Showing 15001 words to 18000 words out of 29267 words

Chapter 6 - Masarautarmu Book 3 Complete Hausa Novel By Sumayya Takori Kabara .pdf

bude fuskarta daga cikin laffaya ba, duk
kokarin Yarima Sageer na son gano halin da kwayar idon ta ke ciki a wannan lokacin hakan bai
yiwu ba. Tana jin sanda Uncle Sageer da yan uwan sa mata da maza da abokai suka yi ta yi
mataruwan liki. Har tsakar dare ana wannan shagalin kafin taron wushe-wushe ya tashi. Kuma
Yarima bai samu damar ganin Saadeprivately ba har su Maman Rahimah suka kama ta suka
koma cikin gida.

Ranar asabar kuma aka yi KELATUL wato aka wanke wa amarya gashi aka yarfa mata kitson
bare-bari kanana-kanana sun kai guda dari uku. Da yammacin ranar kuma aka yi biji-ginata
inda aka shimfida manyan tabarmi aka ajiye amarya a tsakiya ana kida ana wakoki irin na
barebarin Askira. Bayan an yi mata kwalliyar masarauta. Ranar lahadi aka yi kaulu na amarya da na ango da safe. Kaulu shi ne za a ajiye miyar yauki
a gaban amarya bayan an mata kitso da kwalliya. Baaba suka goya amarya suka kai ta filin da
ake yin kaulu. Yan uwan Yareema na ciki daya da na sauran dakunan suka dinga dibar wannan
miyar yaukin suna shafa mata, sannan daya bayan daya suka zo suna ajiye mata kyaututtuka
na bajinta haka sauran matan Maimartaba.
Da yammacin ranar aka yi dubdo, wato wunin biki a harshen Hausa. Biki ya yi biki ba ka jin
komai a masarautar Askira sai kade-kade da bushe-bushen algaita. Duk wadannan events din
da ake yi ango bai ga fuskar amarya ba, kuma Fulani Bilkisu ita ke da alhakin yin miskero, wato
abincin da ake kai wa gidan amarya. Kuma ita ke ciyar da ango da amarya dadadan girke-girke
masu kara lafiya da kuzari.
In ta girka sai kuyanginta su kai sassan Yareema su ci shi da Awaisu. Korafi kam Awaisu ya
sha shi gurin Yareema, kan cewa shi fa bikin nan ya ishe shi hayaniya ta yi masa yawa. A ba shi
amaryarshi kawai su kama hanya. Shi ba auren fari ba to wadannan aladun duk na menene?
Awaisu sai dai ya yi murmushi don ya gama gane Yareema Sageer ya karbi auren nan da
hannu bibbiyu. Har fiye da auren sa da baturiyar sa mai kananan ido. Auren da yake kira na
soyayya kuma babu ya shi. Abin da bai sani ba, kuma yake matukar son sani shi ne, da ma can
Yareema yana son Saade ne ko sai da aka ce an aura masa ita ya fara son ta?? Sai da Baaba (kannen Maimartaba mata) da kannen Ya Gumsu suka shigo tafiya da amarya
ne idonta ya karasa raina fata. Domin a baya kallon komai take matsayin almara ko mafarki.
Saadatu ta kankame Fulani tana ihu sosai ita ba inda za ta je ta bar Fulani.
Sai yanzu ne ta tabbatar da gaske an yi mata aure, kuma ba da kowa ba da Yariman Askira,
Uncle Yareeman da ta ke girmamawa fiye da kowa in ka dauke iyayenta, Dr. Sageer a NTNU,
kuma mijin Aisha-Sultana.

A karshe Baaba sai goya amarya suka yi tana kuka tana komai, kannen Yareema mata su
Houdda sai tsiya suke mata, ko irin nasihar nan ta uwa Fulani ba ta samu damar yi mata ba
sabida kukan da ta ke tun safe ya daga mata hankali. Su Mama (Babar Raheema) da su
Raheeman suna gidan amarya tun safe inda ake aikin jere da kafi. Duk wasu furnitures da aka zuba a sassan Saade dake gidan Yarima Alhaji Kyari ne ya taho
da su tafiyayyu daga kasar Italiya, wadanda Maimartaba ya yi mata an wuce mata da su Abuja.

