Showing 21001 words to 23849 words out of 23849 words
Chapter 8 - KARYA DA GASKIYA Cigaban Tafarkin Tsira Rubuta littafin Mansur Usman Sufi .pdf
so kar ku shagala da addu'a
domin kariya daga dukkan abin cutarwa;
Da jin wannan batu sai dukkannin su suka gyaɗa kai alamar gamsuwa. sannan aka durfafi
gidan aka shiga izuwa cikin shi, sai da aka yi tafiya mai tsawo a cikin zaure sannan aka iso
farfajiya, daga ciki gidan ya kasance ƙasaitacce mai matuƙar ƙawatuwa yana ɗauke da ɗakuna
biyar. Nan fa aka dinga shiga ɗakunan amma wayam! Babu komai, lokacin da aka shiga ɗaki na biyar
ne aka ga wani abun mamaki.
Bakomai aka gani ba face kayan tsubbe-tsubbe nau'i dabam-daban, babu kyawun gani a
tsakiyar ɗakin an ajiye wani dogon teburi na azurfa, bisa kan teburin wani kyakkyawan yaro ne
mai kimanin shekaru sha uku an ɗaure hannayen shi da waɗansu irin sarƙoƙin tsafi, hawaye na
zuba daga idanuwanshi. Koda ganin halin da yaron ke ciki sai kowa dake wajen ya kamu da matuƙar tausayin shi, kawai
sai Muhassin ya matsa daf da yaron ya karanta Ayatul-kursiyyu da falaƙi da nasi ya tofa a jikin
sarƙoƙin take suka narke suka zamo ruwa suka ɗige a ƙasa.
Cikin farin ciki yaron ya yunƙura ya sakko daga kan teburin,
Har Muhassin ya buɗe baki da nufin ya ce wani abu, kawai sai aka ga wani dubu ya mamaye
ɗakin ta yadda ko tafin sannu mutum ba zai iya gani ba.
Sannu a hankali duhun ya dinga curewa waje guda ya rikiɗa izuwa wata mummunan tsohuwar
aljana,
Tana shirye gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, a hannayenta tana ɗauke
da zaratan takubba masu KAIFI DA TSINI fuskantarta a murtuke babu annuri tamkar an aiko
mata da WASIKAR MUTUWA.
Duk da dakewar zuciyar su jarumi Muhassin sai da suka ji hantar cikinsu ta kaɗa,
Aljanar ta taƙarƙare ta daka masu wata tsawa da ta haddasa raurawar ɗakin, daga bisani ta
haɗe ta buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da haniniyar doki ta ce "ya ku waɗannan
bil'adama ku yi sani cewa haƙiƙa tafka babban kuskure da kuka shiga gona ta, ina mai tabbatar
maku da cewa ɗayan ku ba zai fice daga wannan gida a raye ba"; Kafin aljanar ta gama rufe bakinta Muhassin ya yi ƙarfin hali ya tari numfashinta yana mai cewa
"ƙaryar ki ta sha ƙarya yake wannan la'ananniya kuma tsohon AZZALUMA ba za ki taɓa samun
nasara akan mu ba da yardar Annabi Rahma, zaɓi biyu zan ba ki ki ɗauki ɗaya, ko dai ki miƙa
wuya zuwa ga addinin Allah ki daina shirka da tsafi ki dawo bisa TAFARKIN TSIRA, ko kuma ki
yi mutuwar wulakanci".
Koda jin wannan batu daga bakin Muhassin sai aljanar ta fusata ainun ta sake daka
masu tsawa a karo na biyu ta ce "na rantse da gemun kakana boka Zanzamul-Auƙat sai na yi
maku kisa mafi muni ta hanyar gididdiba naman jikkunanku ta yadda koda tsuntsaye ba za su
mu na yin kalaci ba, sannan na yanka yaro mai hatimin takobi na shanye jininshi domin cika
burina na zamtowa GAWURTACCIYA uwar hatsabiban duniya.
Koda aljanar ta zo nan a zancen ta sai ta taƙarƙare ta kwarara ihu mai firgita DANDAZON
MAYAKA a FILIN DAGA ta ɗaga takubbanta ta ruga izuwa kan su Muhassin.
