Showing 1 words to 3000 words out of 26395 words

Chapter 1 - Kwai Cikin Kaya True Book 1 Hausa Novels Na Marubuciya Billyn Abdull.pdf

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery,
Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko
kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI
HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ ***************************
J*_Typing_*





*_ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_*


#?
Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_Ya rabbi ka bani ikon faɗar abinda zai amfanar da al'ummar MANZON ALLAH (A.S.W), ka
tsare harshena da alƙalamina ambaton abinda zai cutar da ni da ku a duniya da lahira._*

*_Ya ALLAH ka gafartama mahaifina masoyina da dukkan al'ummar musulmi da suka rigamu
kwanta dama, ALLAH ka kawo mana ƙarshen wannan annoba ta corona virus (covid-19), domin
rahamarka garemu_*

*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na ɗaya_
*______________________________________*


...........Ko wacce kafar yaɗa labarai da ta yanar gizo labarinsu a wannan safiya ta laraba shine
sace shahararren mai arziƙin nan *Alhaji Sadi kokino (ba giyar yaro ba)*.
A yanda labaran ke ta yawo an sace Alhaji Sadi kokino ne a daren jiya talata a filin jirgin
sauka da tashi na babban birnin ƙasar. Abu mafi ɗaure kai ga wannan lamari shine ta hanyar da
mutumin da yay garkuwa da shi ya ƙwamushe sa. Da yawan mutane da suka shigo jirgi ɗaya da
Alhaji Sadi kokino sun tabbatar ma jama'a da lafiya lau ya sauka, harma ya gaisa da wasu
tsirarun mutane da suka je tarbarsa. Sannan akwai wasu ƴan jarida guda biyu a filin jirgin da har
suka ɗauki hotansa da gajeren bidiyo. Kowa ya shaida Alhaji Sadi lafiyar ALLAH ya shiga motar
da ɗaya a masu gadinsa ya buɗe masa, sannan amintaccen direbansa yaja motar a gaban
kowa. Sai dai a lokacin da motocin suka shiga harabar gidansa aka sake buɗe masa ƙofa dan
ya fita sai yace ku ɗaukeni inda kuka ajiye, a taƙaice dai Alhaji Sadi kokino yayi ɓatan dabo a
hanyar dake tsakanin filin jirgi zuwa gidansa.
Zuwa yanzu dai jami'an tsaro sun bazu ta ko ina nemansa, tare da buɗe kunnuwa da idanu
ko za'aji wani abu da ga bakin wannan mai ƙwamushe da ba'a san ta yanda yay siddabarun
sace Alhaji kokino ba...


*____________________________________*

A yayin da masu yawun mai da yanda akayi ke kaikawo akan wannan ruɗaɗɗen labari
suma talakawa ƴan bani na iya sai tofa nasu albarkacin bakin suke. Ko wane dandalin sada
zumunta na yanar gizo ka shiga sai kace nace akeyi. A yayin da wasu ke jimamin lamarin wasu
ALLAH ya ƙara suke faɗa, a wani gefen kuwa ma kai tsaye suke ƙaryata lamarin da
dangantashi da farfaganda irinta manyan ƙasa ce kawai, ƙilama yana can kwance a gidansa
lafiyar ALLAH.
Daga masu ƙaryatawa har waɗanda suka gaskata kowa yana da dalilinsa, dan kuwa a yanda
ƙwamishen ya kasance dolene ya bada mamaki, musamman idan mukai dubi da jami'an tsaro
da cctv cameras da ke zagaye da filin jirgin, ga haske ta ko ina tamkar rana.

Koma dai yaya abin ya faru lokacine zai bayyana mana hakan.

*___________________________________*

Kwance yake a bayan motar idanunsa a lumshe tamkar mai barci, lokaci-lokaci yakan
ɗanja guntun tsaki tare da huro zazzafar iska daga bakinsa.
Duk da kasancewarsa gwarzo kuma jarumin mutum mai ƙoƙari da jajircewa a aikinsa kallo
ɗaya zakai masa a yanzu ka hango tarin gajiyawa da ɗunbin kasalar dake tattare da shi.
Tsayuwar motar da buɗe murfin da akayine ya tilasta masa buɗe lumsassun idanunsa
kaɗan tare da ɗago hannunsa ya kai dubansa ga agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun,
kaɗan ya yamutse fuska yana sake huro iska kaɗan kafin ya sauke hannun da maida dubansa
ga ƙofar motar da aka buɗe. Tamkar bazai motsa ba sai kuma ya yunkura a hankali ya ja baƙar rigar sanyinsa jibgegiya
dake gefe ya zura kafafunsa waje.
Da sauri wanda ke tsaye a gabansa da alama shine ya buɗe ƙofar yay azamar kai hannu zai
amshi rigar sanyin yana sake ƙamewa alamar girmamawa.
Kansa ya girgiza masa ba tare da ya bashi rigarba, ya matse idanu kaɗan saboda sara
masan da kansa yake na azabar ciwo, ya sauke numfashi kafin ya fito gabaɗayansa yana tura
ƙaramar bindigar hannunsa a aljihun bayan wando.
Idanunsa da ke jajir ya ɗago yana saukewa akan matasan samari biyu, cikin hanzari suka
ƙame tare da sara masa. Hannunsa na dama ya dinƙule kawai yay gaba ba tare da suma yace
musu uffan ba. bishin sa sukayi a baya suma ba tare da sheresun da yay ya damesu ba.

