Showing 6001 words to 9000 words out of 31939 words
ta
hau dube_dube amma babu shi babu alamunshi.
Ganin haka ya sanya ta wawuro ƙafar Basma, ihu ta hauyi itama ta jawo ƙafar Rabson guy,
shima ci gaba da ihu yayi "wayyoh kakata wayyoh ɗan bunsuruna yau nayi bankwana daku,
mutuwata ta iso." cikin zafin nama shima ya damƙo ƙafar Salma, ita ma bata tsaya bata lokaci
ba ta jawo ƙafar Audu, Nura shi ya riƙo hannun yana ƙokarin cetonsu.
Ganin halin da ake ciki ya sanya Jafar shammatar Aljanar yayi tsalle ya bankata ɗaki ya mai do
ƙyaure ya rufe.
Gidan suka buɗe kowa yayi ta kanshi.
Gudu suke wanda su kansu in akace zasu iya yin shi bazasu yarda ba.
Gudune gudun yada ƙanin wani kowa ta kanshi yake.
duk gudun da suke a haɗe suke ɗayan su bai yarda ya rabu da ɗan uwanshi ba.
Gudu kawai suke amma basu san inda suke nufa ba, har sai da asuba tayi sannan suka zube
suna mai da wani wahalallen numfashi.
Wata azababbiyar ƙishirwa ce ta taso masu, sanadiyyar gudun da suka sha, shawara suka
yanke in safiya ta idayi sunemi ruwan sha.
Safiya nayi suka ƙara nausawa cikin dajin naiman ruwan.
A hankali jikin Audu gwarama yanata komawa green da baƙi, amma babu wanda yasanar halin
dayake ciki.
Wani irin ruwa ne mai mugun fadi da yalwa gashi wucewa yake da mugun guda, suka iske a
gabansu.
Nura har gudu yake ya isa ga ruwan ya sha saboda ƙishin daya addabeshi.
"Aa Nura kada ka sha ruwan nan ban yarda dashi ba." Jafar ya faɗa yana ƙoƙarin tsaida Nura.
"Ya zaka hanani in sha bayan kasan babu abinda muke buƙata yanzu kamar ruwa." ida
gangarawa yayi cikin ruwan ya duƙa ya kam fato da hannuwanshi zai kai baki.
Wasu dogayen hannuwa ne suka bayyana suka, harya juyo zai fita daga ruwan hannuna nan
suka fizgoshi suka nitsar dashi cikin ruwan yayi gaba dashi.
Tsabar tashin hankali su Jafar ƙara nausawa cikin jejin suka yi da azababben gudu.
*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅
*MEEN@RT...✍*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: *BAƘAR TAFIYA*
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE *
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI
RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA
ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN,
ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
♀️♀️♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI
NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
____________________
*PAGE 8_9*
..........Gusu ba tare da sanin in da suke nufa.
Iya gajiya sun gaji, tsayawa sukayi suna mai da numfashi, su Mandiya kuka kawai take tan ƙara
tsinema magajiya da tun farko i ta ce sana diyyarta shiga karuwanci.
Su Rabson guy abun ba magana zama yayi ya miƙe ƙafafu shame_shame yana mai da
numfashi, yana jin wata sabuwar nadama nashigar shi, da dana sanin bijirewa maganar Kaka.
Ranar nan suka wuni, ga ƙishirwa ka yunwa, sallah ma da suka auna lokaci aransu suka ga
yayi nan suka yi taimama su kayita nan.
Ƙara nausawa cikin dajin suka yi naiman ko ƴa'ƴan itatuwa ne su sanyama cikinsu.
Sunyi tafiya mai nisa suka isa wani wuri mai matuƙar kyau, korayen flawer ne ko ina ga wata ƴar
ƙorama ruwa na gudana cikin ta, bishiyoyin kayan marmari ne duk in da ka duba sunyi bul_bul
gwanin sha'awa.
Kallon_kallo suka hauyi ma junan su, suna mamakin wannan Baƙin daji tunda suka shigoshi
basu taba ganin wuri mai kyau irin wannan ba, gashi dai a halin da suke ciki babu abunda suke
matuƙar buƙata kamar ruwa da abinci, sai gashi sun samu amma suna shakkar cin shi.
