Showing 18001 words to 21000 words out of 34144 words
Chapter 7 - Sarautar Mutuwa Book Complete by Mansur Sufi .pdf
Imran ya ce "na yi maki wannan alfarma ya ke yar uwanta".
Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin yaro Imran ma'abocin addinin Musulunci.
A can masaukin sarki Lazwar kuwa, fira ce ta kare tsakanin Lazwar da gimbiya Mashlira, a
inda Mashlira ta ci gaba da ba shi labarin abin da ya faru tsakanin matsafi Sahibul-ukub da
mutanen birnin akan dalilin da ya sanya halittar su ta koma ta maridai inda ta ci gaba da cewa.
Lokacin da rundunar matsafi Sahibul-ukub suka afkawa birnin Madinatul-Adfal sai aka
ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni ban tsoro da ban al'ajabi.
Nan fa su ma mayaƙan birnin suka dinga tuttuɗowa daga kowacce kusurwa ana yin
KARON BATTA.
Nan fa sassan jikkunan bil'adama ya dinga shawagi a sama suna zubo ƙas, hankakan mutuwa
ya yi dirar mikiya a wajen ya wanzu yana kai komo wajen ɗaukar rayuka.
JINI DA ƘASA suka haɗu waje guda, ihun da kururuwar mazaje gami da haniniyar dawakai ta
cika dodon kunne.
A wannan lokaci mahaifina sarki Zammar ya shiga izuwa cikin gidan sarautar yana shirin yaƙi,
jim kaɗan sai ga shi ya fito izuwa filin daga kawai sai ya afka cikin abokan gaba ya hau su da
sara da suka.
Yazamana cewa duk inda ya sanya a gaba sai dai ka ga dakarun matsafi Sahibul-ukub na
zubewa ƙasa matattu tamkar yana sassabe a gonar auduga.
Sa'adda matsafi sahibul-ukub ya ga irin muguwar ɓarnar da mahaifina ke yi mashi, sai ya
ruga izuwa inda ya ke ya tare shi suka kacame da azababban yaƙi mai matukar muni daban
tsoro.
Ana fara wannan arbu ne mahaifina ya fara gane cewa tabbas shayi ruwa ne ba abinci mai
nauyi ba, domin kuwa duk sa'adda matsafi Sahibul-ukub ya kai mashi hari da takobinshi idan
ya kare harin, sai kaga ƙarfin saran ya cilla mahaifina sama ya yi ƙundumbala ya kife a ƙasa,
amma saboda juriya da mafi irin ta GWARAZAN JIYA sai ya miƙe tsaye zumbur, ya ci-gaba da
mayar da martani
A wasu lokutan kuwa idan ya kai mashi harin ya kauce, sai ka ga duk abin da takobin
Sahibul-ukub ta sauka a kanshi ya kama da wuta, kafin cikar rabin sa'a Sahibul-ukub ya
galabaitar da mahaifina ya faɗi ƙasa magashiyan ya na amai na jini ta baki da hanci.
Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin gimmbiya Mashlira 'yar sarkin maridai da Sarki
lazwar.
Kamar yadda ya wakana a masaukin gimbiya Mashlira da sarki Lazwar haka al'amarin
yakasance a masaukin yarinya Shuraiba da aljani ZA'ARATUN-LAYAL
A inda Za'aratun-layal ya ci gaba da bawa yarinya Shuraiba hikayar sarauniya Abidat ta birnin
Sin.
BABI NA GOMA
Lokacin da wannan zakanya ta ruga izuwa inda suhaimat da jaririyar ta ke kwance, koda taga
halin da take ciki sai ta ruga izuwa bakin wata ƙorama ta guntso ruwa a baki ta dawo izuwa inda
take ta fesa mata ruwan a fuska.
Faruwar hakan keda wuya sai suhaimat ta ja dogon numfashi gami da sauke nannauyar
ajiyar zuciya, idanuwanta suka buɗe tarwai ta wartsake daga suman da tayi kawai sai ta miƙe
zaune.
