Showing 3001 words to 6000 words out of 34144 words

Chapter 2 - Sarautar Mutuwa Book Complete by Mansur Sufi .pdf

da yarinyar ke zaune akan ta ita ma ƙwalla
na zubowa daga idanuwanta.
Al'amarin da ya sanya Sarki lazwar da sauran tawagarshi suka ji sun kamu da matuƙar tausayin
yarinya Shuraiba kenan shi kanshi aljani Za'aratun-layal da ya kasance aljani sai da ƙwalla ta
zubo mashi saboda tausayi.
Sai daga can sarki Lazwar ya dubi yarinya Shuraiba ya ce " ya ke wannan yarinya mai abin
al'ajabi haƙiƙa labarin ki cike ya ke da ban tausayi matuƙa, kuma tabbatas sarki Ladiyas ya cika
baƙin AZZALUMI, ina mai ɗaukar miki alƙawarin cewa zan taimaka miki har sai na ga kin cika
burin ki na saduwa da mahaifiyarki da kuma ɗaukar fansa a kan sarki Ladiyas". Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai yarinya Shuraiba ta cika da matuƙar farin
ciki maral musaltuwa.

Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka kafa sansani,nan fa kuyangi suka shiga aikin dafa abin
kalaci, bayan an kammala ne kowa ya kimtsa cikinshi aka huta sai aka sake ɗunguma wa aka
hau bisa kan aljani Za'aratun-layal aka cigaba da tafiya tare da yarinya Shuraiba tare da
damisar ta. Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai sai a ka ga waɗansu
zaratan dakarun aljanu ɗauke da waɗansu miyagun makamai da idanu basu taɓa ganin irin su
ba, gaba ɗayan su suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban
tsoro, adadin su ya kai dubu ɗaya da ɗoriya. Nan fa tawagar sarki Lazwar suka firgice, wasu daga cikin su har suna sakin fitsari a wando
saboda firgici, sarki Lazwar ne kaɗai bai razana ba shi ma a matuƙar firgice ya ke, kawai dai
ƙarfin hali ne da ƙi faɗi irin ta hamshaƙan sarakai.
Shi kan shi Za'aratun-layal duk da kasancewar aljani sai da ya ɗimauce, domin iya tsawon
rayuwarshi ko a labari bai taɓa ganin aljanu masu kwarjini da ban tsoro tamkar su ba.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su na tsawon daƙiƙa latalin, sai daga can wani mummuna
daga cikin aljanun wanda da alama shi ne shugaban su ya buɗi baki cikin wata irin kakkausar
murya mai ban tsoro yace "ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa ban zo gare ku tare da
rundunar mayaƙa na ba domin na yaƙe ku ba sai don ku ba ni yarinya Shuraiba, mu kai ta ga
sarkin mu mai girma Zammar, domin ya yanka ta ya sana'anta jininta don ya yi wa matayen mu
maganin cutar da ke damun su ta makanta fiye da shekaru hamsin.
Ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa matsawar ku ka yi taurin kai wajen damƙa
Shuraiba a gare mu, ina mai tabbatar maku da cewa ɗayan ku ba zai ƙetare daƙiƙa goma a
raye ba.
Ko da jin wannan batu daga bakin shugaban dakarun aljanun sai sarki Lazwar ya yi ƙarfin hali
ya tari numfashin shi yana mai daka mashi tsawa ya dube shi ya ce " ya ke wannan ƙaramin
ƙwaro tabbas ƙaryar ka ta sha ƙarya, kuma ka yi ɓatan basira da ka ke tunanin cewa za ka iya
raba mu da Shuraiba. Ina mai umartar ka da ka janye waɗannan rafkanannun mayaƙan na ka ka koma izuwa ga
matsoracin sarkin ku ga faɗa mashi cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne".
Kafin sarki Lazwar ya gama rufe bakinshi jikin aljanun ya kama tsuma yana kyarma
tamkar za su ci babu.
Kawai sai su ka yi wani irin ihu da kururuwa mai firgitarwa suka ɗauki kan su.
Ko da ganin hakan sai su sarki suka zare makaman su, ana haɗuwa aka yamutse da
azababban yaƙi mai matuƙar muni ban tsoro da tashin hankali.
Kaico! haƙiƙa tashin hankali ba'a sa ma sa rana, kuma duk wanda ya taɓa fita filin yaƙi shi
ne ya gama ganin tashin hankali.
Nan fa karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar dakarun aljanu da bil'adama ta cika dodon
kunne, duk sa'adda makaman yaƙin ɓangarorin biyu suka haɗu sai ka ga walƙiya gami da tsawa
tamkar za a ke ce da ruwan sama.
Ana fara wannan arbu ne sai wani abin mamaki ya faru domin kuwa yarinya shuraiba ta
zame wa dakarun aljanun alaƙaƙai kuma ƙadangaren bakin tulu, ya zamana cewa duk wajen da
ta sanya a gaba sai ka ga aljanun na zubewa ƙasa matattu.
Duk wannan artabu da ake yi tsakanin su sarki Lazwar da dakarun aljanun sarki Zammar
ya gani a cikin madubin tsafin shi, a lokacin da yake zaune a fadar koda yaga cewa an kashe