Jafar lura yayi basu yadda da wurin ba, dan haka ya fuskan ce su ya fara masu jawabi;
"A halin da muke ciki yanzu bamuda mafita face mu dogara da Allah muyi Basmala muci
abubuwan da muka samu, Wamanyatawakkalu Alallah! Fahuwa hasbuhu."
Har cikin zuciyoyinsu sunyi na'am da maganar Jafar.
Ida isa sukayi wurin bishiyar Mangwaro Jafar na tsinkowa Audu na tsincewa.
A haka sun tara kayan marar mari mabanbanta masu yawan gaske.
Zama sukayi zasu fara sha koya bakinshi dauke da Basmala.
Alhamdulillah sun sha sun ƙoshi babu abinda ya faru dasu.
Nan suka yada zango suna hutawa, Basma sai yanzu ta lura babu gyalenta ya faɗi sana diyyar
gudun da suka sha, ga suturar jikinta ba ta kirki ba duk ta matseta, dubanta ta kai ga Salma
wadda ita ma hakan ta kasance gareta dan figaggen gyalenta ita ma tun suna cikin wannan
gidan ya faɗi.
Duk cikin su Biba Ita kaɗai ce shigarta har yanzu hijabinta bata cireba sai dai cukuikuyewa da ta
fara saboda wahalar da suke sha.
Abinda su Jafar basu sani ba tunda suka fara gudun nan wata ƴar ƙaramar barewa ke biye
dasu.
Ba zato ba tsammani suka ga barewa ta nufo inda suke gadan_gadan.
Miƙewa sukayi a matuƙar razane suka dun ƙule wuri ɗaya.
Rike ɗewa barewar tariƙayi har ta koma wani farin tsoho mai cikar kamala da kwarjini.
"Ku kwantar da hankalinku ni taimakon ku nazo yi ba cutar daku ba, nima da kuke gani musulmi
ne ɗan uwanki, abunda nike buƙata ku dogara da Allah ku zauna in sanar daku abinda baku
saniba game da tafiyar da kuke.
Jikinsu kyar ma kawai yake sun kasa zama sai da Jafar da Biba suka ƙara masu tuni akan su
dogara da Allah su zauna.
Mai da hankalinsun sukayi ga wannan tsoho.
"Kamar yadda na faɗa maku a baya ni ba mutum bane, kamarku ni Aljani ne, suna nana
Ammar bin asad, basai na sanar daku yanayin dajin nan ba nasan yanzu kun fara sanin yadda
yake, wannan daji da kuke gani tun asali ya kasance wani irin shu'umin jeji wanda ko dabba ce
ta shigo cikin shi da wuya ta fita araye, asalin fara zaman wannan daji wasu turawa ne
ma'aurata bayan aurensu suna binciken inda keda abu buwan mamaki domin su Allah yayi su
da son abubuwan al ajabi, nan suka binciko wannan daji, sunyi ƙokarin zuwa dan ganema
idanunsu abinda ke faruwa ana hana su zuwa amma suka nace, daga ƙarshe suka sulale suyo
Nageria, bayan zuwansu Nageriya basu yadda sun shiga wannan daji kai tsaye ba gida suka
kama suka zauna suna hulɗa da hausawan mu har suka iya hausa abakunan su, Alƙawari mijin
yayi in matarshi ta haihu ɗiyar tayi shekaru biyu lokacin ne zasu nausa cikin dajin dan gane ma
idanusu abunda ke faruwa."
