Showing 15001 words to 18000 words out of 23849 words
Chapter 6 - KARYA DA GASKIYA Cigaban Tafarkin Tsira Rubuta littafin Mansur Usman Sufi .pdf
ya zaburi
dokinshi da nufin ya farma waziri, amma sai kulairu ya dakatar da shi yana mai cewa shi ne ya
kamata ya tare shi, yana faɗin hakan ya zare takobi ya yi ɗauki kan shi, shi kuma sarkin fada
sai ya tari sarkin yaƙi, magatarda ya tari sarki Rakibu. Su Kulairu suna ƙwala kabbara da ƙarfi, bisa mamaki sai suka ji su waziri suna kabbarar, kaico!
Tir da aikin fasiƙai.
Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da masifaffan yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro
gami da tashin hankali.
Bangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna SARA DA SUKA cikin matuƙar KARFIN DAMTSE
JURIYA DA BAJINTA irin ta MAZAN JIYA.
Ƙarar karafniyar makaman yaƙi ta cika dodon kunne, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, tamkar
DARE UKU ake yi, dawakai suka dinga haniniya suna zubar da mahayan su, sassan jikkunan
bil'adama suka dinga shawagi a sararin samaniya.
Haƙiƙa yaƙi abin tsoro kuma tashin hankali wanda bai san shi ba shi ne yake fatan zuwan
shi.
Cikin ƙanƙanin lokaci dakarun kowanne ɓangare suka zamto tamkar GOBARA DAGA KOGI
suna ƙuntatawa juna daga nau'ikan ANNOBA DARI.
Kashe gari tunda duku-dukun safiya dakarun musulunci da na kafurai suka yi sahu-sahu a
lokacin da hantsi ya ɗaga. kallo ɗaya mutum zai yiwa ɓangarorin biyu ya fahimci cewa kowanne
ya fito ne da shirin ko a mutu ko ayi rai.
Sarki Rayyan, gimbiya Nuwairat da sarkin yaki sune akan gaba a TAWAGAR MUSULUNCI
sanye cikin shigar fararen sulken yaƙi tun daga ƙasa har sama, hatta dawakansu fararen ne sol!
Sarki Rayyan ya ɗaura farin rawani mai ratsin kore.
A can ayarin kafurai kuwa Sarki Lamsarul-Azlam sarkin yaƙinshi tare da waziri ne akan gaba
sanye cikin baƙaƙen sulken yaƙi da dawakai.
A zahiri idan mutum ya ƙare wa rundunonin biyu kallo zai fahimci cewa dakarun kafurai sun
ninka musulunci yawa sau goma, ana cikin wannan hali ne kwatsam! Nazari babu tsammani sai
dakarun musulunci suka ji ana yi masu ruwan kibbbau ta kowacce kusurwa gabas, yamma,
kudu da arewa cikin hanzari aka sanya garkuwoyi, amma duk da haka sai dakaru da dama suka
yi shahada saboda matuƙar yawan kibbbau ɗin.
A lokaci guda tamkar ɗaukewar ruwan sama aka daina harbo su.
Har wasu daga cikin dakarun sun yunƙura da nufin su afkawa kafirai sai gimbiya Nuwairat ta yi
masu nuni da su ja da baya kamar taku goma.
Da ganin hakan sai kafirai suka suka ruga izuwa kan musulmai suna ihu da kururuwa mai
firgitarwa domin suna ganin cewa Musulmi sun ji tsoro ne.
Kaico! Abin da arna ba su sani ba shine abin da masu iya magana ne ke shirin faruwa na cewa.
Ja da baya ga rago ba tsoro ba ne salon faɗa ne. Kuma haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu.
Lokacin da ya rage saura taku goma tsakani sai dakarun kafurai suka dinga faɗa wa a cikin
miyagun tarkuna suna sheƙawa barzahu. Kafin su farga fiye da mutum dubu goma sun zube
ƙasa matattu. Koda musulumi suka ga yadda maƙiya Allah ke wulaƙanta sai suka cika da
matuƙar farin ciki Su dai waɗannan tarkuna an binne su ne tun a daren jiya.
