Showing 27001 words to 30000 words out of 34144 words
Chapter 10 - Sarautar Mutuwa Book Complete by Mansur Sufi .pdf
Mashlira dake sanye cikin tufafin dakaru cikin ɓaddakama, ta ga an
sanya masoyinta Lazwar a cikin ɗakin duhu sai takaici da baƙin ciki suka mamaye zuciyartq taji
kamar ta ƙwallawa ƙara.
Amma sai ta danne saboda ta san cewa ba don komai masoyin nata ya shiga wannan hali ba
sai domin kawai ya sadu da baiwa Sharifa da zata taimaka mashi wajen mallakar abubuwan da
zasu warkar da shi daga sihirin da abokin gabar shi ya yi mashi, sai kawai ta shiga yi mashi
fatan samun nasara, amma har yanzu hankalin ta a matuƙar tashe ya ke ainun. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin sarki Lazwar da halittun, kuraye biyu zakuna biyu sai
waɗansu rin mucizai masu kawuna biyar.
Duk da kasancewar sarki Lazwar GWARZON MAYAƘI kuma GWARZON DUNIYA sai da
hankalin shi ya dugunzuma ainun, domin iya tsawon rayuwarshi bai taɓa gani ko jin labarin
halittu masu kwarjini da ban tsoron tamkar su ba.
Tsawon daƙiƙa hamsin halittun na kewaye lazwar suna gurnani gami da hargagi mai
matuƙar ban tsoro, sai daga bisani ne suka yi ɗauki kan shi suna kururuwa da ihu mai ɗimauta
DANDAZON MAYAƘA suna masu kai mashi cizo da yakushi da faratansu, macizan na kai
mashi sara gami da furzar da dafi daga bakunansu cikin wani irin baƙin zafin nama da ya
ɗimauta hankali.
Shi kuwa sarki Lazwar ya wanzu ya na zillewa tare da kaucewa hare-haren halittun cikin
zafin nama JURIYA DA BAJINTA. Sai da sa'a ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi
ba tare da ɗaya daga cikin su ya samu nasara ba, a dai-dai wannan lokaci ne halittun suka fara
galabaitar da Lazwar ya zamana cewa ba ya iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kanshi.
Ana cikin artabun ne wani daga cikin zakunan ya yakushe shi a cinyarshi ta hagu take ya
yi mashi mugun rauni, sarki Lazwar ya kurma wawan ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da
ya ji jini ya kwaranya.
Kafin ya sake yin wani yunƙuri wani maciji ya kafta mashi wawan sara a gadon bayanshi,
saboda matuƙar azaba sai da sarki Lazwar ya faɗi a ƙas yana nishin wahala.
Nan fa masoyan sarki Lazwar suka cika da matuƙar baƙin ciki har waɗansu na zubar da
hawayen takaici bisa ganin halin da jarumin su ke ciki.
Shi kuwa Sarki Ladiyas dake hakimce bisa karagar mulkin sai ya shiga ɓaɓɓaka dariyar
mugunta har da kyakyatawa nan fa sauran 'yan majalisa da fadawa suka yi koyi da shi.
Al'amarin da ya sanya zuciyar gimbiya Mashlira ta karaya kenan har kwalla ta cika mata
idanu, bisa ganin halin da masoyinta ke ciki amma saboda tsoron kar wani ya gane halin da
take ciki asirinta ya tunu sai ta yi sauri ta goge hawaye dake kan fuskarta, dai-dai lokacin ne ta
hango bawa Shamsal da sarkin yaƙi a cikin jama'ar gari suka zubar da hawayen takaici bisa
ganin halin da shugabansu ya tsinci kanshi a ciki, da koyaushe zai iya rasa rayuwar shi.