Koda ganin hakan sai Muhassin, Aslaima da Abu-Ayub suka zare makaman su suka ruga izuwa
gare ta aka tari juna aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini, muni da tashin
hankali.
Cikin hanzari yaro usaiba ya ruga izuwa can gefe yana kallon fafatawar da ake yi.
Aljanar ta wanzu tana kai masu miyagun hare-hare ta sama da ƙasa, su kuwa suka wanzu suna
kare hare-haren tare da mayar da martani cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin ta
MAZAN JIYA da suka saba yin KARON BATTA a BIRNIN SADAUKAI.
Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA ya fi ƙarfin ƙananan ƙwari, idan gwani da gangaran suka yi
KARON BATTA dole yaƙi ya zamo abin sha'awa da tashin hankali.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa ɗari da sittin ana wannan ɗauki-ba daɗi babu nasara ga kowa
ne tauraro har ya zamana cewa gwanayen sun lalata duk wani abu mai muhimmanci a ɗakin
sun fara rushe ginin duk da irin ƙwarin shi.
Ba shiri yaro Usaiba ya ruga ya fice daga ɗakin domin tsira da rayuwar shi, domin dai masu iya
magana na cewa 'faɗan da yafi ƙarfin ka sai ka mayar da shi kallon.
Ana cikin wannan hali ne Muhassin ya sanya takobinshi ya kaftawa aljanar sara a kanta take
takobin ta fasa hular kanta ta fasa kwanyarta. Kawai sai ta faɗi ƙasa tana mai shure-shuren
mutuwa, jim kaɗan sai komai na jikinta ya sandare, ashe shirin tsafin aljanar yana cikin hular
kanta. Koda samun wannan nasara sai aka nufi inda yaro Usaiba yake, jarumi Muhassin ya dube shi
ya ce " ya kai wannan kyakkyawan yaro shin mene ne labarin ka kuma mene ne abin da ya
haɗa ka da wannan aljana?
Koda jin wannan tambaya sai nan take Usaiba ya kwashe labarin abin da ya wakana tsakanin
su da Fitinatul-amir tun daga farko har ƙarshe ya zayyanawa Muhassin.
Koda jin wannan labari sai kowa ya cika mamaki ainun, ba tare da ɓata lokaci ba aka cigaba da
tafiya, ana cikin tafiyar ne Usaiba ya dubi Muhassin ya ce "ya kai wannan GWARZON GAWAZA
so ɗazu lokacin kana magana da wannan aljana na ji ka ambaci Ubangiji shin wane ne shi";
Koda wannan tambaya sai Muhassin ya yi murmushi a gare shi ya ce "Tabbas Ubangijina
shine ya halicci komai da kowa babu wanda ya samar da shi kuma babu abin da ya gagare shi,
kuma shine ke taimako na a wannan yaƙi da muka yi.
Usaiba cikin mamaki ya ce "haƙiƙa girma da buwayar Ubangijin ka ya kai, idan har ka taimaka
mana ni da ummana muka kawar da Fitinatul-amir za mu bayar da gaskiya da wannan Ubangiji
na ka;
Muhassin ya gyaɗa kai ya ce "babu damuwa da yardar Ubangiji".
Daga wannan furuci kowa ya yi shiru aka cigaba da tafiya, tafiyar daƙiƙa arba'in aka yi aka
hango su Rusayyat suna tsaye suna kai komo, daga Usaiba ya hango ummar shi sai ya ruga
gare ta suka rungume juna cikin farin ciki daga bisani suka janye jiki Usaiba ya buɗi baki da
nufin ya sanar da ita labarin abin da wakana tsakanin sa da su Muhassin. Amma sai Rusayyat ta dakatar da shi ta hanyar duban Muhassin ta ce "ya kai GWARZON
MAYAKI ka yi sani cewa mun ga dukkan abin da ya wakana tsakanin ka da ɗana kuma ni da
'yar uwata mun gamsu cewa yadda ubangijin ka ya baka nasarar tseratar da yaro na zai baka
nasara wajen kawar da mai gidana Fitinatul-amir, muna masu yi maka alkawarin karɓar
addininka bayan mun yi nasara.
