Showing 15001 words to 18000 words out of 38778 words

Chapter 6 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala 4 Book By Sumayya TAKORI.pdf

****

Duk wani shiri na tafiyar hauwa Mama ta gama sbhi cikin lokaci, komai da tasan zata bukata

ta tanadar mata. Kuma ita da kanta ta kai su filin jirgin Malam Aminu a ranar tashin nasu. Bata
dawo gida ba sai da aka kira fasinjoji domin shiga jirgi.
A daren ranar duk kokarin Sarham na samun Madinah a waya bai yiwu ba, ko network ne ko
wayar tata a kashe take? Ya so tun a daren ya gaya mata cewa tareda Hauwa zai dawo. Ta
shirya mata daki daya cikin dakuna biyun da bata amfani dasu. A zuciyarsa baabu fargabar
komai, don yarda zuwa yanzu dole ya kara zama namijin duniya a tsakanin matan nasa kuma
ya zauna da Hauwa cikin iyalinsa cikin adalci, bai yarda da raba gida ba shi raayin sa shine
samar da kyakkyawar muamala ta fahimta da taimakekeniya tsakanin Jiddah da Madinah
kasancewar Hauwa nada lalura. Ba zai kaita wani gida ta rayu ita kadai ba.
Yana fatan wannan din ya hada kan iyalin sa da samar da zaman lafiya da kaunar juna a
tsakanin su. Don shi wai bai yarda da hargagin Madinah na cewa ita Madinah tafi Hauwa komai
ba, wai don tana takama da tanada zurfin ilmi da iyaye masu kudi yen-yen-yen to shi ina
ruwansa da wadannan din, tunda dai shi ko wani nasa bai taba aikawa gun Daddy neman
taimako daga ISDB ba, itama ba su ne dalilan da suka yi mujazar auren shi da ita ba.
Dr. Sarham Abbas ne rike da hannun matarsa Hauwa Bilyaminu, suna taka matattakalar jirgin
‘emirate’ wanda zai tashi da su zuwa kasa mai tsarki a daren yau.
Hauwa kankame ta ke da hannun Sarham cikin tsoro na rashin sabo take taka matattakalar,
shi kuma ba tare da damuwa da kallon da ake musu ba ya rike hannun nata sosai yana gaya
mata cewa,
Mind the stairs (ki kula da matattakalar).
Lokacin da jirgin ya karci kasa zai tashi, Hauwa ba ta san sanda ta saki salati ta kara damqo
Sarham ba. Wasu Larabawa mata da miji a kusa da su, sai da suka yi mata dariya, don sosai ta
ke cikin gigita da karar tashin jirgin. Wani hargagi ne da bata taba ji ba mai barazanar buga
dodon kunnenta.
A cikin jirgin, shi ya sanya hannu a kwibin Hauwa ya daura mata belt, lokacin da larabawan
na kusa da su suka fahimci cewa matarsa ce kuma bata gani ba karamin burgesu Sarham yayi
ba sabida yadda yake kula da duk wani motsinta. Ga idanun nata a bude tar masha Allah dasu.
Sai da matar ta karbi adireshin su na can Jeddah suka ce su kuma a Taif suke zaune In sha
Allah suka shigo Jeddah Sayayya watarana zasu kawowa Hauwa ziyara har gida.
Ba su tsaya a koina ba wato babu transit sai a airport din Sarki Abdulaziz.
Hannun Sarham still cikin na Hauwa, a lokacin da suke (passing immigration checks) na
shiga kasar Saudiyyah har suka kammala. Taxi (Ajrah) suka hau, mai Ajrah ya ja mota zuwa
hanyar gidanshi da ke cikin gidajen likitoci na Saudi-German.

Tunda suka hautiti Hauwa ta cire yatsunta daga cikin na Sarham. A lokacin shi yanata
kokarin saka layin shi na Saudiyyah a wayarsa. Ta mika cikin tunani. Ba kuma tunanin komai
take ba face tunanin irin tarbar da matar likitan nata zata yi mata. Da kuma irin zaman da zasu
yi tare, duk da cewa na dan takaitaccen lokaci ne wato hutun ta na semester inji Mama. Shikuma ya sa a ransa Hauwa ta zo Jeddah kenan, wato bazata koma Najeriya ba. tun a
cikin motar ya soma browsing din makarantu a cikin birnin Jeddah don nema wadanda ke hada
karatun su da speciality na masu bukata ta musamman wato makarantun da ke yin (Inclusive
Education).

