Showing 12001 words to 15000 words out of 31939 words
dogaye masu tsananin tsini, doguwace sosai tsaye take saman iska kamar
tsuntsu doguwar rigar dake jikinta dogowace har ƙasa shiyasa ko ƙafafunta baka iya hangowa.
Jikin su Mandiya da Basma tuni ya hau mazari.
Jafar ji yayi kamar an sanya sarƙoƙi an ɗaure bakinshi addu'ar ma ya kasa gurta koda kalma
ɗaya.
Wannan damar Fatalwar ta samu ta nunasu da yatsa wani farin hayaƙi yafito ya zama guguwa
yayi sama dasu Jafar.
Tamkar yadda fanka ke wulwulawa haka aka riƙa wulwula su Mandiya tun suna ihu har ƙarfinsu
ya ƙare sukayi tsit iskar ta watsar da su wani bangare daga cikin jejin batare da sun san mike
faruwa ba.
___________________
Kamar yunwa taccen zaki haka Audu yayo kan Salma da tayi mutuwar.
Tariga ta bada sadaƙar yau kwananta ya ƙare jira kawai take ya kasheta ta huta.
Kamar daga sama sukaji ƙarar wani abu kamar an buga bindiga.
Mace da namiji suka gani tsaye gabansu da wani abu kamar sanda a hannunsu.
Dubansu suka kai ga audu dake kwance ƙasa yanata bullayi da alamu ƙoƙarin tashi yake.
Mace tace dasu Biba mubar wurin nan kafin ya tashi domin gaf dake da miƙewa.
Su duka suka bar wurin suka yi wata siririyar hanya da guda.
Gudu suke ba ƙaƙƙautawa tamkar bazasu tsaya ba.
Ganin sunzo wurin wata gadar icce suka ja suka tsaya suna maida numfashi.
Rabson da sai yanzu hankalinshi ya dawo jikinshi ganin bakin fuska ya sanyashi yin tsalle ya
koma gefe.
"Innahu min sulaimanu...., bayin Allah mutane ko aljannu, daga ina kuke mijya kawoku jejin
nan?, ko dai kuma Horror ɗinne sukazo mana da taku salon yaudarar?."
Namijin daya gama ƙuluwa ya watsama Rabson kallon zaka gane kurenka.
Macen tayi ƙarfin halin fara magana.
"Tsautsayi ne da rabon wahala ya fiddomu daga gida har muka tsinci kanmu cikin Wannan
halin, ni sunana Kulu amma ana kirana Kulu ganin ƙwam, sai abokin tafiyata sunanshi Nasir, sai
kuma abokan tafiyar mu su biyu da suka bace mana Jamcy da Tukur muna kiranshi Tk, mun
kasance masu son kallon abubuwar mamaki ne, Rannan malamin mu na mana lecture yake
sanar damu wannan jajin da haɗarindake tattare dashi, da kuma abubuwan mamakin dake
cikinshi tundaga lokacin muka yanke shawarar guduwa daga gidajenmu domin muzo ganin
abubuwan Al ajabi, mu hudu haka muka shigo dajin nan bala in da muka shiga ya sanya muka
rabu da abokan tafiyarmu batareda mun saniba.
Halin da suke ciki bai hana Rabson fashewa da dariya jin waɗan da suka fisu gantalewa, Nas a
fusace ya taso ganin Rabson ya raina masu wayo, cikin hanzari kulu ta tareshi tana bashi
haƙuri.
Rabson kallon Salma yayi gsnin yadda bakinta yayi Suntum ya haye ga goshinta daya yi
ranƙwalele.
Sake fashewa yayi da dariya yana riƙe ciki, yana nuna Salma da hannu yanaci gaba da dariya.
Tamkar zata kai mashi bugu haka Salma tayo kan Rabson, Biba tayi saurin riƙeta tana bata
haƙuri, ashar kawai take dannoma Rabson amma bai daina dariyar ba.
"Haba Rabi'u! Miye haka Kana ta taƙular mutane bakaga halin da muke cikiba amma har kuke
ƙoƙarin fada?."