******

SAADE A GIDAN YAREEMAN ASKIRA
Daga ita sai Hanne da Raheema a bedroom din da aka zaba aka shigar da ita, wanda shi yafi
kowanne kayatuwa, sai kuyangi da bayin Fulani da ke ta kintsa duk inda aka bata. Fadin
dukiyar da Askirama ya dankara a gidan Yareema Sageer bata baki ne, ki sa a ranki gidan
Yariman Askira mai jiran gado, shi ke nan zance ya kare. Gida ne ginin sarauta (royal mansion) wanda aka yiwa zubi na zamani,turawa suka zana shi

suka kuma zo suka gina daga Amsterdam, da aka yi wa sassan matan aure har hudu, komai da
ke cikin wannan sashe shi ne a wancan sai bambancin kalar fenti. A sashen kowacce mace
manyan faluka ne bi-da-bi har guda Uku da dakunan barci Uku. Babun ce kawai babu a gidan
Yarima Sageer Yusuf Askira. Sassan Aisha Sultana shi ne na farko, sai na Saade sannan wasu guda biyu a rufe. An ware
bangaren bayi da hadimai daga can karshen gidan.
Sassan Yarima kuma yana upstairs wanda girmansa ya yi a hada sassan matan nasa guda
biyu. Komai da ke cikin sassan Yarima ya zo da shi ne daga Amsterdam kuma duk bayan
shekaru biyu ake fidda komai na gidan a sake, a yo odar wasu. A raba wa talakawan gari, ko
bayi da hadimai.
A can gidan Wazirin gari Ibrahim a dakin Awaisu Yarima Sageer ne tsaye jikin mudubin
dogon yaro yana sanya links din hannun farar shadda kal da ya saka, sai tashin kamshin
invictus dakin Awaisu ke yi. Awaisu ya kasa danne dariyarsa ganin irin kwalliyar da Yareema ke
yi wadda ko ranar da zai raka shi dakin Aisha-Sultana bai yi irinta ba, ya karkata hula ya sake
karkatawa yafi sau biyar, ya ga bata yi kyau ba ya cire ya sake canza wata, [to wancan aure ne
da aka riga aka kwashe albarkarsa tun a waje]. A ransa Awaisu godiya yake wa Allah yana
kuma adduar Allah ya sa auren nan ya zamo karshen duk wasu matsaloli na dan uwansa
Sageer.

Amma dai sai gobe za mu je sayen baki ko? Ka ga yanzu dare ya yi sosai, na san duk sun yi
barci bai kamata mu tada amarya ba tana barcin gajiyar biki irin wannan.
Inji Awaisu cikin seriousness.
Wata harara da Yarima ya juyo ya zuba masa sai da ta sa Awaisu durkushewa a inda yake
yana dariya. Kafin ya dago daga dariyarsa Yarima ya gama saka takalmansa ya fice yana fadin.
In ka ga dama kada ka je, da ma ba ni na gayyace ka ba, aure dai ka sani ba yau na fara ba
balle ka ce rawar kafa na ke yi.
Awaisu bai bar dariya ba da ma gwanin ta ne, ya saka takalmansa ya bi bayan Yareema
Sageer yana cewa,
Ko don in bata maka lokaci kafin ka shiga dakin Sa'adatu dole in bi ka.
Yarima ya girgiza kai jin abinda Awaisu ya ce, ya ce, Awaisu! Mind your language. Saadatu is
my step-sister rainon ta na yi wa uwarta alkawarin zan yi, kuma shi zan yi din. Zan ba ka
mamaki, jibi-jibin nan zan koma wurin mata ta.
Awaisu don dariya har da hawaye, ya ce, Aah Yarima, kada wata tara ta cika kuma mu zo
bikin radin suna, wannan rainon in dai kai za ka yi shi Saadatu ba za ta taba girma ba.
Suna ta barkwancinsu na aminai har suka karaso gidan sarki, don Yareema ya ce sai ya je ya
yi wa Ya Gumsu sai da safe, ya kuma nemi albarka kafin ya karasa wajen Saadatu.
[Da ya san abinda zai tarar, da ya yi wucewar sa kai tsaye dakin amaryar sa, in ya so da safe
ya zo tasani].
Dazu da yamma Yaa Maira ta kira shi cikin sirri sun yi magana, inda ta ce ya bi Ya Gumsu a
hankali da duk abin da ta ke so, don ba karamin yaki ta yi da ita kafin ta amince a yi bikinnan
cikin dadin rai ba.