**** **** ****



KAFIN SAUKAR SU DA AWANNI BIYU

S
umayyah na goye da Waheedah tana goge dining, Madina na daki tana waya da Usman cikin
zafin rai, sai Allah ya baiwa kunnuwan Sumayyah damar zuqowa.

Wallahi sai dai ka daina alaka da ni din Ussy, da dai in bari ka auri Sumayya, kai ne ba ka
san irin halinta ba, wallahi annamimiya ce zuciyarta bata da kyau bata kauna ta.
Sai kin gaya min me ta yi miki na rashin kauna, sai kin gaya min me tayi na annamimancin,
alhalin ita din ba kishiyarki ba ce, kanwar mijinki ce, uwa daya uba daya.
Madinah ta kara hassala ta ce, Yaya Usman ban yi niyyar gaya muku ba sam, nikadai na
binne abun ina fama dashi a raina don kada Daddy ya kashe min aure, amma yau tunda ka
dage a kan Sumayyah zan gaya maka, Hajjah Ramlah ma zan gaya mata. Sarham ya kara aure
a Kano, itada uwarsu sun baiwa yarinyar masauki, tun filazal Sumayyah bata taba sona ba, na
rasa laifin da na yi mata.
Ko don in rama abin da Sumayyah tayi min na kiyayyar babu gaira babu dalili na rantse ba
zaa yi auren nan ba, don na lura ita ma munafukar tana raayinka, har da yi min wani sabon
ladabi yanzu, ba ta san kar nake kallonta kamar takarda ba..
Sumayyah ta yi mata gyaran murya daga bakin kofa, Madinah ta kashe wayar ta tsuke fuska,
sai ta karasa shigowa dakin ta kwantar da Waheedah a gadonta hannunta rataye da jakar
kayanta, kamar ba ta ji me Madinah ke fada a kanta ba, ta ce,
To Anty Madinah da alkhairi, zan koma hostel, tunda Yaya Sarham ya ce yau zai dawo,
nagode da zumuncin ki.
Madinah ta harareta kasa-kasa, ta ce,

A gaishe su!.

Sumayyah ta juya cikin bacin rai za ta bar dakin tana fadi a ranta, ko son Usman zai kashe ta
itama ta hakura ba za ta aure shi ba, ko da gold aka kera shi.
Har ta kai kofa zata fita Madinah ta ce, Umh! Ji mana Summy???”
Sumayyah ta dakata ba tare da ta juyo ba, idonta fal kwallah don har ga Allah tana son
Usman Sorondinki. Ba ta san me ya sa zuciyarta ta yi mata wannan rashin adalcin ba, tunda
Yayan Madinah ne da baasa ga maciji.
Madinah ta ce, Makauniya ba ta da Yaya ne? I mean ita kadai ce a wurin iyayenta babu dan
uwa babba namiji haka?”
Cikin rashin fahimta Sumayyah ta juyo tana kallonta.
Madinah ta ware mata fararen idanunta sosai, ta kwance ribbons din data daure gashinta
dashi ya zubu a wuyanta ta girgizashi sannan ta kara daure shi cikin ‘hairbound’ din, ta ce,
Eh, ai ba za ta rasa dan uwa ba, I mean makauniyar gidanku, ina ga shi zai fi dacewa da ke,

