Showing 21001 words to 24000 words out of 38778 words

Chapter 8 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala 4 Book By Sumayya TAKORI.pdf

a dakin Hauwa ba ya fito ya jawo
mata kofar ya ce ina zuwa.
Ya tadda Madina a kitchen ta hada custard da madara a kofi mug ta dauka za ta wuce daki,
sai ya dakata a bakin kofar kitchen din, wato ya tare mata hanyar ficewa.
Ya ce da ita (authoritatively), Munauwarah, abincin da ki ka kwashe daga dining wa zai ci?
Ina ki ka kai shi, ko zubarwa ki ka yi?
Madinah ta yi banza da shi.
Ya ce, Ina soki sani ni ba mai kudi ba ne da zan zubar da abinci a shara wai don kada wani
ya ci, sannan bana son almubazzaranci, kin dafa abinci amma sai fita na yi na sa kudi na saya,
mene ne hujjarki ta yin hakan?
A da dai ban sanki da wadannan baudaddun halayen ba, ko kusa wannan ba Munawwarar
da na sani ba ce ba Giwar Sarham..bace.
Kamar jira ta ke ya fadi hakan, hawayen da ta ke ta tattali tun dazu da ta fito ta ganshi yana
kula da makauniyar matarsa, suka samu yancin kansu yanzu.
Ta ce, Kada ka kara ce min wata giwarka daga yau. Ita giwar miji ita ce matar da ta ishe shi ta
kowanne bangare, ta kuma ke satisfying dukkan bukatunsa, har ta hana shi hango kyalkyalin
wasu matan.
Wato wadda ta dusar da hasken sauran mata a idanunsa, amma ni fa?
Nawa mijin ban ishe shi ba, karewar ban ishe shi ba musaka ya dauko min ya zama bawanta,
ya daidaita matsayina da nata.
Na tsane ka Sarham. Wallahi na tsane ka, ka tafi daga idona kada in yi furucin da Allah zai yi
fushi da ni, wato in ce ka sake ni in koma gidanmu ya fi min alkhairi a kan ganin fuskarka yanzu.
Murmushi ya yi ciki-ciki, ya dauki kofin glass ya zuba ruwan gora ya sha ya juya ya bar mata
kitchen din. Wannan shirun da ya yi mata ya fi komai kara fusatata.
Tun yana tsammanin abin na Madina mai karewa ne amma har zuwa wayewar garin ranar da
shi ya tashi cikin farin ciki mara misaltuwa, na karbar ragamar rayuwar HAUWA-KULU. Hauwa
kuma aka bi sahun sauran mata ya soma jinyar barnar da yayi a matsayin sa na likita bai
wahalar da ita fiyeda kima ba, bai kara ganin kyallin Madinah ba. Ta kulle kanta da yarta a dakinta, ta daina fitowa kwata-kwata, shi kuma tunanin cewa yau
din girkin Hauwa ne a bisa tsari na musulunci daga nan har kwanaki bakwai masu zuwa ya sa
bai kara shiga dakin Madinah ba har washegari duk da ya san ta kulle kanta amma yayi niyyar
duba lafiyarsu. Da safe yana so ya tafi asibiti, amma yana tunanin yadda Hauwa za ta yi coping cikin gidan,
sababbin halayen da Madinah ta tsuro da su na yin biris da alamarinsa balle yayi tunanin za ta
taimaki Hauwa ya daga masa hankali, da ma ya yi niyyar fita tare da ita yau ya kai ta top ten ta
yi sayayyar abubuwan da ta ke da bukata, duk da yasan Mama ba abinda ba ta hado ta da shi
na amfanin ta ba.
Gyaran muryarsa a kofar dakinta ya sa Hauwa da ke idar da sallar walha juyowa da hanzari
don dama a kage ta ke da ganin nasa, tunda ya tafi dakinsa don ya shiryo take jin yunwa.

