Showing 9001 words to 12000 words out of 29267 words

Chapter 4 - Masarautarmu Book 3 Complete Hausa Novel By Sumayya Takori Kabara .pdf

ratsin
golden, an yi masa dinkin riga da zani fitted, ta saka Fanna ta saka shi a kabbasa ya turaru
tukun ta feshe su da turarukanta na musamman, ta kuma zabo mayafin da ya dace da su kalar
golden sannan ta dawo dakin Saade, Hanne ta mika wa kayan, Taimaka mata ta shirya Hanne, tana da baki daga Abuja.
Tana gama fadin haka ta juya. Mamaki ya kama Saade, ita yaushe ta yi kawa a Abuja?
Kawarta daya Saidu ne, kuma Fulani ba za ta ce ta yi kwalliya saboda shi ba, watakila ya gaji
da nemanta a waya ne ya taho har Askira, amma ta ya ya Fulani za ta ce ta yi masa kwalliya irin
wannan? Sai ta mikawa Hanne kayan.
Bar kayan nan Hanne, Fulani ba ta san wanene ne ya zo ba.
Hanne ta ce, Tunda dai ta ce ki saka, to ki saka kawai, baki ganin kin bata mata rai ne?.
Ta mika mata zanin, daya bayan daya ta sanya, sai ga Fanna ta shigo tare da wata mata,
wadda Saade ta san ta mai kwalliyar Fulani ce during occassions, ta ce, Fulani ce ta turo ta ta yi
mata kwalliya.
Haka matar nan ta zaunar da ita kan stool ta yi mata wani irin light serene make up, karo na
farko da cute fuskar Saade ta ga sassanyan fentin bature, tana kunci tana komai matar bata
biye mata ba tunda bisa umarnin Fulani take, a ganin ta ma fushin da Saade ke yi ya kara ma
fuskar ta annuri, classique and gentle amaryar Yareema, [inji mai kwalliya cikin ran ta], bada
jimawa ba tuni Saade ta fito a beautiful Princess dinta.
Matar wadda babarbariya ce ta feshe ta da tsadaddun turarukan humra, sannan Fanna ta
kamo hannunta suka fito, Saade ta kasa magana bin Fanna kawai ta ke, Fanna ba ta tsaya da
ita a koina ba sai falon saukar bakin Fulani na musamman.
Falon shimfide yake da kilisai na alfarma da tumtum a koina, da hoton Mai Askira cikin nadi
da amawali windowsize a gabas maso kudu na dakin, sannan zagaye da golden din kujeru na
zamani. Har bisa royal chairs na falon ta kaita ta zaunar da ita, ta gyara mata lullubi, sannan ta
juya tana fadin, A fito lafiya uwargijiya ta, takawar ki lafiya Gimbiya Saadatu.

Fanna ta fita da kamar minti biyu, angon na Saadatu ya bayyana gabadayan sa cikin falon.
Yana takun sa na kasaita tamkar mai tafiya akan gajimare. Shalelen Askirama da Ya Gumsu.
Kanin Ya Maira da Mairam Murjanatu. Mijin Aisha Sultana. A yanzu kuma angon Saadatu saar
mata. Wato [Dr]Yareema Sageer Yusuf Askira. Kamar dama yana falon dake bin wannan tun
dazu yana jira.
A yau sanye yake cikin royal attire dinsa, shudiyar alkyabba da jamfa na wani rantsattsen
yadin filtex, hular kan sa Dara ce baka gashin jikinta na reto daga gefen damana fuskar sa ba
karamin kyau tayi masa ba.
Tunda Saadatu ta ke a tsayin rayuwar ta ba ta taba ganin mutum maabocin cikar zati, ilhama
da kwarjinin Yareema Sageer da ke tsaye nan a gabanta a yau ba. Gabadaya ya canza mata,
daga wayayyen dan bokon nan da ta sani mai tsukewa cikin suit da necktayil zuwa hakikanin
BASARAKE na gasken-gaske, sarautar ma ta Askira wadda duk yankin Borno babu kamarta.

