Showing 30001 words to 33000 words out of 38778 words

Chapter 11 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala 4 Book By Sumayya TAKORI.pdf

mu lafiya cikin fahimtar juna da kula da bukatun juna zaki hargitsa mu ko, kema kuma
zuwanki kasar nan ne duk kika fara wadannan duniyancin. A da ba haka kike ba wallahi
Sumayyah.
I love my wife and her natural beauty, dont dare try to change her for me.
Haka ya cashewa Sumayyah son ransa, har saida ta fidda kwallah. Cewa take In sha Allahu
Bhaiya bazan sake ba. na tuba nabi Allah na bi ka.
Kafin in dawo ki tabbbatar kin bar min gida na, tunda ba nida ke muka hada kudi muka auri
Hauwa ba.
Jikin Sumayyah na rawa ta shiga dakin Hauwa ta dau jakarta tace Anti Hauwa wannan mijin
naki hummm! Sai Allah ya baki hakuri, kinsan Allah mijin ki aljani ne wajen jin magana, Mama
tace haka yake da zuqo zance a kunnuwansa tun yana yaro, na tafi, sai an kwana biyu.
Bata kuma gaya mata yaji komai data fada ba. Ta bar Hauwa cikin sake-sake tayi tafiyarta
tana cewa Summy kiyi min bayani mana? Daga can bakin kofa ta ce in yazo yayi miki fashin
bakin da kansa kuma bazan kara baki shawarar komai ba, daga yau ba ruwana da sabgarku,
mijin ki ya maida ke duk yadda yake son ganinki, ni dama nawa shawara. Murmushi Hauwa tayi tana fadi cikin ranta Sumayyah da Bhaiyanta ba dama ne, ayi fada ayi
dadi. Inama itama Zulkifl yana raye da haka zasu zama kamar Sumayyah da Bhaiya, yau fada
gobe shiri. In suna shiri kuma sun fi kowa ji da juna.
Sarham bai dawo gidan ba sai dare, yana hanya ma Madina ta kira shi tace motarta ta baci
yazo ya dauketa a asibiti sai ya biya ya dauketa sannan suka wuce gida, suka tsaya suka yi
take away na pizza da KFC don yau girkin Hauwa ne bana Madina ba ko ya saya ne ko ya girka
musu, don har bayan Madina ta dawo bata karbi yiwa Hauwa girkin abinci ba saidai in ta dafa

yanzu tana zuba musu ranar nata girkin.
Suna shiga gida ya nufi dakin Hauwa, ta sha wankanta tana shafa mai ga hoda a gefe. Yayi
salama ta amsa, ya bata peck a kumatu, ya shafa cikin ta wanda zuwa yanzu ya soma turowa
cikin zani, yace hope hes kikcking well? cikin rashin fahimta tace waye? yace baby! Mai sunan
Innata. Ta kare fuska da tafin hannunta ta ce aa gaskiya mai sunan Mama ce Yaya doctor. Nan
suka hau gardama yace sai an fara saka Inna ita kuma tace sai an fara da Mama.
Daman jiranka nake ka dawo, in shafa hoda ka gayamin ko tayi daidai? Shiyasa tun dazu ban
shafa ba yana fesa turare ya juyo ya ce ba na ce ki dinga shafa abarki ko yaya ba? in tayi yawa
inna dawo na gani zan gyara miki? ta soma shafawa ya koma daga bayan ta ya dora kai a
masangalin wuyanta fuskar shi da tata cikin mudubin hannun ta sun yi kyau har sun gaji, sun yi
matching dukkan su choculate incomplexion da wani irin annuri da hasken imani a fuskokinsu.
Daga nan Sarha ya kama hannun ta ya cirata tsaye ya soma kokarin kai mata sumba, nan da
na ta noke ta ja baya, ya sake rikota yace lafiya? idonta narai narai tace wai mu bazamu dinga
hutawa bane? Ina laifin sau biyu a sati ni gaskiya.. Nan da nan ya gane hudubar Sumayyah tayi
aiki ta wanke mata kwakwalwa, yace ok. Ok to bari kiji in gaya miki daga yau Sumayyah na
koreta kada ta kara zuwar min gida. Ya suri mukullin dakin shi ya bar dakin, yayi fushi sosai,
kuma gashi girkinta ne bana Madinah ba don haka ya koma dakinsa ya kunna laptop ya hau
aikin da bai yi a asibiti ba.
Hauwa duk taji guilt ya dameta data tuna tafiyar Summy ba shiri da abinda ta fada mata sai ta
gane yaji hirar su ne. ai kuwa kunya tayi balain kama Hauwa da sauri ta saka doguwar rigar
barci mai kyau ta bi bayan sa zuwa dakinsa don ta san hanyar dakin. Ta kwankwasa ya amsa
da yes daga ciki sai ta shiga. Ya kalleta ya dauke kai zuwa aikin sa, tace Baban Waheedah please kayi hakuri wallahi ba
zan sake ba yayi shiru yana cigaba da operating system dinsa, ta taho kamar zata bi ta kansa
yace in kika fasa min laptop sai kin biya ni ta muryarsa ta san inda yake zaune ta laluba ta
zauna akan cinyarsa shikuma ya hau kokarin zillewa amma Hauwa bata bashi wannan damar
ba.
Sosai ta inganta mishi daren yau kamar babu ciki a jikin ta, kamar babu lalurar ido a tare da
ita, yau Sarham shi ya koma dan gata sai yadda Hauwa tayi da shi. Sun farantawa juna rai
kamar bazasu ragewa gobe ba kafin su koma maida numfashi manne da juna. Saida ya koma
Sarham din sa ya ce mata Maijidda, naji hudubar da kawar ki tayi miki, amma ki sani ni ba daya
nake da sauran maza ba.
Ba wani canjin halitta ko tsofewa da zai sa in daina son matata.
Sannan barin ain samu abinda nake so a lokacinda nake so shi yake kara ninka wannan son
yake kuma kara kusantoki da zuciyata.
Hauhuwa da wuri kuwa kuwa in duk sati ake yin ta ni kulllum nake so kiyi min.
Makaranta kuma ina sane na barki sai wata shekarar don bana son kiyi jigilar karatu da yaron
ciki.
Maganar aikin ido kuma ban gama abinda nake tattarawa ba sannanba zan miki aiki alhalin
kinada ciki ba sai Allah ya saukeki lafiya kinji?
The more you give me access to it, the more I addittionally love you.
Don haka ba Sumayyah kadai ba, duk wani wanda zai baki shawara akaina ko akan abinda
zai amafni jikinki yabi bayan ni. Ban ce kada kiyi kawance da kowa ba amma ina so ya zama

