Showing 6001 words to 9000 words out of 29267 words

Chapter 3 - Masarautarmu Book 3 Complete Hausa Novel By Sumayya Takori Kabara .pdf

daddare (a wannan ranar yan uwa da iyaye za a wuni ana shige da fice a gidan
amarya.
Ke kuma Fulanin Maimartaba ke ce da alhakin yin Miskero (abincin da ake kai wa gidan
amarya ranar wunin) wanda jamaa da ke shiga da fita a gidan za su ci.
Sannan a satin bikin gabadaya har ila yau ke za ki dinga ciyar da amarya da ango abinci mai
kyau. Har zuwa ranar da za a kai amarya, wato asabar.
Idan asabar ta zagayo kuma ana ‘tulur’, wato sati daya da kai amarya, ranar ne ke da
kawayenki (Fulani Bilkisu) da yan uwan amarya za ku je gidan amarya, mu kuma za mu yi mata
kwalliya, sai a saka mata muciya a hannu, a ranar za ta fara girki kenan, ana wakoki da
raye-raye, a ci a sha, to daga nan biki ya kare. Ranar asabar kuma za mu kawo lefe.

Fulani ta ce, Turkashi, wani aiki sai Amale, bikin Kanuri sai Askira! Allah ya sa muna da rabon
gani.
Aka yi adduoi aka shafa, bayan mazan ma sun yi nasu tsare tsaren, sannan duk suka fara
watsewa. Amma sai da daya daga cikin kannen Yarima da ake kira Houdda yar dakin
Yakirjinoma ta je har kofar dakin Saade ta yi magana ta hudar kofar dakin tamkar mai yin waka
cikin harshen Kanuri. Ki gama boyon amarya, kin riga kin zo hannu, da sannu za mu yi miki kaulu, kelatul, biji
ginata da tulur, sannan mu damka wa Yarima ke.
Murjanatu ta zuba mata duka a baya [dundu], ta ce, Houdda kar da ki tsoratata ta kara
kunshewa a daki duk zafin nan da ake yi, in kika firgita masa amarya ke da shi ne, kin fi kowa
sanin halin sa.
Saade da ke cikin daki duk tana jinsu ba ta san sanda ta fashe da kuka ba..

Da gaske dai ya tabbata an yi mata auren kenan, this is the reality da take ta kokawa da
zuciyar ta wajen yarda da shi. Take yaudarar kanta da kanta da cewa mafarki ne. Iyalin
Askirama bazasu bata lokacin su su zo har da na wata kasa ba idan ba gaskiya bane. [They are
very serious people] a sanin data yi musu. Auren kuma ba da kowa ba sai UNCLE YAREEMA!
Yariman da ta yi wa farin sani, uban dakinta mijin Aisha-Sultana. Yanzu ya tashi daga mijin
Sultana ita kadai, ya koma mijinsu su biyu. Da wane karfin zuciya za ta iya karbar wannan
sauyin rayuwar na bagatatan da ya zo mata rana daya?
Ta tura kanta karkashin filo tana ta kuka, wani irin kuka wanda tun lokacin da Fulani ta sanar
da ita zancen auren ba ta yi shi ba sai yanzu. Yanzu data ji ana shirye-shiryen biki kain da nain
daga kowanne bangare.

Daga bakin kofa ta ji ana sallama da wata irin murya cike da doki da zakuwa ga son ta bude.
Muryar da ba za ta taba mantawa ba. Ko mutuwa ta yi ta dawo bazata kasa shaida muryar
Hanne ba, Hannenta, Hannen Tsanyawa! Diyar Innar Hanne da Baba Saleh.
Ai ba ta san lokacin da ta isa ga kofa ta bude ta da sauri ba.

