Showing 1 words to 3000 words out of 23849 words

Chapter 1 - KARYA DA GASKIYA Cigaban Tafarkin Tsira Rubuta littafin Mansur Usman Sufi .pdf

KARYA DA GASKIYA
Cigaban
TAFARKIN TSIRA
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi





BABI NA ƊAYA



Al'amarin da firgita gaba ɗaya jama'ar dake fadar kenan suka sha jinin jikinsu, a lokaci guda
Fitinatul-Amir ya turɓune fuska tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA, kawa sai ya dubi
waɗansu ZARATAN DAKARU dake tsaye a gefen shi cikin matuƙar fushi ya buɗi baki ya ce "Ya
ku dakaru ina so ku yi hanzari ku bi sahun dakarun dake ɗauke da haraji ku tabbatar da cewa
ba a sanya dukiyar sarki Madsur a cikin Baitul-Mali ba, kuma ku tabbatar da cewa kun kawo
mini Madsur da tawagarshi cikin ƙoshin lafiya domin na yanke masu hukunci dai-dai da abin da
suka aikata mani,

Na rantse da girman halarar tsafi na idan ku ka yi kuskure a wannan aiki da na baku sai KAIFIN
TAKOBI ya sha jininku,

Kafin sadauki Fitinatul-Amir ya gama rufe bakinshi dakarun su kimanin dubu sun zare
makamansu sun ruga izuwa wajen fadar suka bazama cikin gari wasu bisa dawakai wasu a
ƙasa, domin farautar sarki Madsur.

A she a ɗazu lokacin da Fitinatul-Amir ke tattaunawa da yaro Usaiba, kuma abin da Usaiban
ya faɗa ya tabbata bayan Fitinatul-Amir ya gudanar da bincike 'yan majalisa sun ji da
kunnuwansu, nan take suka raya a cikin cewa haƙiƙa wannan yaro yakasance ɗan baiwa taban
mamaki, wai shin ma mene ne alaƙar dake tsakanin su,
Amsar tambayar da suka kasa bawa kansu kenan, kawai sai suka zuba idanu domin su ga
sakamakon da dakaru za su dawo da shi.

Al'amarin sarki Madsur da tawagarshi kuwa, lokacin da suka fice daga fadar Fitinatul-Amir,
sai Madsur ya karanta ɗalasiman tsafi suka ɓace ɓat! Tamkar ba su taɓa wanzuwa ba, ba su
bayyana a ko ina ba sai a fadar Madsur dake cikin babban birnin Hairul-Maswat,

Fadar yakasance makekiya da aka ƙarara da nau'ikan ababen more jin daɗin rayuwar duniya, a
wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a makaɗa, mawaƙa tare da dukkan wani mai faɗa a ji,

lokacin da sarki ya zauna bisa kan karagar mulki sai waɗansu irin tsala-tsalan 'yan mata
kuyangi suka shigo fadar ɗauke da nau'ikan kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe suka shiga raba wa
jama'a, nan al'umma suka fara kimtsa cikinsu cikin nishaɗi da annashiwa, makiɗa da makawa
suka fara aikinsu na raye-raye da kiɗe-kiɗe domin ƙara wa al'umma nishaɗi, shi kan shi sarki
Madsur tashi ya yi daga kan karagar mulki ya cire alƙyabbarshi ya zauna cikin 'yan majalissa
suka shiga yin walimar suna shewa da tafi, da yawa daga cikin al'ummar dake fadar ba su
dalilin da ya sanya aka shirya wannan walima ba, domin tsawon shekaru sarki Madsur yana
buƙata daga sharrin Fitinatul-Amir amma bai taɓa farin ciki tamkar yau ba, ana tsaka da wannan
walima ne sarki Madsur ya karɓi wani kofi mai ɗauke da barasa a hannun wani hadimin shi ya
kai bakinshi da nufin ya ƙurɓe ruwan, amma sai kawai aka ga ya yi jifa da kofin ya faɗi ƙasa ya
tarwatse sannan ya miƙe tsaye zumbur yana mai kwarara wawan ihu da ya firgita baki ɗaya
jama'ar dake fadar kowa ya shiga taitayin shi, tsawon daƙiƙa talatin yana kururuwar sai tsuke
bakinshi gami da murtuke fuska tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA, Kawai sai ya
durfafi inda karagar mulki take ya juya ya fuskanci al'umma fuskarshi har gyatsine take yi
saboda tsananin fushi sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya ya ce "Ya jama'ata ku yi sani
cewa bakomai ya sanya ni wannan baƙin ciki ba face lalacewar dukkan wani shiri nawa da na yi
na mallakar dukiyar Fitinatul-Amir shugaban 'yan fashin duniya, kuma ba wani ba ne ya watsa
shirin nawa ba face wani hatsabibin yaro mai ɗauke da hatimin takobin SAIFUL-ZAYYAD,
matsawar yaron yana tare da Fitinatul-Amir ba za mu taba yin nasara akan shi ba, sannan
yaron zai zamo ANNOBAR SARAKAI da matsafa gami da bokayen duniya, sai dai kash! Ana
dara ga dare ya yi shi kan shi Fitinatul-Amir bai sani ba cewa yaron annoba ne a gare shi domin
abin da ya daɗe yana farauta dare da rana domin ya hallaka shi ko ya cika muradin shi ya
samun magaji.

