Showing 12001 words to 15000 words out of 38778 words
Chapter 5 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala 4 Book By Sumayya TAKORI.pdf
koina ba. Har ya kai bakin kofa ya juyo. Ya kanne mata ido kamar tana kallonsa. Cikin kankanuwar
murya yace.
This is light kiss, ki shirya ‘hot kiss’ later tonight!.
Hauwa ta danna kai cikin cinyoyinta tana rokon Allah ya sa kasar ta tsage ta shige yau ta
huta.
Mama tana kallon wucewarsa zuwa dakinsa ta baro jamaa ta dawo dakin Hauwa. Gaba
daya dakin Hauwan yanzu kamshin Sandalia ko Oud-Abyad din Sarham yake yi, wato
turarukansa na dindindin (Non-alcoholic Arab perfumes).
Hauwau!
In ji Mama tun daga bakin kofa.
Ashe ni tufka nake kina min warwara?
Hauwa ta kidime iyaka, ta fara mazari na rashin gaskiya murararn. Kada dai motsin data ji
Mama ce? Yau da ta kade har ganyenta.
Mama ta ce cikin takaici,
Ban taba ganin sakarar mace irinki ba, kai jamaa, Allah wadaran rashin wayo.
Sai Hauwa ta soma hawaye nan take kamar an balle famfo. Fadi ta ke,
Wallahi Mama babu ruwana, sai da na ce masa ba zani ba. Ta kifa kai a cinyoyinta tana
rizgar kuka.
Mama ba ta san da zancen fita ba, rikicewa da rashin sabo da karya tasa Hauwa ta fallasa
komai.
Wallahi Mama ban yarda ba, bai yi komai ba nan nan (ta nuna bakinta), kawai na bari, kuma
shi ma din fin karfina ya yi.
Mama takaici kamar ya kashe ta, ta mike tsaye tana cewa, Na kuwa daina tada hakarkarina a
kan a sake ki, don ki auri mai sonki da gaskiya, tunda naga kina son abinki duk rashin kirkinsa,
hada kayanki kafarki kafarsa, kafin a kara yi min abin da yafi karfin idona.
Haba! Hauwa ta rushe da kuka tana, Na tuba Mama, na tuba na bi Allah na bi ki, wallahi ba
inda zan iya zuwa in barki.
Mama ta yi kwafa ta ce, ji min munafurcin Hauwa-Kulu, yau da kika sa kafa kika bishi kika
barni ma na sani? Ni a wa? Bi mijinki a sha soyayya lafiya, da ma tare na ganku.
Na so ki bari mu wujijjiga shi yadda zai kara sanin darajarki, to kin kwashi jiki kin bi shi kun
sha soyayya ko? Bayan ya kwashe shekara bai neme ki ba, da yake ke sakarya ce wadda ta
rako mata, kiss din abun banza ne da ki ka barshi ya samu a arha?.
Hauwa kuka kawai ta ke na nadama da kaka-nikayi ta kasa magana, duk sai ta bai wa Mama
tausayi.
Ta sassauta ta kama hannun Hauwa, ta ce, Ba ki yi min laifi ba Hauwa kin ji, kuma ba ki yi wa
Ubangijinki ba.
Karewa ma lada ki ka samu kinji.
Ni na san Sarham yana sonki duk abin da nake yi kuma ina sane. So nake in sa shi ya gane
da kansa yana sonki ba auren jihadi da taimako ya yi da ke ba. So nake ya furta min da bakinsa
ya janye kalaman kanwar nan da yake jifanki da ita, It does hurts me a lot!
Karshen kaskancin da namiji zai miki kenan, ya tari gaban idon ki yace, ba ya miki so na
soyayya. Sarham ba shi da saiti, ki bar ni in saita shi yadda ko wani ya ji ya ce ke kanwarsa ce
zai musa da bakinsa yace aah matata ce abar so na.
Hauwa na kuka da sharbe ta ce,
Insha Allah Mama ba zan sake yarda ba.
Tausayi ya kama Mama don kuru-kuru ga soyayyar lelen Abba nan ta fito yau a idonta, da ko
gani ba sa yi, ina ga suna ganin cool kamanninsa da kyakkywan sajen sa da murmushinsa mai
daukar hankalin mata?