Cikin nutsuwarsa ya iso wajen da ake buƙatar ganinsa, da ganin yanayin ɗakin zaka
fahimci wajene keɓantacce na jami'an tsaro da sukan tattauna akan wani case ko
shawarwarinsu idan sun tado musamman ta fuskar tsaro.
Ba tare da yay magana da kowa ba ya samu waje ya zauna, suma sauran waɗanda suka
shigo tare wajen zama suka samu. Ɗakin yayi tsit, bakajin komai sai ƙarar AC da na fitar
numfashi, sai kuma ɗan motsin da baza'a rasaba.
Wanda ke tsaye jikin allon bangon yana wani ƴan zane-zane ya ɗago fuskarsa a matukar
murtuke yana kallonsu.
“Nasan kowa zaiyi mamakin wannan taron na gaggawa da muka kira, duk da dai dukkan
tunaninmu zai iya tsayawa a waje ɗaya game da abinda muka wayi gari da shi na sace babban
mutum irin Alhaji Sadi Kokino. Kamar yanda muka sani tun a daren jiya wasu a cikin jami'anmu
suna a wajen domin binciko ainahin abinda ya faru, a yanzu hakama daga can muka tado ɗaya
da ga cikinsu domin ya bamu bayanai dangane da lamarin, sannan musan mataki na gaba da
zamu ɗauka kuma, dan yanzu dai ga agogo ya nuna ƙarfe 7:19am, na tabbata duk inda 8am
tayi wannan labarin zai gama baje duniya ne, sanin kankune kuma mune jami'ai na farko da
kowa zai maida hankalin ji da ga garemu, tun daga kan jama'ar gari zuwa ƴan jarida da iyalansa
dama jama'ar dunaya baki ɗaya”.
A tare suka shiga jinjina kai alamar gamsuwa da bayaninsa.
Cikin gyara tsayuwa ya ke kallonsu, ya sauke idanunsa akansa da har yanzu hannunsa ke
dafe da kansa, *“Jawaad!”*.