Ji ta yi kamar ta narke a wurin lokacin da Yareema ya tako ya tsaya a gabanta, kamshinsa na
Invictus (Paco Rabbanne) da ke hargitsa ta ya mamayi hancinta. Ta sunkuyar da kai ta kasa ko
kwakkwaran motsi.Dr. Sageer ya yi taku daya, biyu, ya tsaya a gaban Saadatu, kwalliyar da aka
yi mata bai taba ganin ta da ita ba haka kalar kayan jikin ta ya matukar karbar lafiyayyar fatar
jikin ta, ya kara fiddo zahirin kyawun ta da kwarjinin ta na Shuwa Arab, duk wani fushi da ya zo
da shi da niyyar sauke mata a kan rashin kunna waya tunda aka daura aure, sai ya ji yana
melting yana bin rariya, yayin da wata matsiyaciyar soyayya ke maye gurbin sa.
Ya zuba hannuwansa duka a cikin aljihun sa, lumsassun idanun sa a kan ta, murya a
sanyaye kamar ba Uncle Yareeman da ta sani ba, ya ce,
Saadatu laifin me na yi miki ki ka ki kunna wayarki? Atleast mu gaisa ko? Rabo na da ke tun
zuwan mu garin nan. Kin san yadda na azabtu a kan hakan? This is sheer punishment! Ba don
Yaa Maira ba kenan har mu koma Abuja ba zan ganki ko na ji muryarki ba Saadatu, me yasa?
Do you know how difficult and tortured is this to me? Maimakon ta ba shi amsa sai hawaye suka zubo. Ganewa da ta yi cewa Yarima Sageer bai
cikin irin bacin ran da damuwar da ita take ciki akan auren bazatan da aka yi musu. Karewa ma
ya karbi alamarin da hannu bibbiyu. Har yana fadin rashin ganin ta tun zuwan su gidan ya
azabtar da shi. To dama can yana jiran hakan ne ko yaya ne? Ko dama akwai wani abu
makamancin so a ran sa da bai taba nuna mata ba sabida girman kan sa? Aka dauke ta a
bagas aka bashi don shi dan gatan Askira ne?
Hawayen da suka sa Yarima saurin durkusawa a gaban Saadatu ba tare da ya san lokacin da
ya yi hakan ba. Ya dora tafin hannun sa akan kafar ta. Zuciyar sa cike da fargabar kada dai
Saadatu bata farin-ciki da kasancewa cikin iyalin sa? Kada dai hawayen ta na nufin..bata yi
naam da zamantowa matar sa wani bangare na rayuwar sa ba? Idan hakan ne a ran ta shi yaya
zai yi da rayuwar sa yanzu? Ya riga ya afka a rijiyar da zurfin ta ya fi na gaba dubu. Babu mai
iya fito da shi sai Saadatu.
Already Saadatu ta dade da mamaye shi, ta mamaye kowanne gurbi da kowanne sako na
zuciyar sa ba tareda ya san lokacin da hakan ya fara ba…
Ya wayi gari ne ya gan shi dumu dumu a soyayyar Saade. A wannan lokacin hes helpless
idan Saade ta ce bata auren sa yaya zai yi? Bai iya sakin ta! Baa saki a gidan su, ko ana yi bai
taba sakin Saadatu. Ba kuma ya so ya nuna mata weakness din sa.
Ya daga hannu zai rike natafor the first time a tarihin rayuwar su don ya korewa kan sa
shakkun kasancewar ta mallakin sa a yanzu, ta yi saurin ja da baya cikin matukar razana! As if
lantarki ya jona mata. Tare da maida hannayen ta duka baya ta sarke su a bayan ta. Yareema
Sageer Ya daga lumsassun idanunshi yana kallon Saade, a galabaice, a susuce cikin wani
yanayi na damuwa da rashin sanin abin cewa.
A lokacin ne Saade ta soma shesshekar kuka a hankali, kukan da ya ratsa har cikin kwanya,
ruhi da zuciyar Yareema ya hargitsa shi, ya sake kai hannu zai rike ta, ta yi maza ta sake ja da
baya.

Kada ka kuskura ka taba ni, ni ba zan auri mai yin ZINA ba, Allah ya tsare ni, kuma ba zan
kuma bin ka Abuja ba!.

Cikin wata irin razana Yarima Sageer ya wara manyan idon sa ya dubi Saadatu, da iyakacin