Hanne da Saade aka tsaya ana kallon-kallo, kafin su runtuma da gudu su rungume juna tsam
tsam.
Cikin yan kallon sakanni da suka yi wa juna, kowacce ta karanto irin sauyin rayuwar da ke
tare da yar uwarta. Bi maana, Hanne ta gano tarin sauyi na ci gaba da nasarar rayuwa a tare da
Saadenta, domin inda a hanya ta ganta ba za ta gane ta ba, to dadin abun mahaifiyarta Fulani
ce da kanta ta tabbatar mata Saade na cikin dakin nan a kwance, in ta yi magana ta ji ita ce za
ta bude mata.
A yayin da Saade ta hango tarin nakasu da koma baya a rayuwar Hannenta, ta zama kamar
mai shekaru arbain bayan ko ashirin ba su rufa ba. Ta yi baki; ta rame; ga goyon wani katon
yaro a bayanta wanda da gani ka san ya wuce goyo domin har rinjayarta yake. Saade ta soma
kokarin kwanto dan daga bayanta don Hanne ta ji dadin zama, suka karasa bakin gado suka
zauna suna hawaye.

Ina Baba Saleh?

Abin da Saade ta fara tambayar Hanne kenan. Hanne ta idasa rushewa da kuka, ta ce,
Baba ya jima da rasuwa Saade. Baba ya dade a kushewar sa. Mu kuma ba mu san garin da
ki ke ba da tuni mun zo, shekara da shekaru muna kewarki.
An yi min aure shekaru hudu baya da saurayinki Naziru, tunda na samu ciki ya gudu birni ya
bar ni yau shekaru hudu ba mu kara jin labarinsa ba, kin ga dan da na haifa masa nan, Inna ta
sa masa sunansa Naziru.
Jiya kawai muna alwala a gindin rijiya sai ga sako daga gidan Maigari wai mu zo an zo
daukarmu za a kawo mu inda ki ke. Inna Laure ta ce ba zaa zo da mu ba, ita kadai zaa dauko,
sai da direban ya ce an ce masa iyalin Baba Saleh da Inna Laure, sannan ta yarda aka taho da
mu. Saade ta rungume dan Hanne a jikinta tana tuno Naziru don kamar su daya, ta ce, Yanzu ina
Innarmu da Inna Lauren?

Aka bude kofar dakin aka shigo, Fulani ce, sai tsofaffin guda biyu biye da ita. Duk sun tsufa
sun yamutse a idon Saade. Tana kuka ta ke rungumarsu daya bayan daya, ta ce,
Inna, ku yafe min. Na dade ban neme ku ba, ajizanci ya tabbata gare ni, wallahi karatu ne ya
sha kaina sam bana samun hutu.
Inna Laure da Innar Hanne suka rike ta suka zaunar a tsakiyarsu suna fadin, Babu komai
Saade kin ji? Allah ne ya nufa sai yanzu za mu sake haduwa, komai kana da niyya sai Allah ya
nufa.
Innar Hanne ta ce, Shi ma Babanku yana ta wakar zai dawo ya sake duba lafiyarki, sai cuta
ta sarke shi, bai jima yana jinya ba mutuwa ta raba mu. Mu kuma ba mu san garin ba, mun dai
san masarauta ce a Borno. Sai yau da ki ka sa aka tura har Tsanyawa aka dauko mu cikin
