Showing 24001 words to 27000 words out of 38778 words

Chapter 9 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala 4 Book By Sumayya TAKORI.pdf

ta taba ganina ba,
sannan ba ita ta ganni ta ce tana sona ba, haka ba iyayenta ne suka ba ni sadakarta wai don ta
makance ba.
Ni na ce na gani ina so a bani, na aureta cikin mutunci kamar yadda na aure ki. Dalilin da
nake ta fada cewa, shi ya sa na aure ta ni ban sani ba, ashe zai iya zama SO. Tunda baka taba
auren macen da ba ka so”.
Yayi shiru yana observing tasirin maganganunsa a tare da ita, da gaske maganganunsa na
dukanta yadda baya zato. Bai damu da yadda fuskarta ta canza tayi jazir ba ya cigaba da
maganarsa.
Na gaji da cewa da ki ke kina kyamar hada jiki da ni wai saboda na auri Hauwau, shin
makaho ba mutum bane, ko shi ba shi da tsarkin addinin musulunci a tare dashi? Madinah ina
addininki ne? Ina imaninki? Ina compassion dinki na likitancin ido? Anya Madinah ke ce? Anya
GIWAta ce wannan ta koma MONSTER haka? Yanzu dai zabin yana hannunki, na ci gaba da zama da mu ko aah, tunda dai na gaya miki
iyakar gaskiyar da ke zuciyata Madinah, da kuma abin da zan iya dauka da wanda ba zan iya
dauka daga gare ki ba. Hauwa zama daram, daga nan har ranar da muka daina numfashi.
Sarham ya mike ya bar dakin ya bar Madinah ta hada tagumi. Sai tsiyayar gumi take yi.
Dakinsa ya koma ya yi wanka ya sanya riga da wando marassa nauyi ya shiga dakin Hauwa sai
ya samu barci yayi awon gaba da ita ya kuma san yunwa ce. Wuyanta ya lankwashe a kan filo,
gyara mata kwanciyar yayi ya fito zuwa kitchen. Tunanin me zai dafa ma Hauwa mai sauki yake yi, don dole ya sanya shiga kitchen da kansa
cikin schedules dinsa na yanzu. Ba zai dogara da taimakon kowa akan kula da Hauwa ba,
tunda shi ya ce da iyayenta da nasa zai iya.
Ko da kuwa Sumayya ce ba zai kawo ta gidan ta zauna wai don ta kula masa da mata ba, sai

dai ta zauna don radin kanta. Yayiwa Mama alkawarin shi da kansa zai kula da ita, kuma zai
fara daga yanzu.

Madinah dai na jin motsi a kitchen ba ta san waye ba, don haka ta fito don ganin waye a
kitchen dinta kada ayi mata barna tunda ta san dai amaryar ba gani take ba.
Sarham ta gani ya yi kace-kace yana aikin girki. Yana hada zufa na rashin sabo. Ko iblis ce
ita, dole ta ji ba dadi a ranta, zuciyarta kuma ta kara gasgata abubuwan da ya fada mata na
matsayin da shi Sarham ya baiwa Hauwa-Kulu a rayuwarsa.
Yana kallonta ta zo kofar kitchen din ta koma cikin sauri, ga jin kishin mijinta na dafawa
kishiyarta abinci ga guilty conscience daya hanata sakat, na cewa bata kyautawa, ta kasa
zaune ta kasa tsaye, a tsakar dakinta, ta yaya ita za ta dinga dafawa miji abinci? Shi kuma ya
zage kwanji yasa ‘apron’ ya dafawa kishiyarta? Kuka wiwi Madina ta soma, abu goma da ashirin ya damu Dr. Madinah Sorondinki, a karshe
ta yanke wa ranta fita sabgar Sarham da matarshi Hauwa-Kulu take ko Kululu! Gara ta saka su
a gefe kafin su manna mata ciwon hauka.
Don cikin abubuwan da ya lissafa bakidaya wato abubuwanda ya bata zabi ciki har dana
zama da shi ko aah? Ko yin muamala mai kyau da matarsa Hauwau, ko ta dinga dafa abinci
tana bata ita tana kwana da miji, ko ta zauna da matarsa cikin aminci, babu wanda za ta iya
aikatawa a cikinsu gabadaya. Don haka ta yanke shawarar yin abinda take ganin ya fiye mata aala, wato komawa aikin
asibiti, in yaso ta dauke ido daga kansu ta bar musu filin gidan ya cinye matarsa Hauwa-Kulu
makauniya Kulu don soyayya.
Amma ita kam ta gama hada jiki da Sarham! Don zuciyarta ba za ta jure sharing miji da
makauniya ba. Sannan ba za ta zabi zuwa gida ta yi rayuwar zawarci da yi masa rainon
Waheedah a gidan iyayenta saboda kishiya ba.
A take ta dauki waya ta buga zuwa Dr. Siddiqah Hospital Jeddah. Zuciyarta a matukar
kuntace. Hakika kishin mijin da kake matukar so abu ne mai matukar ciwo da sai wanda aka
yiwa ne kawai zai iya bada labari. Amma abu daya zamu tuna mu kwantar da hankulanmu cewa
auren mazajenmu sunnar Annabi ne, umarnin Ubangiji ne, na su aura daga abinda yayi musu
dadi daga daya-daya ko biyu-biyu ko uku-uku har hur-hudu, don kare kansu daga dattin zina.
Abinda ya kamata Madinah da sauran mata irinta mu duba kenan, mu sassautawa
zukatanmu.
Ta tabbatar musu da amsar aikinta da ta ce a dakatar sai ta yi yayen Waheedah, Dr.
Madinah dai ta yi kyakkyawan kudiri na fita harkar mijinta a dalilin kishiyar da ta ke ganin ba ta
isa zama kishiyarta ba, saboda makasar ido da Allah ya dora mata da kuma da asalinta.
Har gobe tana son Sarham dinta, kuma matsayinsa bai canza a zuciyarta ba, amma ta yanke
shawarar jingine shi a kan dai ta yi sharing dinsa da Hauwa.
Maganar da ya yi na bata zabi na zama da shi ko aah ya girgiza ta, tabbas namiji ya baka
option na zama da shi ko barinsa to hakika ya kasa jure drama dinka ne. Yanaso ya kawo
karshen ta ya huta.
A rayuwarsu bata taba yi wa mijinta horon yunwa ba amma yau kishi ya koya mata, bata taba
kwararsa a shimfidar auren su ba, amma yau duk kishi ya koya mata har ta kware da hakan, ta
jingine komai na hidimar mijin, wato shi kansa Sarham din ta yafe, da ita kanta soyayyarsa da