gaba ɗaya tawagar shi sai ya cika da matuƙar baƙin cikin maral musaltuwa kuma ya takarkare
ya kurma ihu.
A ɓangaren su sarki Lazwar kuwa bayan sun samu nasarar hallaka dakarun aljanun sarki
Zammar, sai kowa ya shiga sanya magani a raunukan shi, amma aƙalla anyi asarar dakarun
yaƙi mutum ɗari biyu da ashirin.
Bayan komai ya samu dai-daituwa ne ba tare da wani ɓata lokaci ba sai aka sake ɗunguma aka
ci gaba da tafiya.
Ana fara wannan tafiya ne sai fira ta ɓarke tsakanin yarinya Shuraiba da aljani Za'aratun-layal,
A inda Shuraiba ta dubi Za'aratun-layal tayi gyaran murya ta ce " ya kai wannan dattijon aljani
wai kuwa idan ba za ka damu ba nayi maka wata tambaya mana.
Ko da jin wannan batu sai Za'aratun-layal ya ce " faɗi tambayar ki ya ke Shuraiba
Shuraiba ta ce "wai kuwa a yanzu a cikin jinsin ku na aljanu akwai wanda yafi ka yawan
shekaru?
Koda jin wannan tambaya sai Za'aratun-layal ya bushe da dariya har da kyakyatawa ya ce "a
halin yanzu ni ne ɗan auta a cikin jinsin mu na aljanu a ƙalla zan kai shekaru dubu ɗari uku da
haihuwa'' .
Cikin matuƙar mamaki shuraiba ta ce "ai kuwa in dai haka ne jinsin aljanu sun fi kowa daɗewa a
duniya.
Za'aratun-layal ya ce "kwarai kuwa zancen ki dutse".
Shuraiba ta ce "amma kuwa mai yasa kuke yiwa bil'adama bauta alhalin kunfi su sanin
halin da duniya ke ciki
Za'aratun-layal ya ce "Tabbas ke yarinya ce ba ki san komai game da halin duniya ba amma
bari na ba ki hikayar sarauniya ABIDAT ta birnin Sin wata ƙila ki shaida batu na.
Za'aratun-layal ya yi gyaran murya sannan ya fara da cewa

