Showing 18001 words to 21000 words out of 29267 words

Chapter 7 - Masarautarmu Book 3 Complete Hausa Novel By Sumayya Takori Kabara .pdf

tsumi ba dabararsa. So duk wani protest da zai zo daga
gareta zai iya shanye shi. Tunda iya wuya ita aka kwara. Matsalar sa daya sarautar sa bazata
barshi ya iya lallashin mace ba, ko ya nuna weakness.
Ta ya ya zai yi wasa da wannan kyautar bazata mai daraja da mahaifinsa ya yi masa?
Bai kara bi ta kan Saade ba yana ta latsa wayarsa. Da Awaisu yake magana kasa-kasa, inda
Awaisu ya tabbatar masa ya maida su Raheema wajen Fulani, ya kare da cewa,
Ka tausaya wa yarinyar mutane please Yareema. Ka rike ta amana. Ka san dai a cancanta
baka cancanci auren ta ba Allah ne ya dube ka da rahmar sa. Dubi yadda ta ke ta kuka kamar
ranta zai fita, wallahi ta matukar bani tausayi. Very young da aure.
Ya san Awaisu gaskiya ya fada. Amma a ki-fadi irin nasa. A kufule ya amsa.
Ina ruwanka da matar mutane da har ka kalle ta ka san kuka ta ke yi? Awaisu ka fita idona in
rufe, ka fiya shiga sabgata da yawa, ko kukan jini ta ke bai shafe ka ba, tunda dai ba Asiya ba
ce. Wannan maganar da kake yi ba hurumin ka bace. Awaisu sai dariya yake har Yarima ya
kashe wayarsa. Malama, in kin gama kukan ki yi mana light-off, zan kwanta.
Saadatu ta sake bare baki tana kuka da sauti kamar karamar yarinya, wane irin light-off ita da
namiji a daki daya? Kukan nata sai ya koma bai wa Yarima dariya, amma da yake ba gwanin
yinta ba ne, sai bai yi ba. Ga tension din da Ya Gumsu ta saka shi a ciki. Ga maganar Awaisu ta
taba shi. Ya mike zuwa closet din jikin bango yana canzawa zuwa pajamas. Ta gefen ido Saadatu ta sato kallonshi, ai kuwa riga yake kokarin sa wa ta hango
ingarmanphysique chest din Yareema Sageer Yusuf Askira da manyan damatsansa wanda ke
lullube cikin muscles da ba shiri ya sanya ta kauda idonta. Jikin ta ya hau tsuma. Ta kuma
durkushe a kan kafafunta ta bude shafin sabon kuka wanda ya ratsa har cikin kwakwalwar
Yareema Sageer.
Zuciyarsa ta karaya, ko kusa bai yi niyyar rarrashinta ba a yau, so yayi su yi duk irin rigimar
da zasu yi ya nuna mata ba gudu ba ja da baya a auren su duk rashin son ta da auren. Auren
su mutu-ka-raba ne. Amma kukan nata ya karya lagonsa, ya ji ba abin da yake so irin ya san
hakikanin damuwarta a kan aurensa. In dai har za ta yi hakuri ta zauna da shi cikin kowane hali,
shikuma zai yi duk abinda take so komai tsaurin sa.
Gefen gadon ya koma ya zauna, ya dunkule hannayensa cikin junansuya dora habar sa akan
su, ya rasa abinda yake masa dadi. A yanzu ko bata furta ba ya gama gane Saade bata