Bai daina dariyarba yaci gaba da magana"Habibalo kiyi haƙuri wallahi inna kalli bakin Salma
yadda yayi tsawo kamar shantu bani iya danne dariyata, masoyiyita Salma kiyi haƙuri kinji nifa
tunda muka shigo jejin nan nike jin ƙaunarki na ratsa jinin jikina."
Ya ƙarashe maganar yana dariya.
Salma kamar ana zugata haka ta riƙa zagin Rabson tana fadar tafi ƙarfin tayi soyayyah dashi,
da Ƙyar Biba ta shawo kan Salma tayi shiru.
Gurnanin da sukaji bayansu ya sanya bashiri suka fara bi ta saman gadar katakon ba shiri.
Doguwar gadace wadda aka ƙerata da katako gefe da gefe kuma iggiyace wadda zaka riƙe
hangu da dama, kasanta ramine mai tsananin zurfi baka iya hango ƙarshenshi.
Tafiya suke da sauri Rabson na taka wani katako ya balle yayi ƙasa , lokaci ɗaya gadar ta fara
karairayewa ta yin ƙasa, hankulansu atashe wasu suka fara ihu, wasu suna addu'o'i.
Rabson atake ya fara bada wasiyyah yana;
"Salma masoyiyata inkin samu komawa gida kice ma Kaka na barmata ɗan bunsuru na duniya
da lahira ta yafe mani , wayyoh kaka lokacin mutuwata yayi."
Igiyoyin gefen gadar suka rirriƙe suna gudu gadar na ƙara karairayewa.........
*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅
*MEEN@RT...✍*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: *BAƘAR TAFIYA*
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE *
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI
RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA
ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN,
ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
♀️♀️♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI
NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
*WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN
ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA*
*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON
BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH
YA ƘARA DAƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA
MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA
BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.*
____________________
*PAGE 16_17*
........Sanyin da sukaji yana ratsa fatar jikinsu ya sanyasu fara bude idanunsu.
Jamcy da Tk dake tsaye kansu da wani icce ahannuwan su, suna jiran farkar warsu, a
tunaninsu suma Horror ne lambo sukayi masu.
A firgice suka miƙe, Mandiya ganin mutane biyu saman kanta ya sanyata kwala ihu cikin
tsananin kaɗuwa, kafin ta rufe baki Jamcy dake tsaye kanta atunaninta horror ce bata 6ata
lokaci ta kwadama Mandiya sandar nan, a take Mandiya ta baje ƙasa a sume.
Sallallami su Jafar suka hauyi tare da yo kan Mandiya.
"Mutane ko Aljanu?, mikuke naima awajenmu da har kuka sumar da abokiyar tafiyarmu."
Tk da idanunsu suka raina fata cikin ƙarfin hali ya fara jawabi.
Nan ya kwashe komi ya fada masu har batan abokan tafiyarsu wato Kulu da Nas.
Sun yi matuƙar mamakin ƙarfin hali irin nasu Jamcy, kawai saboda ganin ƙwam irin nasu zasu
baro gida.
Mandiya da ta samu ta farfaɗo buya tayi bayan Basma tana mai da numfashi.
Bata yarda dasu Jamcy ba sai da Jafar yayi da gaske sannan ta yadda su ɗin mutane ne.
( Niko nace Mandiya anji sambaɗebaɗe)
Wurin da suke wurine mai wuyar misaltawa, domin tunda suka fara tafiya basu taba tsintar
kawunan su a irin wannan wurin ba.
Tsabar duhuwar dake wurin tamkar dare ya fara haka yanayin wurin yake.
Kallon_kallo suka shiga yi, tamkar yau suka fara ganin juna.
Da dai sukaga basu da wata mafita face su ci gaba da tafiya, miƙewa sukayi tare da kakka6e
jikinsu suna makyarkyata saboda tsananin sanyin da ake zabgawa wurin.
Mandiya kai ko ɗan kwali babu ga kitson attach ansha ga kayan jikinta sun matseta, Basma riga
da siket ne jikinta wanda suka sha ɗinki yayi rigar nan daga sama ta matse ƙasa kuma ta buɗe,
ga siket ɗin irin wanda ƴan mata ke yayi wanda ake kira mai guiwa.