BABI NA UKU

Wata mace 'yar kimanin shekaru ashirin da uku ɗauke tsohon ciki a jikinta sanye da tufafi
na fatun dabbobi riga da wando.
Zaune take a bisa kan wani ingarman doki baƙi, tafiya take a cikin wani irin daji mai
tattare da sarƙaƙiya, kwazazzabai gami da duwatsu.
Kallo ɗaya za ka yiwa mata ka fahimci cewa tana cikin mawuyacin hali.
Kaico! Tana cikin wannan hali ne sai ta ji alamun naƙuda sun bijiro mata, kawai sai ta ja
linzamin dokin ta tsaya cak sannan ta kama ta sauko ƙasa kawai sai ta taka da ƙyar ta durfafi
kofar wani kogon dutse.
Kafin ta isa sai kawai ta yanke jiki ta faɗi ƙasa, a cikin wannan hali ta haife abin da ke cikin
ta.
Cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ta ɗauki abin da ta haifa domin ta ga mene ne, ai kuwa
sai ta ga wata santaleliyar yarinya ce kyakkyawa ta gaban kwatance,
duk da cewar tana cikin halin laulayi, ba ta san sa'adda hawayen farin ciki suka kwaranyo daga
idanuwanta ba, a dai-dai wannan lokaci ne kukan jaririyar ya cika dajin baki ɗaya, cikin hanzari
ta ɗauki wani ice mai kaifi ta yanke cibiyar jaririyar.
Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai ta hango waɗansu dakaru sun durfafo inda take
a bisa dawakai.

Kafin tayi wani yunƙuri ɗaya daga cikin dakarun ya ɗame kibiyarshi ya harbe ta a gadon
bayanta, saboda tsananin zafi da raɗaɗin da ta ji bata san sa'adda ta kurma wawan ihu ba ta
sulale ƙasa sumammiya jaririyar ta shiga tsala kuka.
Har badakaren ya sake yin shiri a karo na biyu da nufin ya sake harbin ta.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wata murgujejiyar zakanya ta yi fitar burgu
daga cikin wannan kogon dutse dake dajin, ta dako wawan tsalle ta daki badakaren a kirji.
Saboda matuƙar ƙarfin bangazar sai da badakaren da dokin shi su ka yi sama tamkar an janye
su da ƙungiya, sannan daga bisani suka faɗo ƙasa matattu ko shurawa ba su yi ba.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin zakanyar da mayaƙan.
daga can sai zakanyar ta yi gurnani gami da hargagi sannan ta dako wawan tsalle izuwa kan
mayaƙan.
Ko da ganin hakan sai dakarun su ka ɗaga makamansu suka yi ihu da kururuwa mai firgitarwa
suka yi ɗauki kanta aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni, ban tsoro da ban
al'ajabi.
Wohoho! Haƙiƙa yaƙi shi ne matattarar dukkan bala'i da musiba, kuma idan gwani ya haɗu da
gwani JURIYA DA BAJINTA suka game waje guda, dole ne artabu ya zamo abin tsoro.
Nanfa zakanyar ta wanzu tana hallaka dakarun, ya zamana cewa duk inda ta sanya gaba
sai dai ka ga dakaru na zubewa ƙasa matattu, a inda za ka ga ta mako badakare faga kan
dokinshi ta bishi ta turmushe.
A duk sa'adda dakarun su ka kaiwa zakanyar hari sai ka ga ta wurƙila haɗe da zame wa ta
kaucewa saran, kafin badakare ya sake daga takobinshi zakanyar ta dako tsalle sama ta sanya
faratanta ta tsire mashi idanu ruwan cikin ya tsiyaye, take zai sulale ƙasa daga kan dokinshi
yana mai kurma wawan ihu. Kai wasu lokutan idan ta daki badakare a wuya sai ka ji wuyanshi ya ƙara ya karye ya yi
ƙara ji kake ruƙus!! Ƙas! Ya faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba.
Haƙiƙa waɗannan dakaru suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa ganin irin shi ba. Domin
kafin cikar rabin sa'a zakanyar ta kashe fiye da rabin su.
Nanfa ƙarar karafniyar ƙarafa da ihun mazaje, haniniyar dawakai haɗe da gurnanin zakanyar ya
cika dajin baki ɗaya, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin
turmutsutsu, kofatunsu na kartar ƙasa.
Wohoho! tabbas masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce wuya ko da magani babu
daɗi, kuma wuya mai sa dole.
Hakan ce ta faru ga sauran dakarun, domin koda su ka ga cewa a kowanne lokaci za su iya
baƙuntar barzahu sai suka cika wandunansu da iska domin GUDUN TSIRA da rayuka,
sai zakanyar ta dunga ƙure masu gudu tana make su suna faɗuwa ƙasa matattu. Kafin wani
lokaci ta zubar da gawarwakin su a ƙasa.
Kawai sai ta juya ta durfafi inda wannan mata da jaririyar ke kwance a ƙasa tana fitar da wani
irin gurnani.