dangin yar Badala yan cikin gari ba nawa dan uwan ba haifaffen Saudiyyah.
Sumayyah ta saki kwallar idonta, ta fice ba tare da ta ce da Madina komai ba, tana tsoron tayi
abinda zaa ce tayi fitina a gidan Yayanta amma data baiwa Madinah amsa, ta so ta ce da ita
“dadin abun ma mun san asalin balbela, kowa ya san SORONDINKI a Kano, nan ma cikin
Badalar ne yar rainin wayo kawai hankaka maida gidan wani naka. Wannan da yar sarkin Kano ce watakila ko daga ido ba za ta rika yi tana kallon mutane da
kima ba.
Shin me ta maida yaran cikin badala ne? Yan kauye ko? Za kuwa ta ga kauyanci ganin
idonta, sai ta kilar da HAUWA, duk da haka ma Mama tana yawan gaya mata irin ci gaban da
Hauwa ke samu a jamiah tun dawowarsu.
Daga karshe kuma tana tafe a hanya don komawa hostel ta canza shawara, ta sa a ranta
rashin mutuncin Madina a kan alakarta da Usman ba zai sa ta fasa son Usman ba, kuma ba zai
sa ta barshi ba, don kam tana matukar sonshi. Gara ma ta rike abinta tayi ta gumawa Madina
haushi. Ai Usman gaba yake da ita ba shine kanin ta ba da zata saka shi ko ta hana shi ba,
bakin cikin ta daya yadda ta gama bata ta gun mahaifiyarsu Hajjah Ramlah.
Ko awanni biyu Sumayya ba ta yi da komawa hostel ba, Ajrah ta sauke Dr. Sarham da
maidakinsa, wato amaryarsa Hauwau a kofar flat dinsu. Watakila Sumayyah da ta san cewa da
Hauwa ya taho da ba ta tafi ba.
Shi kuma bai gaya wa kowaccensu cewa tare zai zo da Hauwa ba. Ita Madinah bai samu
wayarta ba ita kuma Sumayyah surprising dinta yaso yi.
Usman ne ya yi mata waya cewa su hadu a jamiarsu don Madina ta masa iyaka da zuwa
gidanta, shi ya sa ta bar gidan, da kuma maganganun data ji Madinah nayi da Hajjarsu a kanta
sun tsoratata.
Dr. Sarham ke danna kararrawar shiga kofar falon gidanshi, Hauwa na daga dan bayansa ta
sha glass da shudiyar abaya, harde da hannuwanta biyu a kirji.

Dr. Madinah wadda a lokacin take shilla Waheedah cikin lilonta cikin murnar ta kori
Sumayyah at the same time tana waya da Hajja Ramlah, korafin dai taci gaba da kai mata iri-iri
kan kanwar mijinnata wadda ta tabbatar ba tun yau ba ba ta kaunar ta bude ido ta ganta tare da
dan uwanta. Ta ce ma Hajja Ramlah,
Ban taba gaya muku ba don bana son ki ce in dawo gida Hajjah, Sarham ya dade da kara
aure, kuma sun baiwa yarinyar masauki a gidansu.
Hajjah ke shaida ce kan cewa raina ne kawai ban cire na bai wa Sarham da uwarsa da
kannensa ba don so da kauna, duk wata kulawa da mace ke yi wa dangin mijinta babu irin
wacce ban yi musu ba. Ta karasa cikin karyewar murya.
Hajja Ramlah bata san sanda ta yi wani ashar mara dadin ji ba, lokacin da Madinah ta idasa
gaya mata irin macen da Sarham ya aura da irin nakasarta.
Idan dai ni na haife ki Madinah, to tattaro kayanki ki ajiye masa yarsa ki dawo gida,
martabarki da ajinki bai yi wannan lalacewar ba.
Bari Daddy ya shigo in ma kin ki tahowa ni da kaina zan zo in fito da ke tunda Sarham ba shi
ne autan maza ba.
Madinah ta ce, Abin da na guda kenan da yasa tun farko na ki gaya muku Hajjah, Sarham ba

zai taba sakina ba, don haka ina amfanin in tafi gida da dakon aurensa watarana in dawo?
Besides na lura yanzu baya ta yarinyar, for as long as a year bai je inda ta ke ba, sai yanzu
da ya tafi daurin auren kanwarsa ta farko.
Ta ci gaba da dannar mahaifiyarta ta roke ta kada ta daga wa Daddy hankali a kai saboda
Sugar (diabet) dinsa yayi tsanani, taroketa tayi shiru kawai, za ta iya da rayuwa da Sarham a
duk yadda ta same ta.

Hajja Ramlah ta san cikin yaranta, Madina ce kadai mace amma Allah ya azurtata da hankali.
Sau tari ita ce mai yi mata fadan tayi ba daidai ba in ta kuskure wa mahaifinta. Hajja Ramlah ta
samu kanta da cewa,
Ke dai ki ka kawo yaron nan ki ka ce kina so Madinah, kada ki tilasta kanki zama da shi in
akwai wulakantarwa da tozarci, abu ne da daga ni har mahaifinki ba za mu lamunta ba, wato ya
wulakanta ki ko ya kaskantaki ko ya hada matayinki da makauniya.
Hajja kada ki damu, I can handle everything, I can take care myself, amma babu batun ‘yaji’ a
policy dina. Yau in Sarham ya sake ni zan bar masa gidansa, amma ba zan taba yin yaji da aure
a kaina ba.
Karar kararrawar shigowa ta sa ta yi wa Hajja Ramlah sallama, ta dauki Waheedah da ta fara
kuka a kan kafadarta, ta isa ga kofar bayan ta amsa da cewa,
Ina zuwa.