"Ba'a ɗauki wani dogon lokaci ba Matar wannan Bature ta haihu, ranar da ɗiyarshi ta cika
shekaru biyu ranar suka ɗauki hanyar wannan daji da duk guzirin da suke buƙata, Sanin halin
wannan daji yasan ya dereban dazai kai su dajin yace sai dai ya ajesu nesa da dajin su ida isa
da ƙafafunsu, idansu ya rufe ga son shiga wannan daji dan haka basuji komi ba suka amin ce ,
gorinsu ya cika sun samu damar shiga cikin wannan daji daya kasan ce shine zai zama
ajalinsu, tun shigar su dajin suke murna ganin dajin ko ƙasashen su basu taba ganin daji mai
duhuwa da manya_manyan duwatsu, dajin kallonshi kaɗai abun tsorone amma su a wurinsu
wannan shine kaɗan daga cikin abubuwan mamakin da suke naima,itatuwa mijin da matar suka
hau sarewa suna haɗa katakan yin gidan da zasu zauna, sunyi aiki natsawon watanni biyu iya
wahala sun wahala kafin suyi nasarar i hada gidan, har yau babu abinda ya firgita su koya
tsorata su tun shigarsu dajin, rayuwa suke tajin daɗi acikin dajin nan suna ɗiyarsu, ranar da
bazasu taba mantawa ba ita ce ranar suna daga wajen gidan ɗiyarsu na nesa dasu tana wasa
su kuma suna zaune suna hirarsu, wata irin ƙara kunnuwan su suka Jiyo masu, a firgice suka
kwalama ɗiyarsu kira dake wasa nesa dasu baban ya ruga ya ɗauko ta suka nufi gidan, sai dai
mi! Suna buɗe gidan suka ga ɗiyarsu nata wasanta ita ɗaya cikin gidan, dagowa tayi ta kallesu
tana sakar masu murmushi, sakin wadda ke hannunsu sukayi suna nunata da yatsa suna ja da
baya, su duka taran biyu da ta cikin gida da ta hannunsu nufo su sukayi suna momy ni ce Lara
ɗiyar ku waccen ƙarya take, ruɗewa sukayi sun rasa gane ainahin ciki wacece ɗiyarsu, Lara ta
ƙarya ta shago wuyan ta gaskiyar ta ɗagata sama ta wujijjigata ta wullata gefe, juyowa tayi kan
iyayen tana dariya idanunta na zubda jini, nuna su tayi da hannu take wata iska ta yi sama dasu
tana bugasu da bishiyoyin wurin tun suna ihu suna kiran abun bautar su har suka daina
numfashi, bacewa. Basu farfaɗo ba sai da marece yayi sanyi bugesu sannan suka farfaɗo kan
ɗiyarsu sukayi da gudu suna kiran sunan ta, kayansu suka haɗa suka nufi haryar da suka shigo
dajin, abun mamaki haka suka ƙaraci yawonsu har duhun dare ya fara amma hanyar ta bace
masu, dole suka haƙura suka dawo gidan suna tunanin abunda zai same su nadamar shigowa
dajin na shigarsu , dare ya raba babu abuda kunnuwanka ke jiyo maka illa kukan tsuntsaye da
ya haɗe da Iska yake bada wani firgitaccen sauti, ƙofar da suka kulle sukaji tana budewa da
kanta ɗiyarsu suka jawo suka ƙara rungumewa, wani baƙin wayaƙi ya Cika ɗakin, a hankali ya
fara haɗewa wuri ɗaya yana komawa doguwsr halittah mai suffar mutum, ko ina jikinta hannuwa
ne, idon ta guda a tsakiyar goshi, dariya ta kece da ita "ku masu taurin kai yau kwananku ya
ƙare,yau zaku bar duniyar nan sakamakon ganin ƙwaf daya kawoku dajin nan," tana rufe baki ta
chafko miji ta wullashi sama ya fado ƙasa kanshi ya fashe ko shurawa bai yi ba ya mace, matar
ta nuna da hannu take wani hayaƙi ya fito ta hannunta ya shigajikin matar da ɗiyarta take jini ya
riƙa ambaliya ta hancinsu da baki suka sulale ƙasa matattu, atare gawawwakin su suka bace
tare da wannan hali halittar, wannan shine abunda yafaru da waɗan da suke shigowa ɗakin
nan, taimako ɗaya zaniyi maku shine kada kusake wannan addu"ar ta fita daga bakunan ku,
*LA'ILAHA ILLAH ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTUMINAZZALIMIN*, san koda wasa kada
kusake ku sake ku rabu da abokan tafiyarku, ƙarfina bazai iya fiddaku daga dajin nan ba
addu'ar ku ita zata taimake ku, nabarku lafiya Allah ya fitar sadaku, ya bace."