Uwa uba Jamcy da ta takesu wurin wayewa zamuce ko gantalewa, jikinta T.shirt ce ta ɗan kawo
guiwa sai wandon ta jins wato crazy wanda matasanmu ke yayi.
(Wasu mutanen ganewace basuyiba wani fa inya kalleka bada halayenka zai duba ya gano kai
waye ba, shigar jikinka ita zai fara kallo yayi maka hisabi, dan haka musan irin shigar da zamu
riƙayi, in bakajin tsoron Allah to akwai lalatattun mutane in babu su akwai Shaiɗanun Aljanu.)
Tafiya suke suna bankar juna saboda sanyin da suke ji bakunan su har farin hayaƙi ke fita.
Tun suna tafiya iyakar ƙarfinsu har ƙarfin ya ƙare suka koma jan ƙafa.
Tsayawa suka yi da tafiyar tare da bajewa ƙasa suna huttai.
Ga yunwa ga ƙishirwa da basu iya tantance yaushe rabon da su kai wani abu bakinsu.
Fashewa da kuka Basma tayi tana faɗar;
"Wayyo mijina! Wayyo gidan aurena, shikenan a haka zani ƙare nayi bankwana da asuwaki da
cinyoyin kaji gani nan abinda zanisa cikina yana gagarata,da gida nike da ina chan ina asuwaki
da naman kaji abinci sai wanda naga damarci, amma yanzu ganinan na ƙare a daji,Ta gaban
goshi Allah ya isa tsakanina dake da kika turani na bijiirema maganar Habib nafito damin
halartar bikinki, Wayyo Ɗana wayyo mijina."
Haka taita sambatu tana kuka kamar ta 6a66a.
Kece wa da dariya Jamcy tayi tareda kallon Basma.
"To la'anan na mai kama da ƴa'ƴan yahudawa wakikema dariya?."
Ci gaba da dariyar Jamcy tayi ta nuna Basma da yatsa.
"Wa fa nike ma dariya in ba ke ba, tsabar gantali da aurenki amma kika baro mijinki kika taho
bikin wata ƙawa."
Ashariya Basma ta tattaro ta ɗurama Jamcy tare da miƙewa tayo kanta gadan_gadan.
Da ƙyar Jafar yayi nasarar raba wannan faɗan daya yaso barkewa.
Ƙutawa kawai Basma keyi tana hararar Jamcy, ita kau Jamcy da sun haɗa ido saitayima Basma
kwalo tana mata dariya.
Iya ƙuluwa ta ƙulu da Jamcy, jira kawai take Jafar ya ɗan kauce tasamu sa'ar tumurmusa
Jamcy.
Jafar daya lura Tk ɗan zafin kai ne tunda suka haɗu sai wani shan ƙamshi yake yana hura
hanci.
"Tk ka taso muɗan zagaya cikin jejin nan musamu abinda zamu sama cikunnan mu."
Kallon up and down Tk yayima Jafar.
"Ok muje."
Yafaɗa yana yamutsa fuska kamar yaga kashi.
"Ku su Basma ku tsaya nan kujiramu mu dawo."
Tsalle Mandiya tayi ta dire ita bazata tsaya nan ba wani abu yazo ya hallakata.
Suma sauran mara mata baya akan bazasu zauna ba.
Sunyi tafiya mai ɗan tsayi suka iso wani wuri mai yalwar ganyayen bishiyoyi.
"Laaah! Kuduba ku gani chocolate da sweet a chan."
Dubansu suka kai wurin suna masu mamaki ganin kayan daɗin da ko a cikin gari sai kanada
manyan kuɗi zaka mallakesu.
Hannun Jamcy Tk ya kamo saboda yasan mayyar kayan zaƙice.
"Sweety ka sakeni in ɗauko, kasan fa yadda nike bala'in son chocolate."
"Aa ƙaunata kada ki ɗauka zai iyafa cutar mani dake, kinsan da wani abu ya sameki ƙara ni ya
sameni."
Shamatarshi tayi ta fizge ta ruga tana dariya ta nufi wurin chocolate ɗin.
