Showing 18001 words to 21000 words out of 23849 words
Chapter 7 - KARYA DA GASKIYA Cigaban Tafarkin Tsira Rubuta littafin Mansur Usman Sufi .pdf
dariyar mugunta, ta ɓace ɓat a cikin gajimare tamkar bata taɓa
wanzu wa ba.
Lokacin da ma'aji Kulairu, sarkin yaƙi Lauzar, waziri Yazid da sarkin fada suka kacame da
azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, duka jagororin suna yaƙinne cikin JURIYA
DA BAJINTA irin ta MAZAN JIYA.
Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya ana wannan fafatawa babu sassauci kuma babu alamun
nasara ga kowanne ɓangare. Al'amarin da ya matuƙar karya zukatan dakarun musulunci kenan
suka fara tunanin cewa da yiwuwar babu nasara a wannan karon ma, abin da ba su sani ba
shine kamar yadda suke neman taimakon Ubangijin musulunci suma su waziri suke yi. Tur! Da aikin fasiƙai maƙiya Allah, ga shi dai su waziri sun kasance maƙiya Allah da
Manzonshi, amma suna roƙon shi ya ba su nasara akan ingantattun bayinshi.
Ana cikin wannan hali ne su waziri suka samu rauni da addu'a, al'amarin da ya bawa tawagar
musulunci nasara kenan suka fara samun RINJAYE akan arna, kafin a ɗauki wani lokaci su
waziri Yazid sun galabaita ainun har suna suɓutowa daga kan dawakansu.
Kwatsam! Sai aka hango wani kyakkyawan aljani yana saukowa daga sararin samaniya ɗauke
da wani kyakkyawan dattijo ma'abocin kwarjini da haiba sanye da fararen tufafi tun daga sama
har ƙasa yana ɗauke da wata sharɓeɓiyar takobi da jikin aka rubuta kalmar shahada.a dai-dai
lokacinne ma'aji Kulairu ya take wuyan waziri Yazid yana shirin soka mashi takobi a
maƙogaronshi. Cikin kuzari aljanin ya shimfiɗe fuka-fukanshi a turba.
Lokacin da jama'ar dake filin yaƙin suka yi arba da dattijon sai suka cika da matuƙar mamaki ba
wani ba ne dattijon ba face sarki Nu'umanu.
Wannan shi ne abin da ya faru da dakarun birnin Zainul-Ansar da su waziri Yazid.
Darul-Ashmar
Sadauki Ukaiza shugaban dakarun da suka fita farautar yaro Usaiba mai hatimin takobi yana
zaune a cikin 'yan uwanshi fursunonin kurku. Sai wani kyakkyawan saurayi mai matuƙar kwarjini
da haiba ya duba shi ya yi gyaran murya ya ce "ya kai Ukaiza an ya kuwa ba za su amfani da
tafiyar sarki Lamsarul-Azlam yaƙi domin nemar wa kanmu 'yanci ba daga KANGIN BAUTA,
kuma mu yi mashi JUYIN SARAUTA
Tun da kai jarumi kuma kwararre da ya san dukkan wani sako da lungu na wannan birni da
kuma sanin tuggun yaƙi, kuma a jiya lokacin da muke gudanar da aiyukanmu na gifta ta wajen
masu gadi na ji wani na cewa sarki Lamsarul-Azlam ya buƙaci a sake tura nashi ƙarin dakarun
yaƙi, kaga kenan babu tabbacin ga lokacin da zai dawo tun da bai yi nasara ba. Kuma zamu
dami damar yin GABA DA GABA da duk wata barazana, domin matuƙar yawan fursunonin dake
kurkukun nan ya isa ya sanya mu cimma nasara, domin masu iya magana na cewa SARKIN
YAWA yafi SARKIN KARFI, kuma tabbas hannu da yawa maganin ƙazamar miya ne";
Koda jin wannan batu daga bakin bawa Amral sai gaba ɗaya fursunonin dake wajen suka
zurfafa izuwa kogin tunani domin samun mafita.
Tsawon daƙiƙa ɗari ana cikin wannan hali sai daga bisani wani daga cikin su ya yi gyaran
murya ya ce "gaskiya ni shawara ta ina ganin mu tsaya a batun samun 'yancinmu mu ajiye
batun JUYIN SARAUTA domin sanin kanku ne cewa karo da sarki Lamsarul-Azlam tamkar
tunkarar ANNOBA DARI ne". Da jin wannan batu sai sadauki Ukaiza ya yi caraf! Ya tari numfashin shi ya ce "ba za mu
taɓa janye juyin mulki ba domin koda ba mu yunƙurin hakan ba. Ƙarshe dai mutuwa ce
makomar mu. Shin yanzu ina amfanin baɗi babu rai, ka sani cewa har abada matsoraci ba ya
zama gwani. Koda jin wannan batu daga bakin Ukaiza sai kowa ya yi na'am da batun.
