Showing 9001 words to 12000 words out of 34144 words
Chapter 4 - Sarautar Mutuwa Book Complete by Mansur Sufi .pdf
aka shige da su sarki Lazwar cikin gidan ba lallai ne suka kasance a
raye ba, lallai dole ta yi dukkanin ƙoƙarin da ya dace don ceto rayuwar su kafin gari ya waye.
Gama tunanin hakan keda wuya sai Shuraiba ta hangi wani tsuntsu a saman ta yana
yana wani irin kuka da ta ga ya durfafi wani ɓangare na musamman a wannan gida da za shige
da su sarki Lazwar, cikin matuƙar farin ciki ta dunga bin bayan tsuntsun, ba tare da waɗannan
dakaru sun ganta ba. Koda isowar ta kusa da saitin inda dakarun suke a dai-dai lokacinne aka iso da su sarki Lazwar
za a shiga da su cikin.
Sai kawai ta ga wannan tsuntsu ya buɗe bakinshi ya busa wa gaba ɗaya dakarun wani irin
koren haske, kafin ka ce me sun ɓingire ƙasa suna sharar barci har da munshari, kuma koren
hasken ya shiga cikin kejunan su sarki Lazwar, take suka narke suka zama ruwa, sarƙoƙi da
aka ɗaure aljani Za'aratun-layal suka ɓace ɓat!. Daga can sai tsuntsun ya rikiɗa izuwa wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa, ba wata ba ce
face gimbiya Mashlira 'ya ga sarkin murida Zammar.
Nan fa sarki Lazwar, Shuraiba, sarkin yaƙi da bawa Shaiban suka cika da matuƙar al'ajabi.
Cikin wata irin zazzaƙar murya mai ɗan karen daɗi tamkar ana busa sarewa, gimbiya Mashlira
ta dube su su duka huɗun ta ce "yanzu ba mu da lokaci da zamu tattauna domin a kodayaushe
mahaifina zai iya biyo sahun mu, matsawar ya riske mu ɗayan mu ba zai tsira da rayuwar shi
ba. Ko da jin wannan batu daga bakin Mushlaira sai sarki lazwar ya umarci aljani Za'aratun-layal ya
ɗebe su baki ɗaya, zuciyarsu cike da matuƙar farin ciki bisa ganin cewa yarinya shuraiba ta na
raye cikin koshin lafiya, kuma gimbiya Mashlira ta ce ci rayuwar su.
A dai-dai wannan lokaci ne sarki Zammar da tawagarshi suka bayyana a wajen, koda ya
ga dakarun kurku kwance suna sharar barci kuma babu su Lazwar da 'yarshi Mashlira, sai
kawai ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu, ihun shi ya haddasa wata girgizar ƙasa da ta sanya
gine-gine suka dunga rushewa, nan fa birnin ya kaure da gujegujen jama'a domin TSIRA DA
RAYUKA.
Sai da sarki ya tsuke bakinshi sannan komai ya samu dai-dai ta gidaje suka dai na rushewa
mutane suka daina hallaka.
Kawai sai ya ɗauko madubin tsafinshi ya shafe shi da hannunshi na hagu, yana mai karanta
waɗansu dalasiman tsafi, yana gama rufe bakinshi hoton aljani Za'aratun-layal ya bayyana a
kai, yana tsala azababban gudu ɗauke da su sarki Lazwar da 'yarshi Mashlira.
Koda ganin hakan sai takaici ya ƙara turnuƙe zuciyarshi har ƙwallar baƙin ciki ta zubo
mashi, kawai sai ya runtse idanuwanshi yana mai karanta waɗansu dalasiman tsafin na daban,
koda kammala hakan sai ga wata irin halitta ta ketowa daga cikin ƙarƙashin ƙasa.
Halittar ta nunka aljani Za'aratun-layal a girma, muni, da kwarjini gami da cika idanu.
