Showing 6001 words to 9000 words out of 23849 words
Chapter 3 - KARYA DA GASKIYA Cigaban Tafarkin Tsira Rubuta littafin Mansur Usman Sufi .pdf
tazarar dake tsakanin su bata huce taku talatin ba dai aka fara kallon-kallo na tsawon
daƙiƙa goma, daga can wannan mikiyar da ta ceci rayuwar su Usaiba ta yi girgiza take ta rikiɗa
izuwa surar wata kyakkyawar budurwa.
Budurwar takasance mai matsakaici jiki mai launin fata wankan tarwaɗa tana sanye da tufafi na
fatun dabbobin daji da suka kama jikinta har surar kyawun ƙirjinta ya bayyana a tsaye suke
ƙyam! Basu rankwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi, ƙugunta
daga gaba a tsuke yake ta baya kuma ya yi tudu inda za a sanya tuffa zata ita zama daram,
dara-daran idanuwanta farare ƙyal da baƙin cikinsu ya kasance siɗik mai kwarji da haiba haɗi
da yalwataccen gashin kanta da ya zuba har ƙasan kwankwasonta sune abubuwan da suka
sake tona asirin kyawun ta.
Haƙiƙa babu wani ɗa namiji mai hankali da zai tozali da wannan kyakkyawar sura face ya kamu
da matuƙar ƙaunar ta.
A gadon bayanta tana rataye da wani rantsattsen Kwari da baka da kwansonta, a kwiɓin
cinyarta tana ɗauke da wata sharɓeɓiyar takobi a cikin kubenta.
Sa'adda shugaban'yan fashin duniya sadauki Fitinatul-Amir ya yi arba da kyakkyawar
budurwar sai ya cika da matuƙar mamaki da al'ajabi,
Ita kuwa sai ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta,
Al'amarin da ya fusata shi kenan ya daka mata tsawa wacce ta sanya hantar cikin 'yan majalisar
shi ta kaɗa saboda firgici, amma bisa mamaki sai ga ko gezau ba ta yi ba, sai da ta yi dariyar ta
ishe ta sannan daga bisani ta tsahirta ta buɗi baki cikin zazzaƙar murya mai tamkar sarewa cike
da taƙama da BAƘAR IZZA ta ce "ya kai Fitinatul-Amir ka yi sani cewa na ɗauki tsawon lokaci
ina tsumayen zuwan wannan rana da zan yi GABA DA GABA da kai domin ɗaukar fansa,
haƙiƙa na san ba ka san ko ni wece ce ce ba wannan ba abun damuwa ba ne amma na san
cewa baka mance wane ne sarki Kushuful-Himras ba, ni 'yarshi ce Shalmirat bintu
Kushuful-Himras";
Koda jin wannan batu daga bakin Shalmirat sai idanun Fitinatul-Amir suka zazzaro ya cikin
matuƙar firgici ya nuna Shalmirat da ɗan yatsanshi bakinshi na kyarma ya ce "ke 'ya ce ga sarki
Kushuful-Himras?
BABI NA BAKWAI
Shalmirat ta bushe da dariyar mugunta a karo na biyu sannan daga bisani ta murtuke fuska ta
ce "shin kana tunanin cewa ka kashe mahaifina da jama'ar birninmu a banza? Haƙiƙa ka kashe
maciji ne baka sare kanshi ba.
Babban kuskuren da ka yi shine bayan ka ƙone dukkan gidaddajinmu ka shafa'a baka rushe
wani ɗakin bauta ba, abin da baka sani ba shine lokacin da mahaifina ya fahimci cewa babu
wata halitta da zata tsira da rayuwar ta a cikin jama'arshi, sai ya ɗamƙa min dukkan sirrikan
tsafin shi ta hanyar busa mini wani koren hayaƙi daga bakinshi, sannan ya sanya ni a ciki ɗakin
bautar ya janyo ƙofar ya rufe, sannan ya ruga izuwa filin daga.
Tun daga ranar da na rasa mahaifina na rasa duk wani farin cikin rayuwata, babu abin da idan
na tuna yake sanya ni zubar da hawaye face yadda ka yiwa abbana yankan rago ka farke
cikinshi ka fito da zuciyarshi ka daddatsa ta da takobi ka cinye ta a haka, hatta lokacin da ku
kazo giftawa ta daf da ɗakin bautar ina rusa kuka amma ba ku iya jina ballantana gani na,
sakamakon sirrikan tsafin abbana dake bani kariya";
Lokacin da Shalmirat yazo nan a labarin ta sai hawaye suka kwaranyo daga idanuwanta.