Ukaiza ya ci gaba da cewa "muhimman abubuwan da zamu yi sune. Samun haɗin kan dukkan
fursunonin dake cikin kurkukun nan cikin sirri ba tare wani bare ya sani ba.
Na biyu kuwa muna buƙatar haƙa rami da ya kai tsawon kamu ɗari, sannan mu cika shi da
itace, za mu yi wannan aiki ne a tsakiyar dare lokacin da dakarun ke sharar barci.
A cikin daren zamu tattare a waje guda tun daga mata yara da tsofaffi nesa kaɗan da inda ramin
yaje. Wasu a cikin mu sai su kaure da faɗa da hayaniya ta yadda dakaru su zasu kawo ɗauki,
wajen kawo agajin za su afka cikin wannan rami, sai mu jefa wuta izuwa cikin rami dakarun su
ƙone ƙurmus ba tare da an zubar da jinin kowa ba. Hatta sauran dakarun da za su farmake mu
za mu jefa su cikin ramin.
Hikimar yin hakan shine babu wasu dakaru da za su kawo ɗauki domin sai an samu ƙarar
takubba za a yi zaton akwai abun ya faru.
Lokacin da alfijir zai keto za mu tunkari masarauta zamu yi amfani da dawakai da makaman
yaƙin dakarun kurkuku ne.
Amma ya zama wajibi mu sanya yara da mata a tsakiya a lokacin da muke tunkarar abokan
gaba.
Ya ku yana 'yan uwana fursunoni kuyi sani cewa matsawar ba ku sauka daga kan wannan tsari
da na kawo ba haƙiƙa babu abin da zai tsare mu daga kawo KARSHEN ZALUNCI a wannan
masarauta da nahiyar mu baki ɗaya;
Sa'adda Sadauki Ukaiza yazo nan a jawabin shi sai kowa ya cika da matuƙar farin ciki
maral-musaltuwa, cikin hanzari kowa ya watse domin yaɗa shirin bazato ga sauran fursunoni.
Al'amarin shugaban 'yan fashin duniya Sadauki Fitinatul-amir da yan majalisar shi, sa'adda suka
luluƙa cikin gajimare suna tsala gudu akan wannan mikiya, bayan sun kammala fafata artabu da
su jaruma Rusayyat.
Tafiyar rabin sa'a kacal suka yi suka iso gida. Lokacin da suka sauka sai Fitinatul-amir ya huce
kai tsaye izuwa fadarshi. Har A wannan lokacin fadar cike take maƙil da jama'a, bayan ya haye
bisa karagar mulki sai ya yi umarni ga MAGAYAKI ya tara dukkan dakarun yaƙi.
A wannan lokaci duk wanda ya ɗaga idanunshi ya kalli Fitinatul-amir sai kaga ya sunkuyar da
kanshi bisa ganin yadda yake tsananin fushi.
Al'amarin Hairat 'yar uwar yaro Usaiba mai hatimin takobi kuwa, tun sa'adda Fitinatul-amir ya
fita farautar yaro Usaiba da uwar gidansu Rusayyat. Sai ta kasance a hannun waɗansu kuyangi
na musamman ba su bari ta fita koda waje. Duk da cewar Hairat ba ta san abin da ya wakana
da yayanta da ummunsu ba amma ta ji hankalinta a tashe yake.
***
Kamar yadda sadauki Ukaiza ya tsara haka al'amarin yakasance a cikin kurkukun, bayan an
sanar da dukkan bayi abubuwan da aka tsara, wato an kammala ginin wannan ƙaton rami mai
ɗauej itace, a daren kwana na biyu sai dukkan jama'a maza da mata suka taru a waje guda,
kawai sai samari majiya ƙarfi suka kaure da artabu tsakanin su ta hanyar kaiwa juna naushi da
bugu nan take waje ya kaure da ifice-ifice.
Koda jin hakan sai dakarun su ka ɗimauce suka, domin a tunanin su FARMAKIN BAZATO aka
kawo masu.
