Showing 27001 words to 30000 words out of 38778 words
Chapter 10 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala 4 Book By Sumayya TAKORI.pdf
kam sai dai ya gode mata da wannan filin da ta bashi yake wani irin amarci kamar
bai taba samun lafiyayyar mace a hannunsa ba sai a kan Hauwa. Shi da kansa ya hana
Sumayya dawowa gidan, ya gaya mata ba yanzu ba, sai sun gama honeymoon, kada tazo ta
bata masa mata da kilbibi. Ko daga nan Sumayya ta gane Hauwa komai zamzam, don ko waya bata samun amsawa
yanzu, kullum likita na makale da ita, ta nan Sumayyah ta gane komai ya fara saisaita. Farin
cikin Sumayyah ya kasa boyuwa. Ga Usman ya like yana bin Sarham da gaske yana so ya turo
ayi tambayar aurensa da Sumayya. Sarham kuma yana basarwa yana cewa ya nemi
amincewar Madinah.
Madinah wadda a lokacin fama take da kanta, cikinta ya fara girma da ga matsaloli irin na
mace mai juna biyun da ya fara tasawa, ga rashin kwanciyar hankalin data sawa ranta na
barranta kanta da rayuwa da mijinta, wanda ta debi shekara da shekaru cikin fafutukar
samunsa. Wannan yasa ba tareda sanin ta ba, a tsaitsaye BP dinta ya hau, yau tana asibitinsu
tana duba patient mai hakiyar ido, Hauwan Sarham ta fado mata a rai. Tsaki tayi kanta yayi
mugun sarawa, kawai sai ta saki komai ta dafe kanta, ta sulale a kujerarta cikin wani hali na
unconsciousness. With high blood pressure.
Nurse din da suke tare suna duba patient din ce ta ankara da gushewar hayyacin Dr.
madinah, tayi maza ta yi kanta ta, kuma dinga danna ‘alarm’ na kiran likitoci da gaggawa.
A karshe gado aka baiwa Dr. Madinah a asibitinsu. Nan da nan aka shiga bata taimakon
gaggawa don tana bleeding, kokarin su shine su tsayar da cikin jikin ta amma a karshe suka ga
tsayar da shawarar gara su cire shi don ceton nata rayuwar.
Sarham na asibiti yana aiki Usman ya kira shi wai yazo yasa hannu zaa yiwa Madina tiyata a
Dr. Siddiqah.
Tsananin kidima data same shi a lokacin manta hanyar asibitin nasu yayi sai Usman ne suka
hadu a hanya yayi masa jagora.
Ya samu duk yan gidansu Madina sun riga shi hallara a asibitin shikadai ake jira amma kafin
ya zo ma Daddy ya kulu ya saka hannu yace a shiga ayi mata, ciki kuma a cire shi in shi ke
bata matsala. Babban Yayansu Madinah wato Abubakar Attahiru yace Daddy baka da wannan
hurumin fa, ka bari mijinta ya karaso. Sai gashi ya shigo kamar an jefo shi shida Usman. Daga kallon da Hajjah Ramlah take masa duk ya sha jinin jikinsa. Amma ya maida hankali
ga yin needful, wato ya saka hannu aka shiga da Madina dakin tiyata.
Dukkansu jigum-jigum sukayi a reception shida iyayen Madina da yayyenta, Hajjah Ramlah
ta kasa shiru tana tsane ido tace wallahi in Madinah ta rasa ranta saboda kai Sarhamu, bazan
taba yafe maka ba, tun farko ai nace ta hakura da aurennan babu dole tunda har zaka iya rufe
ido kayi mata kishiya da makauniya nace ta hakura, amma da yake kunnenta na kashi ne ta
zauna a gidan kuna guma mata takaicin da yau yake neman ranta.
Alhaji Attahiru Habibu Sorondinki, ya kankance ido akan matarsa yana neman karin bayani
yace me ke faruwa wai? Ki yi min bayani. Hajjah Ramlah na kuka ta zayyane masa komai cewa
Sarham kara aure yayi da makauniya yar talakawa shine fa tun lokacin Madina take boye musu
itama daliline yasa taji data yi tsami tsakanin ta da kanwar mijin nata. Alhaji Attahiru jikinsa har tsuma yake ya nuna Sarham da dan alinsa yace wallahi in ya ta ta
mutu sai nayi karar ka, azzalumi wanda bai san mutunci ba. ai shiyasa tun farko naki yarda ta
aureka don yayan talakawannan ko a tandun mai aka saka ku sai kun fito kandas wajen nuna
halinku na rashin halacci. Banda mutuwa mai tonon asiri ai Madinah matar manya ce ba irinka
ba.