ke ranta duk ta basu baya, da bukatuwarta da shi a matsayinsa na mijin da ta ke matukar so
wanda suka gama gina rayuwarsu tare duk ta yafe, tunda har ya iya rufe ido ya yi mata kishiyar
da bata kai ta komai ba, a lokacin da bata taba tsammani ba, don haka duk ta hakura da su ta
barwa yar cikin Badala, watakila ta hakan ne zai gano muhimmancinta da bambancin da ke
tsakaninta da Hauwa.
Asibitin sun tabbatar mata ko a gobe ne ta zo ta yi reporting don suna matukar bukatarta
dama. Don haka tun a daren ta ce ma Hajjah Ramlah gobe za ta kawo mata Waheedah zata
fara zuwa aiki a Dr. Siddiqah.
Hajjah Ramlah da tausayi Madinah ke bata yanzu, don ta fahimci son da take ma Sarham ya
zama jarabta ga rayuwarta, tunda har ya iya yi mata wannan tozarcin, amma ta kasa barinsa.
Ta ce, Ki kawo ta, bayan aiki ma ki kara da ayyukan sa-kai a asibitin gwamnati da
philanthropic ayyuka duka, kuma ki ci gaba da tafiya programs da ki ke zuwa na marriage
coaches rana daya kika daina yanzu, ki bar musu gidan tun safe har dare, in yaso ki barshi da
makauniyar ya ci uwar da zai ci da ita, fitinannen yaro kawai marar godiyar Allah, ina ganinsa
mai kirki ashe macijin sari ka noke ne, in ki ka daina wuni a gidan na ga wanda zai kula masa
da makauniya.
Tunda aurensa ya zame miki jaraba kema dai kamar aka ce shi ne autan maza.
Murmushi Madinah ta yi, Hajjah ba za ta gane ba. Tabbas Sarham shi ne autan maza, amma
a wurinta da duniyarta kadai, don ita kadai ta san ko waye shi, da darajojin da Allah ya yi masa,
wadanda ba duka maza ya yi wa alfarmarsu ba.
Za ta ci gaba da zama karkashin aurensa har karshen rayuwarta, ko da ya sake ta ne a kan
karan kansa to kuwa za ta ci gaba da zaman rainon Waheedah don ba za ta iya auren kowa in
ba shi ba, Sarham is her life, her happiness, amma dole ta jingine shi yanzu, tunda ya ki zame
mata namiji dan goyo. Sannan maganganunsa na yau sun kara kashe jikinta daga tunanin rabuwa da shi
haihata-haihata, amma dole ta janye masa.
Tayi zurfi a wannan tunanin lokaci mai tsaho, tana jin sanda ya gama girkinsa ya rufo kitchen
din, gidan duk ya bade da kamshin farfesun kayan ciki da jallop din cous-cous da Sarham yayi,
don su suka fi masa saukin hadawa. Ya dauka da kansa akan ‘tray’ ya jera duk abinda zasu
bukata ya dauka zuwa dakin Hauwa. Sai Madinah ta yi mishi ‘text messege wanda bata da tabbacin ya gani ko ya karanta, cewa
gobe in Allah ya kaimu za ta yi reporting fara aiki da Dr. Siddiqah hospital.
A karshe ta ce masa “tana neman yardarsa”.

