Showing 24001 words to 27000 words out of 29939 words

Chapter 9 - Rainon Soja Part 2 Complete By Maman Teddy .pdf

04 Nov 2025

368

ta tana faɗin Allah
yasa ya ceceni daga Hannun Uncle , Da'alama ya Sanni tun ba yau ba , Gashi da ganin sa zaiyi
Rahma kaman ba Soja ba . Maganar take a zuciya kamin taji Muryar Areef yana katse ta tare
da Ɗagota daga jikin sa yana furta “ Ma'eesha kenan , ma'eeshan Uncle Aliyu, Yana ji dake
sosai na sani, Don a da baya kina yarinya shi yake Miki komai , baya taɓa yarda ko sami namiji
ya rungume ki kamar yanda nayi Miki harta Ni kuwa , wanka komai shi yake Miki sosai yasha
wahala akan..... It's Okay please! Ya isa Areef , yanzu mu wuce dai daga ciki , sai kaji meke tafe
Dani.

“ Aliyu ya furta yana katse shi tare da maganan yana kallon yanayin fuskar Ma'eesha wacce ta
faɗa duniyar tunanin maganan Areef , Anya kuwa da gaskiya a maganar sa , Bai san yanda
yake mun bane a yanzu , Da kuma ai abun da ya wuce ne ta furta a zuciyar tare da ɗaga
kafaɗa alamun bai dame ta ba , Maganan ma bata yarda dashi ba . Da A yanzu nike shan
wuyar kace i will definitely trust you for that , Amma kace wai shi yasha wuya akai na tabbas
ƙaryata ka xanyi don Mami ke kulawa dani sai Ya Khalil . Duk mai Sona yaso ya Khalil shi ke
kula dani yake So na sosai ...........“Ma'eesha!!! Muryar Areef ya katse Ta inda cikin sauri tace “
Na'am Canonel ”. No ki rani da Yayanki inda hali ɗauke Ni tamkar yanda kika Ɗauki Hausar i
will be happy if you do that for me”. You are always welcome sir”. Ta furta cike da confidence ɗin
nan nata . Shikam Ali caɓe baki yayi yana dalla mata harara a Zuciyar shi cewa yake “ See how
she did like a brave girl , Amma Sam ba haka take ba, raguwa ce , Common running kasa ta
yanzu zata fashe da kuka da yake hawayen basa mata wuyan zubowa ”. Common baby let go
in ”. Muryar Areef ya katse su yana riƙo hannun Ma'eesha tare da fara barin wurin yana nufar
Masaukin sa da su .

Mamaki ne ya kama ma'eesha ganin yanayin tsaruwar Musamman falon Canonel Areef tamkar
ba'a wurin training ɗin sojojin yake ba . Ɗaga kan ta tayi sama tana kallon Hoton Areef cikin
kakin soja inda yayi ƙyau Ainun, kana ta kalli Aliyu da suke zaune suna ɗan taɓa hiran su . Wow
Uncle Areef you look so Gentle man , Kuma kana da kyau kaman ya Khalil . Murmushi Areef
yayi kana yace “ Ko Ma'eesha yanzu a ina kike da karatu ?”. Yanzu ina M.S.U international
school , I'm SS 1 student . Wow that's very good. Yayi ƙyau, me kike sha'awar zama a matsayin
ki na mace nan gaba?. Yayi maganan yana kallon ta kana ya ɗan gyara zaman sa yana cewa “
No need nayi Miki wannan tambayar ba yanzu ba tukuna atleast sai kun kai SS2 kana hankali
ya ɗan fara shiga ko?” . Shiru tayi masa tana ƙasa da idanun ta tare da wasa da dogayen
yatsunta . A'a SOJA zata zama! Muryar Aliyu ya katse su .

Soja? Areef ya furta yana kallon Haidar kamin ya kalli Ma'eesha yana furta “ Amma tsarinta bai
kama dana macen SOJA ba . Just forget about that topic , Wani Soja barta tayi karatu har ta
kammala secondary You will understand what I'm trying to say now”. Amma Sam bata yi kalan
soja ba . Kalli yarinya the most cutest girl kace Wani SOJA ? Ko da yake ban sani ba ko itace ke
da Wannan Ra'ayin ?.

