Showing 1 words to 3000 words out of 44786 words

Chapter 1 - AMANI BOOK 1 HAUSA BOOK BY TAKORI KABARA .pdf

AMANI




​​ Littafin






SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)
takorikabara@gmail.com

AMANI
TARE DA NI, SUMAYYAH ABDULKADIR

SHIMFIDA
Safiyar yau wadda ta kasance Lahadi, an wayi gari da lullumin hadari mai hade da sassanyar
iska mai dadi a gidan su Amani, wanda ke cikin rukunin gidajen GRA a birnin Katsinan Dikko.
Kasancewar lokacin ya kasance lokaci ne na tsakiyar damuna, kada ka so ka ga yadda
shuke-shuken dake harabar gidan suka bude ganyayyakin su suka yi korra sharr, suna bada
kamshin furanni da bishiyu kala-kala, musaman da bada jimawa ana iskar sai yayyafi ya soma
sauka, don haka iska ce mai dadi kawai take kadawa a gidan mai sanyawa alummar gidan
nishadi, ciki harda Amani dake can upstairs, ta bude tagogin dakin ta iskar na tadda har cikin
toilet din da takw wanka.
Dai dai lokacin da aka tsuge da ruwan saman kamar da bakin kwarya. Amani ta fito wanka,
daure da towel a jikin ta, ta karasa ta rufe tagogin ta don dakin ya soma jikewa, ta zauna gaban
mudubin kwalliyar ta dan kasar Mexico mahadin furnitures na gogaggen katakon kasar waje
dake dakin kamar dakin matar aure. Kamar yadda yake a aladar ta kullum, daga fitowa wanka
sai ta bata lokaci tana kwalliya a zaune a kan stool, kamar mai shirin tafiya beauty contest in ka
ga yadda take bata lokaci wajen tsantsara kwalliya kullum.
To yau ma hakan ce ta kasance, Amani ta kwashe kusan mintuna talatin tana gyara fuskar ta
da serene make-up, bakin nan ya dauki maikon wet lips na Elizabeth Arden sai sheki yake
kamar ka sace bakinka gudu irin wanda ake kira kissable lips, ta shirya cikin wani dan shafal din
swiss lace ruwan gwaiduwar kwai da feshin golden a jikin sa, duka wannan adon na karshen
mako ne bana zuwa wani waje ba, koda-yake dama tun filazal ita maabociyar ado ce da son
kyale-kyalen mata irin wanda ya wuce kima, musamman a renaku irin wadannan na karshen
mako da take wuni a gida, don ita bata yawace-yawacen gidan kawaye ko bukukuwa don basu
ishe ta kallo ba.
An yi mata wani kyakkyawan dinki na zamani na doguwar riga wadda ta kama ta daga sama
ta bude daga kasa sosai kamar (A shape). Kai da ganin dinkin nata kasan na yayan gata ne