Ba wata ba ce wannan halitta ba face aljani Durusul-fannar,
Durusul-fannar ya faɗi ƙasa ya yi sujjada ga sarki zammar,
Zammar ya du be shi fuska a murtuke babu annuri, tamkar an watsa mashi garwashin wuta kan
ta.
Cikin kakkausar murya mai ban tsoro ya ce "ya kai uban hatsabibai kuma kakan
kangararru na duniya ka yi sani cewa, fiye da shekaru dubu ɗaya da ɗoriya rabon da na kira ka
domin aiwatar da wani aiki sai yau, to ina so ka yi sani cewa na kirowa ka ne domin ka bi sahun
su 'yata Mashlira da ta ci amana ta ta kuɓutar da waɗansu bil'adama da muka farauto. Ina so ka kawo min su a raye cikin ƙoshin lafiya domin ni da kai na zanyi hukunci,
Koda sarki Zammar ya zo nan zancen shi, sai Durusul-fannar ya sake yin sujjada karo na biyu
ga sarki Zammar cikin wata irin murya mai kama da saukar aradu ya ce "an gama ya sarkin
sarakai, yin biyayya a gare ka shi ne ibada ta".
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Durusul-fannar ya ya yunƙura izuwa sama domin ya bi
sahun su aljani Za'aratun-layal, take ya shiga keta gajimare cikin wani irin masifaffan gudu
tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.
Wannan shi ne abin da ya faru a acan birnin muridai.
BABI NA BIYAR
Al'amarin su sarki Lazwar kuwa lokacin da suka ci gaba da gudu a bisa kan aljani
Za'aratun-layal, bayan gimbiya Mashlira ta ceci rayuwar su daga hannun mahaifinta, sai suka ci
gaba da tafiya a sararin samaniya cikin hanzari.
Ana fara wannan tafiya ne sarki Lazwar ya matsa kusa da Mashlira ya ce" ya ke wannan 'yar
sarki ma'abociyar tausayi da jin ƙai, haƙiƙa ba mu san da wane irin baki zamu gode miki ba bisa
ceton rayuwar mu da kika yi.
Sai dai abin da muka kasa fahimta ni da abokan tafiya ta shi ne, mene ne dalilin da ya sanya
kika biyo mu bayan cewa baki san daga wata duniya muke ba, kuma baki san ina zamuje ba.
Ko da jin wannan batu sai Mashlira ta yi wani ƙayataccen murmushi da ya kara tona asirin
tsantsar kyawun surar ta har fararen haƙoranta suka bayyana farare ƙal! Cikin daddaɗar murya
ta ce "ya kai wannan sarki ka yi sani cewa kafin na fito daga cikin gidan sarautar birnin mu sai
da na gudanar da bincike bisa halarar tsafina, na gano dukkan labarin ku da duk abin da ya
baro da ku daga biranan ku, na nemo abubuwan da su warkar da kai daga sihirin da abokin
gabar ka sarki Darwazu ya yi maka.
Bakomai ne ya sanya na biyo ku domin gudanar da wannan tafiya ba, duk kuwa da irin
haɗurran dake tattare da ita sai domin mahaifina ya gano cewa nan gaba zan samu ɗaukaka
mai yawa wacce sai labari na ya yaɗu a duniya, bisa binciken da na gudanar a yau na gano
cewa ta silar ku zan samu wannan ɗaukaka. Sannan kuma zan cika burina na samowa jama'ar birninmu maganin da zai warkar da su, su
dawo ainahin surar su ta bil'adama. Da yake duk wannan tattaunawa da ake yi tsakanin sarki
Lazwar da Mashlira kowa yana saurare, ya yin da aka ji abin da Mashlira ta furta sai kowa ya
cika da matuƙar mamaki da al'ajabi. Sarki Lazwar ya dube ta cike da matuƙar mamaki ya ce "ya sarauniyar kyawawa shin dama
jama'ar birninku bil'adama ne kamar mu ba muridai ba?