Kan Sarham a kasa yana jin cin mutuncin da Daddyn Madinah ke masa bai dago ba saida
Daddyn yazo nan. Ya dago a hankali ya dubeshi idanunsa sun kada kamar gauta amma uffan
ya kasa cewa. A lokacin aka fito da Madina daga dakin tiyata zuwa dakin jinya aka kuma hana
su shiga sai bayan awa daya. Saida Madinah ta dawo hayyacinta aka bar su suka shiga, family dinta suka rufu a kanta
Waheedah na hannunHajjah Ramlah shi suka manta da shi a gefe. Abin yayi masa ciwo kwarai
sai Usman ne ya zo ya kama hannunsa zuwa kan Madinah. Ta dube shi, ya dubeta suka kuma
hada ido, ta lumshe idanunta bata kara budewa don bata son ma ganinsa a kanta. Da aka bata sallama ma bayan kwana uku gidansa Daddy ya tafi da ita ba tareda nemsn
iznin Sarham ba. ciki kuma an cireshi bayan ya fara girma.
Ko kusa Hauwa bata san me yake faruwa ba amma ta lura Sarhamya rage magana kuma
baya cikin walwala kamar da. Shiyasa yau da Sumayyah ta nemi zuwa gidan don tayi weekend
tare dasu bai hanata ba yace tana iya zuwa dakinta yana nan. Hauwa kuma yace su koma nasa
dakin don nata yayi kusa dana Sumayyah, ta tambayeshi ko hakan bazai zama matsala ga Anti
Madinah ba? sai yace bata nan tayi tafiya. Da haka sukayi parking dakinsa soyayya a
tsakaninsu sai abinda ya karu.
Jumaah da yamma Sumayyah ta iso gidan daga makaranta.
Har ila yau, shi da team dinsa na Saudi-German suna ci gaba da shirye-shiryen aikin idon da
za su yi wa Hauwa.
Tun ba a je ko ina ba Sarham ya gane shigar ciki a tare da Hauwa, tunda yanzu tare suke a
daki guda duk wani motsinta ya sani. Wanda ita koda wasa bata san da cikin ba.
Kasa shiru ya yi don farin cikin da ya cika shi, wani na tafiya rariya wani na zuwa, har sai da
yayi mata shagube cikin tsokana.
Ya daga PT strip din da ya auna fitsarin ta, yace wai yanzu Hauwa-Jiddah daga zuwa sai
ciki? Bazaki barni ma in gama yada samartakata a jikin ki ba mu tsufa tare? Kamar wadda ta yi
tuntube da shi a dokin kofa?
Hauwa saita saka kuka don tsakani da Allah ta tsorata da wannan maganar, ciki fa na
haihuwa yake nufi? Ta yaya ta sameshi ma bata sani ba.
Yace Cry more Sweetheart, wani kukan ma sai an je labour room!.
Sabuwar kulawa, sabon amarci ya balle wa Sarham da Hauwa a dalilin wannan niimar da ke
tattare da mace mai yaron ciki. Sarham da Hauwa sai sam-barka, a yayin da Dr. Madina ta yi
nisa kan ayyukanta na Dr. Siddiqah, da ayyukan tiyatar ido na sa-kai (philanthropic eye surgery)
da takeyi don taimakon marasa karfi bayan ta warke daga tiyatar da aka yi mata. Daddy ya tabbatar mata tunda Sarham yaki sakinta ta ruwan sanyi kamar yadda ya bukata,
wallahi kotu zaiyi kararsa sai ya saketa. Bazai zuba ido ya kashe masa ya ba.
Hankalin Madinah yayi matukar tashi gashi an hanata sauraron Sarham. Aka ce tsakanin
mace da miji sai Allah, lokacin da ta sauko tana son ta karbi mijinta ya dade da sabawa da
Hauwa, irin sabon da ko ita Madinah da ya kwashi ‘decade’ yana soyayya da ita bai yi shi da ita
ba.
Kasancewar shi ne komai din Hauwa a gidan, dakinsu daya makwancinsu daya kullum,
kullum kafin ya fita sai sun karya kumallo tare wanda shi yake sarrafawa da kansa, da rana
kuma zai sa ‘mudam’ din cikin estate dinsu su yi mata home delivery’ na abincin rana, idan
kuma ya dawo da daddare ya girka musu. Yayi musu wanki a injin wanki ya zauna zaman goge
mata abayoyinta da hoover.
Ita da kanta Madina ta koma tunanin anya wannan sabuwar rayuwar ta zaman gida da
iyayenta suka zabar mata mai billewa ce? Gashi mijin ba sakinta yayi ba yanata bin Daddy har
office da ban hakuri itama Madina yana bata. Ta soma tuno yadda yake saka apron ya shiga
kitchen yana girki tukuru domin hidimtawa miskiniyar matarsa. Duk a kokarinsa na sauke
nauyinsu su duka da Allah ya dora masa da kuma cewa da tayi baza basu abinci duk ranar
girkinHauwa ba.