Yarima ya yi sallama a hamshakiyar turakar mahaifiyarsa Ya Gumsu, Awaisu bai biyo shi ba
ya zauna a mota don ya ba shi dama ya gana da Ya Gumsu. Tana hakimce bisa kujerar
mulkinta sai karkada kafa take yi cikin izza lokacin da Yarima ya yi sallama. Ta hadiye wani
malolon abu da ya tokare ta a makoshi ganin irin kwalliyar da ya caba da bata taba ganin sa
cikin irin ta ba, wanda ke nuna yana farin ciki da auren diyar Fulani Bilkisu.
Har kasan kafafunta ya isa ya gurfana yadda suke gaida iyayensu, ya yi gaisuwa ta amsa
cikin dacin rai. Daga nan duk suka yi shiru. Yarima ya kasa ce mata ya zo neman albarkarta ne
zai shiga dakin amaryarsa, aka ce wargi ma wuri shika samu. Ita kuma tana ta kitsa abubuwan
da ta shirya fada masa ba tare da tunanin me zai je ya zo ba. Ya Gumsu ta dubi dan ta Dr. Sageer wanda kansa ke sunkuye a gabanta. Ji yake kamar ya yi
fiffike ya fice ya tadda Saadatu. Shi kansa ya rasa ko wane irin excitement yake ciki mai neman
karar da numfashinsa. Zuciyarsa har wani irin bugawa ta ke yi in ya tuna Saadatu zai je ya
tadda a matsayin matarsa yau, ba yar amanar da yake riko a gidansa ba kullum yana fama da
zuciyarsa a kanta.
Sai jin muryar Ya Gumsu ya yi a tsakiyar kansa.
An yi aure na gani, kuma na sa albarka kamar yadda Yaa Maira ke so. Maimartaba ma yake
so, amma Yareema ban yarda ka taba yar Bilkisu ba.
Ina nufin ban yarda ka hada shimfida da ita ba, don kuwa jinina ba zai gogi jinin Bilkisun
Askirama ba. Balle in hada zuria da ita. Na ba ka watanni uku ka zo ka kara aure, aure na
mutunci na gidan mutunci, duk wadannan matan naka tarkace ne, tunda babu jinin sarauta ko
daya a cikinsu. Na samo maka mata yar Sarkin Bauchi, sunanta Hajjaju, mun gama magana da mahaifiyarta
ta ce kana iya zuwa ku fara fahimtar juna, in dai da gaske ni na haife ka Yarima wannan shi ne
umarnina.
Ta mike ta shige turakar barcinta ta rufo kofa ta bar Yarima sai tsiyayar zufa yake daga
tsugunne, ya rasa inda zai sa kansa. Don kwata-kwata bai fahimci inda zancen Ya Gumsu ya
dosa ba, ko kuma ya ce ya fahimta, kwakwalwarsa ce ta kasa fassarawa.
Ya Gumsu na da masaniyar cewa weakness dinsa shi ne Mace. Macen ma ta aurensa wadda
zuciya da ruhinsa ya dade yana so da kwadaituwa akan ta, to in ta ce ba zai tabbatar da
aurensa da Saade ba, neman matan ta ke so ya koma wanda ya yi wa Maimartaba alkawarin
ya daina? Ya yi wa Ubangijinsa alkawarin daga ranar da ya mallaki Saadatu ya daina? Wane
irin aure sai ka ce namamajo, aure wata uku ya zo ya kara aure wai Hajjaju? Yo shi ko sunanta
Makkah ina zai kai ta duk son matansa?
Guda biyun sun ishe shi sabida shi ba wai mata yake so ya tara ba, in ya samu abunda yake
bukata a guda daya zai iya kama kan sa. Abin da ya rasa daga matarsa Aisha-Sultana (sai jar
fata da yalolon gashi) wanda ya kai shi ga bin son zuciyarsa da zugar aboki Ziyad maimakon ya
nemi karin aure. Rana daya Mai Askira ya hutar da shi da yake shi uba ne mai tsinkaye, mai son gyara
rayuwar yayansa ba ya dagula ta ba irin Ya Gumsu. Shi bai dauki wannan auren da ta ke son yi
masa gata ba, sai hanyar huce haushinta a kan auren diyar kishiyarta Fulani Bilkisun Askirama.
Amma ya sani a yadda Ya Gumsu ta ke kan dokin zuciya irin wannan, ba wasu kalaman
lallashi da zai yi amfani da su da za su sa ta saurare shi. Mafi aala ya nisance ta har sai ta
huce, tunda dama ga alfarmar da ita ma Fulani Bilkisun ta nema daga gare shi, na cewa zai bar

Saadatu ta gama makaranta kafin ya dora mata nauyin aure.