“Ɗan kallon Areef Ali yayi kana ya kalli ɓangaren da Ma'eesha take , Yana mai cizar laɓɓansa
na ƙasa tare da Ɗan taunawa kana yace “ No nike da Wannan Ra'ayin , Sannan abin da nake
so dole tabi layin nan , Saboda Hatta numfashin ta nawa ne. kame baki Ma'eesha tayi a
Zuciyar ta tana cewa “ Me yake nufi? Ai Allah ne mai yi ma mutum numfashi ba wani Ɗan Adam
ba ”. “Alright it's okay . Yanzu ina so ka fahimci Ma'eesha ba zata iya soja ba . Heeeeee!!! Keep
standing don't move anywhere! Muryar Areef ya katse ta , yana sauya mata lokaci guda ya
koma sojan da ya amsa sunan shi na soja , fuskar sa ya murtiƙe . Kusan mintina biyu tana
ƙame kana taji ya furta “ Fara gudu ki dingi zagaye falon nan ina kallon time ɗin da zaki ɗauka
har ki gaji, Oya start it now! . Da gudu Ma'eesha ta fara zagaye falon inda kaiwa da dawowa
biyu tayi ta zube a ƙasa tana fara kuka tare da cewa “ Wayyo Uncles ba zan iya ba ,kuyi mun rai
�”.

Kallon ma'eesha duka suka yi , kana Ali ya kalli Abokin nasa yana mai sauraren Abun da zaice .

Ka gani she can't be a soja at all , just ka barta a hanyar ta na ƴa mace , ka duba ko gudun minti
ɗaya bata iya yi, Wannan zata fi dacewa da....... Enough , ya isa haka da ALLAH. Aliyu ya
katse shi cike da ɓacin rai kana ya kalli inda Ma'eesha take Yana furta mu wuce masauki na .
Yana furta zancen tare da miƙewa yana barin Falon . Kallon Areef Ma'eesha tayi kana tace “
Gaskiya kai me SO nane, thanks to meet you Uncle, ka bani Numbern ka don kana faɗa masa
gaskiya ....Ga Wayata! Murmushi Areef yayi kana ya Girgiza kai yana furta faɗa mun number
naki i will call later ”. Saurin Amsan wayar tayi tana loda masa nombobin tare da Ficewa da
Sauri bayan ta basa Wayan tana bin bayan Haidar ”.
[1/17, 5:00 PM] Real~Mamanteddy: *️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*

https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS
Subscribe to my channel@maman teddy.


28.
*Don Allah kar ki karanta wannan labarin indai baki biya kuɗin sa ba . Ga masu buƙatar
payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake.... Regular group₦500 Vip group₦1000
SPC payment₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta
Wannan number 08081202932*
________________________

Mami~.
Saukowa Mami take yi gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta , Haka zalika bata ko kallon gaban ta
, a haka ta sauko daga stairs ɗin nan . Su duka maida hankali suka yi ixuwa gare ta . Janar
Khalil da Kuma Jidder . Cikin Sauri Khalil ya miƙe daga tsaye yana kallon Mami kana bakin sa
ta furta “ Mami lafiya kuwa? Meke faruwa ne?” . Kallon shi Mami tayi wacce take isowa inda
suke. Kamin ta juya tana kallon direction ɗin da Daddy yake shima ita yake kallo tare da jiran
jin Menene ke faruwa don babu makawa yasan da Aƙwai Abun dake faruwa a halin yanzu ” .
“Janar....! Janar Wai yanzu Hajiya Alawiyya ke faɗa mun anga Hajara kuma tana Raye!