Kash! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, da yake a wannan lokaci gaba ɗaya fitilun kurkukun a
kashe suke sai dakarun suka dinga afkawa izuwa cikin wannan rami suna masu tsandara ihu,
kuma wani abin mamaki da al'ajabi shine da zarar sauran dakarun sun daina jiyo motsin 'yan
uwansu sai su kunno kai wajen, lokacin da su Ukaiza suka tabbatar cewa dukkan dakarun sun
afka izuwa cikin ramin sai nan take zaratan samarin suka kunna fitilun ice gami da jefa izuwa
cikin wannan rami, nan take wuta ta kama jikkunan dakarun suna ihu da kururuwar neman
taimako wasu lokutan sai dai ka ji randan cikin su tana bindiga suna fashewa.
Koda kammala samun wannan nasara sai aka shiga aikin mayar da ƙasar da aka tono cikin
matuƙar farin ciki suna masu kiɗe-kiɗe da raye-raye.
Daga nan sai aka shiga fir-fito da fursunonin dake kunne a ɗakunan duhu, aka ɗebi makaman
yaƙi aka buɗe ƙofar kurkukun aka kunna kai izuwa gari kamar yadda aka tsara.
Tun kafin a iso izuwa fada aka fara gwabza artabu da dakaru, nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa da
ihun mazaje ya cika dodon kunne, jama'a suka kaure da guje-guje gami da ifice-ifice.
Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN KARFI sai ya
zamana cewa an murƙushe dakarun ta hanyar saukar masu da azabar KAIFIN TAKOBI.
Sa'adda al'ummar birnin suka hango cewa fursunoni ke yin YAƘIN YANCIN BAYI sai suka dinga
ɗebo makaman su suna yin shirin yaƙi suna shiga cikin ayarin, domin suma sun gaji da zama a
KANGIN BAUTA na sarki Lamsarul-Azlam, wasu kuma farin ciki ne ya cika zukatansu bisa
saduwa da masoya da 'yan uwansu da suka shafe tsawon shekaru a kurkuku suna cikin azabar
sarki Lamsarul-Azlam.
Kafin shuɗewar daƙiƙa ashirin birnin ya cika da mayaƙa babu masaka tsinke,
Nan fa birnin ya ƙara yamutsewa da azababban yaƙi mai matuƙar muni da daban tsoro, a wasu
lokutan sai kaga badakare ya cika wandonshi da iska, amma sai kaga jama'a sun yi tara-tara
sun rafke shi ya faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba.
Nan fa JINI DA KASA suka cakuɗu waje guda, sassan jikkunan bil'adama suka dinga shawagi
a sama suna zubowa ƙasa, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda kofatun dawakai ke
kartar ƙasa suna turmutsutsu.
Kaico! Haƙiƙa yaƙi abin tsoro ne da tashin hankali ga dukkan wata halitta a doran ƙasa,
domin wata musiba bata kai yaƙi ba, shi ne ke haifar da rasa rayuka, dukiya, mutunci da daraja
kuma mayar da yara marayu mata ta zamo bazawara, yaƙi maishar da 'yan maza mataye kuma
ya haddasa yunwa, fari da cutuka.
Wannan shi ne abin da ya wakana a ƙasar Darul-Ashmar a lokacin da fursunonin kurkuku suka
yi yunƙurin JUYIN MULKI a lokacin da sarki da sarki Lamsarul-Azlam ya kai FARMAKI birnin
Madinatul-Afnan.
Sa'adda boka kaddad ya rikiɗa izuwa mucijiya mai kawuna arba'in ya kanannaɗe jarumi
Muhassin domin ta kafta mashi sara da kawunan arba'in, a bisa saman tekun Baharul-saljir.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai gimbiya Aslaima ta dako wawan tsalle tamkar an harbo ta
daga cikin baka ta sauka akan mucijiyar ta ƙwala kabbara da ƙarfi gami da dunƙule hannayenta
biyu ta gabzawa wuyan mucijiyar ɗaya wawan naushi ji kake ruƙus! Ƙas kan ya kare. Kafin cikar
daƙiƙa ashirin Aslaima ta ƙarya kawuna ashirin na mucijiyar. Wohoho haƙiƙa JARUMTAKA baiwa ce daga Ubangiji, babu abin da zai burge mutum face idan
ya ga yadda Aslaima ke ƙarya wuyan mucijiyar tamkar tana ƙarya siraran busassun ƙirare. Wani
abun al'ajabi ma shine yadda Aslaima ke iya zillewa hare-haren mucijiyar.