Jiki a salube Yareema Sageer ya baro turakar Ya Gumsu, ya tadda Awaisu a mota, bayan
dogarai sun bude masa ya shiga, Awaisu ya ja motar ta kofar shiga gidan Yareema ta baya
suka bi, duk da cewa ba wata tafiya ce mai nisa ba, trackable distance ne daga masarautar.
Hanne, Raheema da Saadatu ne kadai a dakin, Hanne da Raheema hirar tsaruwar gidan
Saadatu suke yi da komai da ke cikinsa. Yayin da Saadatu ke ta kuka har zuwa lokacin, tun
suna lallashinta har sun gaji sun kama hira sun koma yi mata dariya. Hanne ta ce,
Sai ki yi ai, dadi ne ya yi miki yawa. Ni mijin nake so ya gudu ya bar ni, ke Allah ya kashe Ya
ba ki kina so ki yi butulci, kukan dadi ki ke yi, ki ci gaba Saade.
Raheema ta ce, Ni in ni ce na samu wannan gidan na Saa ai bude ido zan yi in sha kallon
abuna mu more niimar da Allah ya ba mu.
Sai jin gyaran muryar Awaisu suka yi daga bakin kofa. Ya yi sallama suka amsa, sannan ya
dan shigo ya dube su ya ce,
Me kuke jira ba ku kama gabanku ba?.
Hanne ta ce, Kudin sayen baki mana!.
Ya yi dariya don daga jin maganarta ya san yar kauye ce futuk, ya ce,
Ai ke ce sayen bakin amma fadi me ki ke so a ba ki ki fito ki bar Yarima da Sa'adatun sa?
Sai ga Yariman ya iso kofar dakin ya ce cikin kasaitarsa da muryar da ke gigita Saade har
cikin kwanyarta. Ba jimawa kuwa jikin ta ya hau tsuma.
Awaisu please drop them at home, na gaji da yawa.
Awaisu ya ce, Sun ce kudin sayen baki suke jira.
Ya ce, ka ba su ko me suke so, amma ku kama gabanku dukkanku, har kai.
Ai kuwa Saade ta sake rushewa da kuka ta kama hannun Raheema ta kankame.
Yanzu tafiya za ku yi da gaske ku bar ni ni kadai Raheemah?
Yareema ya jiyo abinda Saade ta ce, da kukan da ta ke yi mai ratsa zuciya, zuciyar sa ta
motsu, ba zai iya jure jin sautin kukanta ba, daga Awaisu har su Raheema ba su ankara da
sanda ya shigo dakin ba, sai sunkuyawarsa da daukar Saadatu kacokam a hannayensa biyu
kamar ya dauki karamin yaro, ya juya ya fice yana ce da su.
please....Mun sallame ku, mu kwana lafiya.

Saade wadda kanta ke rufe ruf cikin laffaya tana aikin kuka, bata gane me ke faruwa ba, har
sai da Yareema ya soma hawa matattakala da ita a hannun sa,wadda zata sada su da turakar
sa, sannan ne ta gane a hannun Uncle Yareema ta ke dungurugum, ta hanyar jin kamshin
invictus paco rabbanne da taushin hannayen sa da ya mamaye ta. Ta kuma ji an raba ta da
kasa kacokam. Kukan ya makale don kansa ta koma salati tana wutsil-wutsil da kafafunta. Su
Raheema me za su yi ba dariya ba?
Yarima bai sake bi ta kansu ba ya bi matattakala da Saade a hannunsa zuwa upstairs dinsa.

Bai dire ta a koina ba sai a kan sofa. Yana ajiye ta tana zabura tana mikewa suka tsaya a
tsaye kamar zakaru suna kallon-kallo, idanunta jazur wadanda suka sha kuka suka koshi.
Idanunsa a lumshe, wadan suka jiku da soyayya. Ba ta ankara ba ta ga Dr. Sageer ya juya cikin

tafiyar sa ta kasaita, ta dauka daya dakin zai shiga don rage manyan kayan dake jikin sa, don a
sanin data yi masa bai iya zama da kaya masu nauyi na tsayin lokaci, ta samu damar da ita
kuma zata fice ta koma kasa.
Maimakon hakan data yi hasashe, sai gani ta yi ya isa ga kofa ya murzawa dakin keydin dake
jikin kofar, ya kuma zare mukullin ya jefa a aljihun gaban rigarsa.
Ya koma can jikin gado yana rage nauyin kayan alfarmar dake jikinsa, ya cire babbar rigar ya
ajiye a gefe, sannan ya zauna a bakin gado ya dauki wayarsa yana daddannawa ya baiwa
banza ajiyar ta. Har zuwa lokacin Saade na tsaye inda ya barta kamar mutum-mutuma. Ta kasa
motsawa ko nan da can. A yadda Yarima ya ganta ya san ba karamar rigima ta ke ji ba, sai motsi take da baki amma
ta kasa magana. A yadda yake ji shikuma ya shirya wa kowacce irin rigima da za ta zo da ita,
koda zasu babbaka kan su a dakin, tunda finally ya mallake ta shi ke da nasara cikin kudura da
iradar Ubangiji, ba don ya isa ba, babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login