Showing 1 words to 3000 words out of 34144 words
Chapter 1 - Sarautar Mutuwa Book Complete by Mansur Sufi .pdf
SARAUTAR MUTUWA
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071
Haƙƙin mallaka
SUFI
Shekarar bugu
2023
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071
GODIYA
Ta tabbata ga Allah (SWT) bisa iko da ya ba ni na rubuta wannan littafi mai suna
SARAUTAR MUTUWA.
Tsira da amincin Allah ya ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu (SAW) da iyalanshi
tsarkaka da sahabbanshi masu haske.
SADAUKARWA
Wannan littafi sadaukarwa ne ga ɗaukacin masoya Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi a ko
ina suke a faɗin duniya.
Tsarawa da bugawa SUFI PUBLISHING COMPANY
R/lemo L/ Pol Kano Nigeria.
BABI NA ƊAYA
A ƙarni na biyu bayan yaƙin duniya na ɗaya, a yankin arewacin larabawa anyi wani
ƙasaitacce birni da ake yiwa laƙabi da zawatul-ifdar.
Birnin zawatul-ifdar ya bunƙasa a harkokin kasuwanci, noma, kiwo da ƙarfin tattalin arziki.
Sarkin dake mulkin birnin ya kasance gawurtaccen matsafi kuma mashahurin attajiri ana yi
mashi laƙabi da Lazwar ibn kaulat.
A gaba ɗaya nahiyar larabawa babu mashahurin sarki tamkar shi bisa wannan dalili ne ya
sanya ya zamto GAGARABADAU a tsakanin sarakunan nahiyar.
Duk waɗannan abubuwan da sarki Lazwar ya tara da ya danganci ƙarfin sihiri da tarin dukiya
gami da ƙarfin masarauta ya tashi a banza, domin a daren kowace rana sai na kulle ƙan shi a
turakarshi ya yi ta kukan takaici da baƙin ciki, har sai kuyanginshi sun shayar da shi barasa
sannan yake samun barci. Ba komai ne yake sanya sarki Lazwar wannan kuka ba face wani dalili guda ɗaya jal!
Dalilin kuwa shine bisa binciken da ya gudanar bisa halarar tsafin shi ya gano cewa har abada
ba zai samu haihuwa da kowace 'ya mace ba face ya karya wani sihirin da abokin gabar shi
sarki Darwazu ya yi mashi.
Matsawar kuwa ya yi ganganci ya sadu da wata 'ya mace koda kuwa kuyangarshi ce,
take dukkanin sirrikan tsafinshi da duk abin da ya mallaka zai ƙare zai dawo talaka (faƙiri).
Tsawon shekaru biyar sarki Lazwar yana cikin wannan baƙin ciki dare da rana.
Kwatsam! Wata rana sai kawai aka ji ya ƙwalla ƙara sannan ya bushe da dariya, sautin dariyar
tashi ya amsa kuwwa izuwa gidan sarautar baki ɗaya.
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa kowa mamaki kenan, domin yau tsawon shekaru biyar ba'a
taɓa jin shi ya yi hakan ba.
Abin da mutane ba su sani ba shi ne bakomai ba ne ya sanya sarki lazwar wannan dariya
ba,
sai domin yau ne ya gano hanyar da zai lalata sihirin da abokin gabarshi sarki darwazu ya yi
mashi.
Abu na farko da zai mallaka shi ne hawayen wani gawurtaccen dodo dake zaune a dajin
Darul-shatir dodo Murgazu ya kasance hatsabibi wanda ya addabi fatake da biranen dake
maƙwabtaka da dajin Darul-shatir.
Abu na biyu shine tsumin tsafin bokanya Lazira,
bokanya Lazira ta shafe tsawon shekaru dubu biyu tana tsuma tsumin tsafin domin ta cika burin
ta na tashin kakanta sarkin bokaye daga cikin kushewarshi, domin ya sanar da ita waɗansu
sirrikan tsafi da zata mulki duniya da su.
