Showing 3001 words to 6000 words out of 23849 words

Chapter 2 - KARYA DA GASKIYA Cigaban Tafarkin Tsira Rubuta littafin Mansur Usman Sufi .pdf

ya dubi gawarwakin dakarun dake zube a ƙasa, sannan ya mayar da duban shi ga
saurayin fuskarshi a murtuke babu annuri cikin kakkausar murya ya ce "ya kai wannan saurayi
yi maza ka sanar da ni abin da ya faru da gimbiya kafin na yanke maka hukunci dai-dai da abin
da ka aikata, kuma wane ne kai? Koda jin wannan tambaya sai murmushi mai taushi ya suɓuce wa saurayin da ya ƙara bayyana
kyawun fuskarshi, sannan ya dubi boka kaddad ya buɗi baki a karo na farko ya fara magana
cikin wata irin zazzaƙar murya ya ce "ya kai wannan dattijo kayi sani cewa ba ni da masaniyar
abin da ya wakana tsakanin zakanyar da gimbiya ba sai dai kawai na jiyo kururuwar ta ne kuma
na fahimci tana buƙatar taimako shine na kawo mata ɗauki,
Game da tambayarka ta farko kuwa ita ce suna na jarumi MUHASSIN IBN SHA'ABAN na fito ne
daga nahiyar larabawan yamma a wani birni da ake kira da Madinatul-yusra, domin yaɗa addini
na na bautar Ubangijin talikai a faɗin duniya.

Koda jarumi Muhassin yazo dai-dai nan azancen shi sai dakarun dake wajen suka cika da
matuƙar mamaki ainun jin Muhassin ya ambaci Ubangijin talikai.
Boka kaddad kuwa sai ya murtuke fuska tamkar an aiko mishi da SAƙON MUTUWA ya dubi
Muhassin babu annuri a tare da shi cikin kakkausar murya ya ce "naji dukkan bayanin ka kuma
na fahimci cewa ba kayi yunƙurin cutar da sarauniyar kyawawa ba, saboda haka sai ka kama
gaban ka bamu da buƙatar wani dogon jawabi", Har Jarumi Muhassin ya buɗi baki da nufin ya sake furta wani abu sai boka kaddad ya ɗaga
mishi hannu yana nuni da ya tafi ya basu waje.
Amma sai aka ga gimbiya Aslaima ta miƙe tsaye tsam! Tamkar babu wani rauni a tare da ita ta
dubi Muhassin fuskantarta cike da wani irin ƙayataccen murmushi mai ɗimauta zuciyar duk wani
ɗa namiji, cikin tattausan murmushi mai daɗi tamkar sarewa ta ce "ya kai wannan saurayin
ma'abocin kwarjini da taimako ka yi sani cewa kai ne mutum na farko da taɓa ceton rayuwata a
lokacin da nake gaɓar mutuwa, duk da kasancewar a halin yanzu ina ɗauke da cutar makanta
amma idanuwana suna iya ganin ka, saboda ina neman wata alfarma a wajen ka da ka biyo ni
izuwa gagarumar tafiyar mu ta nemo mini maganin lalurata, na yi maka alkawarin bayan mun
samu nasara zan sanya mahaifina ya baka duk wani abu da kake buƙata da ya danganci
sarauta ko dukiya.
Koda gimbiya tazo nan azancen ta sai gaba ɗaya jama'ar dake wajen suka cika da matuƙar
mamaki, daga can sai ya ci gaba da cewa "idan har ka na tantama akan abin da na faɗa bari
na bayyana maka surar ka da tufafin dake jikinka.
Nan take Aslaima ya shiga bayanin sura da tufafin Muhassin. Tana kammalawa mamaki ya
turnuƙe kowa kuma suka fahimci cewa Aslaima kallon haƙiƙa ta yi mishi ba labari ta ji ba.
Nan fa mamaki ya turnuƙe kowa domin tun da gimbiya ta makance koda aljani bata taɓa gani
ba, amma ga shi yanzu tana iya ganin bil'adama, shin mene ne ya sanya idanun nata iya jarumi
Muhassin suke gani? Ko kuwa ƙarfin sihirin shi ne ya sanya hakan?
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan.
Shi kuwa boka kaddad koda ya ji abin da gimbiya ta furta sai zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya
kama shi ainun, ya ce a ran shi shin ya aka yi gimbiya take iya ganin Muhassin bayan cewa na
wa'adin sihirin da na yiwa idanunta bai ƙare ba, haƙiƙa akwai lauje cikin naɗi, amsar tambayar
da ya kasa bawa kanshi kenan. Shi kuwa Jarumi Muhassin koda ya ji gimbiya ta ce tana iya ganin shi nan take ya fahimci cewa
matsalar aiki ne sihiri, domin kuwa da makanta da gaskiya ba zai yiwu ta iya ganin shi ba.
Ana cikin wannan hali ne ya lura cewa gimbiya na satar kallo shi wanda ke nuna alamun so da
ƙauna, nan take ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi a karo na farko ya ji wani abu ya ɗar su a ran
shi wata 'ya mace ta ƙayatar da shi.
Muhassin ya buɗi baki cikin murmushi mai taushi har fararen haƙoranshi suka bayyana ya dubi
gimbiya ya ce "Ya ma'abociyar kyawu ki yi sani cewa idan har zan yi maku rakiya a wannan
tafiya to akwai bana buƙatar wani lada face sharaɗi guda shine ke da mahaifinki za ku bayar da
gaskiya ga Ubangijina, ku daina bautar gumaka da dodanni har abada". Koda jin wannan batu sai gimbiya ta ja gwauron numfashi ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce
"Na amince da wannan sharaɗi naka, kuma na tabbata cewa Ubangijin da ya baka nasarar
tseratar da rayuwata daga sharrin zakanya zai baka nasara a wannan tafiya. Sai dai na manta
ban faɗa maka cewa a wannan tafiya muna da shugaba wato boka kaddad, kuma shi ne ya san