girman su, a ina ta ji wannan maganar? Ya bude baki zai yi magana, ga dukkan mamakin sa
maganar ta makale ta kasa fita, kafin ya ankara Saadatu ta mike ta nufi kofa da zummar ficewa.
Da wani irin zafin nama Yarima ya sha gabanta, ya kama duka kafadunta biyu ya girgiza ta
da karfi. Sai da kashin kafadar ta ya amsa. Bata san sanda tace,
zaka balla ni!. A kausashe Dr. Sageer yace.
“Kin san da wa ki ke magana Saadatu? Are you scolding me?
Hawayen da ke tare cikin idanunta suka idasa gangarowa akan kuncin ta, ta ce cikin
karyayyar murya marar amo da rashin karsashi.
Im not scolding you. Kawai ina gaya maka abinda na dade da sani ne a kan ka. Na san da
wa na ke magana mana; Yarima ne, Yariman Askira, Yarima Sageer mai jiran gadon Askira,
amma ba mai halin real Askirama ba
Shi Askirama ba ya zina, matan sa ba sa shan giya, ba sa zuwa Bar, sannan suna yin sallah”.
Ta bude dukkan idanun ta dake jike da hawaye ta cigaba da cewa A gidan Yarima duk ana
yin wadannan abubuwan dana lissafa, don haka babu ni a wannan gidan. Matattarar shaidanu
da sabon Allah.
In kuma aka takura min sai na bi ka, wallahi zan gudu! Ba za ku kara ganina ba, da ma ba ku
san daga ina na zo barana daya kawai kuka ganni a gidan ku, don bani da gata ubana talakane
kuma ya mutu, ni sai a yi min aure ba izini na.
Saadatu ba ta yi aune ba idanun ta bakidaya a rufe, tana ta zubda rashin kunyar ta ta hanyar
fadin duk abinda ya zo bakinta wa Yarima, ta hakan ne kawai zata amayar da kuncin dake
zuciyar ta, tunda in ba shi din ba wa zata iya gayawa wannan? Burin ta ya ji haushi ya bar musu
sassan su, in yaso kada ya kara dawowa. Ba zaton ta ba tsammani ta ji Sageer ya janyota jikin sa gabagadi da wata irin azama da
zafin nama, jikin sa na shaking [tsuma] kamar kamar bai taba rike mace ba a tsayin rayuwar sa
sai wannan karon. Har kuma ran sa da zuciyar sa abinda yake ji kenan a zahiri. Kafin ta yi
kokarin zamewa ko kwacewa sai jin taushin bakin Yarima Sageer ta yi ya sauka a kan nata ya
sima sumbatar ta in an abrupt manner, wanda hakan ya rufe sauran bakar maganar da ta ke so
ta furta. Cewa ita a rasa wanda zaa aura mata sai mai yin zina? Ba gara Saidu ba? Kafin ta
tantance what is going to happen next? Dr. Sageer ya soma hawaye, bai taba nadama ba akan
rayuwar sa irin yau, gabadaya jikin sa yayi sanyi da kalaman Sa'adatu, ba tare da yayi shawara
da zuciyar sa ba ya fara sumbatar ta gently, expertedly, and then by dragging her closer, sai ya
cigaba da kissing dinta softly, then a urunce wato [da sauri da sauri].
Tun daga karkashin zuciyar sa sautin sumbar take fitowa tana bada sauti. Duk kokarinta na
kwatar kanta hannun Yareema ta kasa sai da ya yi sumbar mai isar sa tukunna, ya sanyata cikin
jikin sa a hankali ya rungumeta tsam-tsam ta hanyar hada bugun zuciyoyin dake cikin kirjin su
wuri guda, inama zata iya jin tari nadamar dake cin ran sa daga bugun kirjin sa? Yana yi yana
sauke kakkarfar ajiyar zuciya. Sai kuma ya bi hawayen fuskarta yana dauke su tsaf da lips din
sa. Ya dago fuskar ta da hawaye kadai ke zuba tana kakabin abinda ke faruwa a mafarki ne ko
ido biyu?
Dr. Sageer ya sanya fuskar ta cikin tafukan sa, sannan ya sake ta ya ja da baya kadan yana
jifanta da wani irin sassanyar kallo, wanda Saadatu ba ta taba gani a tare da shi ba. Gabadaya
ya rikide mata ya koma tamkar ba shi ba. Ga dai nadama ce fal da tsoron rasa Sa'ade a ran sa
tunda ta san ko wanene shi, amma abinda ya furta ba lallashi bane ba kuma nadamar dake