Yana dakin Hauwa sakon nata ya shigo wayarsa don haka bai duba da wuri ba.
Maijidda barcin bayan isha ba shi da kyau, tashi ga abinci na hada mana.
Jin muryarsa ya sa Hauwa tashi zaune daga kwanciyarta, yace ba kya ko cigiyar mijinki cikin
gidannan. Hauwa ta ji kunya na mijinta da ya ce din don dai ita har yau ta kasa sabawa. Wai
Likitan Innane miji agareta.
Ya ajiye abincin akan ‘center table’. Ya zauna daidai kafafunta, idanunsa na bin yatsunta da
suka sha adon baki da jan lalle a hade da Mardiyyah ta yi mata da wani nisantaccen kallo na
yabawa. Sai ya ji motsin shigowar sakon Madinah a wayarsa.
Fiddo wayar ya yi, ya karanta sakon nata. Girgiza kai ya yi, ya kuma mayar mata da

gajeruwar amsar cewa,

Allah ya yi jagora.

Daga haka ya kishingide abinsa a gadon Hauwa, ya dora kansa bisa cinyoyinta, ita kuma
tana zaune tsakiyar gadon ta mike sambala-sambalan kafafunta, ta bar masa cinyar yana shan
raba, ya ce kasa-kasa kamar cikin rada.
Ba ni labarin rayuwar makarantarku BUK, da yadda ki ke coping a aji kullum, I know it will not
be easy for you at all.
Sannan kuma dai an gayamin wai har da samari da Farfesoshin jamia ke bin layi gun Abba,
duk da aure na? Ya fada (with a little bitterness) a muryarsa. Hauwa dai bata tanka ba sabida a
lokacin hannunsa ya kai bisa lallausar tafin kafar ta, ya ja babban yatsanta da wani irin salo, mai
bayyana manufa ingantacciya. Kafin ya mirgina ya kai bakinsa tsakiyar tafin kafar tata ya sumbata. Tsigar jikin Hauwa ta
tashi yarrr! Gabadaya, ta kasa ce masa komai, tana jin sanda Dr. Sarham ya janyo ta bakidaya
jikinsa ya ce,
Maijiddah, zo ki samu lada kinji, wannan yunwar da ke ji tafi wadda nake ji ta abincin dana
dafa mana.
Nan ma shiru ta yi, jikinta ya soma bari, don ba duka ta gama healing ba, kamshin jikinsa da
niimar numfashinsa su suka agaza mata tsoron yake raguwa, lokacin da ya fara sarrafata son
ransa, bakidaya ya hautsina Hauwa-Kulu. Yayi sama da bakinshi a hankali ya bata kyakkyawar
sumba a kuncinta da lips dinta hannunsa sarke cikin yatsunta. Daga nan yace. “wannan barin jiki haka? Ki yi hakuri zan yi a sannu, I promised I will not hurt
you kamar jiya.
Hauwa ta rasa inda za ta saka kanta don kunya, gabadaya Sarham ya shige cikin jikinta, ga
numfashinsu ya sarke wuri guda, wato ya zamanto numfashi guda suke shaka nasa kadai
sabida kusancin da ya assassawa fuskokinsu, da lips dinsu daya sarke wuri guda yana
caressing dinsu softly. Hannunsa ya kai ga zip din rigarta kuma ba tare da ta samu sukunin
rikewa ko gardamawa ba, ya kai zip din kasa. Cewa yake cikin gigicewa.

Na kara janye kalamaina, na kara janye su daga gareki Maijidda, YOU ARE MY LOVE! My
true love and eternal happiness. Not a sister!.

Hauwa ji ta yi hawayen farin ciki na sauko mata ta koina saboda yadda Dr. Sarham ya
himmatu wajen fassara son nan a aikace, by caressing her tears da tsinin halshensa. Ya hanata
kowanne irin katabus, nauikan sumbar yau daban suke, sumbace yake mata kala-kala
naui-nauI data kassara dukkan gabbanta, ta kuma fahimtar da ita irin yadda Dr. Sarham yake
da matukar son sumbatar matarsa har fiyeda ya tara da ita.
Wayyo Inna! Hauwa ta furta cikin son kasar ta tsage ta hadiye ta kawai ta huta da kunyar da
Sarham yake jefa ta a yau.