nine amininki sama da kowa, feel free to discuss everything about our marital life with me kin ji?
Not the third party wadanda ba lallai bane su san meye sexual likes and likes dina ba.
Kunya sosai ta kama Hauwa, ta roki gafara, ta dauki alkawarin bazata sake yi masa rowar
wannan ba, sannan bazata zancen mijin ta da kowa ba sai da shi kansa. Kuma daga wannan
ranar ne, HAUWA BILYAMINU, ta fara kiransa da suna MY PACESETTER!!!.

Sati mai zuwa insha Allah za mu shiga umrah cikin makkah ni da ke, daga nan muje
Madinah ziyara mu yi addua solely a kan Allah ya saukeki lafiya HAUWA, ya bamu Inna mai
albarka, mai irin dukkan halin INNATA, mai tsafta mai kyautar abinci mai kula da yayan ta kamar
yadda take kula da ranta. A karshe ya shafa kanta tana durkushe gabansa yace Allah ya saukeki lafiya Hauwa-Jiddah,
Allah yayi miki albarka Hauwau-Maijiddah, yadda kika faranta min yau, Allah ya faranta dukkan
rayuwarki.

Hauwa ta ji wani irin dadi ya mamaye ruhinta, ya daura hannunsa a kan nata hannun, ya
matse su sosai cikin na juna, alkawari ne ya dauka tsakanin sa da Ubangijinsa; zai yi duk iya
kokarinsa ya gyara idanun nan na Hauwa-Kulu, koda remnant cikin yarda da amincewar
Ubangijii wato koda ba duka aka samu dawowar su ba.
***​ ***​ ****

Can daga nesa na hango Dr. Sarham Abbas da matarsa Hauwa-Kulu suna dawafi a Kaabah,
hannunsa makale cikin nata. A zagayen karshe na kowanne dawafi addua daya suke yi, Allah
ya sauki Kulu lafiya, ya bata ikon sharwa da kula da yayanta koda idanun ta basu bude har
abada ba, aikinda zaayi mata kuma, wanda zaayi ne immediately bayan ta haihu, Allah yasa ayi
shi cikin nasara.
Suka gabatar da cikakkiyar Umrah suka dawo gida Jeddah.
Mama tasa rigimar ya dawo mata da Hauwa ta haihu a gida, tunda haihuwar fari ce. Sarham
yace Ina! Ya gama wannan daga haihuwar Waheedah. Saidai a kawo wata ta zauna masa da
ita har tayi arbain din.

“Na kwana guda bai iya jure zaman gidan da babu HAUWA!.
A lokuta da yawa har wani kirarin baitocin waka Sarhamu ke rero mata, daga baitocin wakar
mawaki (Ali Jita), a irin lokutan da soyayya ta cicciko a kirjinsa, wato tayi tantsan a zuciyarsa;
Zana gaida HAUWA-KULU.Sannu HAUWA-..HAUWA..
Baa raina suna da lokacinki HAUWA.
Baa finki haske a zuciyata HAUWA..