baibaye da shi bane. Yarima Sageer is always bold, baya yarda ya nuna weakness din sa a
komai.
Kin fara da kissing mai yin zina Saadatu, kafin ku sha giyar tare ke da matar sa. Daga nan ku
zarce BAR din ke da ita ku sha ku yi mankas ku dawo gida ina jiran ku. Na bar ki lafiya sai mun
hadu a kauyen naku na Tsanyawa in kin gudu, amma ina rokonki don Allah in kin tashi gudun, ki
fi ruwa gudu. Ya zuba hannuwa cikin aljihu yana kara jifarta da killing smile dinsa wanda shi kadai ya iya
abunsa, ya kuma san maanarsa.
Bai tsaya sauraron amsarta ba ya juya cikin sassarfa da takunsa na haiba da mulki ya bar
falon. Ya bar Saadatu a tsaye kamar an kafe ta a wurin. Ta kai hannu ta shafo kasan lips dinta a
hankali. Damshin yana nan. Haka kamshin mouth freshner din bakin sa yana nan. Shin abin da
ya faru yanzun da gaske ne ko a mafarki ne? Ta yi kissing da mijin auren tafor the first time a
rayuwar ta? Kuma ba kowa bane Uncle Yareema ne, guardian din ta na NTNU Dr. Sageer Yusuf
Askira?
Ta fi karfin minti goma a tsaye, ta kasa maida nutsuwarta, ta kasa yardar wa kanta abin da ya
faru ba mafarki bane, ta dauki everything as an illusion. Kafin ta ja matattun kafafunta ta zauna.
Me wannan ke nufi tsakaninta da Yareema Sageer? Ba dai wannan shi ne rayuwar kusancin da
ake nufi yanzu zasu yi tare har abada ba, maimakon tasu ta Guardian da step sister irin ta
baya?
Koda take yarinya karama ta san me aure yake nufi a darasin biology. Kawai sai ta ji kuka ya
kwace mata. Shikenan ita tata ta kare. Ta zauna a dandaryar kafet ta yi kukanta mai isarta.
Kanta cikin cinyoyinta, kan ta har sarawa ya shiga yi.
Fanna da ke jiran fitowarta daga daya falon, ta ga fitar Yarima da sassarfa da jimawa, da ta ji
shiru-shiru Saadatu ba ta fito ba, sai ta biyo bayanta ta same ta a zaune tsakiyar kilishin falon
tana ta kuka.
A zuciyarta ta ce, Dole ki koka Saadatu, wannan mutumin ya fi karfinki ta koina. Da dai sun
barshi da bayahudiyar matarshi ita kadai zata iya dashi, amma ina innocent yarinya irin Saade
ina fitinannen Yariman Askira? Tun suna yara suke da labarin sa cikin gidan nan, wa ya san irin
rayuwar da yake yi a Abujar? Fanna ta tsugunna da gwiwa bibbiyu a gaban Saade, cikin lallashi da ladabi ta ce,
Ranki ya dade ki yi hakuri ki tashi mu koma daga ciki.
Tana so ta gaya wa Fanna damuwar ta. Don ta san ita kadai ce a yanzu zata saurareta har ta
fahimce ta. Ko ta fada mata abin da Yarima ya yi a gare ta yanzun nan, da abin da ya ce da ita,
amma sai ta ji ta kasa. Maganar ta yi mata nauyin da ba za ta iya furtata ga kowa ba koda kuwa
Fulani ce. Ta mike cikin mutuwar jiki, Fanna ta kama hannunta suka koma ciki.
Ta gaban Fulani da su Inna Laure da ke zaune suna raba kayan daFulani ta diddinka musu
suka wuce zuwa dakin Saaden. Fulani ta daga kai ta dube su. Idanun Saade jawur da alama ta
ci kuka ta koshi. Ko me aka yi mata kuma? Fulani ta fada a ran ta.
Suka wuce zuwa dakin Saade inda suka tadda Hanne tana gyara dinkunan Saaden da aka
kawo daga wajen dinki. Fanna ta koma bayan shigar Saade daki.
Bisa gadonta ta haye ta ja duvet ta rufa har saman kanta. Ba ta son magana da kowa, don ko
Hanne ba ta jin za ta iya gayawa abin da Yarima ya yi mata wanda ya kara tsoratata da auren.

Ita ma Hanne har ta gama abin da ta ke ta yi wa danta shirin kwanciya ba ta tambaye ta
komai ba.
Fulani ta so ta kira ta don ta ji dalilin kukan da ta fahimci ta yi, wata zuciyar ta hane ta. Gara
ta bar Saade ta koyi rike sirrin auren ta yanzu girma ya hau kanta. In dai ba matsala ce wadda
ta zama dole su sani ba.

Washegari duka gidan ya rikice da hayaniya ana shirye-shirye. Kowa da ke cikin masarautar
nan ya ci wa bikin nan na Yarima buri da alwashi don huce haushin wanda ba a yi ba a aurensa
na farko.
Maimartaba ya aika da goron gayyata zuwa dukkan masarautun Borno guda bakwai, (Bama,
Borno, Dikwa, Gwoza, Shani, Uba sai kuma Askira wadanda su suka hadu suka bada Borno
Empire. Hakan nan ya aika da sakon gayyata har fadar Shehun Borno don haka Mai Askira ba
karamin shiri yake wa wannan auren ba. Duk wani gyara da ake wa amare na kayan mata Fulani ba ta yi wa Saade, banda Su dilke su
halawa da dukhan kafin a mata lalle, (mai gyaran jikin Fulani daga maiduguri ta zo ta mata
gyaran jiki), a cewarta Saade yarinya ce sai nan gaba in ta kara shekaru koda zata bata kayan
mata, duk da tana tantama idan Yarima zai daga kafar yadda ya alkawarta. Kodayake fa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login