Ta yarda Sarham ba mijin yadawa bane domin nagartarsa ta wuce ta sauran mazan da
ubanta ke mata hange. Don haka ta soma tunanin mafita, wato yadda zata koma dakinta ba
tareda daddy yayi fushi da ita ba don ita kanta ta san Sarham bai yi mata laifin komai ba laifinsa
daya ne kara aure na tawaliu. Don haka ta koma lallashin Daddynta, ta tuna sanda Sarham ya
ce in har ba za ta dinga dafawa tare da Hauwa ba kuma ba za ta yi muamalar makwabtakar
musulunci da ita ba, to ya yafe cin abincin nata shima da take ajiyewa a dining ta fita.
Ta tuno irin kalaman batancin data ke masa amma duk Sarham ya shanye bai taba korarta
daga gidansa ba. Irinsu;
A wane dalili za ka ce wai lallai sai na zama kukun matarka? Ka gaya min inda shariah ta
dora min wannan nauyin.
A wane dalili za ka dage lallai sai na yi muamala da matarka? Na gaya maka in na raina
kasuwa ko sauti bana bayarwa a cikinta.
Shin ajin rayuwata da na matarka daya ne da za ka ce sai na muamalanci wadda ko
matsayin zama yar aikin gidanmu ba ta kai ba?
Ire-iren kalamanta kenan gareshi tun zuwan Hauwa, da saidai Sarham ya daga ido a hankali
ya dubeta da wani irin kallo na mamaki da disappointment.
Ya ce,, In wani ne ya gaya min cewa Madinah za ta rasa hankalinta, kyakkyawan tunaninta
da iliminta na jin kan alumma kai har ma da imaninta, a dalilin KISHI wallahi zan musa. Sai dai
kash! Im witnessing it myself to the mere of my disappoitnment.
Ina fatan wannan halin da ki ka ara ki ka yafa babu gaira babu dalili ba zai shafi rayuwar
yayana ba, wato ba zai sa ki raba min kansu ba. Da sunan Mamar wadancan ba ajinki ba ce. Ya
Allah ka cire rabon shaidan daga zuciyar matata Madinah.
Ya Allah Ka raba ta da GIRMAN KAI da superiority complex wanda shi ya hallaka Kakanmu
Annabi Adamu A.S.
Daga fadin hakan sai ya sa kai ya bar mata dakin. Jikin Madinah ya yi matukar sanyi yau, da
tunaninta yazo nan, irin sanyin jikin da rabonta da shi har ta manta, tunda Hauwa tazo zuciyarta
ta zama gardamammiya ta tsaya cur a kirjinta sai yau ta russuna.
Dr. Madinah Attahiru. Ta soma kokarin tattaro ragowar mutuncinta wanda ta san, har abada
ba mai gushewa ba ne daga idanun Dr. Sarhamu.
Itada Usman sukayi shawarar Sarham ya gayawa Haj. Lailah hukuncin da Daddy yayankewa
auren ta. tace ita kuma tanason komawa dakinta bazata kara tada hankalinta ba.
Haj. Lailah suka shiryawa zuwa Saudiyyah itada Usman musannan don ta lallashi Daddy tayi
sasanci, har bukatar Usman na auren Sumayyah sun gayawa Haj. Lailah ita kuma ta kama
Attahiru da fada tace wannna ba gata yakewa yaransa ba yaranma sun fi shi hankali, ita Madina
wacwcw data fi karfin ayi mata kishiya? Taga Nana Aisha da Nana Khadija ma duk da kishiyoyi
suka zauna. Tayiwa Daddy kaca-kaca ta kuma saka shi ya kira Sarham a waya yace ya zo ya
dau matarsa.
Sarham a take ya baro office yaje ya taho da Madina daga gidan mahaigfinta. A hanya kuma
kafin su iso gida suka kara dinkewa, suka fabhimci juna, ya kara yi mata kyakkyawan bayanin
da yafi na baya akan Hauwa da muhimmancinta ga rayuwarsa kuma ba wadda za iya bari
saboda yar uuwarta. Abu na farko da Madinah ta fara yi bayan dawowarta gidan shi ne, in za ta fita office ta kan
leka ta ce wa Hauwa za ta fita, Hauwa da yake bata kullace ta kamar yadda ita ta kullace ta ba
sai ta amsa har da adduar.
Allah yasa a dawo lafiya”.
Ya dawo gida yau da wuri than usual ya samu Sumayyah ta zo gidan, suna falo itada Hauwa.
Lokacin an kai kudin auren su itada Usman Kano. Duk basu ji shigowarsa ba daga ita har
Sumayyah sun baiwa kofa kofa baya. Sumayya na mata famfo irin na yaran likitoci.