Lokacin da sarki Lamsarul-Azlam ya ga yadda jama'arshi suke hallaka sai ya cika da matuƙar
takaici da baƙin ciki, kawai sai ya dako wawan tsalle sama daga kan dokin yana mai zare
zabgegiyar takobi a gadon bayanshi tamkar yana ɗauke da fuka-fukai ya dinga shawagi a sama
yana sare kawunan dakarun musulunci. Tamkar haɗin baki a lokaci guda tawagar kowanne ɓangare suka yi ɗauki izuwa kan juna,
musulmi na kabbara kafirai na ihu da kururuwar banza. Ana haɗuwa aka ruguntsume da
azababban yaƙi mai matuƙar muni da tashin hankali.
Wannan shi ne abin da ya wakana tsakanin sarki Rayyan ma'abocin addinin Musulunci da sarki
Lamsarul-Azlam.
A can birnin Zainul-Ansar kuwa bayan ficewar dakarun musulunci izuwa filin artabu sai baƙi
ɗaya mutanen birnin maza da mata yara da manya suka ajiye aiyukansu suka duƙufa addu'a
masu karatun Alkur'ani nayi masu salati ga fiyayyen halitta (S'A'W) nayi. Ƙananan yara kuwa
suna istigfari domin riƙon Allah akan ya bawa tawagar musulunci nasara a wannan yaƙi ya
kuma tashi kafaɗun sarki Nu'umanu.
Wannan shi ne abin da ya wakana a cikin birnin Zainul-Ansar.
Sa'adda da wannan shirgegiyar halitta ta taso daga ƙarƙashin tekun Baharul-imfal ta daki
kwale-kwalen su boka kaddad ya dare gida biyu suka tsunduma izuwa cikin tekun, sai
kowannen su ya shiga yin iyo yana tasowa sama domin ya ga halittar da ta kawo masu farmaki.
Koda aka yi arba da halittar sai kowa ya cika da matuƙar mamaki da firgici, ba wani ba ne
halittar ba face wani narkeken namijin kada, kadan yakasance ƙato mai tsawon tsiya gami da
kwarjini muni da ban tsoro, yana da zabga-zabgan jela guda biyu, yana da waɗansu
wargatsattsun haƙora masu fasali da KAIFI DA TSINI, idanunshi jajaye ne tamkar garwashin
wuta, gadon bayan kadan ya kasance mai gurji-gurji tamkar duwatsu aka jera mashi, kallo ɗaya
za ka yi masa ka tabbatar da cewa abu ne mai matuƙar wahala a samu KAIFIN TAKOBI ya yi
tasiri akan shi.
Koda kadan ya ga cewa ya samu nasarar tarwatsa jirgin ruwan sai kawai ya yunƙura izuwa
kan su yana wani irin kuka mai ban tsoro.
Koda ganin hakan sai kowa ya zare makamin shi ya afka mashi. aka ruguntsume da azababban
yaƙi.
Sai yazamana cewa a duk sa'adda suka sari jikin kadan sai su ji tamkar dutse suka sara ko
gezau bai yi ba.
Shi kuwa ya wanzu yana kai masu hari da jela da haƙora gami da faratanshi, kuma duk inda ya
kai FARMAKI sai ya salwantar da ran ɗaya daga hadimai.
Shi kansa boka kaddad da aljani Ramsisul-Ayyam wankin hula yana neman kai su dare.
Wani abu da ya basu mamaki shine gimbiya Aslaima na tsaye a gefe guda amma kadan ya
kasa afka mata. Abin da ba su sani ba shine a halin yanzu gimbiya ta musulunta domin kadan
ba zai iya cutar da ita ba.
Shi kuwa jarumi Muhassin yana tsaye a gefe guda baya kai hari sai idan kadan ya kawo
masa MAMAYAR BAZATO.
Kaico! Haƙiƙa tashin hankali ba a sa maka rana, iya tsawon wanzuwar wannan teku halittun
dake ciki basu taɓa ganin tashin hankali tamkar na yau ba, saboda yadda tekun ke yin
famjam-famjam sai ka rantse cewa YAKIN DUNIYA ne ya taso.
Kafin shudewar daƙiƙa ɗari kadan ya hallaka gaba ɗaya hadimai da dakarun rakiya kuma ya
yunƙura izuwa kan su boka kaddad a dai-dai lokacin da ya zamana cewa basu iya mayar da
martani sai dai ƙoƙarin kare kansu.