Mama ta tashi ta fita kwallar tausayi fal idonta.
Mardiyya ta dawo dakin tana cewa,
Anti ba ki ci abinci ba, Anti don Allah ki daina kuka yana daga min hankali.
Ta hau share hawayen da gefen mayafi ta ce, Na daina Mardi!.
Ta ce, To abincin fa?
Sai an jima, ki kulle mu ta ciki, ko Yaya Doctor ne ya buga kada ki bude kin ji? Murajiar
karatuna zan yi.
Taje ta dauro alwalla, sai ta ga cewa ba za ta iya alwala a haka ba, dole sai ta yi wanka don
abin da ba ta taba gani ba ne ta gani a tare da ita yau.
An gaya mata kuma da jimawa wankan iri daya ne da na sallah.
Ta yi sallah ta dora da nafila ta zauna tana murajiar karatun da Mama ta kara mata jiya.
Cikowar yan uwansu da abokan arziki a gidan ma bai barshi ya iya sake shigowa da
daddaren ba balle ya tadda kofar tasu a kulle da mukulli bisa umarnin ko ya buga kada Mardiya
ta bude.
Dangin mijin Surayyah suka ce su a wannan ssatin zasu dauki amarya zuwa Ikko don haka
dole aka zarce da bikin maimakon sai sati mai zuwa da mama ta saka. Don haka a washegari
aka yi wunin Surayya a Gadon Kaya, da daddare dinner sai shirin kai amarya gidan su Engnr.
Aliyu a Dorayi washegarin ranar. Hauwa ba ta je dinner ba ta kulle kanta a daki, amma Mardiyya ta je. Mama ta sameshi har
dakinsa ta kora masa ‘warning’ din kada ya kara shiga dakin Hauwa sai ya zo mata da hukuncin
da ya yanke wa zamansu.
Shi ma kuma yana ta nasa shirin duk don ya wanke ran Mama, ya kuma yi ‘repenting’
kuskurensa, tuni ya karbo passport din Hauwa ya kai gun visa.
Yan biki duk sun watse bayan an kai Surayya family house din su mijinta. Yau kwana uku
kenan Mama na gadin Hauwa, ta hana shi kebewa da ita. Ta hanashi rawar gaban hantsi.
Iyakar tsaka mai wuya Sarham ya shige ta don sosai yake cikin bukatuwa da Hauwa, don haka
ya maida hankali wajen sakin kudi a yi a gama visarta. Ga Abba ya ki shiga maganar, ya ce shi
a bayan mai sharia yake.
*** *** ***
MUTANEN JEDDAH
Sumayyah ce kadai zaune a falon gidan Yayanta tana karatu da gilashi a idanunta, aka
danna kararrawar son shigowa, Sumayyah ta mike ta aje littafin da ke hannunta tana fadin,
Naam, ina zuwa. A zatonta Madinah ce ta dawo daga unguwar data tafi.
Tana budewa suka yi tozali da wani sardidin saurayi son kowa. Amma kuma fuskarsa looks
so familiar to her.
Ya yi mata murmushi, ya ce, Salam, how are you? Tana ciki ne matar gidan? Na kasa kama
ta a waya”.
Sumayyah ta kasa magana, don gayen ya kai makura wajen kyau, ga tsafta ga sanyin murya.
Da kyar ta iya cewa, Ba ta nan!.
Sai ya mika mata wata leda ya ce, ok. Please ga shi ki bata, kice in ji Hajja Ramlah.
Hannun Sumy na rawa ta karba sai ya ce, Ke bakuwa ce suka yi halan daga Nigeria?
Eh. Kawai ta ce.
Ya ce, Ok, toh. Ki gaya mata zan dawo bayan magriba. Sunana Usman Attahiru, yaya sunan
malamar?
Oh! Are you? Usman?
Ya ce, Yeah.
Anti na yawan zancenka, ina ji kullum. Nice meeting you.
Ya ce, Na gode, kin san sakuwata ce. Kullum fada muke a baya, ina cin zalinta in more,
shiyasa yanzu nake kyautata mata, na maida kaina ma direbanta at times, don in wanke
kuruciya mara dadi da muka yi nida ita.
Duk suka yi dariya mai sanyi.