Wato wannan din ita ce rayuwar da Mama ke mata fighting mata don ta samu, shima kuma
akan karan-kansa ita ce irin soyayyar da yake ikirarin ita baya yi mata a can baya?

Tana iya jin amon sautin muryarsa har zuwa lokacin cikin kwanyarta, a sanda yake cewa, ya
janye kalamansa na baya.

Yau kam ta gasgata cewa Mama Uwa ce ta gari kuma mai sonta da alkhairin da kowacce
mace ke samu a gidan aure, ta yarda Mama Uwar kowa ce ba ta Sarham kadai ba, domin yau
ne ita ma ta san tana da wani boyayyen feeling mara fassaruwa a kan Sarham da ba ta san da
shi ba sai yau. Kuma yau ne ta san mecece soyayyar kanta. Da kyar ta roke shi kan yayi hakuri tana jin yunwa kuma bata yi sallah ba. Abincin da sai da
ya sandare Sarham da Hauwa suka samu cin sa. Kasancewar dama a bowl na tangaran ya
zuba musu baa warmers ba.
Da ya dawo sallah ya samu itama tana sallah, sai ya dauki abincin ya ajiye a kan
‘center-table’ ya jira har ta idar, shi ya zuba musu abincin suka ci a bowl guda.
Tun kafin ma ta gama cin abincin ya karkade gadon ya sake shimfida da sabon zanin gado
hade da duvet dinsa, ya dauke wancan ya saka a kayan wanki, ya gyara dakin ya kimtsa komai
da ta bata a dakin ya fesa room fresh, ya kuma hada mata ruwan wanka.
Hauwa na kammala cin abinci ta ji ta dauke a hannun Sarham. Bai direta ko a ina ba sai cikin
ruwan wankan da ya hada ya saka ta da kayan jikinta da komai gaba daya, yace I wish you
could see.. cewa yau tare Sarham da Hauwa zasuyi wanka abinsu. Gadaya ya sukurkuta
Hauwa, ya kidimata da abinda yake fada. Daga bisani ta dauka marfi take yi saboda alamuran
da yake gudanawar a gare ta masu ruda kwakwalwa ne da kidima masoyi, Hauwa-Kulu za ta
iya cewa a cikin kwamin wankannan ta kara amsa sunan matar Sarham ba tare da ta ankara da
yadda hakan ta faru ba. Amma hakika ta yi dauriyar da shikansa ya yaba mata. Don ba ta yi
wani hobbasa don hana shi samun nutsuwar da ya nemi samu daga gare ta ba don ganin cewa
a toilet ne, ta jure duk ta faranta masa rai a yadda ya bukata.
Shi ma kuma ya biyar da ita ne ta hanyar da ya kara mamaye zuciyarta da so da
matsanancin so da kaunarsa.
Tun daga ranar Sarham da Hauwa suka dinke suka zama abu guda, musamman da Madinah
ta ba su fili ta hanyar fita sabgar mijin kwatakwata, sai hakan ya bashi damar samun wani irin
kusanci da Hauwa-Kulu, Madinah ta fara zuwa aikin dole datasa kanta, su kuma sun zama
tantabaru don soyayya a gida. Wani lokacin yana office da ya samu sararin aiki kawai zai tuko
motarshi ya dawo gida, ya kuma samu Hauwa matan da ake shuara bata nuna gazawa bata
korafi akan dukkan bukatunsa, Hauwa sai yadda yake so ta ke yi, wato sai abin da ya koyar da
ita.
Madinah na tunanin bar musu filin gidan da ta yi shi zai sa Sarham ya yi marmarinta, ya gane
banbancinta da Hauwa, wato ya gane bambancin da ke tsakanin musaka da mai aji, bata san
cewa a fannin matantaka duk mace sunanta mace ba, in dai tanada koshin lafiya kuma tana
kula da jikinta, bata san hakan ya bai wa Sarham da Hauwa damar dinkewa ba suka manne wa
juna suka like kamar tip da taya cikin morar niimar da Allah ya halatta a tsakaninsu, da wata irin
soyayyar auratayya mai wuyar fassaruwa.
Kusan kullum ne Sarham sai ya sato jiki daga office ya dawo gida, don dai ya tabbatar da
lafiyar Hauwa dama kuma Mama ta gama shirya yar ta tsaf, fiye da tsammanin dan Adam, don
haka Hauwa ta gama tashin kan Sarham gaba daya, tunda Madinah ta shata layi a tsakaninshi
da ita tun zuwan Hauwa gidan, a cewarta ta barwa Hauwa, tana kyamar hada miji da mijin

musaka.
Madinah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login