farin-ciki ko kadan da zamowar shi barin rayuwar ta. Wannan kukan data ke yi ya wuce na
amarci, kuka ne mai nuna an zalince ta, an katse mata rayuwa. A hankali ya kira sunanta da
wata irin lallausar murya da shi kansa yake tababar kasancewar tasa ce.
Saadatu!
Ba ta amsa ba, haka nan ba ta fasa kukanta ba, kukan da ke cin ran sa, sannan ba ta dago
ta dube shi ba. Tana nan durkushe a inda ta ke kamar an kafe ta a wurin, nannade cikin jar
sassalkar laffaya ta bare-barin usli. Yarima ya mike daga zaunen da yake a gefen gado, a
hankali ya soma takawa zuwa gaban Saade, kafarsa na nitsewa cikin tattausar kilishin tsakiyar
dakin.Pajamas ce ruwan toka kawai a jikin sa iya gwiwar sa samfurin Marks and Spencer, ya
daure tsakiyar da igiyar ta.
Yana zuwa hanayenta da ta rufe fuska da su ya kama, ya tsuke su tsakiyar tafukan tausasan
hannayen sa, ya bude fuskarta wadda ta yi kaca-kaca da hawaye ta yi jazur, da ka ganta a
wannan lokacin za ka san BAGGARA ce. Kamar uwa da uba duka shuwa-arab suka haife ta.
Hannayenta da ya kama ya ja ta a hankali zuwa jikinsa daga tsayen da suke. Bata kai shi
tsayi ba iyakacinta kirjin sa.Slowly yake rungume ta tightly, ta yadda kowacce gaba ta jikinsu sai
da ta hadu da yar uwar ta.
Haduwar fatar jikin su wuri guda tamkar jan wutar lantarki ya haifar ga kowannen su. Da wata
irin azama Saade ta soma kokarin janye jikinta daga na Yarima Sageer, saboda wani alamari ne
da bai taba faruwa da ita ba (physical contact) da kowanne Da namiji, balle wanda ta ke wa
ganin matsayin babban Yayanta. Tsatstsauran rikon da Yarima ya yi mata ya sa ta kasa kwacewa, tun tana kokawar da
mutsu-mutsun kwatar kanta har ta gaji tubus! Ta bari, hawayen fuskarta Yareema ya soma
wiping da lips dinsa, wanda hakan ya jefa Saade cikin wani hali da ta kasa ganewa. Wani
ignition ne tamkar electrical shocking ke yawo a cikin gangar jikinta a duk lokacin da lips din
Yarima ya sauka a kan fatar fuskarta. Duk da haka kokari ta ke ta kwace jikinta amma bai bata
damar hakan ba.

Kina so in cika ki Saadahtouh?
Muryar Yareema Sageer tamkar ba tashi ba. Ta zama very pale idan aka kwatanta ta da ta
dazu da yake magana cikin izza da sarauta.
Kai ta daga, domin kwarai ta ke so ya cika tan ko ta shaki numfashi yadda ya kamata, sabida
ba ta saba da hakan ba. The feeling is awesome, and their closeness is so intoxicating.
(Kusancin ta da shi mai bugarwa ne). Kai za ta iya rantsewa babu namijin da ya taba rike mata
hannu in this manner ta ji irin abinda ta ji yanzun tun tasowarta, don haka komai da Yarima yake
yi a yau is so strange to her, zuciya da gangar jikin ta sun kasa karbar sa.
Maimakon ya cika ta kamar yadda take fata, sai ya kwantar da kai gabadaya a kafadun ta ya
kanainaye cikin jikin ta. Har tsayuwa ta soma gagarar ta domin ya saki duka nauyin sa a jikin ta,
amma yasa hannu daga bayan ta ya tare ta.
Yareema ya soma magana da murya mai kassara zuciyar diya mace, mai nuna karbar laifi da
shirya repenting, zaka rantse ba shine Dr. Sageer din da ka sani a NTNU ba. Kuma Yariman
Askira mai jiran gado. Mafi soyuwa a zuciyar Mai Askira.
“Na ji kuma na yarda da korafin ki na cewa an miki laifi an aura miki mai yin zina. Ba tare da
an nemi yardar ki ba. Ba zan iya cewa kin yi karya ba. Sai dai kada ki manta su din iyayen mu

ne bamu da kamar su, nima baa nemi yarda ta ba, da an nema da na gaya musu ban cancanci
mallakar pure soul irin ki ba Saadah!.
Tunda bakin alkalami ya riga ya bushe ni da ke duka bamu da abin yi banda fuskantar reality
na rayuwar da ke jiran mu a gaba, mu manta da ta baya. Ko me ki ke so zan miki Saadah, in
har za ki amince ki zauna da ni. Duk sharuddan da za ki kafa min a zamanmu zan bi su, in dai
za ki ci gaba da amsa sunan matar Sageer Askira. Saadatu this is not the right time to discuss anything sensitive like this, dukkan mu hutu muke
bukata, don haka so nake ki kwanta ki huta na gaji Saadahtouh, bikin Askira mai wahala ne,
hutu kawai nake bukata yanzu, ke ma kin gaji da hidimar bukukuwan mu na aladah, ki yi hakuri
da kukan nan haka mu kwanta mu yi barci. Mu bar wa gobe tattaunawar, komai dacinta zan
saurare ki!
Na yi alkawarin canza komai na rayuwata zuwa mai kyau daga ranar dana mallake ki
Sa'adah na yi alkawarin nan.

Ka bude min kofa in fita to.