BABI NA HUƊU

Lokacin da aljani da aljani Za'aratun-layal ya zo dai-dai nan a hikiyar sarauniya Abidat ta
birnin Sin sai ya ja bakinshi ya yi shiru.
Cikin alamun matuƙar damuwa Shuraiba ta dube shi ta ce "haba ya masanin HIKAYAR DUNIYA
mene ne ya sanya za ka yanke ba ni wannan labari mai matuƙar daɗi gami tsantsar tausayi,
haƙiƙa na matsu naji a wane hali wannan mata da jaririyarta su ke ciki?
Kuma wace ce wannan zakanya da ta ceci rayuwar su? Shin mahaifiyar jaririyar ta na raye ko
kuwa ta mutu sakamakon harbin kibiya da wannan badakare ya yi mata a gadon baya".
Ko da jin wannan batu sai Za'aratun-layal ya cewa da Shuraiba ''shin baki lura da inda
muka iso ba ne? Leka izuwa kasa ki gani".
Da jin hakan sai ta sunkuya da kanta ƙasa aikuwa sai ta hangi wani irin baƙin daji mai matuƙar
kwarjini da ban tsoro.
Sarki Lazwar ya dubi aljani Za'aratun-layal ya ce ''shin me ka fahimta da wannan daji dake
gaban mu?
Za'aratun-layal ya yi shiru kamar mai tunanin wani abu sannan ya ce " ya shugabana wannan
daji dake gaban mu yana ɗauke da tsananin sanyi don haka dole ne kowannen ku ya sanya
suturun kariya, sannan kuma dukkanin daji da ya kasance yana tattare da irin yanayin to dole
ne a samu miyagun halittu masu shan jinin bil'adama da cin naman su, sai inda kizo ke saƙar
shi ne bani da tabbacin waɗanne irin halittu ne.
Ko da jin wannan batu daga bakin Za'aratun-layal sai kowa yasha jinin jikinshi.
Cikin hanzari sarki Lazwar ya zira hannunshi a aljihun rigarshi ya ɗauko madubin tsafin shi da
nufin gudanar da bincike, amma sai aljani Za'aratun-layal ya yi wuf da dakatar da shi ya ce ''ya
shugabana ka yi sani cewa amfani da sihirin tsafi a irin wannan tafiya abu ne mai matuƙar
haɗarin gaske domin baka da tabbacin cewa wanda za ka yi binciken bai fi ka karfin sihiri ba.
Sannan shin ka manta cewa kowa a gidanshi sarki ne,
mafita ɗaya ce a gare mu kowanne ku yakasance cikin shiri tun da gashi yanzu la'asar ta riske
mu, ba zamu ɗauki wani tsawon lokaci ba duhun magariba zai gaba ce a dajin kenan dole yaɗa
zango cikin dajin dole ne domin mu kwana mu huce gajiyar dake tare da mu.
Da jin wannan batu sai kowa ya shiga sanyawa kanshi rigunan sanyi tun daga ƙasa har sama
kuma kowa ya gyara riƙon makamin shi.
Za'aratun-layal ya yi ƙasa-ƙasa ta fuka-fukanshi sannu a hankali har aka sauka a bisa turba .
Sa'adda kowa ya yi arba da dajin sai tsoro ya kara kama shi.
Shi dai wannan daji yakasance gaba ɗayan shi yana ɗauke da waɗansu irin dogayen
bishiyu masu rassa masu matuƙar kaifin tsiya masu tattare da sarƙaƙiya, babu wani waje da
mutum zai ajiye kafarshi face ya taka dusar ƙanƙara ce, Babu abin da zai ƙara firgita mutum
kuma ya jefa tsoro a zuciyarshi sai jin shiru da ya wanzu a dajin tamkar babu wani abu mai rai a
cikin shi, kai hatta irin tsuntsaye haka a saman bishiyoyin babu su.
Nan fa aka fara tafiya a cikin ɗar ɗar domin shirin ko ta kwana, amma bisa mamaki sai ga shi an
shafe tsawon rabin sa'a ba tare da an jiyo motsin wani abu mai cutarwa ba.
Al'amarin da ya sanya kowa ya fara sakin jikinshi kenan, ana cikin wannan tafiya ne tsinin
reshen wata bishiya ya yanki bawa zafiyar a cinyarshi jini ya zuba a ƙasa.
Kawai sai a ka ji gaba ɗaya dajin ya kaure da wani irin gurnani mai ban tsoro ba shiri kowa ya
tushe kunnuwanshi domin ƙarar na iya kurumtar da mutum.
Abin da su sarki Lazwar ba su sani ba shi ne zubar jini a dajin shine alamun da halittun ke gane
cewa bil'adama ya shigo dajin.

Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu irin zaratan muradai na fitowa daga
kowacce kusurwa a dajin.
Muridan sun kasance masu matuƙar tsawo tamkar bishiyar kuka. Jikkunansu a mummurɗe suke
tamkar duwatsu suna da rafkeken kai mai ɗauke da idanu ƙwaya ɗaya jal! Wanda ya kasance
jajur tamkar garwashin wuta, fuskokin su munana ne babu kyawun gani, duk sa'adda su ka
wangame bakunansu sai ka ga cewa wani irin yawun mai yauƙi na dalala, a hannayen su kuwa
suna ɗauke da waɗansu irin masifaffun makamai na yaƙi da idanu basu taɓa gani ba, a ƙalla
adadin muridan ya kai dubu uku da ɗoriya.
Lokacin da muridan suka kammala yiwa su sarki Lazwar ƙawanya, sai aka fara kallon-kallo
tsakanin ɓangarorin biyu,tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali sai daga bisani ne
muridan su ka yi wata kururuwa mai firgita dandazon mayaƙa a filin daga, su ka yi ɗauki izuwa
kan su, Koda ganin hakan sai su sarki Lazwar su ka yi kururuwa suka ruga izuwa kan muridan.
Ana haɗuwa aka yi muguwar KARON BATTA.
Wohoho! Haƙiƙa tashin hankali ba'a sa mai rana, kuma ita wutar bala'i kafin ta zo ne ake
guje mata, amma idan tazo kawai miƙa wuya ake yi a tare ta ko dai a mutu ko a yi rai.
Kaico! ana fara wannan arbu ne su sarki Lazwar suka fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci
mai nauyi ba, domin muridan sun zame masu tamkar GOBARAR ANNOBA.
Duk sa'adda ɗaya daga cikin ya kai wa su sarki Lazwar hari da makaminshi, idan su ka goce
saran ya sauka akan bishiya sai ka ga ta rabe gida biyu ta faɗi ƙasa rikica za ta danne su.
Kafin ka ce me tuni muridan sun hallaka fiye da dakaru gami da kuyangi fiye da guda dubu.
Al'amarin da ya yi matuƙar figita su sarki Lazwar kenen, babban abin da ya fi dugunzuma
hankalin su shi ne yadda muridan suka kasance masu matukar zafin nama, tamkar jikkunan su
na amfani da wata na'ura dake sarrafa su.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login