Sa'adda mucijiyar ta ji TSANANI DA UKUBA sun tsananta gare ta sai ta saki jarumi Muhassin
ya faɗo ƙasa ba tare da ya nutse cikin tekun ba yana mai fitar da numfashi sama-sama,
Duk wannnan abu da yake wakana aljani Ramsisul-Ayyam yana tsaye a gefe inda gawar
wannan kada yake yana kallo sai ya cika da matuƙar mamaki bisa ganin irin bajintar da Aslaima
ke yi ya ce a cikin ran shi "haƙiƙa Ubangijin jarumi Muhassin buwayi ne gagara misali domin ga
shi ya bawa Aslaima JARUMTAKA wacce ba ta daɗe da yin imani da shi ba, amma ya aka yi
gimbiya ta kasance jaruma bayan cewa a wannan tafiya koda sauro bata iya kashe wa, amma
tana iya yiwu wa saboda makauniya ce ya sanya bajintar ta bata bayyana ba. Amsar
tambayoyin da Ramsisul-Ayyam ya kasa bawa kansa kenan kawai ya yi shiru yana mai zuba
idanu.
Koda gimbiya ta samu nasara sare kawunan mucijiyar baki ɗaya sai ta sake dako wawan
tsalle cikin gwaninta tana mai taka tekun da ƙafafuwanta tamkar tana tsaye a turba.
Take mucijiyar ta rikiɗa izuwa boka kaddad an yi mashi yankan rago jininshi ya kwaranya a kan
tekun, fuskarshi ta yi baƙi wuluk! Idanuwanshi da harshen sun zazzago, kaico! Tir da mutuwar
fasiƙi maƙiyin Allah da Manzonshi, inda ace yana tsaye a wannan waje zai ga yadda boka
kaddad ya yi mutuwar wulakanci, dole ne ya ji tsoron Ubangiji ya kama shi, domin babu wani
abun halitta da ya gagare shi hukunci.
Cikin matuƙar farin ciki Muhassin ya sakarwa Aslaima wani kyakkyawan murmushi, take ta
mayar mashi da martani cikin annuri, sannan ya juya ya dubi Ramsisul-Ayyam ta ce "ya kai
wannan aljani shin za ka bayar da gaskiya da ubangijin halitta ko kuwa ka zaɓi ka yi mutuwar
hasara tamkar yadda mai gidanka ya yi"; Koda jin wannan batu daga bakin Muhassin sai Ramsisul-Ayyam ya ce cikin ladabi "ya
shugabana ai tuni na imani da ubangijinka tsoron ubangidana ne ya hana ni bayyana wa, yanzu
a shirye nake na shiga addinin ka".
Koda jin hakan nan take Muhassin ya karanta KALMAR SHAHADA Ramsisul-Ayyam ya
maimaita.
Faruwar hakan ke da wuya nan take duk wani gashi dake jikinshi da ya sanya mashi muni ya
ɓace ɓat! Kuma ya ji wani ƙarfi da nutsuwar zuciya ta musamman ta same shi.
Muhassin ya ci-gaba da cewa "ya kai wannan aljani ka yi sani cewa sunan da ake kiran ka da
shi baya da wata ma'ana a Musulunci yanzu zan canja maka shi izuwa ABU-AYUB, sannan
yanzu sai ka ɗauke mu daga nan izuwa birnin su gimbiya Aslaima";
Abu-Ayub ya risina ya ce "an gama ya shugabana, amma a shawara ta a ciro ALLON
TSAFI daga cikin wannan kada domin kar wani ya mallake shi ya cutar al'umma".
Muhassin ya ce "kwarai kuwa haƙiƙa ka kawo shawara mai kyau, nan take ya karanta
Ayatul-kursiyyu da falaƙi da nasi ya tofawa kadan, nan take ya kama da wuta ya ƙone ƙurmus!
Kawai sai Abu-Ayub ya shimfiɗe gadon bayanshi jarumi Muhassin da gimbiya Aslaima suka hau
bisa kan shi suna yin bisimilla, sannan ya yunƙura yana tashi zuwa sama ya na mai kaɗa
fuka-fukanshi ya ɓace ɓat! Cikin gajimare.
Sa'adda aljani Abu-Ayub ya wanzu yana keta gajimare cikin matuƙar sauri tamkar giftawar
tauraruwa mai wutsiya, sai aka tsawon sa'a ɗaya ana tafiya babu sassauci.