Abu na uku shine ruwan tekun Bahar-dawa'u, tekun Bahar-dawa'u na yamma maso
arewacin duniya, yana ɗauke da waɗansu irin musifaffun kifaye da macizai da adadin su ya kai
dubu biyar, tsananin ƙarfin damtsen ɗaya daga cikin halittun ya nunka na bil'adama sau hamsin.
Abu na huɗu shine alƙyabbar sarkin bokayen duniya na ɗaya boka Murkatul-azab, a halin
yanzu alƙyabbar na ajiye a fadarshi dake ƙarƙashin tekun Bahar-maliya, matsafa, bokaye da
masu hasashe sun tabbatar da cewa a halin yanzu a duniya babu wani waje mai tattare da
musibu tamkar fadar sarkin bokayen duniya. Abu na ƙarshe shi ne wata jaruma da ake yiwa laƙabi da Sharifa bintu Usman.
A halin yanzu Sharifa na bauta ne a ƙarƙashin masarautar birnin Istanbul a matsayin baiwa,
mahaifanta sun rasu ne a bisa KANGIN BAUTA a masarautar.
Baiwa Sharifa ce kaɗai zata iya taimaka mashi ya samu nasarar mallakar waɗancan abubuwa.
Sa'adda darki Lazwar ya ga wannan al'amari sai ya cika da matuƙar farin ciki, sai dai wani
abu daya dugunzuma hankalin shi, shine halarar tsafinshi ta bayyana mashi cewa ba zai taɓa
samun nasarar saduwa da baiwa Sharifa ba har ya samu damar bayyana mata buƙatar shi na
son taimaka mashi ya samu don mallakar waɗancan abubuwan da zai karya sihirin ba, face
shima ya mayar da kanshi bawa ya yi bauta a ƙarƙashin masarautar na tsawon shekaru.
Sannan ma inda gizo ke saƙar shi ne, ba lallai ne Sharifa ta iya amincewa da buƙatar shi
ba, tunda a halin yanzu ta rasa dukkan wani farin cikin rayuwar ta.
Kasancewar masu iya magana na cewa biyan buƙata yafi dogon buri, kuma inda rai da rabo.
Kawai sai ya yanke ranar da zai fita farautar baiwa Sharifa.
BABI NA BIYU
Kashe gari tun da duku-dukun safiya sarki Lazwar ya fara shirye shiryen tafiya izuwa
birnin Istanbul , a dai-dai lokacin da rana ta fara haske ne ya kammala shirin tsaf!
Tun daga kuyangi masu hidima, dakaru, gami da bayi.
A can fada kuwa jama'a sun cika maƙil babu masaka tsinke. Duk inda mutum ya kalla kawunan
bil'adama ne rututu babu saka tsinke tamkar dandazon kiyasai.
Kowa ya zuba idanu ana jiran fitowar sarki domin ganin wane zai baiwa riƙon sarautar shi.
Tsawon daƙiƙa latalin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne aka jiyo bushin algaita haɗe
da bugun tambura.
Daga can sai ga sarki Lazwar tafe tare da tawagarshi yana sanye cikin surutu na alfarma da
sukayi matukar yi mashi kyawu, kai tsaye ya huce izuwa kan karagarshi ta mulki ya tsaya
sannan ya fuskanci jama'a ya yi gyaran murya ya ce "ya ku mutanen wannan fada tawa mai
albarka ku yi sani cewa a yau ne zan yi gagarumar tafiya izuwa nemo abubuwan da za su
warkar da ni daga sihirin da abokin gaba ta sarki Darwazu ya yi mini.
A bisa al'adar wannan masarauta sarki da kanshi yake zaɓar wanda zai bawa riƙon sarautar
shi.
Bisa ga nazari da kuma hasashe da nayi babu wanda zai riƙe sarautar wannan birni da amana
face magajin gari Yasiran".