Koda Muhassin ya hango abin da ke shirin faruwa sai kawai ya ƙwala kabbara da ƙarfi sai
ga shi ya taso izuwa saman tekun ya ruga izuwa kan kadan yana takawa da ƙafafuwan shi
tamkar yana tafiya a turba, sannan ya daka tsalle tamkar an harbo shi daga cikin baka ya dira a
gadon bayan kadan ya shiga zabga mashi sara da takobin shi. Haƙiƙa! JARUMTAKA baiwa ce daga Ubangiji dukiya da mulki basu bayar da ita sai dai
tsananin rabo.
Nan fa boka kaddad, Ramsisul-Ayyam suka cika da matuƙar mamaki domin ko da a tarihi basu
taɓa ganin jarumi mai sadaukantakar Muhassin ba.
Ana cikin wannan fafata wa ne kadan ya mako Muhassin da jelar shi ya faɗo ƙasa saboda da
ƙarfin makewar sai ya yi nutso izuwa ƙasan tekun ya ɓace ɓat!.
Kawai sai kadan ya yunƙura kan gimbiya Aslaima ya wangame bakinshi domin ya laƙume ta ya
yi loma ɗaya da ita.
BABI NA SHA UKU
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai a kaga jarumi Muhassin ya yi fitar burgu daga
ƙarƙashin tekun Baharul-imfal tamkar an janyo shi da ƙugiya yana mai ƙwala kabbara ya sauka
akan ƙoƙon kan kadan ya zabga mashi naushi a haƙoranshi. Saboda ƙarfin naushin take haƙora
uku suka yi fitar burgu daga cikin bakin jini ya yi tsartuwa. Ya yin da kadan ya ga haƙoranshi sun zube ƙasa sai ya fusata ainun ya kaiwa jarumi
Muhassin wawan hari da nufin ya taune shi a baki, amma sai Muhassin ya wurƙila ya zame wa
harin.
Kawai sai kadan ya takarƙare ya kurma wawan ihu ya afkawa Muhassin a lokacin da ya
suɓuto ƙasa daga kan shi, bisa mamaki sai su gimbiya suka ga Muhassin yana tsaye bisa
diga-diganshi tamkar yana tsaye bisa tsanɗauri ba saman ruwa ba.
Nan take suka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro, Muhassin ya wanzu
yana yakin cikin JURIYA DA BAJINTA.
Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya ana wannan baƙin artabu, nan fa ya zamana cewa tekun ta
hautsine tamkar annobar GOBARA DAGA KOGI ce ta bayyana ga halittun tekun, ana cikin
wannan fafatawa ne Muhassin ya shiga taimakon Ubangiji yana yiwa annabin shi salati, kawai
sai ya sanya hannayenshi biyu ya shiga ɓara bakin kadan da dukkan ƙarfin shi yana kammala
hakan ya yi jira da gawar shi gefe.
Wohoho! Haƙiƙa JARUMTAKA baiwa ce daga Ubangiji, komai hassadar mutum idan ya ga
wannan BAJINTA da Muhassin ya yi dole ne ya jinjina mishi ya tabbatar da cewa ya cika
GWARZON MAYAKI kuma MAGOGIN KARFE.
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa Aljani Ramsisul-Ayyam da boka kaddad kai kenan domin
koda a tarihi basu taɓa jin gwarzo mai SADAUKANTAKA tamakar Muhassin ba.
"Haƙiƙa kowa ne Ubangijin Muhassin ya cancanta a bauta mashi domin ya zartar da abin
saboda kaddad ya gaza a matsayin shi ya mashahurin boka";
Ramsisul-Ayyam ya yi wannan furuci a ranshi batare da bayyana wani ya ji ba.
Gimbiya Aslaima kuwa nan take ta ji ƙarfin imani da ubangijin halitta ya cika zuciyarta,
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka ga boka kaddad ya ɓace ɓat an neme shi sama ko
ƙasa an rasa.
Al'amarin da ya yi matuƙar ba Muhassin, Ramsisul-Ayyam da Aslaima mamaki kenan.