Saurin miƙewa General Saleh Yelwa yayi yana kallon Mami kamin cikin Sauri yace “ Me kike ce
? Hajara fa kike magana an ganta ? Wacce ta bar gida Na Tsawon sheƙaru sha shida(16) .
Ƙwarai Janar yanzu Alawiyya ke sanar dani, Wai yanzu haka tana Gidan Mahaifinmu Bara na
tafi yanzu ”. Tayi maganan tana gyara zaman Keys ɗin hannun ta tare da juyawa tana nufar ƙofa
. Cike da Rashin Sanin Wacece Hajara ? Jidder ta furta “ Mami zan biyo ki , Sannan kin manta
baki ɗauki mayafi ba”.

Hummm Jidder idan zaki biyo Ni bismillah amma mayafi bana takan shi a yanzu . Mami ta furta
tana mai saurin ficewa daga Falon .

Da Sauri jidder ta bi bayan ta , don itama a yau tana son sanin Wacece Hajara , duk da Tasan
Ƙanwar Mami ce , Amma bata san menene yabar da ita gida ba , kuma sannan a yanzu a wani
hali take ? Tabbas zata so ganin ta Wannan yasata bin bayan Mami cikin Sauri , Don sau da
yawa kafiyar Aliyu da gayunsa ana cewa “ Babu inda yabar ƙanwar Mami wato Hajara , sai dai
ita kuma rashin son jama'a musamman talakawa , sam bata son raɓuwa da ƙaasƙantattu , a
cewan ahalin Wai ita wayayyace Shiyasa . Bayan Mami jidder tabi inda ita take Driving, Mami
ba ɓangaren Hannun dama gaba Ɗaya hankalin ta baya jikin ta duk ta ƙosa ta gan ta gata ga
Hajara , damuwarta na tsawon shekaru ”.
Early in the morning
7:00am......

Gudu take yi kaman tare da jijjiga jikinta tana kaiwa da komowa takaici duk ya ishe ta ga zufa
dake tsatstsafo mata . Ƙwallah na bin kuncinta . Tun da nake ban taɓa ganin mugu irin Uncle
Aliyu ba . Ta furta tana kallon can inda yake daga nesa yana kallon yanda take running exercise
ɗin, shikam Hannun sa Ɗauke da Wani mug na coffee yana kaiwa bakin sa a hankali ƙwance ”.
Go! go...!!!

Ta tsinkayi Muryar sa daga can yana mata magana ganin ta tsaya , tana hutawa .

Da Sauri Ma'eesha ta ɗaga ƙafafunta tana cigaba da gudun tare da kukan zuci dana zahiri .

Fiye da minti talatin tana a haka , kana ta fara ganin Jiri Jiri na ɗibarta .

Cak taja ta tsaya tana ganin hazo² tana ganin duniyar na juya mata zuwa gida da yawa .
Cike da ɗaga murya babu wasa ya furta “ Tsayuwar mene kike yi anan , Ma'eesha na iso inda
kike ranki zai ɓaci , zan zane ki anan Wurin , a haka ne zaki je training ɗin Sojan? What kind of
nonsense exercise is that? . Zaki Cigaba ko kuwa sai na ƙariko nan??? Ya ƙare maganan cike
da Tsawa da Ɗaga murya mai tare da amsa kuwa na cikakken Gwarzon namiji”. Maimakon ya
ga tayi wannan kiɗimewar da ta saba yi a duk sa'ilin da taji Muryar sa ko faɗan sa amma a
yanzu sai gani yayi tayi baya luuuuuuuuui tana zubewa a ƙasa sharaffff”. Hasbunallahu
wani'imal wakeel Innalillahi wa'inna.....ƙasa ƙare magana yayi da Gudun sa a matuƙar kiɗime ya
nufo inda take yana ɗagota cak tamkar bai ɗauki mutum ba , kaman ƴar tsana ya ɗaga....yana
mai barin wurin tare da nufar moton sa yana bude gidan baya yana shimfiɗa ta , don ya lura Ko
numfashi bata fitarwa ,ƙwance take tayi sharɓan wannan yasa hankali a tashi ya fice daga
Barikin Sojojin yana nufar Wata asibiti na kuɗi (private hospital) dake kusa dasu .