Saboda haka da nan zuwa kowanne lokaci zai iya kawo mana FARMAKIN BAZATO domin
ɗaukar fansa, saboda haka wajibi ne a gare ni na gudanar da bincike mai zurfi domin tunkarar
duk wani ƙalubale da zai iya biyo wa baya, sannan akwai buƙatar a daren yau a shirya tawagar
dakarun kar-ta-kwana".
Lokacin da sarki Madsur ya zo nan a jawabin shi sai ya taka da ƙafafunshi ya durfafi ƙofar
da za ta sada shi da gidan sarauta, cikin hanzari waɗansu ZARATAN DAKARU ma'abota
baƙaƙen sulken yaƙi suka mara mashi baya har sai da suka ƙule izuwa cikin ƙofar sannan
jama'a suka watse kowa ya kama gaban shi, zukatansu cike da matuƙar bargaba domin sun
san cewa gwabzawa da Fitinatul-Amir tamkar mutum ya sayi ajalin shi ne kuɗinshi.

Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Madsur a lokacin da ya bayyana a fadarshi, bayan ya
miƙa haraji ga shugaban'yan fashin duniya sadauki Fitinatul-Amir.



Lokacin da dakarun sadauki Fitinatul-Amir suka fice daga fada sai suka kasu rukuni biyu, kaso
na farko suka durfafi hanyar da zata sada su da Baitul-Mali, na biyun kuwa suka bi sawun
tawagar sarki Madsur, rikuni na farko sun riski dakarun dake ɗauke da harajin sarki Madsur, sai
suka garzaya baki ɗayan su suka dawo izuwa fada, bayan sun gurfana gaban sarki sun kwashi

gaisuwa sai Fitinatul-Amir ya dubi shugaban dakarun fuskarshi a murtuke babu annuri tamkar
an watsa mashi garwashin wuta a kan ta cikin kakkausar murya ya ce " Ya kai Huzlaif haƙiƙa da
a ce wani acikin ku ya yi kuskure an sanya duniyar sarki Madsur a Baitul-Mali da ɗayanku ba
zai tsira da rayuwar shi ba, bayan tafiyar ku na gudanar da bincike bisa halarar tsafi na na gani
cewa sarki Madsur ya ɓace tare da tawagarshi yanzu haka yana birninshi, saboda ina so ka
shirya dakarun yaƙi domin kai farmaki izuwa ga sarki Madsur kafin wayewar gari ina so a
hallaka duk wata halitta koda kiyashin birnin ba na so a bar shi a raye"

Koda Fitinatul-Amir yazo dai-dai nan azancen shi sai ya mayar da duban shi ga wani garjejen
ƙato ma'abocin kwarjini, ƙasumba da gemu baƙaƙe siɗik daga cikin jerin 'yan majalisar shi ya ce
da shi "Ya kai dirkar birnina kai ne za ka jagoranci wannan kai FARMAKIN BAZATO ka tabbatar
da an zartar da komai yadda ya dace"
Koda gama faɗin hakan sai sarki Fitinatul-Amir ya miƙe tsaye tsam! Daga kan karagar mulki ya
durfafi ƙofar da zata sada shi da gidan sarauta cikin hanzari waɗansu ZARATAN DAKARU suka
rufa mashi baya har sai da suka ƙule izuwa cikin cikin ƙofar sannan fadar ta watse kowa ya
kama gaban shi, inda ace mutum zai ga yadda fadar ta yi watan! Sai ya rantse ya ce wata
halitta bata taɓa wanzuwa a fadar ba.