Ya karaso har inda take ya dagata daga kan dardumar suka karasa gefen gadon, ya zaunar
da ita bisa cinyoyinsa yana wani irin sunsuna ta, yace cikin taushin murya,
Maijidda ya ki ka tashi, ya kwanan bakunta? Hope babu pain din sosai yanzu?
Dan murmushi ta yi. Tana sunne kanta a kirjinsa.
Ya ce, naga kamar ba ki yi sallah daidai ba, nan din ba nan ne gabas ba, let me adjust.
Ya gyara mata inda za ta fuskanta a dakin yayin sallah, ya zauna nan makale da ita ya kasa
tafiya asibiti, ya ce, Ba ni labarin yadda ki ka kwana a gidanki? How do you feel the night? I
know its hurting a little, amma da kinsan rahma da gafarar dana roka miki daren jiya
bakidayansa da kin san cewa kin rabauta da albarkar aure. Aljannarki in dai har tana kasan dugadugaina, ni Sarham na daga miki ki shiga cikin
amincewa ta udkhuluha bissalam.
Hauwa dai murmushi take tayi ba ta amsa ba.
To zan tafi asibiti, ko za ki bi ni mu je in fara kai ki ki sayi abin da ki ke so kafin na wuce?
A nan ne ta yi magana, ta ce,
Ba ni da bukatar komai, Mama ta hado ni da komai na bukatata, ka je lafiya ka dawo lafiya
Yaya Doctorau! Baban Waheedah.
Yana jiyo bude kofar Madinah ta fito cikin shiri dauke da Waheedah, sai ya ajiye Hauwa a
gefensa ya tashi ya fita, yana cewa cikin ransa, zai yi maganin Madinah.
Yana fitowa daga dakin hauwa suka hada ido shida ita, Madinah ta hadiye wani bakin ciki da
ya taso mata, ta juyar da kai gefe tace.
Zan fita neman aiki.
Har ya kai bakin kofar nasa dakin sai ya dakata, kafin ya juyo ya yi mata wani irin kallo na
gargadi. Madinah ta kauda kai ta ce,
Ah toh, dole in fara aiki yanzu, don ba zan zauna jire maka musakar da ka ajiye a gida ba, ko
in zama yar jagora.
Allah ya tsare ni aikin wahalar da babu lada wai aikin kishiya.
Wallahi da ma don kai da yarka ne bana aiki, don in samu lokacin kula da gidana da iyalina,
a yanzu na gane ba abin da mace za ta yi ta mallaki namiji da sunan kyautatawa da kiyaye
hakkokinsa don hana shi hango wata, sai dai kawai ta bata wa kanta lokaci.
Ya gyada kai yana kallonta da budadden ido, Shi ya sa yanzu ki ka zabi fita gantali, tunda ba
ki mallake ni din ba kuma don na yi aure cika sunnar Manzo SAW? Don dai na san ba za ki ce
neman na kai ne ya saka ki yin aikin ba.
Ai kamar ba ka ji ba Dr. Sarham, in zauna yi maka gadin mata ne ba zan yi ba, sabida ni dai
duk danginmu babu makaho, ban iya yar jagorar zuwa bandaki da kitchen ba.
Sarham ya shige dakinsa da sauri gudun kada ya yi loosing temper ya kai mata mari again
irin jiya, yana cewa,
I can relate. Lalura dai ba ta wuce kan kowa ba. Kuma Hauwa ba ta dora wa kanta ba, ni din
dai ni na jawo mata.
Haka ko da ya je office din kasa zama yayi ya jima yadda ya saba saboda tunanin halin da
Hauwa ke ciki. Don haka karfe biyun rana na bugawa wato lokacin cin lunch dinsa ya baro
Saudi-German zuwa Estate dinsu.
Yana hanya Sumayya ta kira shi, yana ganin kiran nata ya ki dagawa, ya shiga gida kenan
ya yi parking. Sumayya ta sake kira, tsaki ya yi ya daga kiran nata, bai ce komai ba, Sumayya

sai ta sa kuka.