Daga can sai aka gan shi ya bayyana a saman tekun yana tsaye sanye cikin matsananciyar
shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro a hannunshi na hagu yana riƙe da wani dogon
mashi mai baki biyu, fuskarshi a murtuke babu annuri tamkar an watsa mashi garwashin wuta
akan ta, aka fara kallon-kallo tsakanin shi da Muhassin, daga can sai taƙarƙare ya bushe da
dariyar mugunta mai kama da kukan jaki daga can ya haɗe rai cikin kakkausar murya mai kama
da haushin kare ya ce "ya kai Muhassin ka yi sani cewa haƙiƙa ka tafka babban kuskure da ka
shiga soyayya da wacce zata zamo mata a gare ni bayan na mallaki rigar tsafi, yanzu ba tare
da ɓata lokaci ba zan aike da ruhinka izuwa barzahu, sannan na farke cikin wannan kada na
ciro ALLON TSAFI wanda da shine zan samu nasarar shiga kogon dutse na ɗauko hular
LAUHUL-SIHIR, domin cika muradina na mulkar duniya baki ɗaya. Ina mai rantsuwa da boka
kuddamul-Barzahu mai mallaki hular LAUHUL-SIHIR sai naga bayan ka.
Kafin kaddad ya gama rufe bakinshi Muhassin ya tari numfashin shi yana kai daka mashi
tsawa ya ce "ƙaryar ka ta sha ƙarya ya kai la'anannen Allah ka yi sani cewa ba za ka taɓa
cimma mugun nufin ka domin har kullum KARYA DA GASKIYA ba su taɓa kasancewa a haɗe
ba sai gaskiya ta ji RINJAYE kuma abin da baka sani ba shine tuni gimbiya Aslaima ta yi imani
da Allah yar uwata musulma a halin yanzu, kuma tun farkon wannan tafiya idanuwanta suka
warke daga shirin da ka yi mata domin cimma buƙatar ka. Ka sani cewa da yardar Allah ba zaka
ci amanar mahaifinta ba, domin masu iya magana na cewa RAMIN KARYA kurarre ne".
Koda jin wannan batu daga bakin Muhassin sai kaddad ya takarƙare ya kurma wawan ihun
baƙin ciki ya ɗaga mashin shi izuwa sama ta ruga izuwa kan Muhassin. Koda ganin hakan sai
Muhassin ya zare takobin shi ya ruga gare shi domin tarar juna yana kabbara.
Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni daban tsoro.
Jaruman biyu suka wanzu suna kaiwa juna SARA DA SUKA cikin matuƙar zafin nama JURIYA
DA BAJINTA irin ta GWARAZAN JIYA.
Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA sai SADAUKAN DAUKAR FANSA da suka saba
GWAGWARMAYA a SANSANIN AZABA.
Idan juriya da naci a yaƙi suka haɗu waje guda dole ne tsagwaron KARFIN DAMTSE su yi aiki,
kuma idan gwani da gwani suka haɗu a yaƙi dole artabu ya zamto abun tsoro da tashin hankali.
Wohoho! Nan fa Taurarin biyu suka wanzu suna bawa hammta iska, duk sa'adda makamai
suka haɗu da juna sai kaga tartsin wuta ya tashi gami da wata farar walƙiya.
Sai da sa'a ɗaya ta shuɗe ana wannan fafatawa babu nasara ga kowanne ɓangare.
Sa'adda boka kaddad ya ga cewa ya gaza nasara akan Muhassin sai ya shiga aiki da shiri, inda
ya dinga tura mashi musibu idan ya tura masa wuta da zarar ta doshi inda Muhassin yake sai
kaga ta zamto hayaƙi. Idan ya tura kibbbau, da sun isa gare shi sai su ɗige a ƙasa su zama
ruwa. Koda kaddad ya fahimci cewa wankin hula kai shi dare sai kawai ya rikiɗa izuwa mutum
huɗu, masu matuƙar kama da shi tamkar an tsara kara, komai kallon ƙurillar mutum ba zai iya
tantance boka kaddad na gaskiya ba.
A lokaci guda mutanen huɗu suka yiwa Muhassin rubdugu domin yi mashi farat ɗaya, suka
shiga kai mashi sara ta sama da ƙasa. Amma saboda juriya da ƙarfin addu'a sai Muhassin ya
zamto tamkar shaiɗani a tsakanin su yana kare hare-haren su kai kace wata na'ura ce ke
sarrafa shi.
Duk wannan artabu da ake yi gimbiya Aslaima da Ramsisul-Ayyam suna kallo cike da
matuƙar mamaki.