Jikinsu sanyi yayi dajin wannan bayanin, basu ankara ba wurin da suke ya fara duhu
bishiyoshin na komawa baƙaƙe flower ɗin wurin suna bacewa, Basma tsalle tayi ta faɗa jikin
Biba jikinta na kyarma, Rabson Basma dake kusa dashi ya maƙalƙale.
"Bakada hankali?, ina matar aure zaka riƙa shigemani?."
"Ke da auren na haɗaku a turmi na Ƙulƙule, kina matar aure tsabar gantali miya fito dake
wannan tafiyar?."
Kafin ya rufe baki duhu ya ida rufe idanunsu, ji sukayi an shure su anyi sama dasu
shuuuuu!✈️✈️
*MASOYANA KU KOYAMA WANNAN LITTAFIN YAWO, YAJE KOWANE GROUP NA
NOVE*
*COMMENT*✅
*SHARE*✅
*MEEN@RT...✍*
08133562798
[10/11, 10:29 PM] Meen@t A Yandoma: *BAƘAR TAFIYA*
( *HORROR STORY* )
*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*
*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*️
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*SALONSHI NA DABAN NE *
*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI
RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA
ABBANA*
*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN,
ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*
♀️♀️♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI
NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
*WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN
ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA*
__________________
*PAGE 10_11*
.....Lulawa akayi dasu a sararin samaniya, addu'ar da suke ta sanya aka yo ƙasa dasu ba shiri.
Wuri ne mai tsananin huduwa da manya_manya duwatsu, ga bishiyoyi masu wata firgitacciyar
suffa ko ganye ɗaya babu jikin su, sai wasu irin dogayen saiwa ajikinsu.
Aka watsosu, sanyin daya fara ratsa jikinsu ya sanya su buɗe idanu suka miƙe a firgi ce.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, Mi mukeyi nan?, ina sauran abokan tafiyar mu."
Jafar ya faɗa yana mai kallon mandiya da Basma da suke rarraba idanu ido.
Hannu Basma ta ɗora akai ta fashe da kuka.
"Wayyo Ɗana wayyo Mijina ashe kallon ƙarshe nayi maka bazamu sake haduwa ba ajali ke kira
na."
Ya isa, Jafar ya daka mata tsawa, "da kukan ki zamujin ko da halinda muke ciki, harkin manta
da nasihar Ammar?, babban tashin hankalinmu ayanzu shine an raba mu da abokan
tafitayarmu."
Sai lokacin su Mandiya suka lura da basu tare da abokan tafiyarsu.
Nau sawa suka ƙarayi ciki jejin suna kwalama abokan tafiyarsu kira.
Tun suna kiran sunayen su da ƙarfi har muryoyinsu suka shaƙe amma ko alamunsu babu.
Tsayawa sukayi suna mai da numfasha saka makon tafiyar da suka sha.
"Ni fa ina ganin an rabamu da abokan tafiyarmu ne dan ayi galaba akanmu."
Mandiya ta fada tana fuskantar Jafar.
"Nima zuciyata ta kawo mani wannan tunanin tuni, amma duk da haka mu dage da Addu'a,
Allah shine kaɗai mai iya fitar damu daga cikin wannan halin."
Tashi sukayi suka ci gaba da tafiya, sun ɗanyi nisa da wurin da suka baro sukaji takun tafiya a
bayansu.
A hanzar ce suka juyo suna dunkulewa wuri ɗaya.
Sal...Sasa..Salma!.
Baku nan su, suka furta suna in ina.
Salma dake nesa dasu takowa ta farayi zuwa inda su Basma suke.
Mandiya murnan sun fara ganin abokan tafiyarsu ya sanyata rugawa ta maƙalƙale Salma.
"Muna ta naimanku ina kuka shige Salma?."
Shirun da taji anyi mata ne ya sanyata dago fuskarta tana kallon Salma.
Ganin fuskar Salma da ta chanza ta koma irin suffar Horror, rabin fuskarta ya kowa abun tsoro
duk yayi dameji wani farin ruwa mai haɗe da jini na zuba,idanunta ɗaya babba ɗaya ƙarami ga
bakinta daya rabe biyu jini na ɗiga, faratan hannuwan ta sunyi zaƙo_zaƙo irin na Horror.