Ya yin da tayi arba da zakanyar sai ta razana ainun ta ja da baya tana mai ɗaukar jaririyar ta ta
ƙanƙame ta a ƙirji.
Koda ganin halin da suhaimat ta shiga sai zakanyar ta juya ta ruga izuwa cikin wannan
kogon dutse dake dajin.
Cikin matukar farin ciki suhaimat ta mike tsaye taje bakin wannan ƙorama ta yi wa jaririyarta
wanka, ita ma ta tsafta ce kazantar da ke jikin ta, sannan ta dawo izuwa ƙarƙashin wata bishiya
ta zauna ta shiga sharar da jaririyar tana mai shafa gashin kanta, zuciyar ta cike da matuƙar
farin ciki maral misaltawa. Kuma ta shiga tambayar kanta a cikin ranta tana cewa,
dhin wane ne ya kashe waɗannan dabaru? Ko kuwa wannan zakanya ce?
Amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenen,tana cikin wannan hali ne zakanyar ta
dawo gare ta bakin ta rike da waɗansu tarin ganyayyaki ta a jiye a gaban ta,
Bisa mamaki a wannan karon sai Suhaimat taji ko kaɗan ba ta tsora ta da ganin zakanyar ba,
bata re da fargabar komai ba ta ta duba abin da ta kawo ɗin. Ai kuwa sai taga a she nau'ikan
kayan marmari ne dangin su ayaba da inibi, kawai sai ta shiga kimtsa cikinta har sai da ta ci ta
ƙoshi, sannan ta fasa kwakwa ta shanye ruwan cikinta. Zakanyar na tsaye na tsaye a gefe guda tamkar mai jiran umarni, a sannanne Suhaimat ta
lura cewa jikin zakanyar akwai jini, take ta fahimci cewa ita ce ta kashe waɗannan dakaru domin
ta ceci rayuwar ta da jaririyar ta.
Lokacin da aljani ZA'ARATUN-LAYAL ya zo dai-dai nan a hikiyar sarauniya Abidat ta
birnin Sin da yake bawa yarinya Shuraiba sai ya tsuke bakinshi ya yi shiru.
Al'amarin da ya sanya yarinya Shuraiba ta dube shi cikin alamun tsananin damuwa ta ce
"ya kai masanin HIKAYAR DUNIYA shin mene ne yasanya zaka katse min wannan daddaɗan
labari? Tabbas ina so naji wace irin rayuwa Suhaimat da jaririyar ta za su yi a nan gaba, kuma
menene dalilin da ya baro da ita daga birnin su? Shin ma mene ne ya sanya dakarun ke farautar Suhaimat?
Koda jin waɗannan tambayoyi sai aljani ZA'ARATUN-LAYAL ya bushe da dariya ya dubi yarinya
Shuraiba ya ce "ya ke Shuraiba shin baki gani ba ne har alfijir ya keto safiya ta yi".
Koda jin wannan batu daga bakin Za'aratun-layal sai Shuraiba ta cika da mamaki, ai kuwa
sai ta miƙe tsaye ta domin ta fara shiri kamar yadda sarki Lazwar ya yi masu bayani.
Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin yarinya Shuraiba.
Kamar yadda ya wakana a masaukin Shuraiba haka al'amarin ya kasance a masaukin darki
Lazwar da gimbiya mashlira.
A inda Mashlira ta katse labarin bawa sarki Lazwar na matsafi Sahibul-ukub da mahaifin ta sarki
Zammar.
Saboda ganin ketowar alfijir a sararin samaniya.
A ɓangaren masaukin yaro Imran kuwa, ya yin da ya ga alfijir ya gabato sai ya ɗaura alwala ya
shiga gabatar da nafita, bayan nan kuma sai gudanar da sallar asuba, q lokacin da hadima
khadijat ta bisa a baya a matsayin mamu.