kuma ya ja kudi a jikin sa.
Amani tana sakkowa daga matattakalar bene inda dakin ta yake a cikin gidan su, wata irin
tafiya take yi kamar hawainiya, kamar bata son taka kasa, kuma kamar tsinin takalmin ta bai
dame ta ba. Sakkowa take daga benen cikin takun ta na kasaita da rangaji irin na yan matan da
ke cikin lokacin su, suka kuma yi katarin samun rayuwa ta gata da wadata, dai-dai da yadda
suke buri ko suke son samun ta a duniya.
Daga nesa sai tayi maka kama da matashiyar macen Dawisu saboda iya ado da iya baza
tafiyar kasaita, koko zangarniyar dabinon da iskar hunturu ke kadawa sabida yadda ilahirin
kyakkyawan jikin ta ke rangaji tana zuba kamshi. Kai Amani karshe ce a class da gayu karshen
duk inda zaka iya kwatanta ta. A haka ta isa babban falon gidan su, inda ta tadda mahaifin ta
yana aiki cikin wasu muhimman takardu da naura mai kwakwalwar bisa cinya (laptop) a gaban
sa.
Tun kafin ta gama sakkowa daga benen hankalin mahaifin ta Hon. Usman ya kai gare ta
sabida karar takalmin ta mai tsinin dunduniya. Ya daga ido ya dube ta, sai ya sunkuyar, yana
cigaba da danna naurar gaban sa cikin kwarewa, ita ta san baban ta Guru ne a computer da
lissafi bay a taba yarda kwandalar sa ta bata cikin lissafin sa, in ma ka sace ta don kana
maaikacin sa zai gane, kuma sai ka yi aman ta.
Cikin sigar kirari kamar ba mahaifin ta da ya haife ta ba, sai ka yi tsammanin wani saan ta ne
koko abokin wasan ta, Alhaji shiga fadin TA-FISU YAR GIDAN BABAN TA! Ya saki dariyar farin
cikin ganin ta ba tare da ya dago ba, hankalin sa na bisa lissafin sa don kada ya bata kwandala,
ya ce Ta-fi-sun Daddy an fito?. In ji Alhajin cikin kulawa, sai yanzu da ya kammala kirgen sa kaf! Sannan ya dago ya dube ta,
ya kuma bata hankalin sa, bayan ya kashe naurar gabadaya, cikin murmushin kauna da kulawa
cikin yan kananun firi-firin idanun sa masu kama dana yan China.
​ TA-FISU-KIN FI SAURAN MATA! Ya kara fadi cikin kambama yar tasa, wadda a kullum
ya dube ta surar mahaifiyar ta Jalan ke masa gizo, har kullum yana godewa Allah da wannan
kyakkyawar halitta da ya bashi a matsayin diyar sa, yana godewa Allah da ta debo komai na
Jalan bata ko dauko farcen sa ba, ji yake kamar ya lika ta a goshi don So da alfahari, banda
Allah sarkin hikima da tsara halitta yadda yake so, wa zai iya hakan? Mai sanya mummunan
mutum bakikkirin kamar sa ya haifi irin wannan kyakkyawar halitta? Ai sai Allah Al Khaliqu
Sarkin kaga halitta a yadda ya ga dama, Ubangijin sammai da kassai. Mai sanya mummuna ya
haifi kyakkyawa. Shi da kan sa Uban yau da ya dube ta sai da ya ce tsarki ya tabbata ga sarki
Allah!
Domin gani yayi gabadaya ta rikide masa ta koma mahaifiyar ta Jalan, sau tari har gizo take
masa da Uwar ta, shi yasa har kullum yake kara kaunar ta, duk soyayyar da yake wa uwar ta
kan ta ya koma. Har gobe bai auri macen da yake so yake darajjawa irin Jalan ba. A yau ganin
ta yayi replica din Maman ta, wato kamar Jalan ce gaban sa shekaru ashirin a baya. Amma Amani har ta fi ta sheki da daukar ido, don nata kyan ya hadu da gyara da
kyale-kyalen zamani mai tsada.
Alhaji Usman Faskari, baki ne wuluk, tittirna, gajere, kuma mai dagaggen hanci da kananun
idanu mitsi-mitsi kamar na yan birnin Sin. Kai babu wata suffa a jikin Alhajin da zaa kira
kyakkyawa, a cewar sa shi yasa Jalan ta ki zama da shi duk arzikin sa. Jalan mai kama da
matan Hurul-eeni don kyau. Ta sha ce masa firgita ta yake cikin dare, ya daina shigo mata daki