Wallahi Aunty Hauwa kin bari kinyi saurin samun ciki, maimakon ki bari sai nan da yan
shekaru biyu haka kina sa shi kuna yan dabaru da bazasu cutar da lafiyarki ba, not necessarily
family planning na asibiti ai kin gane, amma kawai kika bari kika dau ciki as early as six month
da zuwanki ko amarcin baku ci yadda ya kamata ba. Ga zancen aikin idon ki ya shantakar dashi
tunda ya lura kinada ciki, kuma ke kullum yazo shikenan sai ki amsa kira ba dan jan ajin nan
namu na mata koyaushe yake so zai samu, ai ni wallahi sai mun shekara uku nida Usman kafin
mu fara tunanin tara yara, kuma sau biyu ko sau uku a sati zan ke yarda, ba kya ko tunanin
yaya ake haihuwa, bafa sauki ne da ita ba, ke kinga yadda mata ke gumurzu a dakin haihuwar?
Alhalin in kin haife shi ke ba ganin dan zaki yi ba, maimakon ki bari sai bayan aikin idonki muga
abinda Allah zai yi.
I am imagining yadda zaki raini yaro a hannunki without seeing him, it will not be easy for you
a halin yanzu, ga Bhaiya ba hakuri kullum yana like dake ko zama a office baya yi sosai yanzu,
baya barinki ki huta ko kadan ki maida jikinki, bayan ana son gap don a maida ruwan jiki,
shiyasa sanda Madinah ta tafi bai damu da tafiyar ta ba, ya san yana hutawa sosai, har fiyeda
in tana gidan. Na tabbata ita ba haka take barinsa yana caskalar ta kullum ba, duk kin wani
rame kamar ba luscious Hauwar Mama ba.
Yanzu da kin haihu baby yana tsotseki, shima ba hakura zai yi ba, duk su taru su tsofar dake
(at twetieth) dinki. Maganar karatunki ma naga alama ta bi ruwa, Mama tayi tayi ya dawo dake
in bazai saki a makaranta ba har ta gaji ta zuba masa ido.
Sarham ya yi maza ya koma da baya ya bar gidan, yana lissafa irin yadda zai ci uban
Sumayyah laada waje.
Asibiti ya koma ransa a mugun bace da Sumayyah. Ya kirata a waya lokacin tana dakinta ita
kadai ta bar Hauwa cikin zurfin tunanin, kome Summy ta fada haka ne Sarham baya tausayinta
ta wannan fannin kuma ta tabbata ba haka yakewa Madina wannan rashin tausayin ba, kullum
ba hutu kamar ya samu engine har gashi mutane sun soma noticing tana ramewa. Dole ta sake
lale itama ta koyi jan aji kamar yadda Sumayya tace.
Sumayyah na dagawa da sallama yace Summy! Tace naam Bhaiyana
Ba wani nan. I am no more your Bhaiya daga yau. Fito ki bar min gidana kada ki lalata min
tarbiyyar matata.
Na rantse da Allah in sha Allah wata mai kamawa zaa tattaraki ki tafi naki gidan mijin, shi ki
je ki ja masa ajin ki gane in zai yi tolerating iskancin ki, kada in kara ganin kafarki a gidana sai
kin haihu kinsan ciwon haihuwa da darajar mijin aure.
Sumayyah ta bude ido da baki a tare, nan ta gane ya ji gulmarta. Ta soma afi tana hurwar
kayimin rai na tuba Bhaiya, kayimin aikin gafara Bhaiya, subutar baki ne, I dont really mean it.
Yace subutar baki ko raayin banza na mata yan duniya kike son cusa mata, naki nayi mata aikin
idon, da can ke kika sani? Ko kuwa mace na fama da kanta sai in kwantar da ita in fede mata
ido wani abu ya samu Baby na? Wallahi Sumayyah kilbibinki ya isheni dama nasan kina kaita
Saloon a cikin estate kuma na gaya miki tun na farko bana so, tunda ina sayo mata shampoo
na wanke kai dana zaba mata, wanda bazai canza mata launin gashin kanta daga asalin na
hausawa ba.
Sannan ina sane da cewa kin kawo mata wasu mayuka da sabulai na banza da hofinki, wai
irin wadanda kike shafawa, kina so ki koya mata bleaching ne? Na taba ce miki kina da kyau ko
shafe-shafen yammata yana burgeni? Itada ko ido babu!
I am observing you Summy, ke shaidaniya ce wasa-wasa, duk abinda kike yi wai ke a dole
sai kin mayar min da mata yar duniya ko, na ce bansan kalarta bane sanda na aureta?
Ko bansan yadda gashinta yake ba? Ko nace miki in farin fata nake so na Madinah bai ishe
ni ba? Ke dai wallahi Usman ya shiga uku, Maijiddah ki bar min kayata yadda nake sonta, muna
zaman