Showing 6001 words to 9000 words out of 29939 words
, Kar ka manta
tun muna yara muke samun matsala akan ma'eesha a yanzu ne har ka nuna kasan darajar ta? .
Ɗaga kafaɗa yayi alamun bai dame shi ba . Yana juyawa tare da wuce Khalil da ya tsaya yana
kallon sa .
Takawa yayi yana isa inda Ma'eesha take sai raba ido take don tsoron sa Ma'eesha keji ƙwarai
da gaske .
Wuce ki bani wuri!
Ya furta fuskar sa babu alamar wasa ko sakewa. Sum-sum ta juya tana wucewa tare da bashi
wuri . Ya Khalil ina kwana . Ta furta da Sauri tana raba shi ba tare da ta jira Jin amsar da zai
bata ba . Cike da fara'a ya furta lafiya lau Ma'eesha maza ki yi break fast .
Takaici ne ya kama Aliyu , Humm Wai me Khalil yake nufi ne? Son Ma'eesha yake yi ko mene?
Zuciyar sa ta fara masa wannan tambayoyin. Saurin Girgiza kai yayi yana cewa “ a'a Sam ba
haka bane ba , don Khalil a wannan watan za'a sanya baikon sa da Rahama. To mene wannan
tijaran nasa yake nufi kawai saboda nayi hugging ɗin ta. Ya manta Meye ban sani ba na jikin
Ma'eesha. Hattara tsarki Ni nake yi mata amma a yanzu yake faɗa mun munanan
maganganu....ko yana tunanin ina jin wani abu dan gane da ita...Aikin banza sai na shayar
dashi mamaki tare da shi za'a yi mana baiko dole na fidda ɗaya a cikin biyu , Maryam ko Mimi.
Hummmm....sauke numfashi yayi mai huci kana ya cigaba da maganar zuci da cewa “ Duka ba
zaɓi na bane....Mami ke liƙa min su , a wannan karon i must accept it. Dole na zabi ɗaya don na
ƙaryata tunanin Khalil akaina da Ma'eesha.............✍
Tom kunsan night update Babu yawa mu tara ana safe lafiya....muje yanda al'amarin zai
kasance . Shin waye Mimi??? Sannan kuma Wacece Maryam? Wacce a cikin su Ali gadanga
zai zaɓa ya kuke kallon wanga tafiyar......ku Cigaba da biyo alƙalamin mamanteddy✍ . Yau
inshallah zamu bude Comment GRP don jin sharhin ku bisa ga wannan labari na rainon
soja.......!
[12/20/2023, 7:52 PM] Real~Mamanteddy: *️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
Page 15
______________________
*Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ba ban
yafe ba...ga masu buƙatar payment regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special
payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number
08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama ƴan Niger katin Artel 500f.*
#Always Alhamdulillah ________________________
Da wannan tunanin ya nufi falon Mami inda Ya tadda su duka a Dinning table suna breakfast.
Takawa yayi yana isa gare su tare da jan kujera yana zama , Bin sa da kallo Mami tayi a ranta
tana cewa “ Da'alama Khalil ne ya hana shi wahalar da Ma'eesha da wannan masifaffen
morning exercise ɗin nasa”. Dariya ta Gimtse ganin yanda yake cika yana batsewa ita dai
Ma'eesha tun da ya zauna tayi ƙasa da kan ta tana sabgogin ta don bata son su haɗa ido bare
ya ce tayi wani laifin. Gaishe da General Saleh yayi kana y juya yana ma Mami Barka da
Safiya...daga nan kuma ya ɗaure fuska yana mami na fara serving din shi ....Kallon Mami yayi
yana cewa “ Mami kina gida gobe? ”.
Ɗago fuska mami tayi tana kallon sa kana ta ɗan Girgiza kai tare da furta “ A'a gobe ina so na
leƙa gidan Hajiya na gaida ta ....da wani Abu ne Haidar?. Girgiza kai yayi alamu a'a , yana
Cigaba da Karin kumallon sa....Sam Ma'eesha ta' rasa' samun natsuwar ta , haka ta kasa sakin
jikin ta .