Lokacin da rana da fito ne ta yi haske sai khadijat ta yi umarni aka kaiwa kowannnen su
bahon ruwan wanka, bayan kowa ya tsaftace jikinshi ya yi kalaci, sai aka ɗunguma izuwa cikin
gari domin gudanar da abin da aka zo nema.
Wannan shi ne abin da ya faru da su sarki Lazwar a lokacin da aka kai su izuwa masauki.
Babi na sha ɗaya
Lokacin da amarya Munirat ta ci gaba da tafiya a cikin gidan sarautar birnin Darul-usur
bayan ta kuɓuta daga sharrin magajin gari Yasiran.
Sai ta cigaba da tafiya a cikin gidan sarautar tana ratsa ƙofofi da dakaru iri daban-daban,
zuciyarta cike da matuƙar farin ciki maral musaltuwa.
Ta na cikin wannan hali sai wannan tsuntsu ya sake bayyana a gare ta a sama cikin iska
Tsuntsun ya riƙiɗa izuwa wani kyakkyawan aljani mai kyawun sura, aljanin ya na ɗauke da sura
irin ta bil'adama, sai dai yana ɗauke da fuka-fukai.
Aljanin ya dubi Munirat ya ce "ya ke Munirat ki yi sani cewa da farko dai suna na Lailatul-azhar
kuma ni hidimi ne ga sarkin musulmin aljanun duniya baƙaƙen fata.
Ubangiji ya bayyana wa sarkin mu halin da ki ke ciki dama sauran mutanen birnin ku na
irin baƙin zaluncin da magajin gari Yasiran ke yi maku, sannan kuma ya turo ni ne domin na
kawo ƙarshen mulkin zaluncin shi baƙi ɗaya.
Ki yi sani cewa kalaman da ki ka karanta a jikin fuka-fukaina har kika tsira daga sharrin magajin
gari, ba wasu kalmomin ba face KALMAR SHAHADA wacce duk wanda ya furtata ta da
tabbatar wa a zuciyarshi to ya yi imani da Ubangijin gaskiya da ya halicci komai da komai.
Idan har kin bayar da gaskiya da Ubangijin ɗaya daya baki nasara akan magajin gari to
tabbas zamu samu nasarar ganin bayanshi.
Koda jin wannan batu daga bakin aljani Lailatul-azhar sai amarya Munirat ta cika da matukar
farin ciki maras musaltuwa, ta dube shi ta ce "ina so yanzu ka shigar da ni addinin ka".
Ba tare da wani ɓata Lailatul-azhar ya karanta mata KALMAR SHAHADA.
Nan fa ya zamana cewa kafin mako guda fiye da mutanen birnin sun karɓi addinin musulunci a
hannun amarya Munirat.
Magajin gari Yasiran kuwa sai ya kamu da wata irin rashin lafiya, sakamakon wannan wuta
da ta ƙona jikinshi,
Nan fa aka rasa wanda zai gaje shi a kan karagar mulkin shi.
'Yan Majalisar suna ganin cewa tabbas yanzu hawa karagar mulkin Yasiran ana iya kiran shi da
SARAUTAR MUTUWA. Domin su ganin a ko da yaushe magajin gari zai iya samun lafiya, ko
kuma sarki Lazwar ya dawo daga tafiyar da ya yi.
Saboda ba zai yiwu a zauna haka babu shugabanci bisa dole jama'ar gari suka ɗora
amarya Munirat a matsayin sarauniyar su.
Nan fa jama'a suka fara samun yanci, farin ciki gami da walwala sakamakon hasken musulmi
da bayyana a gare su,
Al'amarin Shuraiba kuwa Lokacin da ta cigaba da tafiya a cikin birnin Istanbul domin nemo
mahaifiyarta sai ta wanzu tana tafiya babu sassauci, tana cikin wannan hali ne sai ta hango
wajen waɗansu almajirai ke zaune suna bara a kasuwar, kawai sai ta matsa izuwa daf da inda
suke ta shiga yin nazarin su. Abu na farko da ya faɗo mata a rai shine shin yanzu ina kike da tabbacin mahaifiyarki take, ki
na ganin cewa mahaifiyarki zata kasance daga cikin waɗannan almajirai dake yin bara? An ya
kuwa sarki Ladiyas bai mayar da mahaifiyar ki matar shi ba?
Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenen.
kawai sai ta ɗauki mayafi ta ɗaure fuskarta da rawani, kana ta ɗauki wani ƙoƙo ta ajiye a gaban
ta, sannan ta shiga izuwa cikin su ta saje da su tamkar ba ita ba.
Zaman ta ke da wuya sai wata dattijuwar almijira dake kusa da ita ta du be ta ta ce "ya ke
wannan yarinya shin ke kuwa me kika rasa a rayuwar ki da za ki fito bara, baƙya duba wa ki ga
cewa ke yarinya mai karancin shekaru".
Koda jin wannan batu daga bakin dattijuwar sai Shuraiba ta cika da matuƙar mamaki ta
dube ta ta ce "ya ke wannan dattijuwa ki yi sani cewa bakomai ba ne ya sanya ni aikata wannan
bara ba sai domin na samu abin da zanyi kalaci. Mahaifina ya mutu tun ina da shekara bakwai a
duniya, mahaifiyata ce take a raye ina neman ta ruwa a jallo, domin ita ce kaɗai ta rage min a
duniya.
Koda jin amsar wannan tambaya sai dattijuwar ta bushe da yar karamar dariya ta dube ta
ta ce "tabbas yaro yaro ne kuma duk wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi, na san
cewa akwai muhimmin al'amari daya sanya ki zuwa wannan waje domin, ban taɓa ganin ki ba
tun da nake fitowa wannan bara tawa". Koda jin wannan batu daga bakin dattijuwar sai Shuraiba ta yi dariya ta ce "tabbas da
akwai buƙatar hakan da na nema a wajen wani tun kafin na iso wannan waje, amma tambayar
da zan yi maki wace matsalar dake tattare da wannan waje?
Dattijuwar ta yi dariya ta ce ''ya ke wannan yarinya ki yi sani cewa bakomai yawan dinaren da
mutum zai samu na sadakar da za a bashi, sai dakarun sarki Ladiyas sun zo sun karɓi haraji,
da ƙyar za ka samu ka tsira da kaso ɗaya cikin goma. Idan kuwa aka yi rashin sa'a baka samu
sadaka ba, to fa sai sarki ya sanya an kai mutum aikin horo a gidan sarauta domin ka yi aiki
adadin wannan dinare da baka biya harajin ba";
Da jin wannan batu daga bakin almajirar sai yarinya Shuraiba ta ji ta ƙara tsanar sarki
Ladiyas fiye da komai a rayuwar ta. Sannan ta dubi almajirar cikin alamun matuƙar tausayin ta
ce "tabbas sarki Ladiyas ya cika azzalumi kuma maras tausayi, yanzu a ce almajirai ma sai sun
biya haraji, Koda jin wannan batu sai mamaki almajirar har ta buɗi baki da nufin ta ce wani abu sai a ka
hango dakarun sarki Ladiyas sun shigo kasuwar a bisa dawakai su kamanin ɗari biyu shirye
cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensu ɗauke da waɗansu murtuka-murtukan kulake.
Nan fa kasuwar ta hargitse jama'a suka dunga kwashe kayayyakin su suna buɗa wa
dakarun hanya, domin idan har suka iso mutum bai kwashe ba take za su bi ta kan kayan da
dawakan su su tattake.
Lokacin da dakarun suka iso wajen da su Shuraiba su ke sai suka shiga karɓar harajin a
wajen dukkan almajiran dake wajen, suna cikin karɓar ne suka iso kan wannan dattijuwar
almajira dake zaune kusa Shuraiba.