Ana cikin wannan hali ne gimbiya Aslaima ta buɗi baki sannan ta yi gyaran murya ta ce "ya
masoyina abin alfaharina ka yi sani cewa a halin yanzu ƙaunar da nake yi maka ba zan iya
misalta taba, ina jin zan iya rasa rayuwata idan babu kai, ka zamto tamkar gudan jini dake
kewaya wa a zuciyata, soyayyar ka ta zamto tamkar bugun numfashi na, ina godiya ga Ubangiji
da ya bani abin ƙauna ma'abocin kwarjini, SADAUKANTAKA da DAUKAKA DA BAIWA".
koda jin waɗannnan daɗaɗan kalamai daga bakin Aslaima sai 'yar ƙaramar dariya ta
suɓucewa Muhassin har kunci shi suka loma fararen haƙoranshi suka bayyana cikin tattausar
murya ya ce "ya abar bege na a dare da rana ki yi sani cewa ni ina sonki ne tsawan rayuwa,
dukkan wani abu da ya shafi rayuwar mu addini ya tsara mana shi, Ubangiji ya umarce mu mu
ƙaunaci ababan ƙaunar mu da Allah, domin idan saboda da kyawu, kuɗi ko mulki ne wata rana
za su gushe;
Inda ace kin taɓa karanta hikayar littafin JARUMAN DUNIYA za ki ji yadda yarima Muzaifar da
ya kamu da soyyyar almajira Sharilat yar tsoho Kuhairu da za ki tabbatar da cewa soyyya ta
gaskiya babu ruwan ta da dukiya, mulki ko nasaba";
Da jin wannan batu sai gimbiya Aslaima ta gyaɗa kai cikin annurin fuska ta ce "haƙiƙa
wannan bayani ya sanya na ƙara ƙaunar Ubangiji domin bai bar wani abu mai muhimmanci na
rayuwar mu ba face ya tsara mana yadda za mu yi, kuma bayan an ɗaura mana aure sai na
karanta littafin JARUMAN DUNIYA domin jin irin darussan dake cikin shi. Koda gimbiya ta zo nan a zancen ta sai su duka biyun suka bushe da dariyar farin.
Daga bisani jarumi Muhassin ya dubi Abu-Ayub ya ce "akwai buƙatar mu yada zango anan
domin mu yi sallah mu samu abun kalaci tun da guzurin mu ya ƙare"
Koda jin wannan umarni sai Aljani Abu-Ayub ya risina cikin ladabi ya ce "an gama ya
shugabana;
Yana gama faɗin hakan ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luuuh! Ya sauka a turba.
Inda aka sauka ya kasance daji mai ɗauke da bishiyoyu, duwatsu tsilli-tsilli gami ƙoramu, kuma
dajin ya yi tsit tamkar babu wata halitta mai numfashi a cikin shi.
Al'amarin da ya bawa kowa mamaki kenan. Cikin hanzari Muhassin ya yunƙura ya sakko daga
kan aljani Abu-Ayub gimbiya Aslaima tayi koyi da shi, suka durfafi wata ƙorama Abu-Ayub na
biye da su, ya yin da suka isa sai suka tsafta ce jinin dake jikin tufafin su suka suka ɗaura
alwala, sannan Muhassin ya shige gaba ya tayar da iƙama ya tayar da sallah. Bayan an kammala ne Muhassin ya yi gyaran murya dubi abokan tafiyar shi ya ce "ya ku
abokan tafiyata ina ganin bai kamata mu yada zango anan ba akwai buƙatar mu ƙara yar tafiya
kaɗan.
Koda gama faɗin hakan sai Muhassin ya miƙe tsaye ya shige gaba gimbiya Aslaima da aljani
Abu-Ayub suka mara mashi baya a ka ci gaba da tafiya.
Ana cikin wannan tafiya ne aka hango wani gida guda jal da aka yi ginin shi da zallar duwatsun
wuta masu ƙwarin gaske a wannan lokaci ƙofar gidan a buɗe take alamun dake nuna akwai
halitta a ciki,
Sa'adda aka yi arba da gidan sai kowa ya cika da matuƙar mamaki, Abu-Ayub ya dubi Muhassin
ya yi gyaran murya cikin ladabi ya ce "ya shugabana shin zamu shiga cikin wannan gida ne
domin mu ga abin da ke ciki ko kuwa zamu ƙetare?
Koda jin wannan tambaya sai Muhassin ya yi shiru yana mai zurfafa cikin kogin tunani daga
basani ya dube shi ya ce "akwai buƙatar mu duba ɗin sai dai ina