Ya ce, Ya sunanki?
Sumayyah Abbas.
Oh-oh! Ko ke ce Sumayyah kanwar Baban Waheedah?
Eh ni ce.
By the way, nice to meet you too Sumayya, I love the name.
Cikin murmushi Sumayya ta ce, Na gode Uncle Usman. A gaida gida.
Bayan tafiyarsa Sumayyah ta adana sakon, amma sai ta kasa zaune ta kasa tsaye, Usman
Sorondinki da muryarsa ya tsaya mata a rai farat daya, irin yadda wani namiji bai taba shiga
ranta ba.
Madinah na dawowa Sumayyah ta bata lokaci ta kintsa, kafin ta kai mata sakon har dakinta,
karonta na afarako da sanya kafarta a dakin Madinah tun zuwanta gidan. Ita kanta Madinah ta
sha mamaki.
Ya zo nan kadan kafin dawowarki, yace shi Yayanki ne, wai Osman sunansa.
Oh! Zai dawo an jima, mun yi waya na manta da zuwansa ne na fita.
Sumayyah ta ci gaba da shiru a tsaye, ta kasa tafiya, Madinah ta ci gaba da sabgoginta ta
manta da ita. Ganin haka ta ja matattun kafafunta ta fito daga dakin.
Ko da ya dawo kamar yadda ya ce zai dawo, Sumayyah ya cimma a falo Madiah tana daka
tana sallah don haka suka balle da hira shi da Sumayyah, kan kace meye wanan sabo ya fara
shiga tsakanin Usman da Sumayyah, bini bini ya zo gidan bayan ada sai in Madinah ce ta kira
shi ko Hajjah Ramlah ta aiko shi, ya zama suna dasawa sosai har ta kai su ga karbar lambar
wayar juna.
Kafin ka ce me? Madinah ba ta ankara ba aka soma yi mata midnight call’ a gida. Sumayyah
har mantawa ta ke Usman Attahiru Yayan Anti Madinah ne, gabadaya ta rufta nan take, kafin
dawowar Sarham.
Ranar da Madinah ta fahimci wai soyayya ake tsakanin Sumayya da Usman ta sha mamaki,
at the same time a take anan ta nuna wa Usman rashin goyon bayanta, da hujjarta na cewa
Sumayyah tun fil azal ba ta kaunarta, kuma an gaya mata ita ce ta hannun daman matar
wulakancin da sarham ya auro mata. Usman kuma ya ce mata, a gaskiya shi bai son gutsiri tsoma irin na mata ba, ya ga
Sumayyah ta yi masa, komai nata ya yi masa ba ruwanshi da shirmensu, Sarham kawai yake
jira ya dawo ya gabatar da kansa.
Madinah ta lashi takobin ita kuma sai bayan ranta Usman zai auri makiyarta. Ko mata sun
kare a duniya bazata bada goyon baya ba, dama dai Surayyah ce kuma tayi aure ita.
**** **** ****
KANON-DABO
A
ka kawo masa visa din Hauwa a wayewar garin litinin, bayan an gama bugawa. Mama na shirin
fita office sallamar Sarham ta dakatar da ita. Ya shigo dakin da karfin gwiwarsa yau dai, da
kallon marairaita da karbar laifi, suka gaisa shi da Mama ba yabo ba fallasa.
Cikin brown envelope ya mika mata abu,
Ga shi Mama na karbo!.
Mama ta amsa ba tare da ta san meye a ciki ba, tana kokarin budewa ta gane passport ne.
Za ta fara fadan har yaushe aka je aka yi passport din ita bata sani ba, ta tuna subutar bakin
Hauwa na cewa, sun fita da Sarham kwanaki. Ta yi kwafa kawai ta aje a gefe ko bude visar ba
ta yi ba balle ta ga wace iri ce ko ta wata nawa ce. Murya fal ladabi Sarham ya dukar da kai
yace, Mama kin yi izni za mu iya tafiya tare? Already na yi mana booking jibi ne tashin namu insha
Allah.
Mama ta yi shiru, ya ci gaba da roko, da ban hakuri da ban baki da alkawarin bazai kara
maimaita kuskurensa ba kuma zai kula da Hauwa tsakaninsa da Allah. Da kyar Mama ta ce,
To karatunta fa?
