Showing 9001 words to 12000 words out of 23849 words
Chapter 4 - KARYA DA GASKIYA Cigaban Tafarkin Tsira Rubuta littafin Mansur Usman Sufi .pdf
matuƙar mamakin yadda aka yi ya iya kare
hare-haren MAZAJEN tare da mayar da martani, bayan cewa shi koda wuƙar yankan lemo bai
iya riƙewa ba.
Lokacin da Jaruman suka shafe tsawon rabin sa'a suna wannan ɗauki-ba-daɗi, sai suka tashi
hankalin duk wata halitta dake dajin bishiyun suka dinga karairaye wa suna faɗuwa ƙasa,
tsuntsaye kuwa suna canza sheƙarsu domin TSIRA DA RAYUKA, inda ace mutum yana tsaye a
wannan waje zai ga yadda tsirarun jaruman suka tashi hankalin dajin sai ya rantse rundunar
ifritai ne ke bawa hammata iska.
Ana cikin wannan fafatawa ne Fitinatul-Amir da jaruma Shalmirat suka kai wa juna wawan sara
a kafaɗa, cikin zafin nama suka zillewa saran, sannan Fitinatul-Amir ya kaiwa Shalmirat wani
domin ya datse mata wuya. Cikin baƙin zafin nama ta sanya takobi ta kare amma saboda ƙarfin
saran ya yi tsanani sai da Shalmirat ta durƙushe ƙasa, kafin ta yi wani yunƙuri Fitinatul-Amir ya
sanya ƙotar takobinshi ya maka mata a goshinta da dukkan ƙarfin shi.
Saboda ƙarfin dukan sai da Shalmirat ta yi katantanwa sau biyu a ƙasa, sannan ta faɗi tim!
Tana mai tsandara ihu lokacin da jini ke zuba daga gashinta.
BABI NA TARA
Cikin matuƙar farin ciki Fitinatul-Amir ya durfafi inda Shalmirat take kwance hannunshi riƙe
da takobi tsirara da nufin datse mata wuya, ya yin da ya rage saura kamar taku ɗaya tsakanin
su sai kawai ya ga Shalmirat ta miƙe tsaye zumbur ta shammace shi ta gabza mashi wawan
naushi a fuska sai ga jini na zuba a hancinshi, cikin zafin nama ta ragi wani yanki a tufafinta ta
ɗaure goshinta ta tsayar da jinin dake zuba.
Koda Fitinatul-Amir ya ga jini na zuba a hancinshi sai ya jifa da takobinshi kuma ya taƙarƙare ya
kurma wawan ihu, kawai sai ya afkawa Shalmirat da dukkan ƙarfin shi yana kai mata naushi da
bugu hannu da ƙafa, ita kuwa ta wanzu tana zillewa hare-haren cikin matuƙar zafin nama
JURIYA DA BAJINTA. A ɓangaren yaro Usaiba, Rusayyat da 'yan majalisa kuwa, dukkanin su sun wanzu suna
kaiwa juna hare-hare cikin zafin nama gami da MUGUN TANADI! Inda yan majalisar ke kai
masu hari da makamansu su kuwa da ƘARFIN DAMTSE. Ana cikin wannan BAƘIN ARTABU ne
wani garjejen ƙato mai ƙirar samudawan farko a cikin 'yan majalisar ya kaiwa Usaiba wani
bahagon sara da gatarinshi a kafaɗa da nufin tsarga shi gida biyu, cikin zafin nama baban
al'ajabi ya kaucewa harin tare da ka tsalle sama ya kai mashi wawan naushi a fuska, saboda
matuƙar ƙarfin naushin sai da kan bafaden ya gwaru da wata ƙatuwar bishiya ya tsage jini ya yi
feshi, kuma ya sulale ƙasa rikica! matacce ko shurawa bai yi ba.
Sa'adda sauran 'yan majalisar suka yi arba da gawar ɗan uwansu sai mamaki da al'ajabi suka
turnuƙe zukatansu, shin ta ya aka yi yaro Usaiba ya samu salon yaƙin da ya kashe bafade
Nafiyaz.
Amsar tambayar da suka kasa bawa kansu kenan, abin da ya fusata su shine ta ya za a ce yaro
ƙarami ya zame masu tamkar ANNOBA ƊARI sun rasa yadda za su yi da shi, a matsayin su na
GWARAZAN JIYA da suka saba yin KARON MAZA a FILIN ARTABU, wannan shi masu iya
magana ke cewa ɗan hakin da ka raina shi ke tsone maka idanu.