mutunci a mota. Ashe Saade aure ya zo? To Allah ya sa an yi ke nan, Ya ba ku zaman lafiya.
Saade kamar jira take sai ta rushe da kuka, ta ce, Innar Hanne ku roki Fulani, don Allah ta bai
wa Maimartaba hakuri, bana son auren.
Inna Laure ta ce, Kul Saade! Aure sunnar Annabi ne, wanda ba ya son sunnar Manzon
sallallahu alaihi wasallam hakika Manzon rahma ya ce ba ya tare da shi. Ni dai rokonki zan yi ki
yafe mini, na ga babbar ishara a kanki, duk abin da na yi miki kin manta ki ka ce a je a dauko
miki ni har Tsanyawa. Ta saka kuka sosai. Saade ta ce, Inna Laure, ni ba ki yi mini komai ba sai alheri, rike ni da ki ka yi tun ina karama
shi ne babban alherinki gare ni, don haka ni komai ya wuce a wurina.
Daga nan hirar ta koma kan yadda auren Hanne da Naziru ya kasance, Innar Hanne ta ba ta
labarin Naziru ya sha kuka bayan tafiyarta Askira, A karshe da ya tabbatar ba za ki dawo ba ya
like wa Hanne, Baba Saleh ya cire ta daga makaranta ya ba shi aurenta cikin mutunci. Amma
tunda Hanne ta samu ciki aka neme shi aka rasa a Tsanyawa sanadin kamuwar Babanku da
hawan jini ke nan.
Hanne ta haihu a gida, ba ta jima da haihuwa ba Babanku ya cika, ni na yi ta dawainiya da su
da sanaoin hannu iri-iri har kawo yau.
Fulani ta ce, tunda ya shekara hudu bai dawo ba kuna da damar kai kara kotun muslunchi a
ba ta yancinta, ko ta samu ta yi wani auren. Shi kuma in da gangan ya gudu ya barta Allah zai
saka mata, in kuma wani uzurin ne ya rike shi, Allah ya sada su da alkhairi. Zan yi magana da
Maimartaba ya shige muku gaba Hanne ta samu yancinta. Hanne ta ce, Burina kenan, ban san ina da wannan damar ba da tuni na yi amfani da ita. Ina
matukar son in koma makaranta in raini Naziru shi ma in sa shi makaranta.
Fulani ta ce, Kada ki damu Hannatu, insha Allahu komai zai yi daidai bari mu kare bikin
Saade.
Sai da suka raba dare suna hirar yaushe gamo, a dakin Saade duk suka sauka don saboda
zuwansu ta manta da damuwar ta, ta cire wa ranta kunci, ta ware suna ta hira da Hannenta.
Washegari Fulani ta raka su suka yi gaisuwa wajen Askirama, ya ji mutuwar Baba Saleh
sosai, Fulani kuma ta gaya masa maganar Hanne, Askirama ya ce zai shiga maganar bayan
biki insha Allahu.
Tun zuwansu Hanne, Saade ta samu walwala, amma ta ki kunna wayarta. Tabbas da ta ga
sakonnin Yarima Sageer har guda uku. Sako na farko ga abinda Yarima Sageer yace.
“Thank you for being the PRINCESS Im waiting for.Thank you for coming to my life when my