Koda jin wannan batu sai Muhassin ya ɗago fa kanshi koda ya haɗa idanu da jaruma Shalmirat
take suka ji wani abu ya ɗar su a zukatansu a karo na farko a rayuwar su.
Sannan ya buɗe baki ya yi gyaran murya ya ce "haƙiƙa ina mai tabbatar maku da cewa zamu yi
nasara da yardar Ubangijin Musulunci.
Ashe duk wannan abu da ke faruwa gimbiya Aslaima ta lura da irin kallon da jaruman ke biyu
ke yiwa Muhassin don haka nan take ta ji kishi ya turnuƙe ta, domin ta lura cewa dukkaninsu
suna yi masa kallo ne mai tattare da tsantsar so da ƙauna.
Ana cikin wannan hali ne aka jiyo haniniyar dawakai gami da ƙarar takun sawaye ta cika dajin
baki ɗaya, domin haka sai kowa ya zare takobinshi aka ruga izuwa iyakar dajin. Nan take aka ji
arba da wata ƙasaitacciyar runduna mai matuƙar kwarjini daban tsoro, babu wani sadauki da zai
yi arba da rundar dole ya ɗimauce domin a iya kiranta suna ANNOBA DARI. Kai ko makaman
yaƙinsu ma abin tsoro ne.
Ba wani ba ne ke jagorantar tawagar face sadauki Fitinatul-amir, yana shirye cikin
matsananciyar shigar yaƙi ta baƙaƙen sulke, jikin shi cike da guraye da layu na tsafi, tamkar
wani tsohon mahaukaci yana zaune akan tsuntsun tsafi a hannunshi yana rike da wani
zabgegen gatari da aka yi da zallar ƙarfen jauhari. Lokacin da yazamana cewa tazarar dake tsakanin su bata huce taku ashirin ba sai kowanne
ɓangare suka ja suka tsaya aka yi kallon-kallo na tsawon daƙiƙa talatin,
daga can sai Fitinatul-amir ya dubi uwar gidanshi Rusayyat fuskarshi a murtuke tamkar an
watsa mashi garwashin wuta akan ta cikin kakkausar murya irin GWARZON SADAUKI ya ce
"ya ke uwargidana ki yi sani cewa wannan fito wa da na yi ta musamman kuma ina mai tabbatar
miki da cewa ɗayan ku ba zai bar nan a raye ba. Har Rusayyat ta buɗi baki da nufin ta ce wani abu sai Muhassin ya tari numfashinta ya dubi
Fitinatul-amir ya ce "ya kai Fitinatul-Amir ka yi sani cewa JARMAI SHA YAKI shine ke fitowa filin
artabu ya tari maza ba wai ya fito da karnukan farauta ba".
Koda jin wannan batu daga bakin Muhassin sai Fitinatul-amir ya fusata ainun ya dube shi ya ce
"ya kai wannan tsagera mai tsaurin idanu ka yi sani cewa yanzu zan gane da kai kuskuren ka
domin ya zamo izna ga ƙananan ƙwari irin ka.
Gama faɗin hakan ke da wuya sai Fitinatul-amir ya dako wawan tsalle daga kan abin hawan shi
ya falfala da azababban gudu zuwa kan Muhassin yana ihu da kururuwa mai firgitarwa
DANDAZON MAYAKA komai tsananin yawan su yana mai ɗaga gatarinshi sama.
Koda ganin hakan sai Muhassin ya yi koyi da shi yana mai ƙwala kabbara,
Lokacin da Taurarin biyu suka haɗu da juna sai aka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar
kwarjini daban tsoro suka wanzu suna kaiwa juna SARA DA SUKA cikin matuƙar zafin nama
JURIYA DA BAJINTA irin ta MAZAN JIYA da suka saba yin KARON BATTA.
Duk sa'adda makamansu suka haɗu da juna sai ka ga tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara
mara daɗin saurare.
Wohoho! Haƙiƙa a wannan Ubangiji ya nuna ikon shi akan halittarshi, domin duk irin ƙarfi da
sihiri na Fitinatul-amir ya tashi a banza domin kuwa Muhassin ya zame mashi ƙadangaren bakin
tulu, kuma bisa taimakon Ubangiji ya samu nasara hallaka shi ta hanyar sare mashi wuya da
takobi a lokacin da ya rikiɗa izuwa tsuntsun batoyi.