Kallon Haidar tayi tare da kallon Daddy cike da zazzaƙar Muryar ta wanda tana fara magana
Haidar ke furta yi mun shiru ki rage mun murya. “Daddy Uncle Haidar gobe zai koma ko
yaushe? ...Dariya ne ya kama General Saleh Wanda sai da yayi mai isar shi kana yace“
Ma'eesha bagaki ga Uncle ɗin naki ba? Ki tambaye shi mana....ya kare maganan yana kallon
inda Ali Haidar yake ,yana jin duk abun da suke cewa amma tamkar baiji ba ko baya a gurin.
Muryar Daddy ne ya katse su yana Cewa “ Ali kayi shiru Ma'eesha fa tambaya take yaushe
zaka koma? . Dariya mami ta sheƙe dashi tana buɗe baki zatayi magana Muryar Jidder ya
katse su wanda cike da masifa ta furta “ Tun da gidan na uban ki ne dole ki ƙosa ya koma ”.
Shiru Ma'eesha tayi ta tsaya turusss gwiwar ta yayi sanyi qlau.
Wannan wacce irin ɗabi'a ce kike dashi Jidder? Wani irin mugun hali ne ke gareki? Ina yawan
faɗa Miki ki kiyaye mawa Ma'eesha billahil Azeem ranar da na shige Miki ba zakiji da daɗi ba
......! Mami ta furta tana ƙanƙance idanun ta cike da faɗa don ranta ya ɓaci. Muryar General
Saleh ne ya katse su yana furta“ Maza Ma'eesha kiyi karin kumallon ki ,idan kin gama kizo Falo
na yau zancika Miki alƙawarin ki ....Buɗe baki Ma'eesha tayi tana wangalewa tare da washe shi
tana furta “ da Gaske Daddy?”.
Ƙwarai kuwa....” Gimtse fuska Jidder tayi Khalil na kallon ta yana zabga mata harara.
**
Da hantsi wuraren ƙarfe 12 na rana bayan Mami ta tafi gidan Hajiya tsohuwa mahaifiyar
General Saleh Yelwa...tun daga falon farko har zuwa na tsakiya zuwa Ɗakunan barcin su
kowanne shiru kake ji tamkar babu ɗan adam a cikin gidan . A dai-dai wannan lokacin ne
Ma'eesha ta zauna tsakiyar gadon ta tana Fiddo da littafan ta tana karatu . Ɓarayi guda
al'ƙur'ani ne da ta gama karantawa kamin ta fara na karatun boko . Gyfen ta ruwa ne wanda ta
dauko daga ƴar ƙaramar fridge ɗin ta . Littaffin ta na Chemistry take karantawa duk da
kasantuwar Hutu suke yi a wannan lokaci amma hakan bai hanata kullum kasancewa cikin
karatu ba . Atom and molecule take karantawa tanajin daɗin karatun don sai da ya fito masu a
exam nasu na wannan zango . Hummmm.....numfashi ta ja tana saukewa tare da Lumshe
Idanun ta , fuskar Ali haidar ta gani wannan yasa gaban ta yankewa yana faɗi da ƙarfi dafe kan
ta tayi tana saurin ware idanun ta. Zuciyarta kawai taji ya tsinke tsoron jarabar sa take yi a ko
yaushe.
Motsin Handle door ɗin ta yasa ta saurin kallon direction ɗin tana kara zare ido tamkar wanda
tayi ƙarya , a halin yanzu tasan Ya Khalil baya cikin gidan nan don wuraren 11 yazo ya same ta
yana faɗa mata zai tafi wurin zaitoon budurwar sa da'akayi masu baiko , har yana tambayar ta
abun da zai zo mata dashi na tsaraba anan tace masa cup cake take so....Don mai masu kayan
snack jidder Wancen satin tayi mata bakar tijara , Tom kasantuwar itama tana da Dan ilimin ta
kawai dai tana son sana'ar snacks ne yasata yin mawa mami wannan hidimar ana biyar ta duk
wata . To a wannan karon Jidder da tayi mata zagin tijara takasa Haƙuri don dole ta bar aiki a
cikin gidan . Tabbas a yanzu tasan daga ita sai jidder sai kuma dodon nata Aliyu Haidar wannan
yasa tana jin motsin Handle duka ta maida hankalin ta idanun ta duka ga ƙofan....“Daaaam”.