Shi dai Fitinatul-Amir bakomai ne ya sanya hallaka sarki Kushuful-Himras ba sai domin bisa
binciken da ya gudanar a halarar tsafin shi ya gano cewa shine sarkin da anan gaba zai ɗara
shi tarin dukiya da ƙarfin sihirin TSAFI. Bisa wannan dalili ya sanya ya aika manzo gare shi
domin ya yi MUBAYA'A a gare shi, amma saboda kare martabar al'ummar shi ya sanya ya ƙi
bayar da haɗin kai, domin hakan sai Fitinatul-Amir ya jagoranci rundunar MAYAƘA ya afkawa
birin su Shalmirat da rana tsaka.
Koda jin wannan batu daga bakin Shalmirat sai Fitinatul-Amir ya bushe da dariyar ƙarfin hali
sannan daga bisani ya murtuke fuska ya dubi Shalmirat cikin gadara ya ce "haƙiƙa kin tafka
babban kuskure da kike tsammanin cewa za ki iya GABA DA GABA da ni shin kin manta ne
cewa mahaifinka ma da ya kasance JARUMIN KWARAI na ga bayan shi ballantana ke karan
kaɗa miya kuma ƙaramin alhaki, ina mai tabbatar miki da cewa take yanzu ba tare da wani ɓata
lokaci na zan aike da ruhinki Izuwa duniyar da ba'a dawo wa, sannan na kashe babban maƙiyi
na Usaiba mai hatimin takobi da 'yar uwarshi Hairat";
Kafin Fitinatul-Amir ya gama rufe bakinshi Shalmirat ta tari numfashi tana mai daka mishi
tsawa, sannan ta zare takobinta take koren haske naban mamaki ya dinga fita daga jikin takobin
yana shiga jikin su yaro Usaiba, lokacin da ya kammala shiga nan take wani irin gagarumin ƙarfi
ya shige su suka miƙe zumbur tamkar babu rauni a tare da su. Sannan ta riga Izuwa kan Fitinatul-Amir tana ihu da kururuwa mai firgitarwa, koda ganin hakan
sai yaro Usaiba, Hairat da Rusayyat suka rufa mata baya suna masu yin ɗauki kan yan
majalissa su sha biyu batare da sun riƙe wani makami ba.
Wannan shi ne abin da ya faru da wannan mikiya bayan ta ceto rayuwar su Usaiba mai
hatimin takobi daga hannun shugaban'yan fashin duniya.
Al'amarin su boka kaddad kuwa tunda duku-dukun safiya bayan anyi kalaci sai aka cigaba
da tafiya ba aka kan aljani Ramsisul-Ayyam, ana tafiya cikin hanzari tamkar giftawar tauraruwa
mai wutsiya a cikin gajimare. Sai da aka shafe tsawon mako guda ana tafiya, a iya tsawon
wannan tafiya babu abinda ke sanya wa ayada zango face idan lokacin ibadar jarumi Muhassin
ya yi ko gimbiya na buƙatar bawali, ko kuma za a yi kalaci hatta barci da abisa kan
Ramsisul-Ayyam ake yi.
A ranar kwana na takwas ne da la'asar sakaliya Ramsisul-Ayyam ya sauka a cikin wani
ƙasaitaccen daji ma'abocin bishiyu, ƙaramu, duwatsu da sarƙaƙiya, babu wata halitta mai
numfashi da zata tsinci kanta a cikin daji face tsoro da firgici sun mamaye ta, babu abin da zai
sake ɗimauta mutum face yadda dajin yakasance tsit! Tamkar babu wata halitta mai rai domin
koda kukan tsuntsu babu.
Lokacin da aka sauka ne fa kowa ya sha jinin jikinshi kuma ya zare makaminshi domin yin
shirin ko ta kwana.
Boka kaddad ya dubi Ramsis ya ce "kai zaka tsaya anan ka kare lafiyar gimbiya da kuyangin
dake yi mata hidima;
"An gama ya shugaban";
Ramsis ya faɗa cikin ladabi.