Babu wanda zai bata zamaninki a zuciyata HAUWA.
In zaa tara mata wa zata fi ki HAUWA.
Babu wanda zaya ruda zuciyata a kanki HAUWA.
Gimbiyar mata kike a zuciyata HAUWA.
Da zaa bani biro na baki maki HAUWA

To zaki haura lambar da zaa baki HAUWA.
In zaa tara mata wa zata fi ki HAUWA.
To addua nake... Allah ya taimakeki HAUWA.
A irin wadannan lokutan da yake rero mata wadannan baitocin, zaka samu Hauwa-Kulu
manne dashi cikin shauki, tana sauraronsa tana murmushi from ear to ear, kanta ya kumbura..
irin na macen da tayi dacen saar mijin da ta san har zuciyarsa yana matukar son ta.
**** **** ****
Ranar da suka dawo Jiddah Madinah ta karbi girki. Ta dade bata ga Hauwa ba, duk da suna
rayuwa a gida daya, to wata irin rayuwa suke yi ta kowa tasa ta fishsheshi, wato ba mai shiga
shaanin kowa saidai sallama da gaisuwa irin wadda addinin musulunci ya shardanta a tsakanin
musulmi. Madinah ta daga ido taga Hauwa da ciki tororo, alhalin bata gani. Wannan kadai ya
kara ma Madinah tsoron Allah, ganin cewa mijin da matar ko a jikin su akan lalurarta, suna cikin
farin ciki mara misaltuwa na ibadar da suka yo guzurinta suka dawo.
Silar kasancewarsu kullum cikin farin ciki shine wani boyayyen sirri ne na IKHLASI (sincerity);
Sun dade da tsarkake zuciyarsu da karbar kaddarar rayuwar Hauwa da hannu bibbiyu, wato
sun yarda cewa nakasar ba kasawa bace at all cost, kuma ba itace karshen komai na rayuwar
bawa ba. Sun yarda mara lafiyan da ya samu kulawar iyaye da ilmi mai amfani hakika zai iya hada
kafadar rayuwa da kowane mai lafiya, in such a way that, an bashi spacial consideration na
abinda yake bukata don gudanar da rayuwarsa ta hanya mai sauki. Ko yau Allah zai bata Da
mai lalurar gani, dama kowacce irin lalura ta halittar jiki, Madinah sai taji bata fargaba kamar da,
zata maida rayuwar kishiyarta mudubin dubawa ne ta tsaya ta kula da shi tun yana karamin sa,
ta bashi kulawa ta musamman a cikin yayanta kamar yadda Innar Hauwa da Mama suka kula
da Hauwa cikin yayansu basu bar rayuwarta ta wulakanta saboda nakasa ba, zata tsaya ta gina
rayuwarsa yadda in ya girma bazai sha wahala sosai ba, zai rayu ne adequately and
independently kamar kowa da taimakon na jikin sa.
Kenan matar Sarham ta zamo role-model, haka ga duk wani mai nakasar ido ya gane cewa
makanta ba karshen rayuwa bace.
Ya shiga toilet ya bar Madinah nata sake-sake cikin mutuwar jiki da karin imani, Hauwa ta
gaishe da Madina sannan ta wuce dakinta.
Dr. Sarham kenan mai Jidda mai Madinah bada kanka a sare kaje gida kace ya fadi.
Kullum kokarinsa shi ne ya samar da cordial relationship a tsakaninsu, amma hakan ya
faskara. Don kowacce gwanace ta gwanaye a kishin SARHAM! Shikadai ransa, sun fi ganewa
rayuwa ta gaisuwar musulunci da gasar kyautatawa maigida.
Lokacin da cikin hauwa ya shiga watan haihuwa kuma Sarham ya hana ta dawowa gida bata
nuna bacin rai ba, duk dokin ta da ganin iyayenta kuwa, sai yayi kudurin shi kuma zai yi mata
abinda zai faranta ranta matuka.
EDD dinta saura kwana uku, tana zaune akan kilishin dakin ta, tana cin mutumin nata
gugguru, ta saka tirtstsen cikin ta a gabanta, ta ji kamar sallamar Inna a dakinta.
Haan, yau kuma kunnena ya koma yi min gizo da muryar Innata?
To tunda gizo ne bari kawai in koma ya cigaba da gizago. Irin mikewar da Hauwa tayi ta
manta da tshohon ciki a jikinta saida Inna tayi maza ta kamata ta zaunar. Tana fadin Yi a
hankali, likita ya gayamin yan biyu ne a tare dake.