in dare ya yi, ya dinga bari sai gari ya waye. Ta fannin halayyar Alhajin ma sai mu ce sai a
hankali, domin dai a zahiri shi mutum ne mai mammako (marowaci) kuma mai son kan sa da
yar sa kadai. Ya mallaki mahaukaciyar dukiya da shi kan sa bai san adadin ta ba, wadda ya
mallaka ta hanyoyin duka yaki halaal, da ya ki haraam, tunda kuwa gogaggen dan siyasa ne na
jiya ba na yau ba, wadanda suka dade suna ci da tada kai hadi da birgima cikin dukiyar alumma
da sunan siyasa da cigaban alumma.
A halin yanzu yana rike da shugabancin jamiyya mafi karfi, mafi shahara da farin jini a wurin
alummar kasar Najeriya. Wato jamiyyar AC da aka fi sani da (Action Congress) ta kasa
bakidaya. Ya iso ga matsayin shugaban jamiyya ne bayan ya rike manyan mukaman Siyasa da
baza su lissafu ba, tun daga karamar hukumar sa ta Faskari, har zuwa matakin jiha, wato jihar
sa ta Katsina, har zuwa halin da ake ciki yanzu da ake damawa dashi a Gwamnatin Tarayya.
Cikin manyan mukamai na karshe-karshe da Hon. Usman Faskari ya rike har da Sanatan
Katsina ta kudu sau biyu.
Idan ka cire harkar siyasa da yafi bada karfi da yin kaurin suna a kai, don da ita aka san shi,
da ita yayi ficce, har ila yau, shi din kuma babban dan kasuwar ketare ne (International
Business Man) wanda koda siyasa ko babu ya riga ya haye tudun mun tsira.
A can baya tun kafin ya haifi Amani har kasuwancin fidda Iron ore da aluminium ore yayi,
wato exporting natural resources da ake hakowa a kasashen Afrika daban-daban irin Saliyo da
Madagascar, yana da shahararrren kamfanin sa na kan sa a Katsina mai reshe a birnin tarayya,
Abuja wato FASKARI INVESTMENT amma rayuwar sa tafi yawa a garin Katsina. Daga baya bayan Amani ta tasa ya mayar wa da kamfanin suna Amani Faskari Investment,
kamfani ne na komai da ruwan ka a harkar shigo da kayan ginin gidaje dana sakawa a gidaje,
ba irin kayayyakin da basa shigowa da su da suka shafi wannan bangaren daga kasashen
ketare musamman kasar Faransa da kasar Mexico inda ya zuba mafi rinjayen hannayen jarin
sa, har ta kai ta kawo rabin rayuwar Usman Faskari ya zama na yawo tsakanin Najeriya da
Faransa da Mexico, komai na kamfanin sa kowa ya san daga kasashen nan France ko Mexico
yake kawo su, wato daga makerar su sai kamfanin sa kadai, shi yasa baa fiya samun irin kayan
sa a Najeriya sosai ba, abin nufi, kayan ginin kamfanin AMANI FASKARI INVESTMENT LTD
sun fita daban. Kama daga kofofi, tagogi, tiles, marbles, da duk abubuwan ceramic da ake
amfani dasu wajen ginin gidaje. Masu ginne-ginen estates da gidaje a Katsina da Abuja
yawanci duk a kamfanin sa suke order.
A halin yanzu, Alhaji Usman Faskari, wanda alumma ke kira Hon. Faskari, yana da shekaru
hamsin da biyar amma in ka gan shi arbain zaka bashi sabida jin dadi da kula da lafiyar sa,
bashi da wani buri da yasa a gaba yanzu irin diyar sa Amani da rayuwar ta, babban burin sa
kullum shi ne farin cikin ta, jin dadin ta da walwalar ta. Hon. Usman ya wadata Amani fiye da
kima, tun a kananan shekarun ta Amani ta san tafi sauran tsararrakin ta gatan aljihu dana Uba,
ya kuma fifita ta ya sangartata wanda hakan ya shafi tarbiyya da muamalar ta da mutane,
saboda ya jika ta da komai na jin dadi da bukatun rayuwa ba tare da ta yi maraicin mahaifiyar ta
ba, wadda Amani bata taba gani ba ko a hoto, alhalin tana raye ba wai ta mutu ba.
Iyayen ta sun rabu tun tana tsumman haihuwa, a cewar sa saboda munin sa ne Jalan ta ki
zama da shi, wanda kullum take cewa yana firgita ta, a zahiri shi yake tunanin hakan, amma
dalilai da yawa ne suka hana Jalan iya zama da shi, ciki har da halayen sa na kankamo da
rowa, dama kuma auren dole iyayen ta suka yi mata da shi a dalilin ya saye mahaifin ta da