Ko da jin wannan tambaya sai idanun Mashlira suka ciko da kwalla, fuskarta cike da
matuƙar damuwa ta ce "Bbsa labarin da mahaifina ya ba ni ya tabbatar min da hakan, kuma ya
sanar dani maganin da zai warkar da su daga wannan annoba, akwai buƙatar na sanar da ku
labarina a taƙaice.
BABI NA SHIDA
A wani zamani can baya mai tsawo da ya shuɗe lokacin da jahilci ya yi katutu a zukatan
bil'adama, ƙarfi da jarumtaka suka zamto jari, kuma ake yin gashin dankali wato babba a sama
ƙarami a ƙasa
A wannan lokaci anyi wata nahiya mai ɗauke da manyan birane guda biyar,
biranen na ƙarƙashin mulkin wani gawurtaccen azzalumin matsafi da ake yiwa laƙabi da
Sahibul-ukub
Matsafi Sahibul-ukub yakasance GWARZON DUNIYA mai ƙarfi na Allah ya isa, domin an ce a
filin yaƙi yana iya shafe tsawon kwanaki biyu yana yaƙi ba tare da ya ci ko ya sha ba.
Idan ya je farauta daji kuwa yana iya saɓo giwa a kafaɗarshi, ya yi gudun sa'a ɗaya da ita
ba tare da ya gaji ba, komai girman bishiya idan ya naushe ta da hannunshi sai ta jijjigo har
saiwarta sannan ta faɗi ƙasa,
Kai wasu lokutan ma idan zai kai farmaki wani birni ko alkarya, shi kaɗai yake fita ya yaƙi birnin
a dare ɗaya ya farauto bayi, da dukiya mai da ganima mai tarin yawa.
Bisa wannan dalili ne ya sanya duk biranen da suka ji labarin matsafi Sahibul-ukub zai kawo
farmaki, ko da dai su fita su tafi izuwa gare shi su yi MUBAYA'A kafin ya zo, ko kuma su tattare
ina-su-ina-su su fice daga birnin su yi hijira izuwa wata nahiyar daban.
Batun ƙarfin sihirin tsafi kuwa, masu bincike da hasashe sun tabbatar da cewa a halin
yanzu babu matsafi kamarshi, zaluncin shi kuwa ya huce yadda muke tsammani domin saboda
matuƙar zaluncin shi yasa aka gina mashi kurkukun ƙarƙashin ƙasa da ake bautar da mutane
da aljanu. A rayuwar matsafi Sahibul-ukub bai taɓa yin aure ba ballantana a ce yana da magaji da zai
maye gurbin karagarshi.
wata rana yana zaune a turakar shi sai kawai a ka ji ya taƙarƙare ya ƙwala ihu sannan
daga bisani ya bushe da dariya mugunta, bakomai ne ya sanya matsafi sahibul-ukub ihu da
dariyar ba face wani labari da sarki yaƙin sa ya kawo mashi, na wani ɓoyayyen birni mai tarin
arzikin noma kiwo, da ma'adanan ƙarƙashin kasa. Birnin Madinatul-Adfal na yamma maso arewacin birnin Sin.
Sarkin da ke mulkin birnin yakasance GWARZON DUNIYA mai karfi na Allah ya isa, yana
shugabantar jama'ar shi bisa adalci da matuƙar tausaya wa, bisa wannan dalili ne ya sanya
kullum tattalin arzikin birnin yake ƙara haɓaka.
Wani abu da matsafi Sahibul-ukub ya gani bisa halarar tsafinshi shi ne, matuƙar ya mallaki
birnin zai zamo mashahurin attajirin da babu kamarshi a faɗin duniya, kuma a wannan birni zai
gina fadar da take babu kamar ta a duniya baki ɗaya.
Kasancewar birnin yana ɗauke da dukkanin wani yanayi mai daɗi da bil'adama ke bukata.