ƙirjin ma'eesha ya buga ganin Haidar ya shigo yana zuba wani irin Sanyayyar ƙamshi gaba
ɗaya wurin ya mamaye da ƙamshin sa . Sam bata san wani duniya take ba har ya iso inda take
kana taji Arrogant voice ɗin sa ya katse ta yana cewa “ Keeee dallah rufe baki , kin wani saki
baki kaman sakarya.
Kallon sa tayi cike da danne fushin ta don maganan sa ya ɓata mata rai ta kalle sa tana sakin
Murmushi Gyefe da gyefen kuncinta na loɓawa . Uncle Barka da rana. Hummmm Me kike yi
anan ? Yayi maganan tamkar bai ga littafai a gaban ta ba , Cigaba yayi da cewa“ Dama naji
labarin Daddy ya saya Miki waya har da sabon laptop saboda gata . Baki iya komai ba sai
sangarci....Humm yayi ƙwafa yana kallon ta tare da zuba mata Lulun idanun sa . Cike da nuna
irin ke ya dama yace “ Kar ki manta ke yarinya ce karama SS1 yanzu ne ya kamata kiyi amfani
da damarki, sannan charting kar ki so ranar da zan duba wayar ki naga kina ko wani irin media
bana son ganin Film ko wani iri a laptop ɗin ki ko a wayar ki duka . Fatan kin fahimce ni?. Y
furta yana mai Gimtse fuskar sa babu wasa . Cikin sauri jikin ta na kyarma kar-kar-kar ta gyada
masa kai tana cewa “ Ehhh Ehhh..eh Ya khal....Ya Haƙuri Uncle ba zan yi ba Wallahi . Gani tayi
ya kafe ta da ido kaman a wannan ranar ya fara ganin ta a rayuwa . Sosai ya tafi tunani na yan
sakonni kana ya furta “Kin iya girki? Kamin ta basa amsa ne ya furta“ Ko da yake shekarar ki
nawa a yanxu ace baki iya girki ba . Maza miƙe yau wanda tunanin zan iya aure zasu zo . Mimi
da Maryam. A cikin su i must choose one ko mimin ko Maryam amma dole sai nayi masu
jarabawa wacce taci ita nake tunanin..........Shiru yayi yana kallon Ma'eesha da ta zuba masa
ido yana sauraren sa . Tashi ki bani wuri ki ɗaura masu Abinci kala ɗaya ya isa . Sai lemu da
ruwa . Ki haɗa masu da farfesun naman rago.
Idan kin ɗaura girkin ki tafi bedroom dina ki gyara mun ba falo ba.
Gyaɗa masa kai tayi tana sauka daga gadon tare da ƙoƙarin ficewa daga Bedroom ɗin .
Ma'eesha kin iya jaloaf rice ne?.
Ɗan ƙasa tayi da kanta a zuciyar ta tana Cewa “ Oho dama kasan ban iyaba ka sani ..ai na bari
ne nayi maka sai kaci kai da ƴammatan naka ,dagani basa da kamun kai tun da har zaka haɗa
su wai kayi masu jarabawa. Shi me yake taƙama dashi ne wai? . Keeee ba magana nake Miki
ba ?.
Ɗagowa tayi tana motsa masa ɗan motslun bakin ta tare da cewa“ A'a ban iya ba”. What? Baki
iya girki ba? Shekaran ki nawa suke? Kalle ki ? A girki baki iya komai ba kike so Kice mun?.