Abu biyu ya bawa Ramsisul-Ayyam mamaki na farko shine yadda aka yi mutanen huɗu suka
kasa hallaka Muhassin, na biyu kuwa shine yadda Muhassin ke iya tsallake hare-haren.
Ita kuwa Aslaima tana mamaki ne bisa ganin yadda Ubangijin talikai ke zartar da ikon shi a
wannan fafatawa.
Lokacin da sa'a ɗaya da rabi ta shuɗe nan take mutanen huɗu suka fara samun yiwa Muhassin
rauni da masun dake hannayensu, har ya zamana cewa ba ya iya mayar da martani, ana cikin
wannan hali ne suka sanya tsinin masun suka soka mashi a gadon bayan shi, nan take
Muhassin ya ƙwala kabbara saboda raɗaɗi da zurfin da ya ji ya sulale ƙasa magashiyan. Koda samun wannan gagarumar nasara sai mutanen huɗu suka cure waje guda suka rikiɗa
izuwa wata ƙatuwar mucijiya mai ɗauke da kawuna guda arba'in da ɗaya, kowanne kai ya kai
girman na raƙumi.
Komai dakewar zuciyar jarumi idan ya yi arba da halittar dole ne ya ɗimauce.
Kawai sai mucijiyar ta sanya jelarta ta kanannaɗe Muhassin kuma ta buɗe dukkan bakunanta
guda arba'in da ɗaya tana zurfar da dafi domin ta kaftawa jarumi Muhassin sara a sassan
jikinshi, duk inda dafin na ya zuba a akan ruwa sai wuta ta kama.
BABI NA SHA HUƊU
Lokacin da yaro usaiba mai hatimin takobi ya kunna kai izuwa cikin daji babu fargaba a tattare
da shi hannunshi riƙe da sanda domin ya farautowa su shalmirat abin da za su yi kalaci. Sai ya
wanzu yana ratsa hamada, duwatsu gami da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu,ba tare da ya ji koda
kukan tsuntsu ba ko kuma ya ga wani abu mai cutarwa ba. Al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan kuma ya ɗaure mashi kai gami da dugunzuma
hankalin shi.
Yana cikin wannan hali ne ya hango wani kyakkyawar barewa ta kafa kai a bakin wata
ƙorama tana shan ruwan cikinta.
Cikin matuƙar farin ciki maral musaltuwa ya durfafi inda take yana sanɗa domin ya cimma ta,
tamkar barewar ta ji motsin shi kawai sai ta ranta a na kare ya ruga izuwa cikin daji. Cikin zafin
nama Usaiba ya rufa mata baya suka kasa tsere.
Tsawon daƙiƙa ɗari suna wasa diga-digansu ba tare da ɗayansu ya cimma abokin faɗan shi ba.
Lokacin da ya zamana cewa tazarar dake tsakanin su bata huce taku goma ba, kwatsam!
Bazato babu tsammani sai Usaiba ya ga wannan barewa ya rikiɗa izuwa surar wata
mummunan tsohuwar aljana.
Saboda matuƙar firgici bai san sa'adda ya faɗi ƙasa ba jikinshi yana tsuma da kyar ma, koda ya
yunƙura domin ya miƙe tsaye sai ya ji ya kasa koda motsa gaɓarshi.
Koda aljanar ta ga halin da Usaiba yake ciki sai ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta,
sannan ta buɗe baki cikin wata irin kakkausar murya mai kama da haushin kare ta ce "haƙiƙa
yau ni ce na fi kowa sa'a da nasara a duniya domin gashi na tsinci dami a kala, wannan shine
masu iya magana ke cewa rabon kwaɗo baya hawa sama, kuma idan rabo ya ranste to ko kana
barci sai arzikin ka ya same ka. A yau ne zan yanka yaro Usaiba na shanye jininshi, domin na
cimma burina na zamtowa GAWURTACCIYA uwar hatsabiban duniya";
Koda mummunan aljanar ta zo nan azancen ta sai ta busawa Usaiba wani farin hayaƙi daga
bakinta ya shaƙa take ya faɗi ƙasa yana sharar barci.
Cikin matuƙar farin ciki ta sanya hannayenta biyu ta ɗauki Usaiba ta yunƙura izuwa sararin
samaniya tana mai bushewa da