A harabar asibitin tun daga saman Upstairs ɗin Wannan katafaren Asibitin Nurses da gudu suka
fara saukowa zuwa Farfajiyar ajiye moto inda suka hango Aliyu Haidar fuskar sa a kiɗeme, haka
gumi ke zubo masa . Idanun sa sun kaɗa sunyi jah . Ɗagota yayi tamkar ƴar tsana yana saɓa ta
tare da wani irin manna ta da ƙirjin sa . Su kam Nurses hango kalon handon jikin sa na soja ne
yasa su gudu irin haka , don sun san halin sojoji da bakar zuciya . Ƙarikowa garesa suka yi
suna kai hannu tare da Kokarin Amsar Ma'eesha tare da cewa “ Yallaɓai kawota mu bata
taimakon gaggawa”. Hummmmmm wata irin numfashi ya sauke tare da Ajiyar zuciya mai nauyi,
fuskar sa ta sauya , a hankali cike da sarewa da karaya ya furta “ Rayuwata ce! , ku yi mata
kallo tun daga nan , idan zaku iya tada mun Ma'eesha na tsaya , idan ba zaku iya ba , na yi
gaba na nemi asibitin da suka amsa sunan su ....idan kuma kuka ce zaku iya ,amma kuka ɓata
mun lokaci abubuwa suka wuce sai daga baya kuka gaxa... wallahi tallahi na rantse da ALLAH
Ma'eesha ta mutu a asibitin nan ko wani Abu ya ƙara samun ta kowa na Asibitin nan babu mai
fita da rai .�buɗe baki Nurse Zulfa'u tayi kana ta kalli nurse narret tana cewa “ Sister
ma'amshe ta.....Saurin katse ta Nurse narret tayi tana kai Hannun ta tare da Amsan Ma'eesha
daga hannun Aliyu kana tace “ Cool your mind Sir , everything will be okay ” .kamin ta jira jin
mene Haidar zai furta da Sauri ta nufi Emargency da Ma'eesha .

Yallaɓai taho ga wuri ka zauna kamin mu fito .

Muryar nurse Zulfa'u ya katse Ali wanda yake kaiwa da kawowa , Goshin sa har wata jijiya ya
fito masa na tsananin tashin hankali . Kallon banza ya watsa mata yana cigaba da kaiwa da
komowa hankalin sa sam baya jikin sa . Baya ma sani Mene yake fadi a halin yanzu , tun daga
zuwan sa , baya tsammanin zai dawo natsuwar sa sai idan Ance masa Ma'eesha ta dawo
hayyacin sa. Tabbas a yau a kuma yanzu ya fahimci har a yanzu Ma'eesha rayuwar sa ce! Ba
wai kallon da yake kokarin mata bane a yanzu , har a yau soyayyar nan nashi da kulawar da ya
saba tun daga yarintar ta babu abin da ya ragu . Fiye da mintina talatin yana a haka gumi ya
jiƙa shi sosai , don tuni nurse Zulfa'u ta gudu ta bar sa anan , don ta tsorata da lamarin Aliyu
Haidar, ita ko a labarai bata taɓa jin na soja irin wannan ba. Zafin ransa yayi yawa ƙwarai .

Wannan yasa ta nufar emergency don ayi komai a gaban ta , idan Ma'eesha ta tashi to ta tsaya
idan kuwa aka samu akasin haka , tabbas ita zata fara guduwa daga Asibitin tun kan a sanar
mawa Aliyu Haidar ”.

Shikam Ogan namu Aliyu Haidar jin shiru tsawan mintuna kusan Arba'in yasa Shi fara tunanin
nufar emergencyn , dai dai nan Wayar sa ta fara ringing tare da waƙar mum my heart ❤️.
Wannan yasa shi fahimtar mai kiran tun kamin ya kai hannun sa ya ɗaga sunan Mami ya
bayyana masa . “ Cikin sauri tare da dai daita natsuwar sa yana ƙaƙaro murmushin dole tamkar
wacce Mami ke a gaban sa ya furta “ Mami Howfar? How is your day? . Fine HAIDAR where is
my baby love ? Ina Ma'eesha na take ? Ta katse shi cike da annashuwa . Ƙirjinsa ne ya buga
masa da ƙarfi wannan yasa shi ɗan kai hannun sa yana dafewa kana yace “ Mum she's well ,
Yanzu ta samu barci amma zuwa Anjima zan kira ki kiji Muryar Babyn naki.