Bayan Sahibul-ukub ya kammala dariyar mugunta, sai ya juya ya dubi sarkin yaƙin da ke
durƙushe a gaban shi tamkar zai yi mashi sujjada, cikin wata irin kakkausar murya mai tattare
da taƙama gami da BAKAR IZZA ya ce ''ya kai dirkar birnin Jauraful-harbat, haƙiƙa ba ka taɓa
zuwa mii da labari mai daɗi kamar wannan ba, Amma lamarin ɓoyayyen birnin ya ba ni mamaki,
da har na gasa gano shu bisa halarar tsafi na, amma ba abin mamaki bane domin masu iya
magana na cewa shi ilimin tsafi kogi ne komai nutson ka ba za ka iya ɗebe abin da ke cikin shi
ba sai dai ka ɗebi iya gwargwadon ka.
Yanzu abin da nake so shine a tanadar min dakarun yaƙi guda dubu hamsin, tare da
magina dubu goma da kuyangi dubu, bayi da barori, a daren yau ina so alfijir ɗin a subahin
gobe ya keto min a birnin madinatul-Adfal, domin wannan yaƙi na musamman ne a gare ni, ko
da jin wannan batu sai sarkin yaƙi Shamsal ya risina ga matsafi Sahibul-ukub ya ce "an gama
ya shugaba na".
Yana gama faɗin hakan sai kawai ya miƙe tsaye ya fice daga turakar, domin aiwatar da umarnin
da akayi mashi.
A can birnin Madinatul-Adfal kuwa jama'a na gudanar da ayyukan su cikin lumana, masu
saye da siyarwa na yi masu noma da kiwo na yi, sauran yara kuwa na wasanni a tsakanin su
cikin nishaɗi, hakan kuwa ya faru ne sakamakon saukar ruwan sama a daren jiya kamar da
bakin ƙwarya ƙasa ta kwanta kuma gari ya yi daɗi korayen tsirrai sunyi luɓ-luɓ gwanin ban
sha'awa,
A na cikin wannan hali ne sai ka ga gari ya yi duhu dumɗum! Tamakar dare biyu ya haɗu
waje guda, kai ka ce hadari ne ya gangamo zaa ɓarke da da ruwan sama, nan fa gari ya kaure
da gujegujen jama'a gami da ifice-ifice yara da manya mata da maza.
Ba wani abu ba ne ya haddasa wannan duhu ba face bayyanar rundunar matsafi Sahibul-ukub
da ta iso birnin
Sa'adda gimbiya Mashlira yar sarkin muridai Zammar ta zo dai-dai nan a labarin ta sai ta yi
shiru, bakomai ne yasanya ta yi hakan ba, sai bisa ganin wata mummunar halitta da ta bayyana
a gaban su, ba wani ba ne wannan halitta ba face aljani Durusul-fannar da mahaifinta ya turo
domin ya farauto su. Ko da bayyanar aljani Durusul-fannar sai cikin kowa ya ɗuru ruwa, hatta shi kanshi
aljani Za'aratun-layal da ya kasance aljani.
Wannan fa shine masu iya magana ke cewa GABA DA GABANTA wai aljani ya taka wuta, kafin
ɗaya daga cikin su ya yi wani yunƙuri aljani Durusul-fannar ya buda wata irin iska daga
bakinshi, nan take su sarki Lazwar suka kama barci mai nauyi, kawai sai ya damƙe su ya
makale su ajikin fuka-fukanshi tamkar ya ɗauko 'yan tsaki, ya juya izuwa hanyar da za ta mayar
da shi izuwa birnin muridai.
Tofa ana dara ga dare ya yi.
Lokacin da aljani Durusul-fannar ya tsala da azababban gudu, ɗauke da su gimbiya Mashlira,
sai ya ci gaba da keta gajimare cikin gudun huce sa'a domin ya isa ga sarki Zammar,
yana cikin wannan gudu ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai ya yi kiciɓus da wani aljani
agaban shi, Aljanin ya kasance ma'abincin kyawun sura fari sol.
Zaune a bisa kanshi wani kyakkyawan yaro ne mai kimanin shekaru goma sha shida, wanda da
kaɗan ya ɗara yarinya Shuraiba.
Yaron yana sanye cikin fararen tufafi tun daga ƙasa har sama, a gadon bayanshi yana rataye da
wata sharbebiyar takobi.