dukiya.
Tunda ta koma kasar su (Sierra Leone) bata kara dawowa Najeriya ba, wai da sunan ganin
yar da ta Haifa ta tafi ta bari bata ko shayar ba, shi kuma bai kara bin bayan ta ba, bai ma san
tana raye kota rasu ba. Sai ya maida hankali a kan rainon kyakkyawar diyar data bar masa wato
AMANI, ya kuma maida kafatanin soyayyar da yake yi wa Jalan a kan ta, bai yarda ta nemi wani
abu a rayuwar ta ta rasa ba, komai darajar sa, bai yarda ta yi kukan babu ba, ba ya ko tunanin
ya dace ya aurar da ita haka, kullum kallon yar kankanuwar yarinya yake mata, yadda take
shekaru ashirin a baya sanda yake goya ta da kan sa a bayan sa.
Shi kan sa bai san iya son da ya kewa yar sa Amani ba, ko iyakar adadin abinda ya mallaka,
kuma komai nasa da sunan tilon yar sa AMANI yake rubuta hakkin mallakar sa. Wato ita yake
sanyawa hakkin mallaka a rubuce gaban lauyoyin sa.
Wannan ne kuma babban abinda ya assasa bakar kiyayya tsakanin Amani da matar sa
Hajiya Rabi, saboda ita bata taba haihuwa da shi ba. Kafin Hajiya Rabi ya auri mata kusan tara
yana sakin su, duk ba a kan komai ba sai a kan rikon Amani, don sun kasa yi mata irin rikon da
yake so na gaskiya da amana, kankanin laifi zasu yi, ya basu takardar saki in dai a kan yar sa
Amani ne, da ya sakawa suna TAFISU. Yake mata kirari da Kin fi sauran mata.
Haka masu aiki ma basu tsira ba, kullum cikin canzawa Amani su ake, saboda a cewar sa
basa kula masa da ita yadda yake so. Wannan yasa Amani ta tashi yarinya sangartatta,
hamshakiya, mai girman kai, mai yawan alfahari, mai raini ga mutane, kuma mai izzah da
dagawa da son a bata girma koda kuwa mutum ya haife ta. Ga rashin tauna magana da kowa take Magana, har shi mahaifin nata kuwa wani lokacin
bata masa magana da girmamawa, ka yi mata magana ta mayar maka da harara. Yadda duk
magana ta zo bakin ta haka take furzar da ita ga kowa cikin raini da gatsali, bazata yi laakari da
yawan shekarun da ka bata ba zata iya marin ka ko ta tofa maka miyau a fuska muddin ka
shiga gonar ta.
Sabida girman kai irin na Amani ko kawaye cikin tsararrakin ta bata da su domin ta raina
ajawalin kowa, da an fara kawancen zaa babe, saboda ba kowa ke jure halin ta na raini da
dagawa ba.
Kawar ta daya ce da suka yi karatun sakandire tare a (Ulul Albaab Science Secondary
School Katsina) wato Hamida Balewa wadda itama Baban ta tsohon dan siyasa ne, da ya rike
har mukamin gwamna a jihar Baucin Yakubu.
Hamida ta iya da ita da halin ta, don ta fi ta hankali da hakuri kuma tana son Amani kamar
yar uwar ta, shiyasa suka rayu tsayin lokacin nan basu rabu ba, har zuwa yanzu suna tare a
shekarar nan da suka kammala karatun Jamia tare a jamiar Tafawa Balewa.
Har zuwa lokacin da mahaifin ta ya auri Haj. Rabi, ita da kan ta Amani ta roke shi ya rufe
aure-aure daga kan Haj. Rabi saboda mutuncin siyasar sa, da kuma kasancewar tana son ya
zama akwai mace tare da su, duk da dai in ya saki baya jimawa yake kara aurowa, kafin ya auri
Haj. Rabi ya dade babu mata, don ta karshe ta kusa kashe Amani da duka don haushi sabida ta
tofa mata miyau a fuska, ita kuma Haj. Rabi ganin inda raunin Alh. Usman yake wato (son a
taya shi kula da Amani da taya shi soyayyar tilon diyar tasa), sai ta saka kaimi a kai, ta kama
Amanin ta rungume a farkon zuwan ta, har fiye da kima, da ta gan ta zata hau rawar jiki da
hidima da ita a gaban Alhajin, irin yadda Hon. Din yake so matar duk da ya aura ta yi wa Amani,
Haj. Rabi ta shiga nuna mata soyayya har fiye da shi. Hakan yasa ta shiga ran Alhaji. Amma ba

haka abin yake a zuciyar ta ba.
Wannan ne yasa tayi dan nisan zango a gidan Hon. Usman, domin a kalla zuwa yanzu tayi
shekaru kusan hudu a gidan su Amani, sauran matan da ya aura a baya babu wadda ta rufa
shekaru biyu. Amma a zahiri Haj. Rabi ba wanda ta tsana data bude ido ta gani a duniya irin
Amanin. Babban tashin hankalin ta ranar data fahimci cewa komai na dukiyar Alhajin sunan Amani
yake bearing, mai nufin ya gama mallaka mata komai nasa, duk wadda zata zo sai dai ta jira
dan tumunin takaba (idan ma ta yi nasarar dadewa a gidan kenan). Musamman hankalin ta ya
kara tashi da likita ya tabbatar mata shekarun ta sun wuce na daukar ciki wato ta isa
menopause ba matsalar haihuwa ce da ita ba yadda take zato.
Haj. Rabi tana da yara biyu mace da namiji da tsohon mijin ta na baya. Ta aurar da macen,
namijin kuma yana jamia yana hannun mahaifin sa a garin su Minna jihar Neja.
**** ***** *****
Amani ta karasa saukowa daga matattakalar benen, ta karaso ta zauna a jikin mahaifin nata
yadda ta saba duk girman ta, kai ka ce yarinyar goye ce a yadda take masa magana cikin
shagwaba.
Daddy, saboda Allah ba zaka daina kira na da sunan tsofaffi ba ko, bana son wannan Tafisun
da kake kira na da shi, kullum sai na gaya maka ka bari bana so, amma ba dama ka ga na yi
ado sai ka sake kira na da Tafisu-Tafisu. Amani ta fada cikin zumburo baki, tana kallon takardun
da ya kammala sakawa hannu, sakamakon ganin sunanta baro-baro a kan takardar shaidar
mallakar boutique na kayan sanyawa na mata mai suna AMANI COLLECTION.
In bata manta ba tun shekarar data gabata Daddy yake shirye-shiryen bude mata boutique
din nan, wato sai yanzu Allah yasa aka kammala kenan.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login