Da kyar ta soma magana jin Yayan bai katse ta ba, bai kuma tambayi dalilin kukan nata ba,
saida ta gaji don kanta tace.
Ni dama na san Aunty Madinah ce ajalin zumuncinmu, Bhaiya, na san dama sai ta raba mu,
tunda har yau ka ki daga kirana da gangan, kuma ka ce kada in kara zuwa gidanka har abada.
Sarham takaici goma da ashirin ya ishe shi.
Sumayya, wace irin yarinya ce ne ke fitinanniya mai kishi da matar Yayanta?
Sumayya ta zaro ido, kamar Sarham yana kallonta, ya ce, Yes, na gaji da korafinki a kan
Madinah, na gaji da gaya miki ba ta isa ta sa ni ba, ba ta isa ta hana zumuncina da kowa nawa
ba.
Kada ki koma daukan alhakinta, na yi karin auren ma don dai ku yarda Madinah ba ta fi
karfina ba bata mallakeni irin yadda kuke zato ba shima ban tsira ba.
To yau na dauko Hauwa na hada da Madinah, za ku daina yi min kallon sakarai a son
matarsa ko?
Ba tun yau ba na gane ke irin kannen mijin nan ne fitinannu marasa adalci, yadda ki ka dauki
Madinah ita ko kusa ba haka ta dauke ki ba.
Ki bi rayuwa a sannu Sumayyah, ki daina saka wa kowanne dan Adam kahon zuka, babu
mai bai wa wani numfashi ke da ita, kuma ba ki san ranar da Madinah za ta iya yi miki a rayuwa
ba.
Ina yi miki nasihar nan ne a matsayina na dan uwanki ba a matsayin mijin Madina ba.
Change your behaviour Sumayyah da duk kannen miji masu irin halinki, don kuma mata ne,
gidan aure za ku je, kada kaddara ta kai ku gidan masu irin halinku abubuwa su cabalbale
muku. Ki sa a ranki the more ki ka bar matar Yayanki ta zauna lafiya da shi, the more kema za
ki samu zaman lafiya da naki yan uwan mijin, tarihi maimaita kansa yake Sumayyah. Sumayyah na kuka ta ce, Na daina, wallahi Bhaiya na daina kinta babu dalili, ni na ga ishara
Bhaiya don yanzu ga shi tana ramawa, farin cikina duka yana hannunta tunda ta yi rantsuwa ko
ni na saura ya mace a duniya Usman ba zai aure ni ba.
Bhaiya mu kuma, nida Usman, muna matukar son juna.

Sarham ya daskare da mamaki, kafin ya ce, Are you sure kin daina negative behaviour
toward her?
Sumayyah ta yi rantsuwa kan cewa ta daina, ya roki Madina ta yi hakuri ta barta da dan
uwanta, she promised to become a changed person. Daga yau ba ruwanta da sabgar matansa.
And she will treat both his wives equally (tana nufin Madinah da Hauwa) duk zata daukesu abu
guda. Murmushin samun kwanciyar hankali ta fannin Sumayyah Sarham ya yi, ya ce,
Thats my sister, kada ki damu da Madinah idan Usman mijinki ne Allah zai baki, idan kuma
ba mijinki bane Allah bai rubuta ba, amma ki bar mata dan uwanta in ta dage bata so Sumayyah
babu abinda yake dole a rayuwa, kuma bazaki rasa miji ba in sha Allahu har wanda yafi Usman
komai. Ni banason aikin zubar da kima kinji? Ki hado kayanki ki dawo ki zauna tare da mu cikin aminci in fara ganin canji daga yanzu, ga
Maijidda na kawo.