Kallo ɗaya zaka yiwa yaron ka tabbatar da cewa kyakkyawa ne na gaban kwatance domin inda
za'a ajiye shi daf da gimbiya Mashlira ba za ka iya tantance wane ne yafi kyawu a tsakanin su
ba.
Sa'adda Durusul-fannar ya yi arba da su yaji zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya ɗarsu a cikin
ta.
A karo na farko a rayuwar shi ya ji wata halitta ta razana shi, nan fa ya cika da matuƙar
mamaki ainun.
Abu na farko da ya bashi mamaki shine duka aljanin bai kama ƙafarshi a girman jiki da surar
jarumtaka ba, kuma wanda ke zaune a kanshi bil'adama ne yaro matashi.
Kawai sai ya yi ƙarfin hali ya dakawa masu tsawon cikin matuƙar fushi ya dube su ya ce ''ya ku
waɗannan ma'abota GAJERAN KWANA shin wane rashin tunani ya sanya za ku tare min
hanya? Ba ku da labarin cewa nine GOBARAR ANNOBA mai tada hankalin duniya, ANNOBA
ƊARI mai shayar da jarumai TASKAR AZABA? Kafin aljani Durusul-fannar ya gama rufe bakinshi kyakkyawan yaron ya tari numfashin sa yana
mai cewa ''kaicon ka ya kai tsohon mushriki, ka yi sani cewa yau ƙarshen ka ya zo, kai maza ka
miƙo min su sarki Lazwar da ka ɗauko su domin ka kaiwa sarki Zammar ya hallaka su.
Sannan kuma ina kira a gare ka ka bayar da gaskiya da Ubangijin da ya halicci duniya da abin
da ke cikin ta";
Ko da jin wannan batu sai zuciyar aljani Durusul-fannar ta kama tafarfasa tamkar za ta
ƙone ya sake dakawa yaron tsawa a karo na biyu, tabbas yaro man kaza, bai san wuta ba sai ta
narka shi, kuma haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka, tsautsayin akuya gai da kura,
rabon da wata halitta da ɓata min rai yau shekara dubu hamsin, lallai daga kan ku hakan ba zai
sake faruwa ba, domin zan koyar da duniya darasi akan ku".
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Durusul-fannar ya yi ɗauki kan su yana ihu da
kururuwa mai firgitarwa, tamkar zai tashi duniya baki ɗaya,
Ko da ganin hakan sai kyakyawan yaron ya buɗe bakinshi yana mai karanta waɗansu kalmomi,
sannan ya zare takobinshi a gadon bayanshi ya tunkari Durusul-fannar suka yi KARON BATTA.
Kaico! Haƙiƙa KARON MAZA babu daɗi, kuma tashin hankali ba a sa ka mai rana, nan fa aka
ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro gami da ban al'ajabi, nan fa
yazamana cewa, abin nan da masu iya magana ke faɗi ya fara tabbata, wato ɗan hakin da ka
raina shi ne ke tsoka ne maka idanu. Sai ga shi yaron ya zamto wa Durusul-fannar ƙadangaren bakin tulu kuma alaƙaƙai,
Duka sa'adda da ya kai mashi duka da hannayenshi sai yaron ya zille gami mayar da martani
cikin zafin nama, idan takobinshi ta taɓa jikin Durusu sai ka ji ya kurma wawan ihu.
Bakomai ne ya sanya shi ihun ba face tsananin zafi da raɗaɗin da yake ji tamkar ana ƙona shi
da wuta.
Abin da Durusul-fannar bai sani ba shi ne takobin yaron na ɗauke da sirri na musamman,
ana cikin wannan artabu ne yaron ya kaiwa Durusul-fannar wawan sara a kafaɗarshi, cikin sa'a
ya yanke shi, take jikinshi ya kama da wuta, nan fa aljani Durusul-fannar ya kama ihu da
kururuwar neman taimako. Indai ace mutum ya na tsaye a wannan waje yana