Karo na farko da ta yi magana tun shigowarsu dakin. Domin kalamansa sun sanyaya mata
zuciya.
Saadahtouh, ke matar aure ce yanzu, kuma macen arziki ba ta raba makwanci da mijinta sai
bisa lalura.
Muryar Saade bata fita sosai sabida kukan da ta sha. Ta ce. Don Allah Uncle Yarima ka bar ni
in koma wancan dakin, ni ba zan iya kwana daki daya da kai ba. Ta fadi da iyakar gaskiyarta.
Me ki ke tsoro? In kin kwana gado daya da mijin ki Malaiku ne za su yi ta sa miki albarka har
garin Allah ya idasa wayewa, musamman if you act as my messeuse (idan kika zama mai min
tausa) duk jikina ciwo yake mun saboda zirga-zirga da hayaniya. Please Saadah help me... Ya
fada yana kara makalkale ta ta yadda suka dunkule wuri guda kamar curin alkaki, ba tare da
Saade ta san yaushe hakan ta faru ba Saboda gabadaya muryar Dr. Sageer ta gama kashe duk
wani kuzarinta. Ta saukar mata da wata irin kasala.
Ita ma ba ta san me ta ke tsoro a kwanansu daki guda bisa gado guda babut shes
really-really afraid, wani abu ne STRANGE a gare ta, don bata taba ganin inda akai hakan ba.
Duk da ta san a yanzu an daura musu aure amma zuciyar ta ta kasa karbar wannan sabon
dingimemen sauyin da sauki. Tana wannan tunanin mai matukar dagula zuciya, ba ta yi aune ba sannan bata tantance
komai ba ta ji Uncle Sageer ya soma warware laffayar jikin ta tun daga sama cikin nutsuwa har
ya sauketa kasa tsaf, ya saura daga ita sai underwear din dake jikin ta, kallo daya Dr. Sageer ya
yiwa Saadatu cikin fararen under wear ya ji komai na duniya ya tsaya masa; including
numfashin sa.
Daga hakan ya sunkuce ta ba tareda ya tsaya sake kallon ta ba, bai dire ta a koina ba sai a
royal bed din su, ya ja wani lallausar duvet ya lullube su, tare da latsa makunnin lantarki daga
nan inda ya ke kwance. Fitilu shudaye suka maye gurbin masu haske (dim light).
A dirowar jikin gadonsa ya bude ya fiddo turarensa Invictus (Paco Rabbanne) ya soma feshe
su dukkan su, ya ce.
Bana son wadannan turarukan matan barebarin da aka gumbuda miki, daga yau kada ki

sake shafa su, we will be using the same scent, wadannan sun cika karfi da yawa hawa min kai
suke yi.
Daga yau za mu dinga using nawa tare (Paco Rabbanne), you can use it too ba shi da karfi.
Saade ta zumburo baki kamar yana ganinta, ai kuwa ya gani ta cikin dan hasken dim din
wanda hakan ya sa shi yin abin da bai shirya ba. A hankali ya soma sumbatar Saade tun daga
yatsar kafarta
At first hes doing it gentle kafin gabadaya ya koma hungrily, da gani za ka san abu ne da ya
dade yana fatan kasancewar sa. Ya dauki Saadatu diyar Fulani Bilkisu ya kai ta wata kololuwar
duniyar soyayya da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
A yadda Saade ta yi amanna ta mika wuya ko me Yarima ya nema a lokacin tabbas zai
samu, domin ba ta san inda Yarima Sageer ya dauke ta ya kai ta ba. Amma sai me? Kalaman
Ya Gumsu ne suka fado cikin kwakwalwarsa suka katse duk wani hanzari nasa.
Ban yarda ka taba yar Bilkisu ba, ban yarda ka hada shimfida da ita ba.
Sai kuma na Fulani Bilkisun
Ina neman alfarmar ka daga mata kafa har ta kare makaranta.
Yarima ya rasa inda zai sa kansa a wannan lokacin. Ji ya ke tamkar ransa zai bar gangar jikin
sa. A hankali ya mirgina ya koma can karshen gado ya runtse idanunsa yana ambaton sunan
Allah.
Saade na jin shi, amma ba ta san dalilin sa na janyewar ba. Da nutsuwa ta soma dawo mata
sai ta ji wata matsananciyar kunya ta kama ta. What happened like this? Wannan wane irin abu
ne mai tsauri da nauyi yake faruwa tsakaninta da Uncle Yarima haka?
Kanta ta tusa cikin pillow kamar ta roki gadon ya tsage ta shige. Tana jin saukar numfashin
Yareema a hankali har daga baya ta gane ya yi barci. Ta yunkura da zummar ta nemi mukulli ta
fice, amma sai ta ji caraf! Hannuwan Yarima sun maida ta kwanciyar, ya kuma sake mirginowa
ya rungume ta sosai a jikinsa. Bai kuma kara attempting komai ba, tun tana fargabar faruwar
wani abu makamancin na dazu har ta gane barcin sa ya yi nisa sosai.
Akai-akai Saade ke sauke ajiyar zuciya tana tambayar kanta, wannan shi ake nufi da auren
ke nan? Su dunkule su zama abu guda in every aspect kuma marufar sirrin juna? Sirrin da yafi
karfin kwatance ko fadar sa ga wani. As a university student ba za ta ce kwata-kwata ba ta san
manufar aure ba duk da babu wanda ya taba zaunar da ita ya gaya mata, duk sakewar da ke
tsakaninta da Fulani magana irin wannan ba ta taba hada su ba. Baggara akwai kunya tamkar
Fulani suke, sai dai kuma sun fi Fulani ilmin addini.
Sai goshin asubahi ta samu barci, kuma ko na minti daya Yarima bai yarda ya raba ta da
jikinsa ba. In ma ta yi kokarin zamewa tsaf cikin barcin zai kara kanainaye ta. Tun tana jin kunya
har ta gaji ta yi barcin ta a jikin sa. Ko don wannan turaren nasa mai dadin kamshi da sanyaya
zuciya za ta so su wayi gari a haka. Daren yau bakidayansa wani yanayi ne da ba za ta taba mantawa ba a tarihin rayuwarta. Ba
ta maraba da auren Yareema Sageer, ba ta kuma taba mafarkin faruwarsa ba, amma daga
daren jiya zuwa yau sai ta ji dama su dauwama a haka! Ba tareda wani dan adam ya kara ratsa
tsakanin su ba. The moment is awesome because its strange but pleasant ga Saade, don haka image din ya
tsaya a kwakwalwarta. Hoton ta makalkale cikin jikin Yarima Sagir, ya kasa bacewa dagascreen
na zuciyarta. A haka aka yi kiran assalatu.