Ko da ta bude ita ta san ko kowa bai gaya mata ba, wannan din da ya rike hannunta cikin
nasa, na nufin HAUWA-KULU.
To amma a yadda Surayyah ta fasalta mata ita ba a hakan ta ganta ba, wato irin yan tallan
abincin Tashar cikin gari, talauci sama da kasa, yan babu cin yau babu na gobe, almajira,
musaka.
Wannan din da ke tsaye a gabanta wata ‘classy’ yarinya ce da idanu ne kawai ba ta da su,
amma za ta goga da kowacce irin macen kasar Najeriya.
Sakamakon cewa fuskarta fes, babu ko digon pimples, idanunta cikin gilashi mai duhu ainun
don haka ba ta samu ganin kalar kwayar idanunta ba.

Da farko Madinah gabanta faduwa ya yi, amma haka ta daure ta basu hanya. Wani irin
makoko na yunkuro mata, ji ta yi kamar suna shigewa din, ta fita a guje kawai ta bar gidan.
Muryar Baban Waheedah ta dawo da ita tunaninta, yana fadin,
Come on Waheedah.
Ya mika hannu ya karbi yarinyar da ke ta mika masa hannu tana zillo daga jikin Madinah.
Madinah ta ba shi hanya, cikin kauda ido, hannunsa daya rike da Waheedah, daya rike da
hannun Hauwa suka shiga cikin falon.
Sai da ya tabbatar Hauwa ta zauna a daya daga cikin kujerun falon, ya mike ya bi bayan
Madinah wadda ta yi wucewarta daki ba tare da ta ce musu ko ci kan ku ba. ko ta nuna ta san
tare yake da wata halitta, mutum din ma dan adam mai daraja. Wannan abu ya bakantawa
Sarham ba da kadan ba. Tana shiga yana shiga, ya tura kofar. Da ta daga ido ta dube shi bai iya gasgata cewa kwayar
idon Madinah ba ce, sabida yadda ta rine da bacin rai da wani zazzafan kishi mai barazanar

fasa mata ido.
Kin kyauta kenan Madina? Ai ko ni ba ki yi min sannu da zuwa ba, kya yi wa Maijidda wadda
ta zo bakon wuri, ta tadda ke a gidanki.
Dakata don Allah Baban Waheedah!
Ka gaya min za ka zo min da wannan yarinyar?
Kana tsammanin ni Madina zan iya zama gida daya da kishiya ne? Kishiyar ma irin wannan
musakar?
Sarham ya yi kokarin kama hannun Madina, ta yi maza ta ja da baya,
Dont dare touch me again, bayan ka gama tattaba makauniya.
Maganar sai da ta yi amsa kuwwa a kunnen Hauwa sabida yadda ta ware makogaro ta
fadeta.
Sarham kuma ya kai wa Madinah wani wawan mari, sai dai kafin hannun nasa ya sauka a
lafiyayyar fuskar Madinah tayi maza ta kare da hannunta, ta kuma yi saurin ja da baya kada ya
illata mata fuska.
Nashi idon har ya fi nata rinewa da bacin rai, ya ce, Munawwarah, ke ce kuwa? Yau ina
hankalinki da tunaninki ya je ki ke ma wani dan Adam gorin halitta?
Are you not a medical personnel?
Ni kike dagawa murya kamar wani dan ki? Anya ke ce ko sauya ki aka yi kafin naje na dawo?
Tsaki Madinah ta yi, ta juya ta bar masa dakin tana cewa,
Aah, ba ni ba ce, ko kuma kawai kace daga turu na fito. Ka sa a ranka ba zan taba zama
gida daya da wannan musakar ba, balle in hada shimfidar miji da ita. Ko ta fita yanzunnan ka
kama mata wani gidan ko ni in fita in bar muku gidanku, amma tareda takardata don bazan yi
yaji a dawo dani ba. Ta yi maza ta shige toilet ta saka key, ganin yadda maganganunta ke kaskanta shi, baa
fuskarsa kadai ba har a jikinsa dake mazari kamar ana kada masa gangi.
Ka fita a dakina Sarham, don Allah, saboda wallahi bakidaya ka koma min wani musaki….
Kwafa Sarham ya yi ya juya ya fita daga dakin ba tare da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login