Zaro idon da Hauwa tayi shi ya tabbatarwa Inna bata taba jin wannan zancen ko
makamancinsa ba, haba! Biri yayi kama da mutum. Shagalin da take ji a cikin ta da nauyin sa
da girmansa ya wuce na jariri daya. Pacesetter kuma bai taba gigin gayamata ba kada ya
tsoratata amma komai biyu yake saye iri daya unisex. Tuni Hauwa ta soma hango kanta
rungume yaya guda biyu alhalin babu ido. Wata qudururar sai Ubangiji Subhana. Tun tali-tali
Hauwa na kwadayin haifar Da, ko don iyayenta da basu dasu da yawa. Da Ubangiji ya tashi yi
mata kyautar Da sai ya bata da gaggawa kuma guda biyu a lokaci guda ciki lalurar makanta.
Akace sau tari wani farincikin yafi gaban ayi masa kuka ko ayi masa dariya. Don haka Hauwa
a wannan daren kwana tayi sallah a zaunde, ga farin ciki zuwan Inna ga na albishir dinda tayi
mata.
Tun daga ranar Inna ta soma aikin ta na kula da Hauwa dama ta zo da duk wani tanadinta na
jego.
Kwanan Inna biyu da sauka nakuda ta fara, Pacesetter ya kwashe su sai asibitin Doctoor
Sulayman Faqeeh. Ko awanni biyu baayi da karbar Hauwa a dakin Haihuwa ba a hannun
Sarham ta sambalo yammatanta guda biyu, Hassana da Hussaina identical twins masu irin
idanun Hauwa da Sarham yayi fata, yatsun da dogon hancin da sumar fulanin Shanonon kuwa
duk nashi ne.
Madina har asibitin ta zo ta duba su, dama kuma taje har dakin Hauwa ta gaida Inna
shekaranjiya, karonta na farko da shiga dakin Hauwa albarkacin mahaifiyarta. Tayi tayi hajjah
Ramlah ta zo barka ta ki, ta dai yiwa Sarham din barka shikadai don su Hauwa basu isa ba,
itada Usman sukaje MAX’ sukayowa jariran sayayya ta burgewa suka kawowa Hauwa. Dama
wajen kyauta da mikakken hannun alkhairi Madinah ba daga nan ba. Circumstances ne ya
canza Madinah, amma a hankali tana farfadowa tana dawowa Dr. Madinah Sorondinkinta da
kowa ya sani.
Tun sanda suka fado duniya yayi musu khutbah da sunayen da suka dade da zabar musu
wato Hassana (Maimunatu) da Hussaina (Safiyyatu). Mama da Abba dai basu amince ba suka
saka shi agaba kan lallai ya maido su gida sai ya ce ai ga Inna ya dauko tazo daga Ghana.
Sannan ne hankalin Mama ya kwanta. Inna ta shiga Makkah tayo Umarah cikakkiya, ta je Madinah tayi ziyarar fiyayyen halitta SAW.
Tana rokawa Hauwa da Sarham ‘long life and prosperity’ da zasu raini yayansu, su kuma
tarbiyyantar dasu tare a duk inda ta tsaya a indararon Rahma na ubangiji adduarta kenan, ta
kuma roki ubangiji idan Hauwa nada rabon gani a rayuwarta, Allah ya hada idonta dana Sarham
a gidan duniya ba sai sunje aljannah kadai ba. satin Inna daya a cikin Makkah tadawo Jeddah
suka soma shirin tahowa gida Najeriya.
Suna yin arbain suka tattaro har Sarham zuwa gida Kanon Dabo tareda Inna, dona kaima
Abba da Mama yan biyu su gansu. Basu san Malam Bilyaminu yana can yana shirya musu
surprised ba. Wato abun mamakin shine da Sarham ya kira Malam Isa yace masa ya shigo
kasar Kano zai zo ya gaidashi sai Malam Isa yace ai ga BILYAMINU muna tare a soro na, tuni
Malam Bilyainu ya dawo gidansa na BADALA tun kafin Innar Hauwa ta dawo. Ya kwaso komai
da ya mallaka daga Ghana ya dawo dashi Kano, har ya cigaba da raba sanaarsa a Kofar
Wambai ya zama babban dealer dake shigo da gwanjo ya rabasu da kansa ga kananun masu
kwance dealer su sayar da dai-daya”.

Ya kara kawata gidansa tun kafin Inna ta dawo ya zuba musu komai na bukatar rayuwa
yadda suke rayuwarsu a gidan su na Ghana.
Ina rijiyar farin ciki take Hauwa ta fada da jin wannan labari da Sarham ya bata. Hauwa tafi
kowa murnar dawowar iyayenta cikin Badala ba don komai ba sai don cewa har gobe ruhin
HAUWA-KULU yana nan cikin gidajen Badala. Don haka walima sosai Sarham ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login