Ya yin da mayaƙan marigayi Fitinatul-Amir suka ga uwan gidansu ya zamo gawa jarumi
Muhassin ya yi RINJAYE akan su sai baki ɗayan su suka miƙa wuya, ba tare da wani ɓata
lokaci ba ya karanta KALMAR SHAHADA Rusayyat da jama'ar ta suka amsa.
Aljani Abu-Ayub da gimbiya Aslaima suka ɓarke da kabbarar godiya ga Ubangiji,
Ba tare da wani ɓata lokaci ba jarumi Muhassin da gimbiya, yaro Usaiba, Rusayyat da jaruma
Shalmirat suka sake hayewa bisa kan Abu-Ayub suka ɗunguma izuwa birnin sadauki
Fitinatul-amir.
Ya yin da aka isa sai aka kafa TUTAR MUSULUNCI aka rushe gumaka, aka fito da dukkan
fursunonin kurkuku aka 'yan ta su, bisa amincewar sabuwar majalisar sarki sai aka zaɓi yaro
Usaiba mai hatimin takobi a matsayin sabon sarki birnin Madinatu-Salam, 'yar uwarshi Hairat a
matsayin shugabar sarauniyoyin birnin, A rana guda aka yi shagalin naɗin tare da ɗaurin auren jarumi Muhassin da 'yan mata uku wato
gimbiya Aslaima, jaruma Shalmirat da Rusayyat uwar gidan marigayi Fitinatul-Amir.
Mako ɗaya da hakan sai ango Muhassin ya aike da wasiƙa izuwa ga sarki Hilaifu na cewa
'yarshi gimbiya Aslaima ta karɓi musulunci kuma ta samu lafiya da kuma abin da ya wakana
tsakanin su da boka kaddad a wajen ɗauko ALLON TSAFI.
Ya yin da labarin ya riski sarki sai ya yi farin ciki ainun har ya haɗa gagarumar walimar da bai
taɓa yin tamkar ta ba, kuka kuma ya amince cewa gimbiya ta zauna a tare da Muhassin duk
bayan mako huɗu zai dinga zuwa yana ziyararta.
Lokacin da labarin abin da ya faru na mutuwar Fitinatul-amir ya watsu ga sarakunan
nahiyar sai suka dinga yin zuwa suna yin MUBAYA'A ga sarki Usaiba suna karɓar addinin
Musulunci, sannan sarki Usaiba ya tashi runduna ta musamman suka tafi izuwa inda su sadauki
Huzlaif suke fafata yaƙi da sarki Madsur aka kai masu ɗauki aka murƙushe sarki Madsur da
mayaƙan shi.
Wannan rana farin ciki ya mamaye nahiyar baki ɗaya bisa kawo KARSHEN ZALUNCI.
Hasken musulunci ya mamaye ko ina.
BABI NA ƘARSHE
A can FILIN FAMA kuwa artabu ya ci-gaba da wakana tsakanin TAWAGAR MUSULUNCI da
ta kafirai. Haƙiƙa Ubangiji ya nuna ikon shi a wannan rana, domin sai da dakarun musulunci
suka murƙushe baki ɗaya arna ɗayan su bai tsira da rayuwar shi ba. Sarki Rayyan ya yi wa
sarki Lamsarul-Azlam kisan wulakanci ta hanyar sare masa ƙafafu da hannaye, bayan ƙura ta
kwanta ne aka ɗunguma izuwa birnin Madintul-afnan farin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.
A daren wannan rana sarki ya tashi wata tawaga ta musamman suka tafi izuwa birnin
Darul-Ashmar domin a mamaye masarautar tun da sarki Lamsarul-Azlam da mayaƙan shi sun
rasa rayukansu.
Lokacin da suka isa sai suka tarad jama'ar kurkuku na yin YAKIN KWATAR 'YANCI ƙarƙashin
jagorancin sadauki Ukaiza, nan take suka mara masu baya har aka samu rinjaye, lokacin da
labarin abin da wakana ga sarki Lamsarul-Azlam da mayaƙan shi a filin fama sai jama'a suka
cika da matuƙar farin ciki da al'ajabi ba tare da wata jayayya ba Ukaiza da jama'a suka karɓi
KALMAR SHAHADA, sadauki Ukaiza ya sadu iyalanshi cikin farin ciki bayan an naɗa shi sabon
sarkin birnin Darul-Ashmar.