Lokacin da aka garƙame da azababban yaƙi tsakanin Musulmi da kafurai sai yaƙin ya zamo
abin tsoro ga kowa ne ɓangar, kabbarta musulmi haɗe da ihu da kururuwar kafurai gami da
ƙarar karafniyar ƙarafa da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne, rundunonin biyu suka wanzu
suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA, sassan jikkunan
bil'adama suka dinga shawagi a sama suna zubowa ƙasa tamkar ana ruwan su ne daga saman,
JINI DA ƘASA suka cakuɗe waje guda.

A ɓangaren manyan GWARAZAN JIYA kuwa sarki Rayyan da Lamsarul-Azlam sun wanzu
suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama na gaban kwatance sai da sa'a ta
shuɗe a cikin wannan hali ɗayansu bai samu nasarar lakutar jikin abokin gwamin shi ba,

Wohoho! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce kyan faɗa a kwana a na yi, kuma
inda babu ƙasa nan ake gardmar kokawa, koda gwarazan biyu suka fahimci cewa sun kasa yin
nasara ta hanyar amfani da makaman yaƙin su sai kawai suka yi jifa da makamansu suka ja da
baya domin a gwada 'yar Kashi, suka ruga izuwa kan juna ya yin da ya rage saura taku goma
tsakanin su sai suka dako wawan tsalle sama suka kaiwa juna huri suka naushi fuskokin juna,
sannan suka diro ƙasa, koda kowanne su ya shafa hancinshi sai ya ji jini na zuba, kawai sai
suka ruguntsume da sabon artabu, suka wanzu suna naushi da bugun juna hannu da ƙafa
tamkar waɗansu ifritai.



Mu haɗu a babi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari

Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe

ƘARYA DA GASKIYA
BABI NA UKU
Rubuta Labari
Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071



BABI NA UKU


Lokacin da ya rage saura kamu biyu kafin addar ya ratsa wuyan yaro Usaiba, kwatsam!
Bazato babu tsammani sai jaruma Rusayyat ta bayyana a daf da inda yaro Usaiba yake
kwance, tana shirye cikin gagarumar shigar yaƙi a kwiɓin cinyoyinya tana ɗauke da Waɗansu
zaratan takubba. Kafin Fitinatul-Amir ya yi wani yunƙuri uwar gidanshi ta shammace shi ta gabza mishi wawan
naushi a ƙeyarshi. Saboda ƙarfin naushin sai da Fitinatul-Amir ya wuntsila addar dake
hannunshi ta faɗi can gefe guda amma sai ya turje ya ja ya yana mai gyara tsayuwar shi.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin shi da uwar gidanshi, duk wannan abu dake faruwa akan
idanuwan Jama'ar fadar yake gudana. Ya yin da suka ga cewa Rusayyat ta shirya fito-na-fito da
Fitinatul-Amir sai suka cika da matuƙar mamaki suka ce tabbas Rusayyat ta yi wauta ainun,
amma masu iya magana na cewa idan ka ji makaho ya ce ayi wasan jifa to ya ji ya taka duste! Fitinatul-Amir ya buɗe baki cikin kakkausar murya mai tattare da matuƙar fushi ainun lokacin da
idanuwanshi suka canza launi izuwa shuɗi ya ce "ya uwar 'ya'yana haƙiƙa kin ci amana kuma
kin bani kunya da kika tseratar da rayuwar maƙiya na bayan cewa kin san ba zan taɓa cimma
burina na samun haihuwa ba face na hallaka yaro Usaiba, shin bakya farin ciki da nawa farin
cikin, ina mai tabbatar miki da cewa a yanzu zan yanke maki hukunci dai-dai da laifin da kika
aika mini, bayan na aika rayukan Usaiba da 'yar uwarshi Hairat izuwa barzahu...,
Kafin Fitinatul-Amir ya kammala rufe bakinshi Rusayyat ta tari numfashi tana mai bushewa da
dariyar mugunta sannan daga bisani ta turɓune fuska da SAƙON MUTUWA ta ce "Haƙiƙa ranar
wanka ba a ɓoyen cibi! Ya mijina ka yi sani cewa ja da baya ga rago ba tsoro ba ne face shirin
artabu, koda da daƙiƙa ɗaya a rayuwata ban taɓa jin ina ƙaunar ka ba a cikin zuciyata kawai dai
ina yi maka biyayya saboda na cimma burina na ɗaukar fansa akan amininka wato attajiri
Kulbus, a halin yanzu ina so ka sani cewa ɓuyan da wannan ƙwanwa ke yi a bayan kare ya zo
ƙarshe"
Lokacin da Rusayyat ta zo dai-dai nan azancen ta sai ƙwallar takaici da baƙin ciki ta zubowa
Fitinatul-Amir, gashin jikinshi ya mimmiƙe kuma wani tiririn ɓakin hayaƙi ya dinga fita daga
sassan ƙofofin hancinshi da bakinshi, kawai sai sanya hannunshi ya keta alƙyabbarshi gida biyu
ya yi wurgi da ita da ita gefe take waɗansu jajayen sulken yaƙi suka bayyana a jikinshi masu
matuƙar kwarjini, kai idan ka gan shi a cikin wannan hali sai ka yi tsammanin cewa wani ifritu