Ɗan jimmm tayi tana tunanin furucin Hauwa mai girki da takance mata idan zaki fara girki
indomie zan fara koya Miki yafi duka sauƙin iyawa. Cikin sauri Ma'eesha tace da Aliyu “ Dadd....
Sorry Uncle na iya indomie. Tsayawa yayi yana kallon ta yana nazari kana yace tafi ki yomun
jalaop na indomie ki kawo mun .
Tom guda biyu ko uku .
“Biyu ya furta yana kallon ta ”. Juyawa tayi tana saurin ficewa shima yana takowa tare da biyo
bayan ta yana zama a tsakiyar falo na biyu .
Kaman mintuna biyu yaga Ma'eesha ta fito daga kitchen din tana nufar ɓangaren sa . Da yake
shi ba mai yawan surutu bane ba , shiru yayi mata yana rakata da ido har ta shige Zuciyar sa na
mamakin yanda ta tafi ta bar gass wanda a minti biyu ruwan indomie ya juya ta zuba . Cigaba
yayi da latsa wayar hannun sa yana duba Yanayin weather din garin . Har mintuna kusan goma
Ma'eesha bata fito ba. Wannan yasa Aliyu miƙewa yana bin bayan ta .
A Bedroom ya tadda ita tana tsugune bangaren mirror din sa tana tsince kwalban turaren sa da
ta rotsa da ƙasa .... Ma'eesha! Ya kira sunan ta yana bin ta da wani irin kallo wanda sai da
Hantar cikin ta ya kaɗa.....jikin ta ne ya hau kar kar kar....saurin mikewa daga tsugunnen da take
tayi tana yin rau rau da ido kana tace “ Don Allah Uncle kayi haƙuri Wallahi Ni yarinya ce mami
tace saurin girma nayi....... Sakin baki yayi yana mata kallon mamakin magana nata . Tayi
masa laifi tana cewa ita yarinya ce saurin girma tayi ?. Fita ki bani wuri kije ki kawo mun
indomien ina jiran ki anan mintuna biyar na baki yanzu ki kawo mun .
Gyaɗa masa kai tayi da gudu tana nufar ƙofa .cike miskilalliyar Muryar sa ya kuma kiran sunan
ta cakkk ta tsaya kana yace “ Minti nawa nace Miki?. Da sauri ta furta “Five minutes ”.
Lumshe idanun sa yayi yana mata alama da okay kana ta fice da sauri tana nufar kitchen din.
Da kanta take haɗa masa komai kayan yaji kaɗan maggi kuwa bayan na indomie din sai da ta
zuba me star huɗu da onga biyu duka a cikin indomie ƙwaya biyu . Wani irin ruwa ta zabga shi
cimbul a tukunyar tana zuba indomien don ta zo taga yana ta tafasa . Zubawa tayi tana cewa “
Na shiga uku anya ba sai na ƙara ruwan ba , na gode m ALLAH da Uncle bai zo ya ga ruwan
nata tafasa ba. Rufe ƙaramar tukunyar tayi tana ja baya tare da kallon tsintsiyar hannun ta tana
dubawa mintuna uku kenan . Kallon gass din tayi tana miƙa hannun ta tare da bude indomien
da ta ganshi ruwa ya taso sama indomien na ƙasa daga gyefe saboda tsaban ruwan da yayi
yawa . Alhamdulillah nasan yau Uncle zai sha mamakin girkin nan ,don ko ba'a faɗa ba kai
daga jin ƙamshin sa kasan yayi daɗi ƙwarai . Tana maganan ita ɗaya sai farin ciki take yi yau
shine da girkin ta na farko kuma Uncle ne zaiciHummmm Uncle zaici Dadi yau .ko kuma
Ma'eesha jibga zata sha Allah masani....mu tara page 16 na safiyar gobe inshallah . Yau nayi
matuƙar busy ne shiyasa kuka ji shiru har wannan lokacin. Ina maku fatan alheri.