Razanan niyar ƙara ta fasa tana ƙoƙarin kwace kanta a hannun Salma.
Sai da ta makaro domin Salma ta rigada ta mata kyakykyawan ruƙo.
Dariya Salma taci gaba da 6a66akawa da ta sanya dajin amsa kuwwa.
Kunyi kuskuren shigowa dajin nan yau sai dai wasu baku ba.
Ɗaga Mandiya tayi da ta wullata sama, tayi nuni da hannunta wata iska ta riƙa wulwula mandiya
tamkar yadda fanka ke gudu, tun Mandiya na ihun naiman taimako harta daina motsi.
Nuna ta tayi da hannu take wannan iskar ta tsaya nan Mandiya ta faɗo ƙasa tim!.
Darita ta kuma kecewa da ita, sai da tayi mai isarta sannan ta turbune fuska, "ku masu kunnen
ƙashi, yau zakuga yadda zamu ƙare daku musamman kai, tana mai nuna Jafar da yatsa."
"Na haɗa maku tarko amma nasara ya akayi kuka tsallake shi, kunci ƴa'ƴan itatuwanda nina san
da kunci to mutuwa zakuyi, kai kasa suka furta wata kalma wadda lokacin da zakuci wadda ita
ta sanya kuka tsira da rayuwarku abinda kukaci bai kasheku ba, dan haka yanzu anan take zani
raba gangar jikinku da numfashinku."
"Baki isa kiyi mana abinda Allah bai rubuta zai faru damuba, kamar yadda Allah ya tseratar
damu a wanchan lokacin nan ma muna sa ran zai tseratar damu."
Kafin tayi wani yunƙuri cikin jarumta da dakewar zuciya Jafar ya ɗaga murya ya fara karanto
Ayatul kursiyu, ita ma Basma ta ɗauka sukaci gaba dayi tare.
Ƙara Aljanin yake jikinshi na tsagewa ba shiri ya zama guguwa ya bi iska ya bace.
Tsagaita karatun sukayi, suka nufi inda Mandiya ke kwance shame_shame ba alamun tana
motsi.......
____________________
Tunda Aljanin ya wurgar dasu, buguwar dasu kayi ta sanya su sumewa.
Rabson ne ya fara farkawa, a hankali ya matsa kusa da Audu yana bubbuga jikinshi har yayi
nasarar ta dashi.
Hayaniyar da su Rabson keyi suna naiman sauran abokan tafiyarsu ita tayi nasarar tada su
Biba suka tashi.
Sun duba ko ina amma babu abokan tafiyarsu.
Tashin hankalin da suka shiga bai misal tuwa musamman su Rabson da Salma.
Gajikin Audu sai ƙara rikiɗewa yake yana komawa green da baƙi.
Duk cikin babu wanda ya lura da halinda Audu ke ciki tashin hankalin da suke ciki yasa
sunmata da komi.
Ƙara nitsawa suke cikin dajin suna naiman su Jafar, amma ina sai da suka gaji liƙis basu ga
koda sawayen ƙafarsu ba.
Zama sukayi suna mai da numfashin wahala.
"Mu yanzu haka zamu ƙare acikin wahala ga rashin tabbas na zamu fita daga jejin nan, Daddy
dana bi maganarka da banzo wurin bikin nan ba, Hajara ban yafe makiba duk ke kika jawoni
cikin wannan bala'in, gashi nan ke kinyi aurenki nikuma gani nan cikin masifa."
Salma ta ƙarashe maganar ta rashe hawayen fuskarta.
Jugum_jugum suka yi kowa da abinda yake tunanin.
Yana yin wurin da suke zaune bakajin motsin komi sai sautin numfashinsu dake fita.
Motsin tafiya sukaji alamun ana nufo in da suke.
Miƙewa sukayi jikina kyarma Salma ta kama hannun Biba ta riƙe gam kamar wani zai rabasu.
Motsin takun naƙara kusanto su, suna ƙara shigema junansu.
Abinda idansu ya hasko masu ne ya sanyasu suman tsaye la66ansu na makyarkyata suka furta
Garrrba!....
___________________
Da ƙyar