wajen da zamu samu abin da muka fito nema, saboda dukkan wani umarni muna karɓa ne
daga gare shi"
Koda gimbiya ta zo nan a zancen ta sai ta juya ta yi taku ɗaya, take kuyangi suka yi mata jagora
domin komawa zuwa sansanin da aka yada zango, take boka kaddad ya rufa masu baya
fuskarshi a murtuke har gyatsine take yi, dakaru na biye da shi jarumi Muhassin ne a ƙarshe,
'yar gajeriyar tafiya aka yi aka iso izuwa sansanin kowa ya kunna kai izuwa cikin tantinsa, shi
kuwa jarumi Muhassin sai ya koma gefe ya yi alwala ya haye bisa kan wani faffaɗan dutse ya
fuskanci alƙibila ya fara sallah.
Wannan shi ne abin da ya wakana da su boka kaddad akan hanyar su ta nemo maganin
makantar gimbiya Aslaima, wato tekun Baharul-imfal domin ɗauko ALLON TSAFI a cikin
masifaffen kada.

***
Lokacin da aka garƙame da azababban yaƙi tsakanin rundunar sarki Madsur da ta shugaban
'yan fashin duniya sadauki Fitinatul-Amir bisa jagorancin sadauki Huzlaif. Sai yaƙin ya zamo
abin tsoro kuma tashin hankali domin ɓangarorin biyu sun wanzu suna kaiwa juna sara da suka
cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA, nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, haniniyar
dawakai haɗe da ihu da kururuwar MAZAJE ta cika dodon kunne, sararin samaniya ta yi duhu
tamkar dare biyu ya haɗu waje guda,
Wohoho! Haƙiƙa maza sune maganin maza, idan ka ji an ce ga mugu na ɓarna bai haɗu da
mugu ba ne, kuma KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka sha JININ SADAUKAI a
artabun GOGA SHA FAMA, inda ace mutum yana wannan waje lokacin da sassan jikkunan
bil'adama ke shawagi a sama, JINI DA ƘASA suka cakuɗu waje guda, sai ya rantse cewa
YAKIN DUNIYA ne ya taso domin hatta dawakan abokan gaba hari suke kaiwa junun su.
A ɓangaren sadauki Huzlaif kuwa duk inda ya sanya a gaba sai dai ka ga abokan gaba suna
zubewa ƙasa matattu tamkar yana karkaɗe busassun ganyayyakin bishiya a lokacin hunturu.
Haƙiƙa Huzlaif ya cika SARKIN SADAUKAI domin da ace mutum zai ga yadda yake yaƙin babu
alamun gajiya a tare da shi, sai ya rantse cewa jikinshi na ƙarfe ne ba jini da tsoka ba, a wasu
lokutan har da ƙafa make abokan gaba yake yana sanarwa kan shi hanya.
A ɓangaren sarki Madsur kuwa ya zamto tamkar ANNOBA ƊARI tsakanin dakarun
Fitinatul-Amir duk inda ya sanya gaba sai ka ga gawarwaki na zubewa ƙasa, a wasu lokutan sai
ka ga ya taka kawunan abokan gaba ya sanya KAIFIN TAKOBI yana sare kafaɗunsu suna
zubewa ƙasa tamkar ruɓaɓɓiyar kabewa. Kai wasu lokutan ma badakare yake janyo wa daga
kan dokin shi ya take mishi wuya ya sheƙa barzahu, ko ya gabza mishi wawan naushi a wuya
ya jefar da gawarshi gefe guda.



