙoramace mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, kana hango yadda kifaye ke wasansu saboda
ruwan ba zurfi.

Shawara suka yanke sukama kifayen su gasa su ci.

Jafar da Tk su suka shi suka samu wasu dogayen tsinkunan icce suka riƙa chako kifayen dashi.

Basma da Jamcy suna daga wajen ruwan suna kallonsu, Basma jitayi kamar ankira sunanta
waigawa tayi tareda hango wasu kyawawan kifaye sunata iyo nesa kaɗan da inda su Jafar suke
kama kifayen.

Zuciyarta kwadaituwa tayi data matsa taganema idanunta waɗannan kifaye, duƙawar da zatayi
domin ta kamo kifin Taji an fizgi wuyanta anyi Cikin ruwan da ita, ƙarar faɗuwar ta tajawo
hankakinsu Jafar suka nufo inda take aguje, abinda suka gani ne yasanya numfashinsu yakusa
ɗaukewa na wucin gadi, Mandiya suka gani kamanninta sun koma na horror, ƙarar dasukaji
Basma ta ƙwala ce ta dawo dasu cikin hankalinsu, Mandiya suka gani ta kasama Basma haƙora
awuya jini yafara malala, wata wahalallar ƙara Basma ta Ƙwala......................

______________________________
Gudun ceton rai su Rabson suke tamkar zasu tashi sama ga waɗannan halittu Dasun Juya sai
suka sun kusa cimmasu.


Abinda basu saniba halittun nan kamar fara haka suke Tashi sama.

Basu ankaraba sai gani sukayi halittun nan sun dira gabansu, ja sukayi suka tsaya kafin su
ankara halittunnan sun lullu6esu tamkar yadda fara ke lullu6e ganye.

Biba gani tayi halittun nan da ƙarfi taɗaga murya tana ƙwararo addu'a tana kai masu naushi da
hannuwanta, duk wadda ta kaima bugu saida kaga tafaɗi ƙasa ƙasusuwanta sun karairaye.

Rabson dayaga biyu sunyo kanshi gudu yafara kafin ya ankara sun wawuro ƙafafunshi, ganin
sun buɗe baki sunyo kanshi ya fara ihu yana karanto duk addu'ar da tazo bakinshi
"Innalillahi, la'ilaha illallahu, inna ansarnahu, amanarrasulu, wayyo kaka ɗan bunsurulle, wayyo
Salma masoyiya ku kawo mani ɗauki."
Haka yaita ihu, ganin babu mai cetonshi yafara gano mutuwa ido buɗe yasa ya dage iyakar
ƙarfinshi yana kaima halittun harbi da ƙafafunshi.

Kulu da Nas wuri ɗaya suka haɗe Nas ganin halittun sun nufoshi Ya koma bayan Kulu yana.
"Kulu ki taimaka mani wayyoh Allah innalillahi nashiga ukku, Kulu kin cuceni da kikasa mukayi
wannan Baƙar tafiyar."
Yaƙarashe maganar yana ƙara shigewa jikon Kulu.

Ganin addu'ar da Biba tayi Allah ya kawo mata mafita, ta ɗaga murya tana mai umarta su
Rabso dasuyi koyi da ita.

Sunjigatu sun matuƙar jin jiki kafin suyi nasarar gamawa da halittun.

Fuskar kowa tasha karta duk sawune jiki in banda Biba.

Bayan sun sun dawo cikin hankalinsu Rabson yayi ƙarfin halin miƙewa.
"Kun lura kuwa har yanzu muna cikin kogon nan? Kamata yayi mubar kogon nan nidai bazan
tsaya in mutu a banza ba."
Ya ida maganar yana dudduba inda Salma ta shige.


Chan ya hangota ta tayi ɗai ɗaya a ƙasa tana maida numfashi.
"Hhh, Salma masoyiya kece kika zama haka?, kinga yadda kikayi buɗu_buɗu, wayyo masoyiya
miya karceki a fuska taimaka kitashi muƙarasa fita."
Ya ƙarashe maganar yana yimata dariyar mugunta.

"Allah ya isa inka ƙara kirana Masoyiyarka, mugu mai suffar mutanen 6oye."
Taƙarashe maganar tana ƙoƙarin miƙewa.

Baikulata ba dariyarshi yacigaba dayi.

Kulu kallon Nas tayi tare da jan dogon tsoki.
"An daiji kunya, kabani mamaki lusarin banza kawai wanda mace ma tafishi jarunta."
Ta kuma jan wani tsokin.

"Am..uhm..kingane Kululu wallahi kawai kinsan ni ina tsoron ƙwarangwal, amma kin gane kibari
a karo nagaba zani baki mamaki, haba my sweet Kululunah."
Ya ƙarashe maganar da daɗin baki.



"Allah dai yasa da gaske kake."
Tafaɗa tana yamutsa fuska domin yau Nas ya matuƙar bata haushi.

Sun yi yawo cikin kogon harsun gaji basu samu hanya ba.



Har sun haƙura da fita daga kogon sai suka hango wata ƴar hanya ƙarama wadda mutum ɗaya
zai iyabi ya wuce, haka suka riƙa fita da ɗai ɗaya.



Ganin sun fita kogon wani irin farin ciki ya baibaye zuciyoyinsu.


Abinda idanuwansu suka hango masu ne yasasu ja da baya cikin matsanancin tashin hankali
da kuma tsoro...........

*COMMENT*✅
*SHARE*✅














*MEEN@RT...✍*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: *BAƘAR TAFIYA*

( *HORROR STORY* )

*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*️


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*SALONSHI NA DABAN NE *


*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI
RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA
ABBANA*


*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN,
ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*

‍♀️‍♀️‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI

NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*


*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON
BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login