Lokacin da suka zo dai-dai nan a tunanin su sai sake ZAGE DAMTSE wajen kai wa su
Rusayyat miyagun hare-hare fiye da ɗazu.
Abinda ba su sani ba shine babu wani makami da zai yi tasiri akan Usaiba face takobin
SAIFUL-ZAYYAD dake zanen hatimin ta yake a gadon bayanshi. Ita kuwa jaruma Rusayyat
abinda ya sanya makaman basu tasiri akan ta shine saboda sinadarin tsafin dake tare da su ya
fito ne daga tushe ɗaya wato daga Fitinatul-Amir. Kafin cikar sa'a ɗaya yaro Usaiba ya samu nasarar hallaka mutum uku daga cikin 'yan majalisar
ta hanyar karya masu wuya, nan fa 'yan majalisar suka fara amfani da ƙarfin sihirin tsafin su
wajen cutar da shi amma ba ta sauya zani ba jiya i yau.
A ɓangaren Fitinatul-Amir da Shalmirat kuwa labari ya sha bamban, domin masu iya
magana na cewa idan rawa ta canza dole ne rawa ta canza, domin a halin yanzu Fitinatul-Amir
yana yaƙar Shalmirat da tsagwaron ƘARFIN DAMTSE.
Domin kuwa a halin yanzu duk sa'adda ya gabza Shalmirat naushi a jikinta sai jini ya taru wajen
ya yi tsami, a wasu lokutan idan da ƙafa ya dake ta sai kaga ta yi sama tamkar an janye ta da
ƙugiya sannan daga bisani ta faɗo ƙasa tim! Amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta
JARUMAR ASALI sai ta miƙe tsaye cike da jarumataka, ta ci-gaba da kai hare-haren. Haƙiƙa
masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce duk wanda ya riga ka kwana dole ne ya riga ka
tashi, kafin shuɗewar rabin sa'a Fitinatul-Amir ya haɗa wa Shalmirat jini da majina fuskantarta
tayi luhu-luhu.
Inda ba don Shalmirat na da juriya da nacin tsiya ba da tuni Fitinatul-Amir ya yi mat mata farat
ɗaya. Ana cikin wannan hali ne Fitinatul-Amir ya gabzawa Shalmirat naushi a maƙogaro ta faɗi
ƙasa wanwar, kawai sai ya tsugunna a gaban ta ya taffo wuyanta yana mai yi mata murmushin
mugunta, sannan ya ɗora hannunshi a kan goshinta da nufin ya murɗe mata wuya.
***
Lokacin da aljani Husubul-luzwar ya ɓace ɓat! Daga tantin sarki Lamsarul-Azlam, bai
bayyana ako ina ba sai a sansanin musulunci, nan take ya tarad da dakaru na ta kai komo
domin tabbatar da cikekken tsaro, kuma ko ina a haskake yake da fitilun ice ta yadda koda
allura ce ta faɗi ƙasa da zarar muutuiya duba zai ganta. Nan fa Husubul-luzwar ya baza idanu
yana nazarin wajen. Nan take ya fahimci cewa babu wata hanya da mutum zai ƙetare face an
gan shi, domin haka sai kawai karanto waɗansu ɗalasimai tsafi, nan take surar shi ta canza
Izuwa dakarun wajen shanye cikin sulken mai hatimin musulunci.
Koda kammala hakan sai ya durfafi sansanin batare da wata shakka ba, duk inda ya kutsa sai
kaga dakarun na risina mashi, al'amarin da ya yi matuƙar bashi mamaki kenan, abin da bai sani
ba shine sulken yaƙin da ke sanye a jikinshi iri ɗaya ne sak da na sarkin yaƙi, sai dai abin da ya
bawa dakarun mamaki shine lokacin da sarkin yaƙi zai fita daga sansanin ya fita bisa ingarman
doki fari, amma yanzu ya dawo a ƙafa, amma bisa ganin cewa shi shugaba ne mai cikekken iko
babu wanda ya ce uffan.