Jin sunansa da aka ambatane ya sakashi janye hannunsa tare da ɗago manyan idanunsa
da ke a jajur ya sauke akan ogan nasa, cikin dakewar murya da ke tabbatar da shiɗin jarumine
ma'abocin nutsuwa ya amsa da “Yes sir” tare da miƙewa tsaye yana ƙamewa.
Gaban allon ogan ya nuna masa da biron dake hannunsa.
Cike da kasala mai tare da nauyin jiki ya taka zuwa wajen, ya maido kallonsa gaba ɗaya
zuwa ga sauran jami'an tsaron dake cikin ɗakin taron.
Cikin nutsatstsiyar muryarsa mai amo da saka razani ga abokin gaba ya fara faɗin, “Duk
abinda zan faɗa game da wannan lamarin a taƙaice zai iya zama gaggawa, dan har zuwa
yanzu da na baro filina jirgin da gidan Alhaji Kokino babu wani bakin zare da muka samu a kai
sai surutai marasa makama, a cctv cemaras na Airport kuma lafiya lau Alhaji Sadi ya shiga
mota tare da masu tsaron lafiyarsa. A ɗan nazarina ta wannan gaɓar ya nuna lallai mai satar
yanada matuƙar wayo, kuma ƙwararrene mai aiki da ƙwaƙwalwa...”
Kowa jin jina kai ya shiga yi alamar gamsuwa da bayanin Jawaad da ke riƙe da kansa da ke
ƙara ƙarfin sarawa na ciwo.
Wanine cikin waɗanda ke zaune a kujeru na musamman, alamun shima babbane yay
gyaran murya tare da gyara abin maganar dake gabansa. “Wato bayanan JAY abin dubawa ne
kam tabbas, amma ku wace shawara ce da ku a kan hakan?”.
Wani ne da ga can rukunin kujerun da Jawaad ya taso ya ɗaga hannu, damar magana aka
bashi. Bayan ya miƙe ya ƙame sannan ya fara magana cike da girmamawa, “Yallaɓai ƙwarai
maganar jay gaskiya ce, sannan ya kamata muma muyi shiri na musamman akan wanann case
ɗin, dan inhar muka kuɓutar da Alhaji kokino ba ƙaramin daraja hukumar ƴan sanda zata sake
samuba a idon jama'a”.
Tafa masa sukai, wanima ya sake ɗaga hannu aka bashi dama, shima goyon bayansa ya
nuna akan maganar Jawaad. Bayan shi mutane biyu sun sake yin mubayi'a kafin wani ya tashi
shikuma bayan an bashi izini, fuska a ɗaure yana wani hura hanci da fesar da iska yace, “Sam
wannan shawarar tasa bata kan tsari, ya kamata ama ƙalubalancesa, tun a daren jiya bayan
faruwar abin da mintunan da basufi goma ba aka turashi wajen shida wasu jami'an tsaro, amma
ace babu wani bayani na cigaba da aka samu, bayan a ƴan mintunan da sukaje wajen bai kai
nisan da za'ace shi mai ƙwamishen yayi nisa ba, kawai shi dai yace bazai iyaba sai a nema
wanda zai iya kawai, inba hakaba ta silar wannan case ɗin to lallai hukumar ƴan sada tana tare
da babbar barazana ta zubewar kima da sake saka shakku a zukatan al'umma a kanmu”.
Kowa kallonsa yake kawai, yayinda manyan suke jinjina masa kai da wasu a tsirarun sauran
jami'an.
Jawaad kam ko motsi baiyiba balle ya kalli wanda ya gama bayanin, sai dai ya saki wani
ƙasaitaccen murmushi da ya bayyana loɓar kumatunsa guda biyu kawai.
Ba karamin sukar zuciyar Qaseem Ali murmushin Jawaad yayi ba, amma ta wani ɓangaren
ya ɗanji sanyi a ransa ganin maganarsa taso kawo ruɗani, dan sai ya zam kawunan jami'an
tsaron yana neman rabuwa, wasu suna bin bayan Jawaad Abdul'aziz yusuf, wasu kuma suna
bin bayan maganar Qaseem Ali. Dan danan cece kuce ya fara yawaita a ɗakin taron har sai da aka tsawatar.
Murmushi Qaseem Ali ya saki ganin Jawaad ya dafe kai, sannan fuskarsa ta kuma ɗaurewa
alamar ransa ya sosu, dama babban burinsa kenan.
Sai dai kuma sam tunaninsa bai sanar masa gaskiya ba, dan shi Jawaad surutun da ɗakin

taron ya kaure da shine ya kuma saka kansa ƙarfin bugun ciwon da yakeyi sakamakon rashin
samun isashshen barci da yay a daren jiya, ga ruwan sama da yay musu dukan tsiya jiyan da
daddare, bayan dama ya koma gida a ƙurarren lokaci ne jiyan kafin ayi kiransa akan maganar
sace kokino.
Tsitt ɗakin yayi bayan tsawatarwar da akayi, yanzu ma ɗaya daga cikin shugabannin ne yay
magana.
“Duk wani kace nace bama buƙatarsa anan, kowa yasan wanene JAY akan ƙwazon aiki, ba
wannan ne na farko ba da aka bashi irin wannan damar kuma ya magance ta, sai dai ko wanne
irin case da ruɗanin da yake zuwa da shi, dan haka a wannan gaɓar mun naɗa Jawaad
Abdul'aziz yusif matsayin wanda zai kula da wannan case ɗin, sannan mun saka Qaseem Ali
matsayin mataimakinsa, kuna da damar haɗa rundinar jami'ai 30 da zasu taimaka muku, muna
fatan zaku bamu gudunmawa ta haƙiƙa wajen fiddamu kunya ku kuɓutar da Alhaji Sadi cikin
lokaci ƙankani da baza'a ga rauninmu ko gazawa ba”.
Tunda ya fara magana Qaseem yaji sunansa matsayin mataimakin JAY fara'ar fuskarsa ta
ɓace ɓat, hakama magoya bayansa. Ga Jawaad kam bai ko ɗago kaiba balle musan yanayin da
yake ciki.
Sun ɗan cigaba da tattaunawa kusan na awa ɗaya, wandda acikin awa ɗayarnan ba ƙaramin
a takure Jawaad ya tsinci kansa ba, ana kammalawa ya nema izinin zuwa gida ya ɗan huta
koda na awa uku ne.
Babu wani jan zance aka bashi dama, dan yanayinsa ya nuna buƙatuwa sosai na san
hutun.....