Wani dan ihu Summy ta saki na murna da farin cikin isowar Hauwa birnin Jeddah.
Da ya dawo gidan yayi saar ganin Madinah na gida ba ta je ko ina ba, don ga shi nan yana
jiyo sautin talabijin daga dakinta, kuma ba ta rufe dakin ba, don haka tunda ya shiga dakin
Hauwa ba ta kara jin duriyarshi ba, watakila ya manta cewa ko abinci ba su bata ba a gidan.
Ya shiga dakin Madinah da sallama, Waheedah ta taho da saurinta zuwa gare shi ya sure ta
ya dauka.. ya samu Madinah na cin abinci ta yi girkinta na gani na fada iya cikinta.
Ransa ya kara baci sosai, amma ya hadiye fushinsa ya bi ta da lalama.
Ina fatan kin bai wa Maijidda nata?
Ta ciko cokali mai yatsu (fork)da soyayyen dankali ta kai bakinta ta cika bakin taf, ta tauna a
yangace ta hadiye sannan ta ce da shi,
Da ma hakkina ne ciyar da matarka? Gaya min inda addini ya ce ciyar da Hauwa hakkin
Madinah ne, daga kai har matarka ba kwa gabana wallahi, don ni in na raina kasuwa ko sautu
bana bayarwa.
Ba abinda ya hada ni da matarka Hauwa ta ke ko Kuluwa? Face addinin musulunci, kowa ya
iya allonsa a gidan nan ya wanke, tunda dukkanninmu muna kwana da miji daya ban ga dalilin
da zan zama kukunta ko yar jagorarta ba.
Kai wallahi Baban Waheedah idan ka nemi takura min a kan matarka, ko ka ce lallai sai ka
hada sabgata da tata, to kuwa zan nemi wani apartment din in yi parking acan ni da Waheedah,
in ya so in barka da yar makauniyarka ku shana.
Ta soma kuka tana ci gaba da fadin, Sarham! Ka gama wulakanta ni a duniya. Ka ci amanar
yarda da soyayyar gaskiya da na baka.
Jiki babu kwari Sarham ya zauna a gefen Madinah, da muryar da ya san yana sace zuciyarta
a lokacin samartaka yau ma yake yi wa Madina magana cikin salo na mijin da yasan kan
matarsa.
Ki yi hakuri kin ji ko Munauwarahta. Abin bai kai da ki yi parking ki bar mana gida ba. Tunda
har ki ka yarda za ki ci gaba da zama da iyalinki baki barni ba, duk da irin sabawar da na yi miki,
wannan kadai ya sa na jinjina miki.
Sannan na kara martaba ki da na dawo na tarar ba ki yi yaji ba a wancan karon.
Sai yanzu don Hauwa ta zo? Kada ki manta ita ma aurenta nake kamar yadda nake aurenki,
in kika bar mana gidan ai ba za mu ji dadin gidan ba balle mu shana.
Za mu kasance cikin damuwa ne da kewarki, kuma duniya da makwabta su zage ni cewa,
don na auri Hauwa na raba gida da Madinah ta.
Amma ina so ki sani, ni ne uwar Hauwa, ni ne kuma ubanta a kasar nan da ba ta da kowa.
Haka ni ne guardian dinta, ko da ace tare take gari daya kuma kasa daya da iyayenta ni ne
majibincin lamarinta. Don haka duk wani abu da zai cuta mata ko ya taba mutuncinta agidan
nan wai don wannan lalura da Allah Subhana ya dora mata dalilina, kamar yadda kike yawan
gorantawa kamar ba mai ilmin addini ba Madinah ba zan lamunce shi ba.
Son ki da kowa yake fadin ya yi min yawa, bai yi yawan da zai sa in kasa yin abinda ya
kamata ba. Amma Madinah ko ba soyayyah yar usuli tsakanina da ke a matsayinki na matata
uwargidana, sannan my first love, wallahi a kan wata mace daban da na kara aure ba zan taba
wulakanta ki ba. Balle kuma ga aure, ga Waheedah a tsakani, uwa-uba soyayyar nan da nake miki tun tali-tali
ba ta canza komai ba, kullum karuwa ta ke, sabuwa take kara komawa Madinah.

Ni kam kin fi gaban wulakanci da tozarci da ki ke kira min a idona, haka Hauwa, she have a
special place in my heart, ina son gaya miki yau ina son Hauwa ne yadda nake son ki, ba kuma
saboda mahaifiyarta da wasu dalilan da nake ta fada a baya ba aboda wauta da ajizanci, na
dade da janye dalilaina. A yau ina fada ne da babbar murya ina son tane kasancewarta matata kamar ke. Sauran
alamarin na kuma bar wa raina.
Don haka it is up to you now, duk hukuncin da ki ka yankewa aurenmu zan karbe shi
Madinah, wanda ki ka ga shine daidai, ni dai na gaya miki iyakar gaskiyata ina sonki, ina kuma
son zama da Hauwa har karshen rayuwata, ba zan taba ce miki bana son Hauwa ba, wai don ki
daina sababbin halayen da kika tsuro dasu, ko ki daina cewa kin daina hada jiki dani wai
saboda na auri Hauwa bata gani waye-waye, umh, Madinah akwai bukatar komawa islamiyya
anan, bokon naki ya rinjayi addini.
Kisa a ranki daga yau kowacce cikinku da matsayinta a gurina wanda babu na wacce zai
rinjaye ni in yiwa daya abin da bai kamata ba, ko in rabu da daya saboda daya. Muddin ina cikin
hankali na.
Don haka in kin ga barin gidan shi ne mafitarki babu damuwa, ni bana son ganinki cikin
wannan halin da wadannan sababbin halayen da ki ka aro ki ka yafa saboda Hauwau.
Don haka duk abin da kika ga shine daidai har hana ta abinci din da rashin samar da
muamalar musulunci a tsakaninku ki ci gaba Madinah ba kabarinmu daya ba.
Yarinyar nan ko da ta ke makauniyar da ki ke ta goranta mata, tofa ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login