*Don Allah kar wacce ta karanta mun ba tare da ta biyani ba regular group ₦500 Vip group
₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta
wannan number 08081202032...Maman-teddy*
[12/21/2023, 8:08 AM] Real~Mamanteddy: *️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
Page 16
______________________
*Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ba ban
yafe ba...ga masu buƙatar payment regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special
payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number
08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama ƴan Niger katin Artel 500f.*
Morning update️________________________
Tana Tsaye Indomie ɗin ya fara kama jikin sa alamun ya nuna luguf yayi ga uban ruwa da yayo
sama . Sam bata damu da ganin wannan ba ,don a ganin ta Mami irin shi take masu . Plate ta
ɗauko tana juye masa duka tare da saka Fork , tana ɗauka zata fito zuwa falo . Cakk ta tsaya
tana Faɗin Ai ban saka masa Ƙwai ba . Ɗan juyawa tayi tare da kallon saman kitchen cabinet
ɗin tana bin inda ake aje ƙwayayan da kallo . Kai gaskiya ba zan tsaya dafawa ko soyawa ba .
Dole sai dai Na zuba masa kifin Gwangwani.
Hannun ta takai tana sauke plate ɗin tare da aje shi bisa cabinet ɗin tana ɗauko kifin
Gwangwani tana juye masa duka a ciki kana ta dauki plate ɗin indomien tana nufar direct ixuwa
falon sa . Zaune ta tadda shi ya harɗe ƙafarsa tamkar wani basarake. A gaban sa ta aje plate
ɗin tana komawa tare da zama kusa dashi tana bin bakin sa da yake motsa laɓɓansa a hankali
wayan sa na kare da kunnen sa . Duk maganan da yake yi babu ɗaya da taji.
Ɗan shiru Ma'eesha tayi kana a zuciyar ta tace“ Tab a haka ita wacce yake magana da itan tana
ji ? Zama dashi kaɗai wanda yayi wahala yake sha , to inaga wacce tayi gigin fara soyayya
dashi kuma?. Muryar Aliyu ne ya katse Ma'eesha yana cewa“ Ɗauko mun ki bani naci ”. T...tom
. Ga furta tana saurin yin ƙasa tare da ɗauko masa plate ɗin indomien tana miƙa masa .
Lulun Idanun shi ne suka duddulo waje yana bin plate ɗin da indomien ciki da wani irin ƙazamin
kallo . Rintse idanun sa yayi yana ji tamkar yayi mata duka da ita da indomien. Uncle yaune
girki na na farko , kuma nasan yayi daɗi sosai ka cinye sai na ƙara girka maka Wani
yanzu.........Ma'eesha! Ya kira sunan ta cikin wani murya da ta kasa tantancewa .wannan meye
kika yi kenan? Is that how to cook indomie? Haka kika ga mami nayi? Innalillahi wa'inna ilaihir
raji'un..... Gaskiya Mami ta sangarta ki da yawa babu abun da take koya Miki tsawon wannan
lokacin sai sangarci duka kin lalace wannan me kika girka mun faɗa mun naji yanzu ko nayi
ƙasa ƙasa dake anan Wurin ....!!!
Ya furta cike da doka Tsawa yana kallon indomien da ransa ya gama hasala baki ɗaya .
Hannun Ma'eesha kyarma ya kama yi tsoro na ɗarsuwa ma Zuciyar ta . Bakin ta na rawa ta
furta “ Ba indomie bane ba ”. To menene sunan wannan abun da kika girka?”. Hawaye ne ya
fara bin kuncinta narke fuska tayi tana fara kuka ko ina na jikin ta kyarma yake yi kar kar kar na
tsoro. Kayi hakuri Uncle kar ka bugeni don Allah.
Sunan Abun da kika girka mun zaki faɗa idan kuma ba haka ba tabbas yau zan zane ki bari na
ɗauko.....Saurin saka hannun ta tayi tana riƙe ƙafafun sa tare da ƙara fashewa da wani irin