BABI NA BIYAR



Lokacin da sarki Madsur da sadauki Huzlaif suka ga irin muguwar ɓarnar da suke yiwa junan
su, sai zukatansu suka kama tafarfasa tamkar za su ƙone, domin hakan sai kowannen su ya

ruga izuwa kan ɗan uwanshi yana mangare dakarun dake gaban shi domin samarwa da kan
shi hanya.
Lokacin da suka iso daf da juna sai suka taru juna aka ruguntsume da azababban yaƙi mai
matuƙar muni daban tsoro, suna artabun ne cikin zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban
kwatance, duk sa'adda makamansu suka haɗu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami
da ƙara mara daɗin saurare. Sai da GWARAZAN JARUMAN suka shafe tsawon rabin sa'a suna
wannan ɗauki ba daɗi har makamansu suka lalace suka yi jifa da su duka cire waɗansu sabbi a
jikkunansu, suka sake kacame da sabon artabu da ya fi na ɗazu tare da canza salon faɗan su.
Ana cikin wannan GUMURZU ne kowannen su ya kaiwa abokin gwamin shi hari a fuska, cikin
nasara suka yanki juna akan kumatu jini ya yi tsartuwa. Cikin zafin nama suka yagi wani baƙin
yanki a tufafinsu suka ɗaure raunin domin tsayar da jini, sannan suka ja da baya kamar taku
huɗu suka tsaya cak! Suna cirko-cirko suna haki tamkar waɗansu zakaru. A lokaci guda tamkar haɗin baki suka sake yin kukan kura suka afkawa juna, kaico! Hakika
KARON MAZA abin tsoro da tashin hankali, lokacin da jaruman biyu suka fara wannan sabon
artabu a karo na uku sai abin ya yi tsamari yazamana cewa a wannan lokaci sun yiwa junan su
miyagun raunuka jini na zuba a jikkunansu, ma'ana an yi KARE JINI BIRI JINI jiri na ɗibar su,
ana cikin wannan hali ne suka zube ƙasa magashiyan numfashin su na fita saman-sama.
Lokacin da tawagar rundunonin biyu suka ga halin da jagororin su ke ciki sai aka tsayar da yaƙi
suka ruga izuwa gare su, aka ɗauke su kowannen su ya durfafi sansanin sa.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin dakarun sarki Madsur da ta sadauki Huzlaif shugaban
tawagar dakarun sarkin 'yan fashin duniya.


