Showing 24001 words to 27000 words out of 29267 words

Chapter 9 - Masarautarmu Book 3 Complete Hausa Novel By Sumayya Takori Kabara .pdf

Sarki. Wannan kuwa ko asalin ubanta ba mu sani
ba.
Idanun Yarima suka kada kamar gauta, ya bude dukkan idanunsa yana duban kishiyar
mahaifiyarsa Fulani Hibbani, zai yi magana ya ce ita ma sun san nata asalin ba yar kowan ba
ce, sadakarta aka kawo wa Askirama, Awaisu ya toshe masa baki, ya ja shi suka bar sassan
gabadaya. Humaira ta ce, Humm! Aka ce auren hadi ne na Askirama, ashe da ma can yana sonta, dubi
yadda yake neman dukana.
Hibbani ta ce, Tabdijan! Ya Gumsu ta ga ta kanta, ai zama bai gan ni ba, bari in je in gaya
mata Yareema ya gama afkawa har fiye da ubansa sai ta yi da gaske, kin ga yadda jijiyar kansa
da ta wuyansa ke tashi?
Humaira ta ce, Ni tunda nake ban taba ganin makiran mutane irin wadannan Baggaran ba,
kyawunsu ke rudarSarakuna, amma wallahi kyawun da babu asali aikin banza ne.
Hibbani ba ta saurare ta ba ta figi mayafi ta nufi Unguwar Ya Gumsu.
Karya da gaskiya duk ta gaya mata, Ya Gumsu mai neman kuka an jefe ta da kashin awaki
ba ta san sanda ta fashe da kuka ba tana fadin,
Tawa ta same ni, ni Gumsu. To ba inda za ta bi shi a nan za ta zauna a Askira, ya je can
wajen baturiyar ya zauna, ko ba komai su ba sa mugun abu, zuciyarsu ba muguwa ba ce.
Bangaren Fulani suka nufa, Awaisu na ta cooling dinsa yana cewa ya yi hakuri, mata ne haka
suke, sun gaji kananan maganganu wadanda bai kamata a biye musu ba.
Sabida yadda ransa ke bace, duk tsokanar da Fulani Bilkisu ke masa ya kasa tankawa sai
murmushi kawai yake. A karshe ta yi musu addua da fatan alkhairi. Ya sunkuyar da kai da
ganinshi ka ga wanda ke gaban surukar da yake matukar girmamawa, ya ce,
Allah ya taimaki Fulani, ina ganin fa gobe za mu wuce Abuja, nan hayaniya ta yi yawa ba ta
barin mutum ya huta.
Fulani ta ce, Haba Yareema, ka yi hakuri ku cika sati daya a gama miskero sai ku tafin.
Ba da son ransa ba ya amince, don ba zai iya yi mata musu ba, amma kwarai maganganun
Hibbani da yarta sun sa so yake ya dauke Saade su bar Askira. Ba zai lamunci kowa nasa ya
taba mutuncinta ko na mahaifiyarta ba.
Daga nan sai gidan su Awaisu wato gidan Wazirin gari Ibrahim, nan ma suka kai gaisuwa, sai
gidan Galadima, Zanna, Shettima, Wali da dukkan king makers daya bayan daya sai da suka bi
su suka kai gaisuwa, suka kuma yi musu godiya da ban gajiya.
Sai goshin magriba ya dawo gida, Awaisu da ya sauke shi bai tsaya ba ya wuce gidansa.
Awaisu na da matarsa Asiya har da albarkar yara biyu.
Sanda Yarima Sageer ya shigo gidansa koina tsaf-tsaf sai tashin kamshin turaren wuta yake
kuma koina shiru. Kuyangi da hadimai sun kulle koina sun wuce bangarensu. Saadatu ta gaya
musu daga karfe shidda na yamma ta sallami kowa.