Sannan kaddad ya mayar da duban shi ga jarumi Muhassin fuskarshi a murtuke babu annuri
cikin kakkausar murya ya ce "ya kai Muhassin ka yi sani cewa bamu buƙatar taimako daga gare
ka a duk wata musiba da zamu shiga sai idan dukkan wata dubara ta gaza, sai ka nemi
taimakon na ka Ubangijin da kake iƙirarin cewa shine mahaliccin kowa. Gama faɗin hakan ke da wuya sai boka kaddad ya sake zare wani makamin a jikinshi
yazamana cewa yana riƙe da guda biyu,
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ji ganyayyakin tsirrai na motsawa, alamun dake nuna
cewa akwai abu mai numfashi da ya yi tajalli a wajen. Al'amarin da ya sanya kowa ya dage
kuben takobinshi kenan,
Daga can sai aka ga waɗansu irin gabza-gabzan dakaru suna yin fitar burgu daga cikin
duhuwar bishiyu, waɗansu ya sakkowa daga kan rassan bishiyun, su dai dabarun sun kasance
masu ƙirar samudawan farko suna da girma tamkar toron giwa, suna sanye cikin gagarumar
shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro, suna ɗauke da miyagun makamai fiye da nau'i
arba'in, fusakunsu baƙaƙe ne wuluk masu muni tamkar basu taɓa dariya ba, adadin su kuwa ba
zai ƙidayu ba, idan mutun ya kai duban shi babu abinda zai gani face kawunan su birjik babu
masaka tsinke.
Kaico! Haƙiƙa waɗannan dabaru sun cika ANNIBA ƊARI babu wani jarumi da zai yi tozali da
su face ya yi nadamar wanzuwar shi a doron ƙasa. Shi kan shi Ramsisul-Ayyam duk da
kasancewar shi matashin aljani sai da ya ɗimauce da ganin dakarun, jarumi Muhassin ne kaɗai
bai razana ba shi ma addu'o'i ne ke ɗawainiya da shi. Nan fa aka fara kallon-kallo a tsakanin su na tsawon daƙiƙa hamsin ba tare da wani ya yi
yunƙurin farmakar abokin gabar shi ba.
Kawai sai samudawan suka yi ihu da kururuwa mai firgitarwa DANDAZON MAYAƘA suka yi
ɗauki kan su boka kaddad suna masu ɗaga makamansu Izuwa sama.
Koda ganin hakan sai jarumi Muhassin ya ƙwalla kabbara ya yi ɗauki kan su, boka kaddad da
tawagar dakarun rakiya su kayi koyi da shi suna ihu da kururuwa mai firgitarwa, shi kuwa
Ramsisul-Ayyam sai ya tsaya a kofar tantin gimbiya domin kare lafiyar ta hannunshi riƙe da
wata garkuwa ta baƙin ƙarfe gami da wannan zabgegen zatari mai KAIFI DA TSINI. Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka yi GWAGWARMAYA a
DUNIYAR MAYAƘA, haƙiƙa yaƙi abin tsoro ne kuma tashin hankali, lokacin da TAWAGA BIYU
suka yi KARON BATTA sai ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon
kunne suna amsa kuwwa Izuwa cikin daji, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, bishiyu suna dinga
karairaye wa suna faɗuwa ƙasa, a duk sa'adda ɗaya daga cikin dakarun ya kai wa su boka
kaddad hari idan suka kauce duk abin da makamin ya sauka a kan shi sai kaga ya tarwatse ya
yi bindiga koda kuwa dutse ne .
Ana fara wannan artabu ne su boka kaddad suka fara gane cewa haƙiƙa shayi ruwa ne ba
abinci mai nauyi, domin matuƙar zafin naman dakarun ya ninka na su sau arba'in, kuma suka
fahimci cewa idan aka cigaba da wannan yaƙi a haka dakarun za su iya murƙushe su. Nan fa
hankulan su suka DUGUNZUMA ainun.
Wane ne zai samu nasara a wannan yaƙi tsakanin samudawan dabaru da su jarumi Muhassin?
Wane ne zai samu nasara tsakanin Jaruma Shalmirat da shugaban 'yan fashin duniya sadauki
Fitinatul-Amir, shin yana samun nasarar hallaka yaro Usaiba mai hatimin takobi?