Lokacin da sarki Lazwar ya tsinci kanshi a tsakanin RAYUWA DA HALAKA, kuma ya
tabbatar da cewa haƙiƙa a koda yaushe zai iya sheƙawa barzahu, sai kawai ya fara amfani da
zallar ƙarfin sihirin tsafinshi, amma sai ya zamana cewa tamkar yana inziga miyagun halittun
wajen kai mashi farmaki. Kwatsam! sai yaro Imran ya faɗo masa a rai zuciyarshi na raya mashi cewa kawai ka nemi
taimakon Ubangijin yaro Imran tun da dukkanin wata dubara ta ƙwace maka, domin masu iya
magana na cewa da asara gwara gidadanji. Kuma wanda ya faɗa teku ko KAIFIN TAKOBI aka
miƙa mashi sai ya kama domin ya tsira. Tun da a halin yanzu ba wanda zai gane cewa ka nemi taimakon Ubangijin Imran sai
kai kaɗai. Sa'adda sarki Lazwar ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya yi kabbara yana mai
ambaton sunan Allah a cikin ranshi yana mai cewa "ya Ubangijin imran ka tseratar da ni daga
sharrin miyagun halittun nan". A dai-dai wannan lokaci ne wani ɗaya daga cikin zakokin ya wangame bakinshi da nufin ya
cinye yan yatsun Lazwar na hannu.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga Lazwar ya kurma wawan ihu cikin wani zafin
nama na ban al'ajabi yana daga kwance ya kama wuyan zakin da hannayen biyu ya murɗe
wuyan shi, take ya karye ya yi ƙara ji kake ruƙus! Ƙas ya sheƙa barzahu ko shurawa bai yi ba,
sannan ya miƙe tsaye zumbur aka sake yin wani sabon kallon-kallo tsakanin shi da sauran
halittun.
Nan take fadar ta ruɗe da shewa masoyan sarki lazwar suka cika da matuƙar farin cikin
bisa ganin gwaninsu ya miƙe tsaye.
Shi kuwa sarki ladiyas fuskarshi a murtuke take babu annuri domin tsawon shekarun da
aka shafe ana gwada jarumai, ba a taɓa samun wanda ya kashe dabba ɗaya daga cikin halittun
ba.
Daga can sai dukkan halittun suka afkawa Lazwar aka sake ruguntsume wa da azababban
yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro.
A wannan karon sai ya zamana cewa duk wanda Lazwar ya gabza wa naushi a cikin halittun sai
kaga ya yi sama tamkar an janye shi da ƙungiya sannan ya faɗo ƙasa tim.
Amma saboda na ci da zafin nama irin na halittun sai su miƙe tsaye zumbur su sake afka
mashi da dukkanin tsagwaron ƙarfin damtsen su.
Kafin cikar rabin sa'a sarki Lazwar ya kashe gaba ɗaya halittun ya jefar da gawarwakin su a
ƙas, nan fa fadar ta kaure da shewa da ihu jama'a suna ta mamakin wannan jarumtaka ta sarki
Lazwar, domin a tarihin gasar shi ne mutum na farko da ya taɓa kashe miyagun dabbobin baki
ɗaya. Ita kanta gimbiya Mashlira 'yar sarkin maridai bata san sa'adda murmushin farin ciki ya
suɓuce mata ba.
Al'amarin da ya sanya zuciyar mai girma Ladiyas ta ci gaban da tafarfasa tamkar zata ƙone
kenan.
Kodasamun wannan nasara da sarki Lazwar ya samu sai sarkin yaƙi Darusu ya umurci
waɗannan dakaru mutum Hamsin suka je suka buɗe ƙofar ɗakin aka fito da sarki Lazwar, likitoci
suka shiga ba shi taimakon gaggawa domin tsayar da jinin dake zuba a jikinshi tare sanya
mashi magani akan raunukan shi . Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka hango waɗansu dakaru
mutum arba'in shirye cikin gagarumar shigar yaƙi sun tuso ƙeyar yaro Imran da hadima
Khadijat, ɗaure cikin sasari na baƙin ƙarfe hannu da ƙafa.
A gefe guda kuma matsafi Shamrul ne tare tawagar malaman addininsu sanye da tufafi irin
na bauta.