Kafin hannunta ya ida isaga chocolate ɗin tuni sun rikiɗe sun koma wani jibgegen baƙin kumurci
ya fasa kai yayo kanta.
"Nashiga ukku nalalace, Sweety ka kawo mani ɗauki wayyo na bani ni Jamilatu."
Cikin firgici da hargagi yake faɗar" kada ki motsa ƙaunata gani nan zuwa gareki."
Cikin zafin nama ya jawo Jamcy suka ɗiba ana kare,su Jafar take masu baya sukayi, ganin
haka macijin ya bi bayansu.
Abinda suka lura macijin yabar binsu sai yanayin wurin daya chanza duhun wurin ya ƙaru.
Ƙarar tsuntsaye sukaji saman kawunansu.
Ɗaga kan da zasuyi suka ga Wasu irin jibga_jibgan tsuntsaye masu suffar jemage sai dai su
sunfi jemage girma da suffa mai ban tsoro.
Ganin haka suka ƙara ƙaimi wurin gudun, tsuntsayen na biye dasu.
Ƙarar da sukaji an kwala ce ta sanyasu tsagaitawa da gudun suka juyo, Basma suka gani
tsuntsayen sun sureta sunyi sama da ita...........
____________________
........Gudu suke gadar na ƙara karairayewa, sunyi nasarar ida ƙara sawa ƙarshen gadar, suna
ida tsallaketa tana Rubzawa ƙasa.
Duƙawa sukayi wurin wasu kuma suka baje suna maida numfashi.
Mtsw Salma taja dogon tsoki.
"Aikin banza mutum gashi nan mugun rago da anshiga bala'i sai ya hau ihu yana cika ma
mutane kunnuwa yen_yen_yen, mtsw sauna kawai."
Fashewa Rabson ya ƙarayi da dariya.
"Bakomi masoyiyata mai bakin shantu, kin ga yadda bakinki ke ƙara tsayi da kina kwaikwayar
maganata kuwa."
A fusace ta nufo inda yake tana zazzaga masifa.
Ganin da gaske take ya sanya Rabso fara magana.
"Masoyiya kina ƙarasowa wurin nan zani chakumeki muyi ƙasan ramin nan muyi mutuwar
shahada irinta masoya."
Ya ƙarashe maganar yana ƙyalƙyalewa da dariya.
Tsayawa tayi daga nesa tana aiko mashi da baƙaƙen maganganu.
"Heeey! Yau ni naga marasa hankali, yanzu ku a halinda muke ciki har kunada bakunan yimana
faɗa, to duk ɗan....Ta ɗura wata ashariya Daya ƙara mana fada saina hankaɗashi ya faɗa cikin
ramin nan."
Kulu ta fada tana nuna Salma da yatsa.
"To ɗiyar matsiyata waya sako dake?, gantalalliya uwar ƴan yawon ganin ƙwaf."
Salma ta ƙarashe maganar kamar zata kai ma Kulu bugu.
"Wa'iyazubillah! Ku kam ko gasar ƙunduma ashariya muka fito sai haka, abinda ya kamata mu
dage da addu'a amma kun dage sai zagi da ashar kuke ɗurawa, kuyima kanku faɗa kufa ƴa'Ƴan
musulmai ne."
Shiru suka yi kowa na hararar ɗan uwanshi.
"Haba babynah, ki rabu da ita Ke ba sa'ar yinta bace."
Nas ya karashe maganar da sigar rarrashi.
Nausawa suka kuma yi ciki dajin suna rarraba idanu.
A hankali wata iska ta fara kaɗawa tamkar irin in hadari ya fara tasowa.
Jin wannan baƙon lamari ya sanya suka ƙara matsewa wuri ɗaya.
Duhu wurin ya farayi tamkar ruwan sama zai balle.
Gudu suka farayi suna sassarfa,kafin su ankara an kece da wani irin mamakon ruwan sama mai
haɗe da iska mai ƙarfin gaske.
Gudu suke idanunsu rufe basu ganin gabansu saboda Iskar da ake, wani wawakeken kogon
dutse suka gani basu yi wata shawara ba suka afka cikinshi, suna ida shigewa ƙofar kogon
Wani dutse ya tugo ya rufeta garam!......