Sarkin Musulunci Nu'umanu na kuɓuta daga sharrin wazirinshi ?
Shin aljani Husubul-luzwar yana samun nasarar sato sarki Rayyan daga sansanin musulmai ?
Ina makomar sadauki ukaiza da koma Izuwa birnin Darul-Ashmar domin ceto rayuwar iyalanshi
a hannun sarki Lamsarul-Azlam ?
BABI NA TAKWAS
Lokacin da dakarun sarki Madsur suka ɗauke shi daga filin yaƙi cikin mawuyacin hali da ke
tsakanin RAYUWA DA MUTUWA , suka ruga da shi izuwa sansani suka shiga da shi Izuwa tanti
suka shimfiɗar da shi a bisa wani ƙayataccen gado, cikin hanzari likitoci suka duƙufa akan shi
suna shuga bas shi taimakon gaggawa, ta hanyar ɗinke raunikan dake jikinshi suka sanya
magani.
Gama aiwatar da hakan ke da wuya nantake ya samu ƙwarin jikinshi ya tashi zaune, a
wannan lokaci ne waɗansu tsala-tsalan'yan matan kuyangi sun shigo ɗauke da abin kalaci a
bisa ƙayatattun farantai da nau'ikan abubuwan shaye-shaye nau'i daban-dabam suka ajiye
abisa wani dogon teburi dake tsakiyar tantin. Take likitocin suka da kuyangin suka juya suka fice daga turakar, koda sarki Madsur ya ɗauko
wani kofin zinare mai ɗauke da abin sha, koda ya kai bakinshi domin ya kwankwaɗi abin da ke
ciki, nan take ya ga hoton fuskarshi a jiki an sanya mata audugar tsaida jini, kawai dai ya yi jifa
da kofin yana mai kurma wawan ihu.
***
A can sansan su sadauki Huzlaif kuwa tun da aka shiga da shi Izuwa tantinshi likitoci
suka taru a kanshi ba su ɗauki wani lokaci mai tsawo suka samu kan shi ba, har ya miƙe tsaye
yana takawa da ƙafafuwanshi, yana cikin wannan hali ne wani saurayi ma'abocin kyawun ya
bayyana a gare shi, sanye yake cikin baƙaƙen sulken yaƙi tun daga ƙasa har sama, a gadon
bayanshi yana rataye da wata sharɓeɓiyar takobi.
Saurayin ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, Huzlaif ya dube shi cikin nutsuwa ya ce "ya kai
Himar ka yi sani cewa bakomai ne ya sanya na kira ka ba sai domin na ji a jikina cewa a kowa
ne lokaci sarki Madsur zai iya turo mana dakarun HARIN BAZATO, saboda haka bai kamata mu
shantake ba, kasancewar masu iya magana na cewa komai mammakon ka wani a hanya ya
kwana, hakan ba zai sanya mu gaza yin namu tanadin ba, yanzu abin da nake buƙata a gare ka
shine ka tashi dakarun leƙen asiri izuwa sansanin abokan gaba, sannan ka umarci dakarun mu
cewa su kaso uku, kaso na farko su yi barci yanzu, sauran su yi gadin, idan sun farka da
sulusainin dare sai kaso na biyu su yi ko yi da su haka ma na uku, ta a yadda dai gajiyar dake
tare da su ba za ta sanya kashe gari su gaza a filin MUBARAZA ba";
Koda jin wannan umarni sai barde Himar ya ce "an gama ya shugabana".
Yana gama faɗin hakan ya juya ya fice daga tantin.
Wannan shi ne abin da ya faru da rundunar Shugaban'yan fashin duniya da ta sarki Madsur.
***
A can birnin Zainul-Ansar kuwa sai da aka shafe tsawon kwanaki uku ana cikin alhinin
abin da ya faru na asarar rayukan 'yan uwa musulmi a masallaci lokacin da ake gudanar da
sallar asuba. A iya tsawon kafuwar birnin al'umma ba su taɓa tsintar kan su a cikin wannan
yanayi ba. Kuma a iya tsawon kwanaki uku rashin lafiyar sarki Nu'umanu ta yi tsamari, domin ba
ya iya komai sai dai a kwantar a tayar, binciken likitocin ya tabbatar da cewa takobin da aka yi
masa rauni gabar da take ɗauke da ita ba ta yi tasiri a cikin jininshi.
