Showing 33001 words to 34144 words out of 34144 words
Chapter 12 - Sarautar Mutuwa Book Complete by Mansur Sufi .pdf
jini ya yi tsartuwa.
Amma saboda karfin zuciya gami da juriya irin ta manyan GWARAZAN JIYA sai ya miƙe
tsaye zumbur yana mai goge jinin dake bakinshi yana mai gyara tsayuwa.
A dai-dai lokacin da Nabihat ta miƙe tsaye zumbur, aka sake sabon kallon kallo, sannan
suka sake afkawa junan da yaƙi, ana fara wannan arbu ne Nabihat ta shammaci Sharkar ta
gabza mashi naushi a kirjinshi da kafafuwanta biyu, saboda ƙarfin naushin sai da ya yi sama ta
tamkar an janye shi da ƙungiya sannan ya faɗa izuwa tekun Baharul-sawara. Koda samun wannan gagarumar nasara sai jaruma Nabihat ta ruga izuwa inda 'yan
uwanta suke ta kai masu ɗauki su ka cigaba da ragargazar dakarun.Cikin kankanin lokaci suka
hallaka su baki ɗaya.
Kawa sai Nabihat ta umarci 'yan mata uku da su tuƙa jirgin ruwan a cigaba da tafiya
Cikin matuƙar kaɗuwa ɗaya daga cikin fursunonin ta dubi Nabihat cikin tashin hankali ta ce '' ya
ke Nabihat ta ya ya zamu cigaba da tafiya bayan cewa yarinya Lazimat na cikin wannan teku,
kuma bamu da tabbacin a wane hali take ciki tana raye ne ko ta mutu.
Koda jin wannan batu daga bakin Sharimat sai idanun Nabihat su ka ciko da ƙwalla, ta
dube ta ta ce "ya ke Shamirat tabbas a yanzu ba ni da tabbacin yarinya Lazimat na raye, shin
yanzu zamu tsaya neman ta ne? Ko kuwa zamu cigaba da tuƙa wannan jirgin ruwa domin ceto
daruruwan jama'armu da suka haɗar da yara ƙanana da mata gami da tsofaffi,'? Ina so ki
kwantar da hankalinki idan har yarinya Lazimat na raye zamu sake saduwa da ita".
Koda jin wannan batu daga bakin Nabihat sai Shamirat ta gyaɗa kai cikin alamun
matuƙar damuwa ta matsa kusa da 'yan uwanta, suka shiga tuƙa jirgin ruwan domin koma
izuwa birnin su.
A dai-dai wannan lokaci ne shugaba Yasiran ya taso daga ƙarƙashin tekun fuskarshi a
murtuke babu annuri, tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta, gundulmin hannunshi da
Lazimat ta sare mashi na zubar da jini.
Sa'adda jaruma Nabihat ta cigaba da jagorantar sauran 'yan uwanta fursunoni, a bisa
jirgin ruwan dake tafiya akan tekun Baharul-sawara, domin gudun TSIRA DAGA HAKA.
Sai suka shafe tsawon sa'a biyu suna tafiya babu sassauci.
Lokacin da ya zamana an shafe sa'a ɗaya ana tafiyar sai jaruma Nabihat ta yi umarni aka
shiga ɗakin sirri dake ƙarƙashin jirgin ruwan, aka ɗauka gurasar gami taceccen ruwan inabi, aka
shiga rarrabawa jama'arsu domin kowa ya kimtsa cikinshi.
Ana cikin wannan hali ne
kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka hango waɗansu tawagar jiragen ruwa kimanin guda
ashirin, sun bayyana a saman tekun a kowa ce kusurwa, wato gabas, yamma, kudu da Arewa,
Cikin matukar kaɗuwa gami da tashin hankali Nabihat ta yi umarni aka tsayar da tafiya,
kawai sai 'yan matan suka ruga izuwa wani ɓangare a jirgin suka ɗebo makaman yaƙi, sannan
suka ruga izuwa tsakiyar birnin suna masu gyara tsayuwar su zukatansu cike da matuƙar firgici.
Ya yin da ya zamana cewa jiragen ruwan sun matso daf juna, sai Nabihat ta sake
ɗimauce wa, su dai jiragen ruwan suna ɗauke ne da waɗansu irin zaratan dakaru masu ƙirar
samudawan farko, suna sanye cikin sulken yaƙi na baƙin ƙarfe, ɗauke da miyagun MAKAMAN
ƘARE DANGI.
Kaico! Haƙiƙa waɗannan dakaru sun kasance masu ban tsoro, domin babu halitta da za
ta yi arba da su face ta yi nadamar wanzuwar ta a doran ƙasa.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su Nabihat da tawagar dakarun.
Tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali, a lokacin ne su Nabihat suka hango shugaba
Yasiran a ɗaya daga cikin jiragen ruwan, shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannunshi ɗaya
ɗauke da wata sharbebiyar takobi, ɗayan kuwa da ya yi dungulmi ya naɗe shi da wani farin
ƙyalle, fuskarshi a murtuke babu annuri har gyatsune take saboda matuƙar fushi. Al'marin da ya yi matuƙar ba su mamaki kenan, suka tambayi kansu a cikin ransu suna
masu cewa, ya aka yi Yasiran ya rayu shin ina yarinya Lazimat take tana raye ne ko kuwa ta
mutu?
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kawunansu kenan.
Kawai sai Nabihat su ka hango dakaru masu tarin yawa suna dako tsalle daga inda suke suna
sauka akan jirgin da suke suna shawagi a sama tamkar tsuntsaye, suna ihu da kururuwa mai
firgitarwa.
Koda ganin hakan sai Nabihat ta ɗaga takobinta sama cikin ƙarfin hali gami da ƙarfafawa
sauran 'yan matan gwiwa ta falfala da gudu izuwa kan dakarun.
Ya yin da 'yan matan suka ga haka sai suka yi koyi da ita, suna masu mara mata baya.
Tabbas shi ƙarfi a zuciya yake ba wai a girman jiki ba, domin idan ba haka ba taya ya
mutum ashirin za su za su tunkari ɗaruruwa.
Amma dai masu iya magana na cewa shi bala'i kafin ya zo ne ake neman mafita, amma idan
yazo babu abin da ya rage face a karɓe shi hannu biyu.
In da a ce mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan dubban dakarun suka
yunƙura kan su jaruma Nabihat, sai ya yi zaton DANDAZON zakuna ne suka farwa barewa
guda ɗaya jal, saboda matuƙar kwarjinin su.
Ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi mai matuƙar firgici da ban tsoro.
Ƙarar haɗuwar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne.
Ana fara wannan artabu ne su jaruma Nabihat suka fara gane cewa sun haɗu da gamon su.
Domin kuwa kods ba'a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza, kuma ruwa ba sa'an
kwando ba ne.
Tirƙashi muje zuwa domin jin wannan ƙayataccen labari mai taken
FATAUCIN BAYI! FATAUCIN BAYI!!
Ga shi nan tafe
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071