*NIMA KAI NA JIN ƘARAR RUFEWAR ƘOFAR SAI DA WAYATA TA KUSA KUFCEWA*
*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅
*MEEN@RT...✍*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: *BAƘAR TAFIYA*
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE *
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI
RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA
ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN,
ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
♀️♀️♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI
NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*
*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON
BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH
YA ƘARA DAƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA
MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA
BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.*
*NASADAUKAR DA WANNAN PAHE ƊIN GAREKI KHADIJA S SAMSHARE AR GATAN
MAMA, ALLAH YA ƘARA ZAƘIN HANNU*
______________________
*PAGE 18_19*
.........Ihu Basma keyi tana naiman agajin su Jafar.
Lokaci guda ƙwalwarta ta fara tunano mata inda Ammar ya basu addu'a insun shiga bala'i.
"LA'ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN."
Basma ta furta da ƙarfin gaske.
Tsunsun jiyayi kamar ya ta ɗauko garwashin wuta, bai bata lokaciba ya sakota ƙasa shida
sauran ƴan uwanshi suka bace bat! Kamar basu ta6a wanzuwa a wurinba.
Duk da buguwar da Basma tayi sanadiyyar faɗowar da ta yi amma haka ta miƙe tana gudu tana
ɗingishi.
Tun kafin dare yayi sosai suke gudu har saida duhun dare ya raba sannan suka zube suna
maida numfashi.
"Wayyoh! Zani mutu, wayyo Umma na, na shiga ukku, shikenan mu haka zamu dawwama cikin
bala'i muna mutuwa ɗaya bayan ɗaya, koda waɗan nan Aljanun basu kashemu ba yunwar cikin
mu kaɗai ta isa tayi sanadin mutuwarmu, wayyo Ummana shikenan bazan ƙara
ganinkiba."Jamcy ta ƙarashe maganar tana harba ƙafafu a ƙasa kamar ƙaramar yarinya tana
kuka tana kuka.
Tk jiyayi kamar ya mangare Jamcy, amma soyayyar daya ke mata bazata bari ya iya yi mata
komiba.
Dare ya raba sosai ga wani irin sanyi da ilahirin dajin ya ɗauka.
Matan su duka haɗe suke wuri ɗaya suna gyangyaɗi ga kyarmar sanyi sunayi.
Tk da Jafar wuri suka gyara da hannuwansu tareda kwantawa.
Wuri yayi tsit! Bakajin mitsin komi sai kuka tsuntsaye, bacci yayi nasarar sace su.
Cikin Bacci Basma taji kamar ana ja mata ƙafa, ƙara gyara kwanciyarta tayi.
Fizgar ƙafar akayi da ƙarfin gaske aka jawota daga inda take kwance.
Ƙara ta ƙala da tayi sanadiyyar farkawar su Jafar suka miƙe a firgice.
Wasu irin mulmula_mulmulan halittu masu kama da dodanni jikinsu duk gashi,ga wasu
zara_zaran farata masu tsini, in ka kallesu sau ɗaya bakayi Marmatin sake kallonsu ba saboda
tsananin muninsu.
Kafin suyi ko ƙarin guduwa tuni dodannin sunyi nasarar kamesu sun sa awani keji, suka ɗauki
kejin da hannu ɗaya suka ci gaba da tafiya.
Ihu kawai suke in banda Jafar da tuni bakinahi ya fara ambaton Allah da naiman agaji a
wurinshi.
Tsawa ya daka masu wadda tayi sanadiyyar yin shirunsu.
"Bashakka ina ga mun kusa raba tafiyar nan daku, kuna ganin halinda muke ciki amma kun
wage baki kuna wani kukan banza da bazai amfanemu da komiba, Shawara ɗayace muyi
ƙokarin tseratar da rayuwarmu domin bashakka in muka bari dodannin nan suka ida isa damu
lofa lalla mun zama nama cinyemu zasuyi."
"Eh musan yadda zamuyi mu buɗe kejin nan mu kubutar da