Sa'adda sarki Lazwar yazo nan a zancen shi sai jama'a suka ruɗe da shewa da jinjina domin
suna ganin shike nan sun huta da mulkin zaluncin sarki lazwar.
Kaico! Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce rashin sani yafi dare duhu, inda a ce
jama'a sun san wane ne magajin gari Yasiran da sun gwammace gwara sarki lazwar sau ɗari.
Bayan an ɗora Yasiran a bisa karagar mulki sai kawai sarki Lazwar ya buɗe bakinshu ya ƙwala
wa wani hadimin aljanin shi kira sau uku, yana gama rufe bakinshi sai kaga wata halitta
shirgegiya na ketowa daga cikin gajimare tana sauka daga sararin samaniya. Nan fa suka
ɗimauce suka fara guje-guje da ifice-ifice tamkar sun hango mutuwarsu, wasu ma saboda
razani har sakin fitsari suke a wando basu sani ba.
Aljanin ya sauka a turba yana mai shimfiɗe fuka-fukanshi a ƙasa, shi dai aljanin ya kasance
shirgege tamkar tsauni yana da rafkeken kai mai ɗauke da kwala-kwalan idanu jajur tamkar
garwashin wuta, hancinshu ƙato ne kofofinshi tamkar bututun shaƙar iska, bakinshi yana da
girma tamkar bakin rijiya, maƙale a kwiɓin hamatarshi yana ɗauke da manyan fuka-fukai guda
huɗu.
Haƙiƙa wannan aljani yakasance mummuna kuma abin tsoro ga duk wata halitta mai numfashi.
Aljanin ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa ga sarki Lazwar.
Sannan ya ɗago da kanshi ya dubi sarki Lazwar cikin ladabi ya ce cikin wata irin kakkausar
murya mai kama da kukan jaki ya ce "ya mai duniya gani na amsa kiran ka me kake da buƙata
ya shugabana?
Wani alfahari ya shiga kwanyar sarki lazwar jin aljanin ya ambace shu da mai duniya,
cikin BAƘAR IZZA Lazwar ya ce " ya kai Za'aratun-layal ka yi sani cewa bakomai ya sanya na
kira ka nan ba sai domin ka ɗauke ni da tawaga ta domin gudanar da wata gagarumar tafiya
mai matuƙar haɗari.
Sai dai ina so ka yi sani cewa wannan shine aikin ka na ƙarshe da zan 'yan ta ka ' daga
ƘANGIN BAUTA a gare ni".
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai aljani Za'aratun-layal ya bushe da dariyar
farin ciki, dariyar tashi ta haddasa wata gagarumar girgizar ƙasa mutane suka fara halaka, sai
da sarki Lazwar ya daka mashi tsawa, sannan ya tsuke bakinshi, a sannanne komai ya samu
dai-dai ta. Ba tare da ɓata lokaci ba sarki Lazwar da tawagarshi su ka hau bisa kan Za'aratun-layal da ya
haɗar da sarkin yaƙin birnin da waɗansu zaratan bayi gami da kuyangi masu hidima suka zauna
aka ɗora abin guzuri akai.
Sannan aljani Za'aratun-layal ya yunƙura ya tashi sama yana mai kaɗa fuka-fukanshi tare
luluƙawa cikin gajimare yana mai tsala azababban gudu, tun jama'a na daga masu hannu har
suka dai na hango su.
Sai da aka shafe tsawon sa'a bakwai ana tafiya a sararin samaniya ana keta gajimare cikin
matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.
Lokacin da sa'a ɗaya ta shuɗe ne aljani Za'aratun-layal ya saki fuka-fukanshi ya sauka a
turba,inda ya saukar yakasance wani daji ma'abocin kwarjini daban tsoro tun da aka shiga dajin
kowa yasha jinin jikinshi, domin dole ne a samu wani abu mai cutarwa a cikin shi.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka ga waɗansu irin masifaffun kibiyoyi suna sauka
a dajin, duk da irin ƙwarewa ta dakarun sarki Lazwar kafin su yi wani yunƙuri sai da kibiyoyin
suka hallaka fiye da mutum ɗari.