Lokacin da ya zamana tazarar dake tsakanin su da karagar mulki bai huce taku goma ba sai
matsafi shamrul da sauran bokaye suka zube ƙasa bisa gwiwoyin su suka kwashi gaisuwa ga
sarki ladiyas. Suna masu sunkuiyar da kawunansu ƙasa.
Sai da suka ɗauki lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani matsafi Shamrul ya dago
da kanshi sama ya buɗi baki cikin ladabi da girmamawa cikin wata irin kakkausar murya mai
kama da kukan jaki ya ce "ya shugabana haƙiƙa abinbauta ya bada umurnin a yanka waɗannan
mutane biyu mace da namiji da suka shigo mana da wani sabon addini mai suna musulunci
wanda suke jan hankalin mutane wannan birni mai albarka, wanda a dalilin hakan zai janyo
mana musiba da annoba da zata haifar da suɓucewar mulkin ka".
Sa'adda da sarki Ladiyas ya ji wannan batu daga bakin matsafi Shamrul sai zuciyarshi ta
kama tafarfasa tamkar zata fasa ƙirjinshi ta fito waje, yaji ya tsani hadima Khadijat da yaro
Imran.
Kawai sai ya dubi Khadijat da fuskar ta ke rufe da rawani ya ce ''ya ke baiwa Sharifa haƙiƙa kin
yaudare ni kin ci amanata da kika zo da wani sabon addini a wannan birni nawa, na aika ki
zuwa ga sarkin kasuwa domin ki gane ki zamto 'yan leƙen asiri, domin ki taimaka min na samu
nasarar ganin bayanshi, haƙiƙa a yau zan yanke miki hukunci dai-dai da laifin da kika aika ta a
gareni";
Sa'adda da mai girma Ladiyas ya zo nan a zancen shi sai sarki Lazwar dake gefe guda
likitoci na duba lafiyar shi ya cika da matuƙar al'ajabi da mamaki ainun, bisa jin sarki Ladiyas ya
kira hadima Khadijat da suna baiwa Sharifa.
Shin dama Khadijat ita ce baiwa Sharifa da ya fito farautar ta ruwa a jallo?
Tabbas tsugunne bata ƙare ba wai an saci ɗan ɓarawo. Haƙiƙa dole ne ya yi sabon gumurzu
domin ceton rayuwar Khadijat.
Sarkin yaƙi, Bawa Shamsal da aljani Za'aratul-layal dake cikin siffar bil'adama tare da
gimbiya Mashlira dake sanye da tufafin dakaru cikin ɓaddakama, sai suka cika da matuƙar
mamaki bisa jin ashe hadima Khadijat ita ce baiwa Sharifa,
wannan fa shi ne masu iya magana ke cewa "rashin sani kaza ta kwana akan dami".
Ashe sarki Lazwar na tare da abin da yake nema bai sani ba har ya shigar da kanshi cikin
uƙubar sarki Ladiyas.
A ɓangaren jama'a kuwa sa'adda ji cewa yaron nan da yiwa matsafi Shamrul tambaya akan
addininsu za'a yanke wa hukuncin kisa, sai suka yaɗa labarin izuwa cikin gari, nan fa al'ummar
gari suka dinga tuttuɗowa suna cincirindo a fadar domin su ganewa idanuwan su.
Domin a yau ne zasu tantance shin tsakanin Ubangijin wannan yaro Imran da matsafi
Shamrul wane ne na abin bauta na gaskiya.
Sarki Ladiyas na kammala wannan batu sai sarki Ladiyas ya koma kan karagar mulkinshi
ya hakimce.
Kawai sai wani garjejen ƙato ya ɗauki yaro Imran ya ɗora a jikin wani zagayayyan tudu a fadar
sannan ya koma gefe guda ya ja ya tsaya, sarki Ladiyas ya yi wa sarkin yaƙi Darusu inkiya ta
wutsiyar idanu dake nuna bashi umarni.
Cikin dakewar zuciya gami da zafin nama sarkin yaƙi ya zare wata sharɓeɓiyar adda a
gadon bayanshi ya durfafi inda Imran yake domin ya datse wuyanshi.