Ita da za a raba ta da wannan tarin yammatan masu jini a jika daga gidanta da sai ta fi jin
dadi, to ta san ba ta isa ta zauna babu kuyangi ba a matsayinta na matar Yariman Askira mai
jiran gado, ba ta isa ta karya aladar masarauta ba.
Zai wuce ke nan zuwa upstairsdin sa da zummar yayi wanka sannan ya zo ya duba Saade,
sai ya ji motsin mutum, da sauri ya juya, wata siririyar kuyanga ce ta sha hoda da jambaki ta
zube a gabansa.
Allah ya taimake ka dan zakin duniya, sunana Sadiya ko da ana bukatar kwarkwara
(sa-daka).
Kamar daga sama sai ga Saadatu ta bullo daga kitchen din falon za ta wuce, ta yi wannan
kyakkyawan gani ta kuma ji abin da Sadiya ta ce. Kofin tangaran na (mug) da ta hado zazzafan
shayi mai kauri ta saki ya fadi kasa ba da saninta ba, ji-ka ke tush! Kofin ya tarwatse, gilashin
da ruwan zafin duka a kan kafarta. Da sauri ta durkushe ta kama kafar wadda har ta soma fidda jini.
Sadiya da Yarima suka yi kanta a tare. Wata irin tsawa da ta daka wa Sadiya sai da hantar
cikinta ta kada, Dont touch me, get out! Ki hada kayanki duka ki koma cikin gida, kada in kara
ganinki a sassana.
Da gudu Sadiya ta fice ta san yau kashinta ya bushe, ta yi shuka a idon makwarwa. Babu
bayani ga sauran bayi yan uwanta ta hada kayanta ta koma gidan Sarki a daren.
Yarima ya sunkuya ya kama kafar, ta ture hannun sa tana kokarin janye kafarta. Azaba ba
yar kadan ta ke ji a cikin tsokarta ba amma ta fi jin zafin tayin da Sadiya ta yiwa Yareema fiye da
ciwon, kawai sai ya sunkuce ta ya yi saman benen da ita, duk inda suka wuce sai jini ya disa.
Shi ba likita ba, amma ba ya rabo da first aid box a gidansa, toilet ya kai ta cikin jacuzzi ya
wanke jinin ya cire kwalbar da ta makale tana kuka tana kankame shi, sannan ya sa mata
iodine don azaba ba ta san sanda ta rungume shi ba.
Ya dauko ta suka dawo daki bisa sofa ya shimfidar da ita yana ta faman jera mata sannu. He
looked worried and disturbed kamar a jikinsa ciwon yake. Ya dauko pain reliever da gorar ruwan
Faro ya ba ta ta sha. Ya kwantar da kanta bisa cinyoyinsa yana shafa kanta hankali.
Saade sai ajiyar zuciya ta ke, amma bacin ran Sadiya bai gushe daga zuciyarta ba.
Kamar Yareema ya fahimci hakan sai ya ce, Me ya sa ki ka kori yarinyar can?
Da jajayen idanunta ta harare shi.
Ba ka ji me ta ce ba ne? She wantto be your concubine bayan na ce kada in kara ganinsu
daga karfe shidda, amma shi ne don ta raina ni ta dawo da ta ji dawowarka.
Wani murmushi ya subuce wa Yareema, mace ba ta kishi sai a kan mijin da ta ke so, ko ta
fara so.
Ya ce, To me ye abun damuwa anan? Za ta taimaka miki ne ta dauke dukkan lalurorina har
zuwa lokacin da za ki karbe ni a matsayin miji, tunda ba ki sona Saadatu ba laifi ba ne don
sauran mata sun so ni, beside ba haramci ta fada ba.
A hankali Saade ta janye kanta daga jikin Yareema Sageer, ta kwanta daya barin akan pillow,
sabida yadda zuciyarta ke tafarfasa. A wannan lokacin ta tabbata da za ta ga Sadiya sai ta yi
mata mummunan lahani.
Yareema Sageer ya je ya kwanta a barin da ta maida fuskarta, ya yi mamaki da ya ga cewa
kuka ta ke yi.
Im sorry idan maganata ta bata ranki Saadatu. Gaskiyar magana ita ce, ba kya sona, ban san