Jikinta na ƙyarma ta zira hannunta cikin ƙoƙon barar ta lissafo dinare ta miƙa wa wani badakare,
bakinta na karkarwa ta ce "ga shi ya shugabana har da harajin wannan yarinyar da ke zaune a
kusa da ni,
Kafin hannun badakaren ya kai inda dinaren yake yarinya Shuraiba ta shammace shi ta gabza
mashi wawan naushi a maƙogaronshi.
Saboda matuƙar ƙarfin dukan sai badakaren ya yi karanta wa sau biyu a sama, sannan ya
faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba, al'amarin da ya firgitarwa jama'a dake kasuwar kenan
kuma ya harzuƙa zukatan sauran dakarun.
Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya shuraiba a lokacin da shiga cikin gari domin
neman mahaifiyarta.
Al'amarin sarki Lazwar kuwa lokacin da fice da ga masaukin su ya kutsa cikin birnin Istanbul
domin nemo hanyar da zai sadu da baiwa Sharifa, sai ya wanzu yana ratsa layu ka da
unguwanni babu sassauci.
Yana cikin tafiyar ne ya hango waɗansu cincirindon al'ummar a gefen kasuwar, cikin hanzari ya
matsa daf da wajen domin ya ga wata irin waina ake toyawa.
Sa'adda da ya matsa daf da wajen sai ya ga ashe waɗansu ƙarfafan samari ne guda biyu ke
baiwa hammata iska jama'a sun kewaye su suna kallo.
Idan ɗayan ya gabzawa ɗan uwanshi naushi sai ka ga ya faɗi kasa tim q matuƙar galabaice,
amma saboda naci da juriya sai kaga ya miƙe tsaye zumbur ya mayar da martani.
A gefe guda kuwa wani badakare ne mai ƙirar samudawan farko ma'abocin kwarjini da
haiba, kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance GWARZON DUNIYA mai ƙarfi na
Allah ya isa, yana zaune bisa wata ƙasaitacciyar kujera ta alfarma, ya zuba idanu yana kallo
yadda artabun ke wakana da alama shine mai kula da gasar da ake aiwatar wa. Sarki Lazwar ya matsa daf da wani mutum ya dube shi ya ce " Wai shin mene ne amfanin
abin da waɗannan samari ke yi na yaƙar junan su?
Koda jin wannan tambaya sai mutumin ya dubi sarki Lazwar ya bushe da dariyar mugunta
ya ce "da alama kai baƙo ne a wannan birni ko?
Sarki Lazwar ya gyaɗa kai alamar haka ne, Mutumin ya ce "ya kai wannan baƙo ka yi sani cewa
waɗannan da ka gani bayi ne da aka farauto daga can wata nahiya daban, duk bayan mako
ɗaya mai girma Ladiyas yana sanya a fitar mashi da GWARAZAN JARUMI a cikin su da zai
kasance ɗaya cikin masu tsaron lafiyar sarauniya. Bisa wannan dalili ne ya sanya aka tara su a wannan waje domin fitar da zakara.
Koda jin wannan batu daga bakin mutumin sai Lazwar ya cika da matuƙar farin ciki, domin kuwa
dama ta samu wacce zata zamto sanadin kasancewar shi bawa a masarautar Istanbul.
Domin dai ya cika burin shi na saduwa da baiwa Sharifa da za ta taimaka mashi wajen mallakar
abubuwan da zai karya sihirin tsafin da abokin gabar shi sarki Darwazu ya yi mashi.
A ɓangaren jarumai biyun kuwa tuni labari yasha banbam domin kuwa ɗaya cikin jaruman ya
samu nasara akan ɗayan
Inda ya yi masa jina-jina har layi na ɗibarshi yana faɗuwa ƙasa.
Nan fa wannan badakare dake kula da gasar ya shiga ƙyalƙyala dariya bisa ganin yadda ɗayan
jarumin ke yin nasara akan ɗayan, al'amarin da ya fusata sarki Lazwar kenan yaji ya kamu da
matuƙar tausayin jarumin, kawai sai ya