Haka dai ya cigaba da ratsa saƙo da lungu na sansanin, yana cikin tafiyar ne ya hango tantin
sarki Rayyan kuma ya zamana tazarar dake tsakanin su bata huce taku goma ba ga waɗansu
zaratan dakaru ne tsaye a ƙofar tantin ɗauke da miyagun makamai, nan take ya ji zuciyarshi ta
buga da ƙarfi tsoro ya kama shi, har ya yanke shawarar ya ɓace, amma sai wata zuciyar ta ce
da shi ai matsoraci ba ya zama gwani, domin haka kawai ka kusance su.
Koda gama yanke shawarar hakan sai ya cigaba da tafiya har ya iso bakin tantin, dakarun dake
gadi suka risina a gare shi sannan suka buɗe mashi ƙofa ya kunna kai Izuwa ciki, inda ace
dakarun dake gadin za su shiga zuciyar Husubul-luzwar suga yadda take bugawa da sauri
saboda matuƙar tsoro sai su yi tsammanin zuciyarshi zata buga. Lokacin da ya shiga sai ya tarad da sarki Rayyan kwance bisa gado yana sharar barci a gefe
guda kuwa an ajiye wani kofin a zurfa mai ɗauke da ruwan magani, hakan kenan ya tabbatar da
cewa sarki ya sha magani ne domin huce gajiyar dake tare da shi, koda gama tunanin hakan
sai ya matsa daf da gadon da yake kwance ya buɗe bakinshi take wani baƙin hayaƙi ya fita
daga ciki ya durfafi fuskar sarki Rayyan.
ZAINUL-ANSAR
Sarki Nu'umanu na kwance bisa kan gadonshi cikin mawuyacin hali, uwar gidanshi Lawisat
na zaune a gefen shi na dama tana yi mashi fifita hawaye na zuba daga idanuwanta, suna cikin
wannan hali ne sai aka yi sallama a ƙofar shigowa, saboda haka sai Lawisat ta sassauta kukan
ta kuma ta yi gyaran murya tana mai nuna bayar da umurnin shigowa. Jim kaɗan sai ga ma'aji Kulairu ya shigo turakar shirye cikin gagarumar shigar yaƙi, ya yin da
yazamana tazarar dake tsakanin su bata huce taku uku ba sai ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa,
kana ya sunkuiyar da kanshi ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa sannan ya buɗe baki ya
ya gyaran murya ya ce " ya shugabana Ubangiji ya baka lafiya kuwa ya tashi kafaɗunka don
haske zatinshi. Bayan haka kuma ya shugabana binciken da muka yi ya tabbatar mana da
cewa waziri Yazid da sarkin yaƙi ne suka ci amanar ka ta hanyar haɗa kai da sarki Rakibu,
kuma a daren yau ne za mu afka masu domin RAMUWAR GAYYA.
Koda jin wannan batu daga bakin Kulairu sai sarki Nu'umanu ya buɗi baki da ƙyar! Muryar
shi na sarƙewa ya ce "ya kai Kulairu ka yi sani cewa a daren jiya na yi istihara game da batun
FARMAKIN BAZATO da ake kawo mana da kuma batun jinyar rashin lafiya ta, kuma na samu
nutsuwa a raina, hakan ya tabbatar min da cewa nasara za ta zo gare mu asirin makiyan mu zai
tonu kuma zan samu lafiya da yardar Allah.
Sai dai nayi matuƙar mamakin yadda aka yi waziri Yazid ya ci amanata, ya Kulairu ka yi sani
cewa na fi kowa sanin wane ne Yazid kuma tun muna yarinta muke tare babu abinda ke raba
mu da shi face kwanciyar barci.
Haƙiƙa Manzon tsira ya yi gaskiya da ya ce " ka so masoyinka sannu-sannu wata rana zai
iya zama maƙiyinka. Haka ma ka ƙi maƙiyinka sannu-sannu wata rana zai iya zama
masoyinka";
kuma ina ƙarfafa gwiwa ina fatan za ku yi nasara alfarmar Annabi SAW TAFARKIN TSIRA zai
tabbata za'a rabe tsakanin ƘARYA DA GASKIYA";
Lokacin da sarki Nu'umanu ya zo nan a jawabin shi sai hawaye suka kwaranyo daga
idanuwanshi, koda ganin hakan sai Lawisat ta sake fashewa da kuka.