Sarki Ladiyas, matsafi Shamrul da sauran bokayen suka bushe da dariyar mugunta har da
ƙyaƙyatawa.
Jama'a kuwa da yawan su sai suka fara zubar da hawayen takaici da baƙin ciki
Ya yin da sarkin yaƙi ya isa daf da shi sai ya daga addar ya ɗora akan waya yaro Imran.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wata kyakkyawar halitta ta keto daga saman
fadar ɗauke da waɗansu mutane guda biyu.
Ba wani bane wannan halitta da mutanen biyun ba face aljani Hadimul-khairi ɗauke da gimbiya
Lamrat matar sarki Ladiyas da 'yarta yarinya Shuraiba.
Kafin addar sarkin yaƙi Darusu ta yanka wuyan Imran aljani Hadimul-khairi ya ɗauko wata
farar kwalba mai ɗauke da wani koren ruwa ya watsa inda Imran da baiwa Sharifa suke, take
sarƙoƙin dake ɗaure a jikkunansu da addar dake wuyan Imran sun narke suka zama ruwa.
Cikin matuƙar firgici sarkin yaƙi, sarki Ladiyas da sauran jama'ar fada suka ɗaga
kawunansu izuwa sama.
Yaro Imran, hadima Khadijat, sarki Lazwar, sarkin yaƙi, bawa Shamsal, gimbiya Mashlira da
aljani Za'aratul-layal, kuwa sai suka cika da matukar farin ciki maral-musaltuwa.
Aljani Hadimul-khairi ya a sauka a turba bisa diga-diganshi.
Nan fa aka shiga kallon-kallo tsakanin sarki Ladiyas, da uwar gidanshi gimbiya Lamrat,
matsafi Shamrul da yaro Imran da hadima Khadijat wato baiwa Sharifat, sarkin yaƙi Darusu da
sarki Lazwar.
Cikin matukar ɓacin rai mai girma Ladiyas ya dubi uwar gidanshi Lamrat ya ce "ya uwar
gidana shin ina dalilin wannan zuwa naki a cikin wannan yanayi?
Koda jin wannan tambaya daga bakin Sarki Ladiyas sai gimbiya Lamrat ta tari
numfashinshi tana mai daka mashi tsawa, ta dube shi cikin matuƙar fushi ta ce "kai tsohon
AZZALUMI kuma la'ananne ka yi sani yanzu kan mage ya waye, a yau ne zan ɗauki fansar jinin
mai gidana maƙeri Murrasu daka ni da 'yata Shuraiba, haƙiƙa masu iya magana sun yi magana
da suka rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya, ka yi sani cewa tsawon shekarun da ka
shuɗe kana azabtar da jama'ar birnin ISTANBUL kana yiwa mutane BAKIN ZALUNCI, to ranar
ƙin dillanci ta zo maka.
Shawarar da zan baka ita ce ka yi hanzari ka rubuta wasiyyar da kake son bar wa jama'ar kafin
mu zare maka ruhinka daga gangar jikinka. Sannan ina so ka yi sani cewa ni da 'yata Shuraiba
tuni mun karɓi addinin yaro Imran.
A halin yanzu ni ba uwar gidanka ba ce face abokiyar gabar ka, dama dai-dai da rana
ɗaya ban taɓa ƙaunarka kawai ina yi maka biyayya ne bisa dole don tana din gobe na".
Sa'adda mai girma Ladiyas ya ji wannan batu daga bakin gimbiya Lamrat sai zuciyarshi
takama tafarfasa tamkar zata ƙone ya daka mata tsawa a lokacin da idanuwanshi suka kaɗa
suka yi jajur cikin kakkausar murya mai ya ce "kaicon ki yake Lamrat haƙiƙa kin tafka babban
kuskure da har kika yi gangancin haɗa kai da maƙiya na domin farautar rai na, a yau ne zan yi
maki hukunci mafi muni ke da 'yarki Shuraiba".