A can birnin Madinatul-afnan kuwa bayan mako uku da yin nasarar yaƙi sai aka shiga
shagalin ɗaurim gimbiya Nuwairat tare da sarkin yaƙi Zuhairu kowa ya cika da matuƙar farin ciki
maral-musaltuwa.
***
Lokacin da aljanin ya sauka a turba sai sarki Nu'umanu ya yunƙura ya sakko ya durfafi inda
ma'aji Kulairu yake fuskarshi cike da annuri ya yin da ya isa sai ya dubi waziri Yazid cikin
alamun matuƙar damuwa ya ce "ya kai abokina haƙiƙa ka ci amanar addinin Allah (SWT) shin
yanzu ba ka bayar da gaskiya da shi ba ka yi nadamar abin da ka yi tun da ga shi kansa gaɓar
mutuwa";
Koda jin wannan batu daga bakin sarki Nu'umanu sai waziri ya bushe da dariyar ƙarfin hali
ya furzar da GUDAN JINI daga bakinshi muryarshi na sarƙewa ya ce "da na miƙa wuya na
gwammace na yi MUTUWAR JARUMTA".
Kafin ya gama rufe bakinshi sarki Nu'umanu ya sanya takobinshi ya sare mashi wuya, kan yi
fitar burgu jini ya yi tsartuwa gami da jeshi, gangar jikin ta faɗi ƙasa rikici!
A dai-dai wannan lokaci ne Sarkin fada ya hallaka sarki yaƙi Lauzar ta hanyar burma mashi
takobi a ciki. Magatakarda kuwa ya hallaka sarki Rakibu ta hanyar soka nashi tsinin takobi a
idanu.
Nan take musulmi suka yi kabbara domin nuna godiya ga Ubangiji.
Tir! Da aikin mushrikai inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da gawarwarkin
su waziri ke kwance a ƙasa cikin ƙasƙanci da tozarci dole ya godewa Allah bisa ganin yadda
maƙiya Musulunci suka kunya ta.
Babu wata Yarjejeniya sauran dakarun su waziri da suka rage a raye suka karɓi KALMAR
SHAHADA a hannun sarki Nu'umanu sannan ya fuskanci dakarun musulunci ya ce "ya ku
jama'a ta ku yi sani cewa na samu lafiya ne bisa addu'a dake kuke yi min, saboda haka sai mu
sake yiwa Allah guda tare yawaita salati ga fiyayyen halitta S'A'W domin shine tsanin dukkan
wata nasara".
Sa'adda da sarki yazo nan a zancen shi sai aka sake ɓarkewa da kabbara,
Sarki ya dubi ma'aji Kulairu ya ce " ya Kulairu daga yau kai ne za ka maye gurbin karagar sarki
Rakibu. Sarkin fada zai zamto wazirin ka. Magatakarda kuwa shine zai zamo waziri na";
Ya yin da sarki ya sake zuwa nan a zancen shi sai kowa ya kama dokinshi ya haye.
Ma'aji Kulairu da sarkin fada suka durfafi hanyar da za ta sada su da ƙasar sarki Rakibu
dakarun haɗin gwiwa suka mara masu baya.
Sarki Nu'umanu da magatakarda suka jagoranci dakarun musulunci izuwa birnin Zainul-Ansar.
Tun daga bakin ƙofar gari jama'a suka yi cincirindo domin tarar dakarun musulunci cikin farin
ciki da annashiwa aka ɗunguma cikin gari.
Bayan mako bakwai sai uwar gidan sarki gimbiya Lawisat ta samu juna biyu farin ciki a wajen
al'umma ba a cewa komai.
Daga wannan rana farin ciki ya mamaye nahiyar baki ɗaya saboda tabbatar HASKEN
MUSULUNCI.
Ƙarshe
Alhamdulillah
Allahumma Salli ala Sayyadina Muhammad (S'A'W).
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaki
08137237071
Mu haɗu a sabbin littafai na masu zuwa.