Murmushi Mami tayi mai sauti kana tace “ Alhamdulillah har naji sanyi da ya kasance tana lafiya
a yanayin ka ko baka faɗa mun ba nasan Baby Ma'eesha tana jin dadin zaman ta anan , Ka
kula mun da ita sosai Ali kana jina ?"…yeah...Yessss Mami ya furta cikin ɗan kame kame . Cikin
sanyi cike da rashin Fahimtar komai Mami ta cigaba da cewa “ Ina SO Aliyu ka kula mun da
Ma'eesha don Allah ko bayan Raina, bata da kowa da ya kai ka a rayuwa , ina so ka riƙe
Ma'eesha ba matsayin ƴar uwa ba , ba ƙanwa nake so ka riƙe ta ba , ka riƙe mun ita tamkar
rayuwar ka! A taiƙaice da da hali ka gatanta fiye da kowa ciki har Dani kai na. Ka ɗauke ta
tamkar ƴar da ka haifa ko ma fiye da haka . Idan kayi mun wannan To ka gama mun komai
Aliyuuu don Allah ka sauke zafin ranka a kan ta , still now she's a child yarinya ce ƙarama ka fini
sani ka kula mun da ita sosai ko bayan rai na ”. Mami ki daina wannan maganar inshallah nayi
Miki Alƙawari zan kula da ita ”. Daƙyau Haidar thank you my SOJA . � dariyar yaƙe yayi yana
jan Ajiyar zuciya tare da cewa “ Love You ma'am , bye bye ”....ƙitttt ya datse kiran yana Fara
nufar emergency don ganin halin da Ma'eesha ke ciki .

Kai tsaye ya faɗa inda yaga Wayan babu Ma'eesha babu labarin ta tamkar ba anan aka shigo
da ita ba� . Keeee!!! Ya daka ma wata nurse Tsawa inda sai da kayan aikin hannun ta suka
faɗi ƙasa . Malama ina yarinya ta take ? Ya furta a zafafe idanun sa suna jajir tamkar garwashi
jijiyo na ratso masa ta ko ina . Itace Ma'eesha ko? Ta far...far... farfaɗo an kai ta Ɗakin hutawa”.

Ta ƙare maganan tana inda inda don ta tsorata da Aliyu . Huuuuuuuwwwww.....Ya Jah numfashi
mai ƙarfi kana tamkar ba shi ba , ya furta “ Na gode na gode da kuka taimaka wurin ceto mun
rayuwar ta . Zaki iya kaini ɗakin da take . Special room muka kai ta sir , amma muje na kai ka
yanzu . Thanks....ya furta yana bin bayan ta ”. Sun fito daga emergency room dinnne kiran taxt
massage na mami ya shigo masa inda idanun sa ya fara rawa yana ganin Saƙon kaman ba dai
dai idanun sa ke gani ba .

Ga abun da ta rubuta kamar haka ya fara karantawa .
_Hello Am sorry my son , na manta ban faɗa maka duk da Abin na raina , ka tayamu farin ciki
mun ga ƙanwata Hajiya Hajara wacce ta ɓata Tsawon shekaru goma sha biyar . Yanzu haka
tana gidan Hajiya , kuma tana cikin ƙoashin lafiya naji a yanayin ka ɗazu kamar kana busy
shiyasa Nima na manta . But a ko wani lokaci kuka dawo zaku haɗu inshallah, please take care
of my baby girl , idan ta farka kace mamin ta na gaishe ta ”._

Dafe kan sa yayi kana ya tsaya cak yana dakatawa da tafiyar a sarari yana furta “ Mom Hajara
fa tace ?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login