dai wa ki ke so din ba. Amma jikina yana ba ni wannan siririn yaron fari da na ke yawan ganinku
tare nemai wuya uwa marikin lema.
Ni na gaya maka?
Ta tambaya cikin rishin kuka.
Ban taba ce maka bana sonka ba Yaya Sageer, kuma ni ban taba son kowa ba. Karatu kawai
nake so in yi. Auren ya yi min wuri, ka ga fa duka shekaruna sha tara, level 2 nake.
Akwai sauran shekaru biyu a gaba kafin in yi nutsuwar da zan iya daukan marriage
responsiblities, sannan baa nemi amincewa ta ba aka daura mana aure, ba mu fahimci juna ba
in this aspect ta ya ya ka ke tunanin hankalina zai karbi wannan auren?
Sosai Yareema ya fahimce ta, ya sanya hannu cikin jelunan kitsonta yana murzawa a hankali,
ya ce, Na fahimce ki Saadatu. Ni kuma na ba ki dama ki ci gaba da yin rayuwarki yadda ki ka
saba gudanar da ita a Abuja banda kula wannan yaron. Ni bazan takura miki ba. Insha Allahu
ba abin da zai canza har sai lokacin da ki ka ji cewa you are ready to accept me as a husband,
kafin nan ina so ki ba ni dama in zama malamin ki kuma aminin ki, mai koya miki karatu kuma
abokin shawarar ki mai kula da dukkan alamuranki.
Alfarma daya za ki yi mun, duk lokacin da zan sumbace ki kada ki ce min aa, ina matukar
son in sumbace ki, na yi miki alkawarin ba zan wuce hakan ba.
Da sauri Saade ta wara ido cikin jin kunya ta dube shi. A hankali ta ce,
Yaya Sageer ina jin kunya!.
Ya janyo ta gabadaya zuwa jikinsa, ya ce, I will take care of that daga yau, a hankali zan cire
kunyar dukkanta har watarana da kanki za ki zo ki ce, Yareema Sageer.. Saade ta yi maza ta
rufe idon ta. Ta cusa kai kasan filo. Shikuma ya yi amfani da wannan damar ya dauke filon ya
kuma hade bakinsu wuri guda yana kissing din nata gently, softly, affectionately. Tun Saade na
kokarin janyewa har ta soma lumshe yan idanunta. A zuciyarta tambayar kanta ta ke, wato
bayan kissing din akwai abin da ya fi shi kenan anan gaba,tunda gashi Yareema yana cewa, ba
zai wuce sumbar ba? To ko mene ne? Ko wace rana ce Yarima zai nemi hakan? Wannan din
kadai sai ta rufe ido ta kuma kai zuciya nesa sabida nauyin sa..Idan akwai abin da ya fi shi a
nan gaba ba ta san ya ya za ta yi da ranta ba.
Sauran kwanakin su a Askira sai suka zamo na jinyar kafa da sassanyar soyayya, wadda
Yareema Sageer yake matukar kokari wajen ganin bai wuce gona da iri ba. He is not going far
beyond what he begged for. He is only kissing her, sumba mai sunan sumba in dai ga Saadatu
ne ba ya taba gajiya, baya taba koshi. Rannan ya ce mata, “theres charisma in kissing You.
Kwanansu shidda a gidan su na Askira kafarta ta kame, ya ce ta hada duk abin da ta ke
bukata gobe za su bi jirgi tare da Maimartaba da Fulani zuwa Abuja. Alkawarin da Askirama ya
yi na kaita Abuja gidan mijinta da kan sa ya ce zai cika shi da yardar Ubangiji.
Washegari tunda asubahi an shirya motocin da za su kai su Maiduguri (filin jirgi) sannan an
zabi wadanda za su yi wa Maimartaba da Fulani rakiya, cikin masu rakiyar Fulani har da Fanna
wanda hakan ya faranta ran Saadatu sosai, fargabarta ta komawa Abuja ta ragu kashi sabain
cikin dari ganin irin wannan rakiyar gata da zaa yi mata.
******

Jirgin Azman ya sauke su a Abuja da yamma lis. Direban Dr. Sageer da na abokinsa Dr.
Ziyad su suka zo suka kwashe su a manyan motoci zuwa gidajen malamai na NTNU. Tunda
suka sauko daga jirgi yake ta gwada kiran lambar Sultana tana ta ringing amma ba ta dauka ba.
Ya san duk inda ta ke zuwa yanzu ta dawo gida. So yake ya gaya mata tahowarsu tare da su
Maimartaba don ta sa Uche ya tanadi abinci na musamman, amma ga wayar tana ta ringing ba
ta daga ba.
Ya yi tsaki, sannan ya kira Uche, wanda ke Baskwata a lokacin yana wanka, ita ya kamata ta
bai wa Uche umarni ba shi ba, amma da bai same ta ba dole ya kira shi.
Uche, Im already on the way with his Royal Highness, cook to your best, deliciously. Madam
ta dawo?
Uche ya yi shiru da waya a kunne, ta ya ya zai ce masa ta dawo, amma tun shigowarta tana
main falo tana drinking kada ya zo da iyayensa yanzu? Kafin ya hada amsar da zai bai wa ogan
nasa Sageer ya kashe wayarsa. Da sauri Uche ya hau sake kiran shi a waya amma rashin
kyawunnetworkyasa yakasa samun shi. Kuma kafin ya sanya suttura a jikin shi ya wanke
kumfar jikin shi ya baro baskwata (boys quarters) zuwa cikin gidan ya ji saukar dirin motocinsu
suna shigowa get din gidan.
Duk da yake arne ya san drinking alcohol is very bad to Muslims more especially women in
marital homes, its against their religion, tradition and culture. Sai ya ji tausayin ubangidansa ya
kama shi, don yana son Sultana. Allah ya sa kada father din ya ce ya sake ta.
Yana daga kitchen wanda ya bi ya shigo ta kofar baya cikin mutuwar jiki yana lekensu ta
window suna ta shigowa cikin nadi da amawali da kaya na sarauta a jikin kowannensu. Ga wata
mace kuma an lullube a cikin alkyabba wata baiwa ta riko ta. Yarima ya bude kofar falon wadda
sakayota kawai aka yi. Maimartaba shi ne farkon shiga don Yareema ya dan ja baya ya bashi
hanya cikin girmamawa sannan Fulani ta mara masa baya. Suka kuwa yi kyakkyawan gani,
wanda ba su jin za su taba mantawa a rayuwar su.