Al'amarin da ya fusata sarki Lazwar kenan ya karanta waɗansu ɗalasiman tsafi amma bisa
mamaki sai kawai ya ga ya zama hayaƙi.
Al'amarin da ya yi matuƙar bashi mamaki kenan kuma ya ɗaure mashi kai kawai sai ya zare
takobinshi ya kama kalle-kalle da dube-dube a dajin cikin matuƙar fushi.
Kwatsam! sai aka jiyo motsawar ganyayyakin bishiyun daga wani ɓangaren dajin, daga can sai
a kayi arba da wata kyakkyawar yarinya mai kimanin shekaru goma sha biyu, zaune a bisa kan
shirgegiyar damisa jikin ta sanye da kayan fata riga da wando da takalmi, a gadon bayanta tana
rataye da wata zabgegiyar takobi, a hannunta na riƙe da wata irin kwari da baka, nan fa aka
fara kallon kallo tsakanin su sarki Lazwar da yarinyar.
Lokacin da aka shafe tsawon daƙiƙa latalin ana kallon-kallo tsakanin wannan kyakkyawar
yarinya da su sarki Lazwar. sai Lazwar ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar duban yarinyar
cikin matuƙar fushi yana mai nuna ta da tsinin takobinshi cikin kakkausar murya ya ce "ya ke
wannan 'yar ƙaramar ƙwaruwa shin wane irin rashin hankali ne ya sanya ki aikata wannan laifi a
gare ni? Ina so ki bani amsar wannan tambaya kafin na zare miki ruhinki daga gangar jikinki kiyi
mutuwar wulakanci.
Ko da jin wannan tambaya sai kawai kyakkyawar yarinyar ta bushe da dariyar mugunta.
Al'amarin da ya bawa kowa mamaki kenan kuma ya fusata su ainun, bisa ganin cewa yarinya
ƙarama da bata huce ayi mata kwab ɗaya ba amma ta yi GABA DA GABA da dandazon
mayaƙa amma bata razana ba.
A Lokaci guda yarinyar ta murtuke fuska sannan ta dubi sarki Lazwar cikin wata irin zazzaƙar
murya mai ɗan karan daɗi tamkar sarewa ta ce
"Ya kai sarki Lazwar ibn kaulat na birnin zawatul-ifdar ka yi sani cewa fiye da shekaru biyar
baya na san da labarin ka kuma zaka yaɗa zango a wannan daji domin ka gudanar da tafiyar ka
ta nemo abubuwan da za su warkar da kai daga sihirin da abokin gabar ka sarki Durwazu ya yi
maka. Ko da jin wannan batu daga bakin kyakkyawar yarinyar sai sarki Lazwar ya cika da matuƙar
mamaki ya dubi yarinyar ya ce "shin ya aka yi kika san ko ni wane ne kuma mene ne buƙatar ki
agare ni.
Yarinyar ta ce "mahaifina mafarauci Murrasu kafin rasuwar shi ya sanar da ni labarin ka kuma
ya bayyana mini cewa kai ne zaka iya taimaka mini na samu nasarar saduwa da mahaifiya ta
dake ƘANGIN BAUTA a can birnin Istanbul bayan na taimaka maka ka sadu da Baiwa sharifa
wacce za ka je farautar ta a cikin birnin Istanbul. Ko da jin wannan batu daga bakin kyakkyawar yarinyar sai sarki Lazwar ya sake cika da
matuƙar mamaki,
kuma ya taka da ƙafafuwanshi ya durfafi inda take ya yin da ya rage saura taku goma a
tsakanin su sai ya ja ya tsaya.
Cike da matuƙar mamaki ainun ya sake duban ta ya ce "ya ke wannan yarinya mai abin al'ajabi
shin mene ne labarin ki? Kuma mene ne ya kai mahaifiyarki bauta a birnin Istanbul?