Da yake ba ta dade da samun barcin ba, ko motsi ba ta yi ba. Har Yarima ya mike ya je toilet
din da ke makale da dakin ya kammala abin da zai yi ya fito Saade ba ta da alamar farkawa.
Duk da bahagon halin Ya Gumsu, a baya na gaya muku cewa yayanta akwai sallah.
Sai ya tsaya a daidai fuskar Saade yana taje jikakkiyar sumar kanshi. Yarfin ruwan a fuskarta
ya sa ta bude ido kadan, sai idonta cikin na Yarima. Da fari ta dauka a dakinta ta ke na Abuja,
amma ta san Uncle Yarima bai taba shigar mata daki a irin wannan lokacin ba.
Ta sha ganinshi da pajamas ko a gidanshi, amma ya kan daure tsakiyarta da igiyar jikinta,
amma yau bai daure ba, physique chest dinsa dauke yake da suma a kwance luf, wanda hakan
ya sa ta saurin kauda kanta. Sai kuma ta tuna wai fa ashe su din yanzu miji da mata ne.
Ajiyar zuciya ta kwace wa Saade daga kwancen da ta ke. Har sai yaushe kwakwalwarta da
zuciyarta zasu karbi reality na kasancewar ta matar Yarima Sagir ne?
Yareema ya mika mata hannu da nufin ta kama ya taimaka mata ta tashi, amma sai ta juya
daya barin ta rabu da shi.
Ya ce, Tashi Saadahtou mu yi jamin sallah kina makarar da ni.
Saadatu ta yi shiru, ta ya ya za ta iya gaya masa cewa, period ta ke yi?
Ba za ki tashi ba?
Ya fada for the second time yana mamakin abin da zai hana ta yin sallah, sai kuma ya tuna
mace ce, don haka ya juya ya tada sallarsa.
Har gari ya soma haske Yarima na sallah, ita kuma ta kasa komawa barci. Tunanin rayuwar
da za ta riske ta a gaba ta ke yi. Tunda yanzu rayuwarta ta zama dependent upon Yareema. Sai
yadda yayi da ita.
A baya shi din guardian ne, amma a yanzu matsayinsa ya zarta na kowa kenan including
iyayenta. Wannan ba karamin nauyi ba ne aka dora mata, wanda ba ta san ya ya za ta yi da shi
ba.
Ta duba ta laluba cikin tsokar zuciyarta ko za ta ga SO ko akasin sa a kan Yareema Sageer?
Amma sai ba ta samu ko guda dayan su ba, babu soyayya haka babu kiyayya tsakanin ta da
Yarima, sannan daga daren jiya zuwa yau alamuran Yareema Sageer masu ban mamaki ne da
suka soma rikita hankali da nutsuwarta. Tana nan kwance

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login