Al'amarin da ya karya zuciyar Kulairu kenan ya kamu da matuƙar tausayin su, bai san
sa'add ƙwalla ta cika cika mashi idanu ba, kawai sai ya miƙe tsaye tsam! ya juya ya fice daga
turakar ya kama dokinshi ya haye ya sakar mashi linzami yana fitowa ƙofar gidan sarauta ya
iske dakarun musulunci sun yi sahu-sahu waɗansu na zaune a bisa dawakai, wasu a raƙuma
wasu a ƙafa.
Domin haka sai kawai ya shige gaba dakaru suka mufa mashi baya, tun kafin su iso tuni
waɗansu ZARATAN DAKARU sun wangame ƙofar birnin suna zuwa suka kunna kai izuwa cikin
daji aka shiga tafiya cikin sauri domin isa ƙasar sarki Rakibu.
BABI NA GOMA
Sa'adda aka ci gaba da fafata ƁAKIN ARTABU tsakanin su boka kaddad da Waɗannan
samudawan dabaru sai aka shafe tsawon rabin sa'a ana GUMURZU babu sassauci, lokacin da
sa'a ɗaya ta cika sai ya zamana cewa su boka kaddad ba su iya mayar da martani sai dai
ƙoƙarin kare kansu, saboda samudawan sun fara galabaitar da su. Ana cikin wannan fafatawa ne jarumi Muhassin ya hango waɗansu dakarun sun samu
nasarar kai aljani Ramsisul-Ayyam ƙas suna shirin afkawa su gimbiya Aslaima. Koda ganin
hakan sai ya ƙwalla kabbara da ƙarfi, yana mai neman taimakon Ubangijin Musulunci, ya daka
tsalle sama sai ga shi yana shawagi a saman su ya shiga amfani da takobinshi yana sare
kawunansu cikin wani irin zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, domin a cikin
daƙiƙa hamsin yana hallaka dakarun fiye da goma, yazamana duk inda ya sanya a gaba sai dai
ka ga dakarun na zube wa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga JINI DA ƘASA
suka cakuɗu waje guda.
Sa'adda samudawan suka ga irin muguwar ɓarnar da Muhassin ke yi masu sai suka fusata
ainun suka ƙyale kowa suka taru akan shi, kai kashe dandazon kudaje ne suka yanyame
ƙwallon mangwaro. Nan fa waje ya kaure da ƙarar karafniyar ƙarafa haɗe da ihun MAZAJE,
ƙura ta turnuƙe sararin samaniya bishiyu suna rangaji rassansu na karairaye suna zubewa
ƙasa.
Ɓangarorin suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA
BAJINTA, sa'adda boka kaddad, gimbiya Aslaima da sauran dakarun rakiya suka ga yadda
jarumi Muhassin ke ragargazar dakarun tamkar yana sassabe a gonar auduga, sai suka cika da
matuƙar mamaki suna cewa a cikin ransu, anya kuwa jarumi Muhassin bil'adama ne, domin ko
a tarihi ba su taɓa jin jarumi mai jarumta irin ta shi ba.
Ita kuwa gimbiya Aslaima duk da kasancewar ba ta iya ganin kowa da idanuwanta sai jarumi
Muhassin, ya yin da ta ga irin bajintar da yake yi sai ta ji ta ƙaruwa da matuƙar ƙaunar shi a
zuciyarta.
Haƙiƙa jarumi Muhassin ya cika GWARZON DUNIYA kafin cikar sa'a ɗaya ya samu nasarar
hallaka baki ɗaya dakarun babu ɗayan su da ya rage a raye, duk inda mutum ya kalla babu
abinda zai gani face gawarwakin dakarun kwance fulu-fulu cikin jini.
Koda samun wannan nasara sai MUHASSIN ya yi godiya ga Allah maɗaukakin sarki bisa ga
wannan nasara da ya samu. Kawai sai ya durfafi wata ƙorama yana isa ya ɗebi ruwanta ya
ɗauraye jini da jikin tufafinshi da takobinshi, kuma ya ɗaura alwala sannan ya fuskanci alƙibila
ya shiga gabatar da sallah. Duk wannan abu da yake gudanar wa kowa ya kallo, ya yin da suka ga yadda ibadar
MUHASSIN na cike da tsafta da nutsuwa, nan take suka ji kwaɗayin addinin shi ya kama su,
suna masu rayawa a zukatansu cewa anya kuwa addinin Muhassin ba shine addinin gaskiya
ba? Domin ga shi mun kasa hallaka dakarun duk da ƙarfin sihirin boka kaddad, shi kuwa ya yi
hakan.