Da jin waɗannan tambayoyi sai hawaye suka kwaranyo daga idanun yarinyar.
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa sarki lazwar mamaki kenan ya ce a ran shi, shin ina dalilin
wannan hawayena yarinyar?
Yarinyar ta share hawayen ta cikin alamun matuƙar damuwa ta ce "da farko dai suna na
Shuraiba bintu Murrasu, ya kai Lazwar ka yi sani cewa mahaifina mafarauci Murrasu lokacin
yana raye yakasance babban hadimi ga sarkin birnin Istanbul, shi ne mai kula da abin da ya
shafi tufafin da sarki ke sanyawa da ma sauran iyalan gidan sarautar birnin baki ɗaya.
Wata rana mahaifina ya fita farauta daji domin farauto wata dabba da sarki ya ce ke bukatar
a yi mashi alƙyabba da ita.
Tun safe ya tafi amma har la'asar ta shuɗe bai dawo ba nan fa ni da mahaifiyata mu ka shiga
cikin matuƙar damuwa, muna cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu ka
jiyo haniniyar dawakai a can ƙofar gida
Kafin mu yi wani yunƙuri sai muka ga dakarun sarki sun shigo gidan, ina ji ina gani su ka kama
mahaifiyata ta ƙarfin tsiya suka tafi da ita.
Ina ta rusa kuka tamakar raina zai fita a daren wannan rana ne mahaifina ya dawo daga farauta
hankalin shi a tashe idanunshi sharkab da hawaye kuma jikinshi duk jini.
Ko da mahaifina ya ganni a cikin wannan hali sai ya janyo ni a jikinshi ya rungume a lokaci guda
mu duka biyun mu ka fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya daban tausayi.
Sai da muka ɗauki tsawon lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani mahaifina ya janye
jikinshi daga nawa.
Bata re da ya ce mini ƙala ba ya ɗauki wata jakar fata sai KWARI DA BAKAN shi da ke rataye a
gadon bayanshi kawai sai ya kama hannuna muka fice daga cikin gidan muka nufi Kofar gari,
har muka fice daga birnin muka nausa izuwa cikin daji, a kowacce rana sai nayi kuka wiwi ina
mai tambayar mahaifina ina ummana ta ke. Amma sai ya lallashe ni ya kwantar min da hankali
cewa ba wani abu ne ya same ta bazata dawo gare mu cikin ƙoshin lafiya.
Bakomai ya sanya mahaifina yaƙi sanar da ni labarin mahaifiyata ba, sai domin ganin cewa ni
yarinya ce ƙarama bansan komai a rayuwa ba.
Sai bayan na girma ne mahaifina ya bani labarin irin zaluncin da sarki ya yi masa na mayar da
ummina baiwarshi da yake saɗaka da ita, saboda al'adar sarki duk macen da ya ƙyallara idanu
ya gan ta in dai har ta yi mashi to ko matar wane ne sai ya kwace ta ya aure ta ta ƙarfin tsiya.
Baƙin cikin rashin mahaifiyata shine abin da ya yi sanadin mahaifina cutar ajali ta kama shi.
A daren ranar da zai rasu ne ya mallaka mani KWARI DA BAKAN shu da dukkanin kayan
farautar shi bayan ya sanar da ni dukkan sirrikan birnin Istanbul da shi kanshi sarki Ladiyas
kuma ya ba ni dukkanin labarin ka ya kai Lazwar.
Tun bayan rasuwar mahaifina ne na sha alwashin ceto rayuwar mahaifiya ta daga hannun sarki
Ladiyas, dare da rana ina rayuwa a cikin ƙunci da baƙin ciki, babu abin da ke ɗebe mini kewa
face wannan damisa da na gada daga wajen mahaifina.
Sa'adda kyakkyawar yarinyar tazo nan a labarin ta sai ta fashe da kuka mai matuƙar
tsuma zuciya da ban tausayi ga duk wanda ya ji shi.
Bisa mamaki sai sarki Lazwar ya ga wannan damisa