Aisha-Sultana ce daga ita sai half vest da wando three quarter baki, tana kwance
magashiyyan cikin manya-manyan kwalaben whiskey. Ba barci ta ke ba, kuma tana jin
shigowarsu amma ko yatsarta ba ta iya motsawa, idanunta a lumshe. Ba su taba ganin GIYA a
fili ba, amma kallo daya suka yi wa kwalaben da kuma yanayin da ta ke ciki suka gane komai.
Ko da ma can suna da labari. Kunya! A wurin Yareema kamar ya ce da kasar ta tsage ya shige.
Allah ya so shi yan rakiyar sun tsaya daga waje, yau da ya gama tozarta a rayuwarshi.
Maimartaba sai kawai ya juya ya ce da Fulani, Bana zama a inda ake saba wa Allah, sannan
yata ma ba za ta zauna ba. Ku juya mu tafi.
Yareema ya sha gabansa yana roko.
Alaguburo, Allah Kawun jo na tuba, na bi Allah na bi ku. Zan dauki mataki a ba ni dama ta
karshe. Nan shi ne gidan Saadatu sabida cikin makarantar su ne. Ita na riga na kama mata
wani gidan a Maitama, kusa da wajen aikinta.
Maimartaba ya yi tsaki ya fice, amma Fulani ba ta fita ba. Ya ce da dogarawan da ke bakin
kofa a nema masa hotel din da zai sauka gobe da asubah zai juya inda ya fito.
Fulani ta ce da Yarima wanda ya zauna ya dafe kansa da dukkan hannayensa.Bai taba
wulakanta irin yau ba. (Don ma ba shi aka kama a gidan Dr. Ziyad ba ke nan!) Kunyar duniya
kenan da tozarcinta kafin a je lahira. Me ye riba a kin bin umarnin Allah kowanne iri ne? Bai san

ya zai yi da Sultana ba, ya yi fadan ya yi nasihar, ya yi barazanar duka a banza. Har duka ya yi
duk da ba girman sa ba ne. Nadamar nashi laifuffukan suka kara lullube shi. Mai yiwuwa ta nan
Allah yake kama shi kan nasa laifin. Don kuwa duk da halin ta yana son kayar sa. A fili yake
fadin, Astagfirullah! Astagfirullah!!.
Ya kuma alkawarta ma ransa daga wannan ranar duk wani sabon Allah ya bar shi. Sultana
kuma zai dauki mataki na karshe a kanta.
Fulani ta dafa kafadarsa, Ka kwantar da hankalinka Yareema, zan ba shi magana. Amma
tunda ya ce ba zai zauna ba, to da gaske ba zai zauna din ba. Ka yi hakuri ka tashi mu je ka
nema mana masauki, ita Saa zata zauna tare dasu Fanna zan bashi hakuri.
Tuni Fanna ta janye Saadatu zuwa dakinta wadda ke rufe cikin alkyabba ba ta san a kan me
ake cece-kuce ba. Yareema ya mike yana hararar Aisha-Sultana wadda ke sakar masa
murmushi cikin maye.
“Darling you.you are back?
Bai ce mata komai ba ya bi bayan Fulani suka fita.
Hotel din TRANSCORP HILTON ya kai su, ya kama musu daki na musamman kwana daya.
Saadatu ba ta san su Fulani sun juya ba, ita da Fanna kawai aka bari a dakin, ta dauka tare
da su za su kwana cikin gidan suna wani dakin ne. Fanna kuma sai dauke mata hankali ta ke
da hira don kar ta gane abin da ake ciki.
Haka ki ka tsara dakinki ranki ya dade gwanin shaawa? In mun tafi gobe sai ki kara tsara
komai na gidan yadda ki ke so tunda ke kadai za ki zauna a cikin sa. Na ji maigirmaYarima ya
ce Uche ya hada kayan uwargida ya sa a mota. Ki kula da cikin mijinki ta fannin girki bana jinki,
na san Yareema ya gama morewa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login