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan, har Muhassin ya kammala ibadar shi, cikin
hanzari boka kaddad ya bayar da umurnin ya sanya wa waɗanda suka samu rauni magani
waɗanda suka rasa rayukansu aka binne gawarwakin su.
Kasancewar a wannan lokaci duhun magariba ya kunno kai sai aka yada zango nesa kaɗan da
inda aka fafata artabu, domin a kwana anan zuwa safiya a cigaba da tafiya.
Kashe gari tunda duku-dukun safiya bayan anyi kalaci kowa ya kimtsa cikinshi, sai boka
kaddad ya ɗauko madubin tsafin shi ya shiga gudanar da bincike, daga bisani ya ɗago da
kanshi ya dubi kowa dake wajen cikin kakkausar murya ya ce " "ya ku abokan tafiya ku yi sani
cewa bisa binciken da na gudanar ya tabbatar min cewa tazarar dake tsakanin mu da tekun
Baharul-imfal domin ɗauko ALLON TSAFI dake ajiye a cikin masifaffen kada. Ku yi sani cewa
musibar da zamu tarar acan ta shafe wacce mu ƙetare a baya, domin hakan sai kowannen mu
yakasance cikin shiri, da wannan nake yi mana fatan samun nasara.
Koda jin wannan bayani daga bakin boka kaddad sai kowa ya sha jinin jikinshi kuma cikinshi ya
ɗuru ruwa, aka kunna kai cikin dajin kowa na taka wa da ƙafafuwanshi, tafiyar daƙiƙa hamsin
kacal! Aka yi aka iso iyakar dajin kuma aka hango gaɓar tekun Baharul-imfal, domin haka sai
boka kaddad ya sake gudanar da bincike a cikin madubin tsafin shi a karo na biyu, bayan ya
kammala sai ya juya ya fuskanci jama'a ya ce "ya abokan tafiya ku yi sani cewa bisa binciken
da na yi ya bayyana mini cewa ba zamu iya ƙetare takun da ƙarfin sihirin tsafi ba, akwai buƙatar
mu koma da baya domin mu sassaƙa kwale-kwale ( jirgin ruwa ) da zamu yi amfani da shi
domin saura wa zuwa tekun";
Koda jin wannan batu daga bakin boka kaddad sai jarumi Muhassin ya yi caraf! Ya tari
numfashin shi yana mai ce "ina so a bani damar sassaƙa kwale-kwalen cikin sa'a ɗaya kacal
kawai".
Koda jin wannan batu daga bakin MUHASSIN sai boka kaddad da waɗansu daga cikin dakarun
rakiya suka tuntsire da dariya, bakomai ne ya sanya su dariyar ba sai na isa ganin cewa ya faɗi
abin da hankali ba zai ɗauka ba, domin ta ya ya mutum zai iya sassaƙa kwale-kwale a cikin sa'a
ɗaya kacal! Boka kaddad ya dube shi fuskarshi a murtuke ya ce "to shike nan muna jiran ka mu ga ikon
Ubangijin na ka da kake taƙama da shi";
Koda jin hakan sai MUHASSIN ya yi murmushi mai taushi Kawai sai ya juya ya kunna kai izuwa
cikin daji yana mai takawa da ƙafafuwanshi, kaddad da tawagar rakiya suka samu waje suna
zauna suna masu bin shi da kallo.
Jim kaɗan bayan shuɗewar daƙiƙa talatin sai ga Muhassin ya dawo ɗauke wata bishiya a
kafaɗarshi ya sare rassa da jijiyoyinta. Ya zo a jiye a gaban su boka kaddad, nan fa suka cika
da matuƙar mamaki da al'ajabi bisa wannan jarumtaka da jarumi Muhassin ya yi.
Batare da wani ɓata lokaci ba Muhassin ya shiga aikin sassaƙa kwale-kwalen ta hanyar amfani
da wani gatari da ya kasance na waɗannan ayarin muridan.
Haƙiƙa Ubangiji ba ya kunyata bawanshi a duk lokacin da miƙa dukkan lamuranshi a gare
shi kuma ya yarda cewa shine zai yi mishi komai. Domin kuwa cikin sa'a ɗaya kacal kamar
yadda ya yi alkawarin.
Nan fa kowa ya cika da matuƙar mamaki bisa wannan bajinta ta Muhassin suka fara ji aran su
cewa anya kuwa Ubangijin shi shine na gaskiya ba. Shi