A ranar kwana na ukun ne bayan sallar azahar ma'aji Kulairu ya kira taron gaggawa na 'yan
majalisa a wani ɗakin sirri.
Lokacin da ya ga cewa kowa ya hallara a ɗakin taron kuma ya yi shiru sai ya katse shirun da ta
wanzu ta hanyar yin gyaran murya sannan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya ce "Godiya ta
tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, tsira da aminci Allah su ƙara tabbata ga Annabin rahama (
S'A'W) da iyalanshi masu tsarki gami da sahabbanshi masu haske. Baya wani dogon jawabi zan yi ba kowannen ku dai masani game da abin da ya tara mu anan,
sai dai zan yi mabuɗin zance, da farko dai abin baƙin ciki ace ana zaton wuta a maƙera sai a
same ta a masaka, waziri Yazid da yake jagora na biyu a wannan ƙasa da sarkin yaƙi Lauzar
sune suka haɗa kai da sarki Rakibu domin rushe addinin Musulunci da birninmu baki ɗaya,
haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce makashin ka yana tare da kai".
Kuma saboda da illar munufiki Ubangiji ya sanya azabar da za 'a manufukai ta zarta ta kafurai,
domin suna cutar da musulunci fiye da kafurai, yanzu mene ne shawararku game da hakan?;
Sa'adda Kulairu ya zo dai-dai nan azancen shi sai ɗakin taron ya sake yin shiru a karo na
biyu, sai daga bisani wani dattijo ma'abocin kwarjini da cikar kamala ya yi gyaran murya ya ce
"ya ku 'yan uwana 'yan majalisa ku yi sani cewa abin da ya wakana ya tabbatar mana cewa
kakarmu ta yanke saƙa, dalilin da sanya na faɗi hakan kuwa shine da can baya mu gano abinda
ya haddasa mana matsalolin ba, amma cikin taimakon Ubangiji yanzu mun gano bakin zaren,
yanzu za mu shirye rundunar MAYAƘA domin mayar da martani, sannan wane irin hukunci za
mu yanke wa sarki Rakibu tun da ya saɓa yarjejeniyar zaman lafiya da muka ƙulla tsakanin mu".
Lokacin da hakimin unguwar Ɗaibat Sha'aban ibn Kumais yazo dai-dai nan a jawabin shi
sai ya sarkin fada wani kyakkyawan matashi ya yi gyaran murya ya ce "Allah ya taimaki
Sha'aban kamar yadda addininmu ya tsara shine duk lokacin da kafurin amana ya saɓa
yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninku, to za ku yaƙe shi domin kare rayuka, addini da
dukiyoyinku, saboda haka a shawara ta a daren yau mu shirya dakarun yaƙi, kashe gari tunda
duku-dukun safiya mu farmaki sarki Rakibu da su waziri";
Sa'adda sarkin fada yazo nan azancen shi sai kowa ya cika da matuƙar farin ciki
maral-musaltuwa bisa samun mafita, daga wannan kowa ya kama gabanshi ɗakin taron ya
zamto wayam.
A can ƙasar sarki Rakibu tun sa'adda suka yi rashin nasara akan sarki Nu'umanu da
al'ummarshi sai suka kasance cikin matuƙar baƙin ciki a kowace rana sai sun karanta wasu
daga cikin surorin Alkur'ani mai girma domin samun nasara a akan sarki Nu'umanu.
Tir! Da aikin fasiƙi ga shi sun saɓawa Ubangiji amma suna suna neman taimakon shi akan ba
su RINJAYE akan bayinshi mumunai.
Kuma ya zamana cewa a kowa ce rana ana ƙara bawa dakaru horon Yaƙi domin tunkarar birnin
Zainul-Ansar.
***
Wohoho! Lokacin aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini daban
tsoro. Fitinatul-Amir da jaruma Shalmirat suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin
matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, duk sa'adda makamansu suka
haɗu sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara marar daɗin saurare. A ɓangaren su Usaiba kuwa sun wanzu suna kaiwa 'yan majalisar naushi da bugu hannu da
ƙafa tamkar waɗansu ifritai, shi kan shi Usaiba ya yi