ne, kawai sai Fitinatul-Amir ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanshi ya falfala da
azababban gudu a izuwa kan Rusayyat yana ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA
a FILIN DAGA, tsinin takobin yana kartar ƙasa yana tayar da wata kariyar walƙiya.
Al'amarin da ya ɗimauta jama'ar dake fadar kenan suka shiga guje-guje da ifice-ificen TSIRA
DA RAYUKA.
Koda ganin hakan sai Rusayyat ta yi koyi da shi ta hanyar zare takobinta ta ruga gare shi domin
tarar juna,
Wohoho! Haƙiƙa KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA kuma ranar bikin farar kaza balbela ba
abar gayya ba ce, tabbas idan BABBAR GIWA ta fito FILIN FAMA babu wanda ke fitowa ya yi
GABA DA GABA da ita face GOGA SHA FAMA da sha gwagwarmaya a DAULAR MAYAƘA.
Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan taurari biyu ke yin shirin
KARON BATTA dole ya ɗimauce ya tabbar da cewa inda babu ƙasa nan ake gardmar kokowa.
Lokacin da rage tazarar dake tsakanin su bata huce taku huɗu ba sai kowannen su ya daka
tsalle sama suka kaiwa juna hari, cikin matuƙar zafin nama suka sanya takubbansu suka kare
wani tartsatsin wuta ya tashi, sannan suka dira ƙasa bisa diga-digansu cikin gwaninta, suka
shiga kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin ta MAZAJEN
DUNIYA.
Kaico! Haƙiƙa artabun gwani da gwani daɗin kallo gare shi, ana fara wannan ɗauki ba daɗi ne
mutane suka fara gane kuren su, domin su Fitinatul-Amir sun fara hargitsa fadar, duk sa'adda
ɗaya daga cikin gwarazan biyu ya kai wa abokin gwamin shi hari idan ya kauce, duk abin da
takobin ta sauka a kan shi sai ka ga ya tarwatse ya yi bindiga ya yi kan jama'a koda kuwa gini
ne,
Nan fa suka ci-gaba da gudun tsira da rayukansu hatta 'yan majalisar sarki da su aljani
Lattul-kifas cika wandunansu suka yi da iska domin dai ina amfanin baɗi babu rai.
A wannan lokaci babu abin da kunne ke ji ƙarar karafniyar takubba gami da ihu da kururuwar
jaruman, sai da rabin sa'a ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi babu ɓangaren da yake da
RINJAYE, al'amarin da ya fusata su kenan bisa ganin cewa suna artabun ne cikin matuƙar zafin
nama da ƙwarewa. Abin da su duka biyun ba su sani ba shine bakomai ya sanya ɗaya su ya gaza yin nasara ba
sai domin saboda takubban dake ɗauke da su an sana'anta su da sinadarin tsafi guda ɗaya,
Lokacin da Fitinatul-Amir ya fahimci wankin hula zai kai shi dare kuma kimar shi za ta zube a
idanun talakawan shi ace uwar gidanshi ta gagare shi. Koda kammala tunanin hakan sai kawai
ya shammaci Rusayyat ya gabza mata wawan naushi a fuska. Saboda matuƙar ƙarfin naushin
sai da ta yi sama tamkar an janye ta da ƙugiya sannan daga bisani ta faɗo ƙasa tim a matuƙar
galabaice, kafin ta yi yunƙurin miƙe wa tsaye Fitinatul-Amir ya sake gabza mata wani naushin a
fuska take ta langwaɓe ƙasa sumammiya, hanci da bakinta na yoyon jini.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai Fitinatul-Amir ya bushe da dariyar farin ciki sai da
ya yi ta ishe shi sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko mishi da sakon mutuwa, kawai sai ya
durfafi inda Usaiba ke kwance ya yin da ya isa sai kawai ya ɗaga takobinshi domin ya sare
mishi wuya. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai wata irin shirgegiyar mikiya ta bayyana ta saman rufin
fadar ta mangare Fitinatul-Amir ya faɗi ƙasa, kafin ya yi yunƙurin miƙewa tsaye, mikiyar ta sanya
faratan ƙafafuwanta ta ɗauki yaro Usaiba da Rusayyat ta tashi sama ta ratsa ginin fadar tamkar
yadda danshi ke ratsa ƙasa ta ɓaci bar! Tamkar bata taɓa wanzuwa ba.