Lokacin da ma'aji Kulairu ya durfafi ƙofar fita daga cikin gidan sarauta dakaru na take mashi
baya, bayan ya samu nasarar hallaka wannan hadimi mai ɗauke da sura irin ta waziri Yazid,
kuma ya yi umarni an shiga da sarki Nu'umanu izuwa turakarshi domin ba shi taimakon
gaggawa sakamakon sukar takobin da hadimin ya yi mishi. Sai suka ci-gaba da ratsa saƙo da lungu na gidan suka hallaka dakarun sumame. Lokacin
da suka shiga gari sai ƙarin waɗansu dakarun suka rufa masu baya, suna masu ƙwalla kabbara
da ƙarfi suka tari abokan gaba aka ruguntsume da azababban yaƙi.
Sa'adda mata,yara da tsofaffi suka ji gari ya kaure da kabbarar dakarun musulunci sai suka
shiga addu'a suna kai kukan su wajen Ubangijin Musulunci akan ya bawa MUJAHIDAI
RINJAYE. Al'amarin da ya jefa tsoro a zukatan dakarun sumame kenan.
Duk inda Kulairu ya sanya a gaba sai ka ga dakaru na zubewa ƙasa matattu tamkar yana
karkaɗe busassun ganyayyakin bishiya a lokacin hunturu.
A ɓangaren dabarun sumame kuwa duk inda waziri Yazid da sarki Rakibu suka sanya a
gaba sai dai ka ga dakarun musulunci na zube ƙasa, lokacin da waziri Yazid ya fahimci cewa
idan aka cigaba da wannan artabu a haka dakarun musulunci za su samu nasarar murƙushe
su, sai kawai ya shafi wani gurun tsafi a damtsenshi yana mai nuna sarki Rakibu da sarkin yaƙi
Lauzar da yatsanshi na hagu take suka ɓace ɓat! Tamkar ba su taɓa wanzuwa ba.
Sa'adda sa'a ɗaya ta shuɗe a dai-dai wannan lokaci ne dakarun musulunci suka samu
galaba akan dakarun sumame, nan fa gari ya kaure da koke-koken yara da mata, kaico! Komai
rashin imanin mutum idan ya ga yadda yara ke rungume da gawarwakin mahaifansu suna rusa
kuka dole ya kamu da matuƙar tausayin su, har ƙwalla ta cika masa idanu, babu abin da zai

ɗimauta mutum face irin mugun kisan da aka yiwa jama'a waɗansu an farke cikinsu tumbinsu
ya fito waje, wasu an sare kawunan su wasunsu ƙafafu da hannuwa abin babu kyawun gani.

***
Koda ficewar hadimi Masnur daga tantin sai sarki Lamsarul-Azlam ya runtse idanuwanshi ya
karanto waɗansu ɗalasimai, yana gama rufe bakinshi sai wani narkeken aljani ya bayyana a
gare shi, aljanin yakasance mummuna mai kwarjini da ban tsoro, yana da ƙwala-ƙwalan idanu
masu girma tamkar gwanda, hancinshi a takure yake kofofin sirara tamkar ba da su ne yake
shaƙar iska ba, bakinshi makeke ne mai kama da bakin rijiya, a tsakiyar kanshi yana da dauƙe
da wani ƙaho irin na ɓauna, gwiɓin hammatarshi yana ɗauke da waɗansu fuka-fukai guda huɗu
irin na jemage,
Hakika komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da wannan aljani dole ya ɗimauce.
Aljanin ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, sarki ya dube shi cikin kakkausar murya ya ce "yakai
Husubul-luzwar ka yi sani cewa bakomai ne ya sanya na kira nan ba sai domin ina so ka tafi
izuwa sansanin dakarun musulunci ka ɗauko mini sarki Rayyan a raye cikin ƙoshin lafiya, ka
kawo shi izuwa gare ni" Koda jin wannan batu sai Husubul-luzwar ya buɗi baki cikin kakkausar murya mai kama da
kukan jaki ya ce "An gama ya shugabana amma kar ka manta cewa akwai wani sirri da sarki
Rayyan da jama'ar shi ke amfani da shi wanda matukar ka kusance su sai komai naka ya
lalace, sannan kar ka manta cewa wannan shine aiki na ƙarshe da zan yi na samu 'yanci daga
ƘANGIN BAUTA a ƙarƙashin ka",
Koda jin wannan batu daga bakin Husubul-luzwar sai sarki Lamsarul-Azlam ya dube shi ya ce
"kar ka bawa maza kunya mana kaine fa ANNOBA ƊARI mai saukar da gajimaren musifa,
magajin GAWUTACCIYA kake mai shanye JININ SADAUKAI, SARKIN SADAUKAI kake duk
wanda ya ja da kai zai faɗa TURBAR AJALI" Lokacin da sarki ya zo nan a kirarin sai Husubul-luzwar ya kama tsuma yana kyarma, ganin
jikinshi ya mimmiƙe ya buɗi ya ce "kwantar da hankalinka ya mai duniya na rantse da gemun
kakana boka Luzwar sai na kawo maka sarki Rayyan cikin ƙoshin lafiya".
Yana gama faɗin hakan ya bugi ƙasa da hannunshi ɗaya ya ɓace ɓat! Tamkar bai taɓa
wanzuwa ba, kawai sai sarki Lamsarul-Azlam ya bushe da dariyar mugunta sai da ya yi ta ishe
shi sannan ya ƙwallawa sarkin yaƙin shi kira bayan ya bayyana gare shi ya zube ƙasa ya
kwashi gaisuwa sai ya dube shi ya ce "ya dirkar birnin Darul-Ashmar ina so ka tafi izuwa
masarauta ka ƙaro mana dakarun yaƙi mafiya ƙwarewa a harbin kibiya ka tabbatar ka sanya a
cikin duhuwar bishiyun dajin dake dai-dai wajen da zamu fafatawa a da abokan gaba, za su
amfani ne a lokacin da za mu gwabza domin za su yiwa abokan gaba MAMAYAR BAZATO".
Koda jin wannan umarni sai sarkin yaƙi ya ce "an gama ya shugabana".
Yana gama faɗin hakan ya juya ya fice daga cikin tantin ya kama dokinshi ya haye ya sakar
mishi linzami ya sukwane shi ya durfafi hanyar fita daga sassanin.
Wannan shi ne abin da ya wakana a sansanin sarki Lamsarul-Azlam.