Sa'adda sarki Ladiyas ya zo nan azancen shi sai ya miƙe tsaye zumbur daga kan
karagar shi ta mulki ya cire alƙyabbarshi, take wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar
firgici da ban tsoro ta bayyana a jikinshi. Kawai sai ya dako wawan tsalle daga inda yake tsaye
yana saman ya daga hannunshi sama wata irin sharɓeɓiyar takobin sihiri ta bayyana a gare shi,
ya sauka bisa diga-diganshi a daf da inda Lamrat take.
Koda ganin hakan sai yarinya Shuraiba tayi wuf ta zare kwari da bakanta ta yi shirin ko ta
kwana.
Sarki Lazwar kuwa duk da cewar jikinshi ya yi tsami akwai manyan raunuka, amma sai ya
yi wuf ya kwaci wata takobi a hannun wani badakare ya falfala da azababban gudu izuwa kan
sarkin yaƙi Darusu
Baiwa Sharifa da yaro Imran kuwa sai suka yi ɗauki izuwa kan matsafi Shamrul suna masu
ƙwala kabbara, bawa Shamsal da sarkin yaƙi kuwa sai suka tari dakarun dake fadar, aljani
za'aratul-layal sai ya yi girgiza take surarshi ta canja daga ta bil'adama izuwa ta aljani kawai sai
ya rufawa mai gidanshi sarki Lazwar baya, a lokacin ne gimbiya Mashlira sai cire hular ƙarfen dake kanta fuskar ta ta bayyana a fili, nan fa
kowa ya cika da mamaki ganinta, kawai sai ta yi koyi da aljani Za'aratul-layal ta kaiwa
masoyinta sarkin Lazwar ɗauki.
Lokaci guda ɓangarorin biyar suka afkawa juna aka garƙame da azababban yaƙi mai
matuƙar muni da ban tsoro.
Wohoho! kaico haƙiƙa guguwar annoba idan ta taso babu mai maganin ta face Allah,
kuma tabbas in da babu ƙasa nan ake gardamar kokowa, domin KARON MAZA sai JARUMAN
DUNIYA da suka ciri tuta a GUMURZUN SHEKARA DUBU, waɗanda komai TSANANI DA
UKUBA a filin DANDAZON MAYAKA baya sa su gudu. Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan ya ga yadda fadar ta yamutse da gumurzu dole ne
ya ɗimauce ya fita daga hayyacin shi domin dola ne artabun ya zamo tashin hankali.
Nan fa jama'a suka ɗimauce suka kama guje-guje da ifice-ifice domin tsira da rayukansu
Ɓangarorin suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin matuƙar baƙin zafin nama
JURIYA DA BAJINTA tamkar jikkunan su basu kasance na bil'adama mai jini tsoka ba.
Kaico! Haƙiƙa duk wanda bai fita filin yaƙi ba to bai ga ƙarshen tashin hankali ba,
wanda bai san shi ba shi ne yake fatan zuwan shi, ana fara wannan ɗauki ba daɗi ne gimbiya
Lamrat, yarinya Shuraiba da Aljani Hadimul- kahiri suka fara gane cewa tabbas shayi ruwa ne
ba abinci mai nauyi ba, domin kuwa tsananin zafin naman sarki ladiyas ya nunka nasu sai
arba'in,
Nanfa ya zamana cewa mutum uku sun kasa galaba akan ɗaya ya zame masu alaƙaƙai, duk
sa'adda suka kai mashi hari da makaman smmsu idan ya kare da takobinshi, sai kaga
makaman sun dakushe kuwa ko gezau bai yi ba.
Idan kuwa Ladiyas ya kai masu harin idan suka goce sai ya zamana cewa duk abin da
takobin ta saran sai ya yi bindiga ya tarwatse koda kuwa gini ne.
Matsafi Shamrul, yaro Imran da hadima Khadijat kuwa tuni labari yasha banbam, domin kuwa
sun hana tsafi Shamrul rawar gaban hantsi, har sai ya zamana cewa ya daina amfani