*___________________________________*

Tunda Gimba yay fakin motar a harabar gidan ya buɗe idanunsa da suka sake masa
nauyi da ƙyar, ba tare da ya jira Gimba ya buɗe masa murfinba ya buɗe da kansa ya fice, rigar
sanyinsa ce kawai a hannunsa sai bindiga da ƙaramar wayarsa da ya fita da ita kawai.
A yanda ya shigo ya ga falon jiya yauma haka ya sameshi, yaja siririn tsaki yana haɗiye
wani abu mai nauyi da ya tsaya masa a maƙoshi, zuciyarsa a matuƙar cinkushe ya ƙarasa sama
inda nanne ɗakin barcinsa yake.
Kallo ɗaya yayma falonsa ya ɗauke kai, dan hatta da kofin da ya sha shayi a daren jiya yana
a inda ya barsa, sam shi baima san wace irin mace ya aura ba, ƙazama ko ballagaza?. Takaici
bai nemi shake numfashinsa ba sai da ya ƙarasa haɗaɗɗen bedroom ɗinsa ya sauke dubansa a
kan lafiyayyen gadonsa da har yanzu take kwance, ta wani ƙudundune cikin lallausan bargonsa
tana shaƙar barci. Tuni idanunsa sun sake kaɗawa sun koma jajur, yayinda jijiyoyin kansa suka
sake fitowa raɗa-raɗa, yasan ko rantsuwa yay baza a bisa bashin kaffara ba akan Shuhudah
batai sallar asuba ba.
Bai sake kallon gadonba ya jefa rigar sanyin akan sofa tare da zube wayarsa da bindigar
saman tabirin dake shakanin kujerar da gado.
Duk da wani jiri-jiri da yake gani saboda yunwar da ke cin hanjinsa hakan bai hanashi nufar
bayi ba dan ya samu ya watsa ruwa ko zai samo kan jikinsa...............✍

*_Turƙashi, wannanfa shine Cakwakiyoyi ba Cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta
muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da
abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin
matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita, harma da ruguntsumi. Kai lamarinfa
ba'a cewa komai, mai karatune kawai zai banbance tsakanin ay.a da tsakkuwar zancena bayan
mun tsunduma cikin labarin tsundum._*

_Ku kasance tare da ni Bilyn Abdull dan jin yanda wannan littafi mai suna a sama zai kasance,
minene ma ma'anar *ƘWAI CIKIN ƘAYA!!?*, nasan wannan tambaya ce dake cikin zuciyoyin
masu karatu baki ɗaya, wadda ni Bilynku kaɗai zan baku amsarta._


*Zata iya kasancewa cikakken buk ɗin sai bayan sallah ƙarama zaizo muku idan munkai da rai,
idan kuma na samu dama koda ba kullum ba zanyi wasu pages kafin azumi insha
ALLAH☺️*⛹‍♀️







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_**_Typing_*





*_ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!_*


*_Bilyn Abdull ce_*


250F=3000F MTN /1J. Achete ton forfait PLUS sur *222*2# et tente aussi de gagner la nouvelle
voiture Suzuki Spresso de la semaine!

*_Ban yarda wani yaymin amfani da littafin nanba ta kowacce hanya, komin ƙanƙantarta,
inkuwa hakan ta kasance ban yafe ba☹️._*

_Na sadaukar da wannan littafi a gareku auntys ɗina, dan kune taurarin da Bilyn Abdull ke kallo

a duniyar rubutunta, da ku kuma zan cigaba da alfahari *Aunty Fareeda Ado gachi & Aunty
Rahama Abdul-Majeed (writer mace mutum)*, alkairin ALLAH ya kai muku a duk duniyar da
kuke har gadon barci._

*Wattpad* ➖ _BilynAbdull_


*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na biyu_
*______________________________________*


............Motsin ruwan wankansa ne ya farkar da Shahudah, tunda ta yaye bargon da ga fuskarta
nake tsarkake sunan ALLAH buwayi gagara misali da ya halicci wannan ƙyaƙyƙyawar baiwa
tasa. Lallai Shahudah ƙyaƙyƙyawace wadda zamu iya sakata a jerin farko na ƙyawawan
mutane, gata fara tas tamkar wata aljana. Har lokacin bata yaye bargon da ga jikinta ba, kamar yanda alamu suka nuna bata da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login