Lokacin da waɗannan dakaru suka yi arba da abin da zakanyar ta yiwa gimbiya Aslaima sai
suka zare makamansu suka yi ɗauki kan ta aka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar
kwarjini daban al'ajabi. Dakarun suka wanzu suna kai mata sara da suka cikin matuƙar zafin
nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, ita kuwa ta dinga zille da zame wa gami da
mayar da martani da yakushi da ciwo, duk wanda ta bangaza daga cikin su sai ka ga ya yi
sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan ya faɗo ƙasa ko shurawa bai yi ba.
Nan fa ya zamana cewa yawan dakarun ya zamo a banza domin zakanyar ta zame masu
tamkar ANNOBA ƊARI, duk inda ta sanya a gaba sai dai ka ga suna faɗuwa ƙasa matattu, kafin
shuɗewar rabin sa'a ta maishe su gawa babu ɗayan su da yake raye, sannan ta farma kuyangin
dake tare da gimbiya zubar da su ƙasa matattu. Koda samun wannan gagarumar nasara sai zakanyar ta yi wani irin mahaukacin gurnani tana
mai daga ƙafafuwanta na gaba sama tana buga su a ƙasa, sannan daga bisani ta daka wawan
tsalle domin ta turmushe gimbiya Aslaima ta kai ranta izuwa barzahu.



BABI NA HUDU


Lokacin da ya rage saura kamar kamu uku zakanyar ta dira a kayan gimbiya Aslaima ba,
kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga wani kyakkyawan saurayi ya yi firar burgi daga cikin
duhuwar bishiyun dajin, sanye yake cikin fararen tufafi, a kwiɓin cinyarshi ta dama yana ɗauke
da salkar ruwa, a gadon bayanshi kuwa yana rataye da wata sharɓeɓiyar takobi, kallo ɗaya
zaka yi mishi ka tabbatar da cewa ya cika GWARZON MAYAƘI mai ƙarfi na Allah ya isa, babu
wata 'ya mace mai hankali da za ta yi tozali da shi face ta kamu da matuƙar ƙaunar shi.
Cikin baƙin zafin nama saurayin ya daka wawan tsalle ya dira a daf! Da inda gimbiya take ya
gabzawa zakanyar naushi a wuya take wuyan ya karye ji kake ruƙus ƙas! Zakanyar ta faɗi ƙasa
rikica ko shurawa ba tayi ba. A dai-dai wannan lokaci ne boka kaddad da dakaru dubu suka
ruga izuwa wajen ɗauke da miyagun makamai, koda suka ga abin da yafaru sai suka yi turus!
Cikin matuƙar fushi boka kaddad ya dakawa kuyangi tsawa da su kaiwa gimbiya Aslaima ɗauki,
cikin hanzari inda take domin aiwatar da umarnin da aka yi masu.
Boka kaddad

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login