BABI NA SHIDA

Koda ɓacewar makiyar sai sadauki Fitinatul-Amir ya taƙarƙare ya kurma wawan ihu wanda
ya ɗimauta duk wata halitta dake fadar, jama'a suka shiga guje-guje gami da ifice-ificen tsira da
rayuka, domin rabon da Fitinatul-Amir ya yi wannan kururuwa yau tsawon shekaru ashirin tun
ranar mutuwar Mahaifiyarshi. Sai da ya shafe tsawon daƙiƙa talatin a cikin wannan hali sannan daga bisani ya murtuke fuska
tamkar an aiko mishi da SAƙON MUTUWA ya ɗauko madaidaicin madubin tsafi a cikin aljihun
rigarshi ya shafe shi da hannunshi na hagu yana mai runtse idanuwanshi gami da karanta
waɗansu ɗalasiman tsafi, yana gama rufe bakinshi sai ga taswirar mikiyar ta bayyana a sararin
samaniya ɗauke da Rusayyat, Usaiba mai hatimin takobi tare da Hairat, tana tsala gudu tamkar
giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Koda ganin wannan al'amari sai kawai ya ƙwallawa 'yan majalisar shi kira cikin hanzari suka fito
daga maɓuyar su jikkunansu na ƙyarma! Kaifin ɗayan su ya furta wani abu ya nuna su da ɗan
yatsanshi na hagu nan take shi da su suka bayyana akan wata jibgegiyar mikiya mai kwarjini
daban tsoro, cikin hanzari mikiyar ta tashi zuwa sama ta ratsa rufin fadar ta ɓace ɓat! a sararin
samaniya.

***
Al'amarin wannan mikiya kuwa da ta ɗauki Rusayyat uwar shugaban 'yan fashin duniya,
yaro Usaiba tare 'yar uwarshi Hairat, sai ta yi wanzu tana ratsa giza-gizai babu sassauci. Duk
wannan tafiya da ake yi su Usaiba ba su san halin da ake ciki ba domin suna cikin halin suma
su duka ukun. Lokacin da sa'a ɗaya ta shuɗe a wannan lokaci ne ta iso wani ƙasaitaccen daji domin haka sai
kawai ta saki fuka-fukanta ta yi ƙasa luhhhh! Ta sauka a turba a daf da wata ƙorama mai ɗauke
da ruwa garai-garai, kawai sai ta gicciya gadon bayanta ta sauke su yaro Usaiba, sannan ta
kafa bakinta a ƙoromar ta guntsi ruwa ta fesa masu, Rusayyat ce ta fara farfaɗowa ta hanyar
buɗe idanuwanta, sannan yaro Usaiba yana mai jan dogon gwauron numfashi, Hairat ce a
ƙarshe tana mai motsa ƙafafuwanta, nan take kowannen su ya yunƙura domin ya miƙe zauna
amma sai hakan ya gagara bisa dole kowanne ya haƙura zukatansu na bugawa cike da
matuƙar tsoro da firgici.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai aka ji wani abu mai nauyi ya sauka a daf da hanyar
shigowa dajin, ba wani ba ne face sadauki Fitinatul-Amir tare da 'yan majalisar shi guda sha
biyu zaune a bisa kan wannan mikiya.
Da yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login