Ma yi wannan shawarar daga baya in mun je naga yadda abubuwa zasu kasance.
Mama sai ta kasa musantawa, tunda abin da ta ke rokon Allah dare da rana ne yau Ya amsa
musu. Sarham ya dawo kan hanya kuma ya fahimci kansa. Ko bai fada ba ta ga ‘seriousness’ a
kan Hauwa wannan karon a tare da shi sosai.
Duk da haka ta kawo nata kalubalen na cewa, ya zai tafi da Hauwa babu Mardiyyah?
Wa zai dinga taimaka mata?
Sarham ba tare da tunanin komai ba, ya ce, I will take care of her, my self Mama, for the
mean time, kafin in yi deciding akan ko zan iya daukar Mardiyyar a gaba. I will do everthing to
undo the hurt I caused you Sweet Mum.
Mama tayi ajiyar zuciya a karshe, ko bata ce ba hakan na nufin amincewarta.
Hankalin Mardiyyah ba karamin tashi ya yi ba jin Mama ta ce ta hada wa Antinta kaya za su
tafi Jeddah.
Mardiyyah tana kayan Hauwa a jakar matafiya tana kuka wiwi, amma ta danne bakin da
dankwalin ta kada Hauwa taji kukanta, amma saida taji sheshsheka. A kwance take amma
saida ta tashi zaune tace Mardhiyya lafiya? Ta gaya mata abinda aka ce da ita. Hauwa kanta
jikinta yayi wani irin sanyi. Mama ta alkawarta ma Mardhiyyah tafiya Saudiyyah tare da ita duk
lokacin da za ta je umrah, kuma ba za ta mayar da ita Shanono ba ko ba Hauwa a gidan, za ta
ci gaba da zama tare da ita ne har aurenta.
Hauwa kanta na kasa, ko dagowa ta kasa yi sabida nauyin Mama da damuwar data cika
ranta. Mama lakca guda ta hau yi mata a kan ta zauna lafiya da kowa da zama ya hada ta da
shi, kuma ta girmama Madinah tunda ko a girme ta girme ta, ba a aure kawai ba.
Ta ce, Na san ba ki da matsala ko kadan a kan girmama na gaba da ke Hauwau, amma
zaman mata biyu karkashin inuwar miji daya sai an daure an kai zuciya nesa ba kusa ba. in ba
haka ba duk zaku taru ne ku kai junanku wuta. Ki sa a ranki ibadah ki ka je yi domin zaman
aure ibada ne Hauwa, balle wanda ya zamo ku biyu ne a wurin mijin. Jikin Hauwa bakidaya ya yi laasar ta soma hango babban kalubalen dake gabanta, nan take
ta ji kamar ta ce da Mama babu inda za ta je, amma ganin yadda Mama ke ta kai da komowa
wajen yi mata shirin tafiyar, da bata magungunan da bata san ma kona menene ba da yadda
Sarham din kansa ya dauki komen nata Jeddah da matukar muhimmanci sai ta kasa magana,
duk da Mama ba ta kara bari sun kebe ba, ta maida Hauwa dakintama kwata-kwata ana saura
kwana biyun su tafi, tana ta yi mata kyakkyawan shiri da tsumi kala-kala da tukudi.
Ita kanta Hajiyar Abba, wato Hajiyar Gadon Kaya cewa tayi ba ta ga dalilin zaman Hauwa
tare da su ba, in makaranta ce ai babu inda babu ita. Kada su sake su bata mata rai su tattara
mishi Hauwa ya dau kayarsa. In don rashin ido ne ya sa Mama ajiye ta shekara guda a daki ai
ya fi kowa sanin ba ta da idon ya je ya auro ta. Ranar sun sha fadan Hajiya Kulu wadda ta yi tattaki har gida ta sille Mama da Abba don
Sarham ya gaya mata takunkumin da Mama ta saka masa na saki, da yaki kuma ta kuma hana
shi ko magana da Hauwa.
Shi ya sa ma ranar da ya kawo visa mama ba ta yi dogon jainja ba, don Abba ya ce a daina
yin duk abin da zai saka Hajiya Kulu yin fada, saboda BP dinta.
**** ****