heart is desperate to have you..(Madallah da zamowar ki GIMBIYAR dana ke jira tuntuni,
madallah da zuwan ki cikin rayuwa ta a lokacin da zuciyata ta dimauce ga son mallakar ki).
- Sageer.

Na biyu kuma yace.

“Saadatu save a soul by picking my call(Saadatu ki cece ni ki daga kira na).
- Sageer.

Sakon Yarima na karshe ga Saade cikin harshen hausa ne, ga abinda Yareema ya rubuta ma
Saade.

Kin ki bude waya saboda ni ko Saadahtouh? Bonono kenan rufe kofa da barawo. Bari in tuna
miki wani abu guda daya da baki sani ba ko kika manta; daga rana irin ta yau mun zama abu
guda,tare zamu kare rayuwar bakidayan ta,daga nan har gaban abada, ko makwanci bazamu
kara rabawa ba sai bisa unvoidable reason..
Duka wannan bidirin da Yarima ke yi shikadai yake yin abinsa Saade bata san yana yi ba don
kememe ta ki kunna wayar ta kamar ta san tashin hankalin dake jiran ta cikin ta daga zafafan
kalaman sa [ba raba makwanci har karshen rayuwa].
Da ga karshe Yarima ya kasa hakuri, Saade ta kure dukkan hakurin sa, idan ba ganin ta yayi
ba ba zai samu nutsuwar fuskantar bikin nan dake gaban su ba, ba zai koma nitatstsen Sagirun
sa ba, matukar son ganin Saade yake anyhow ko jin muryar ta, don ya ga da fuskar da ta karbe
shi matsayin miji ne ko akasin sa? Ko har yanzu kallon Uncle take masa? Ya aiko a gaya wa Fulani ta yi ma Saadatu magana ta kunna wayar hannunta su yi magana,
mai muhimmanci. Da Fulani ta sa Fanna ta gayawa Saade, sai Saade ta ce ma Fanna ta ce da
Fulani ta kunna har sun yi maganar, bayan kuma ko taba wayar daga inda ta yi mata kyakkawar
maboya ba ta yi ba. To me Uncle Yarima zai ce mata? Na ji auren da aka yi mana bagatatan ni ma bana so ko
me? Ko ki kama kanki ni ina da mata ta da nake matukar so? Ba ta bukatar wata sabuwar
muamala a tsakanin su bayan official one irin wadda ke tsakanin su a baya, cuta ce an gama yi
mata tunda an hada ta da shi, don haka ta yi kememe ta yi kemadagas ta ki kunna waya.
Kulawa ma yabawa ce inji 'yan magana.
Ya gaji da trying wayar Saade a daren yau, ana cewa a kashe, sosai yake son ya gan ta don
ya ga da fuskar da ta karbi wannan babban alkhairin da ya same su. Yes shi a wajen sa alkhairi
ne, GIANT (katoton) alkhairi ma kuwa, da bashi da yadda zai iya bayyana farin cikin sa da
muhimmancin sa gare shi! An bashi abinda ya dade yana so yana kwadayi batare da ya cancanta ba, ba kuma tare da
ya furta ba kuma ba tare da ya sha wahala ba sannan cikin girma da daukaka. A ganin sa hes
not worth enough (bashi da darajar da zai mallaki Sa'ade) innocent soul kaman Saade, in yayi
laakari ga tarin nakasun sa da laifuffukan sa na baya. Ya dade yana sunsunar takalmin, bai san
ta yadda zai yi ya dauka ba. Sabida ganin cewa Sa'ade tafi karfin sa.

Sai Askirama-Mai Askira cikin dimbin alfarmominsa da karamcinsa da ba su taba karewa a
gare shi ya sunkuya ya hutar da shi, ya dauko takalmin nan ya miko masa har inda yake.
Me zai ce da Mai Askira? Me zai ce da Fulani Bilkisu banda Allah ya ja kwanan su? Sun yi
masa gatan da ya kasa yiwa kansa. Ba zai gushe yana rokon Allah Ya kara soyayya a
tsakaninsu, ya ba shi soyayyar Saadatu kwatankwacin ta mahaifiyar ta Fulani ga Askirama!
Da ya gaji da trying wayar Saadatu ta ki kunnawa sai ya kira Yaa Maira. Ya san Yaa Maira ce
kadai zata yi masa wannan taimakon, sabida yadda take son sa da tausayin sa, in ba haka ba
shi da ganin Saadatu sai an gama biki.
Yaa Maira na dagawa ta ce,
Angon Saadatu ka sha kamshi.
Murmushi Yarima ya yi, cikin jin wani irin karin nutsuwa a zuciyar sa da ruhin sa wanda bai
taba ji a baya ba, da wannan daddadan suna da inkiya da Yaa Maira ta kira shi da shi, ya ce,
ni bana kamshi Yaa Maira tunda amaryar ba ta son ganina ko kadan balle ta san min
kamshin, ko murya ta bata son ji Yaa Maira. Ko kai na ya fara furfura ne ban sani ba? Kin san
yammata basa son mai furfura, rabo na da ita tun ranar da muka zo, ko waya ta ki kunnawa don
kar in kira ta in ji muryar ta in samu nutsuwa. Dariya Yaa Maira ta yi, in wani ne yace Yarima ne wannan zata musa, Yariman da magana a
gare shi sai dole, fitar kalma wannan tsada gareta daga bakin sa, amma yau shine yake joking,
lallai Saadatu ta ciri tuta kaman uwarta, wane irin sirri gare su haka? Da suke juya zukatan
sarakuna? Bata tantama in nan gaba kadan Saade bata juye kan Yarima ba kamar yadda
mahaifiyarta ta juye na Askirama. Ita dai in auren Saa zai raba Yarima da bin mata ba ta da
damuwa a kan hakan, ta tabbata dama ranar da ya auri matar da yakewa hakikanin so zai bari,
musamman idan halittar su ta zo daya, tunda Mai Askira ya hakura da kwarkwarori tun zuwan
Baggara Bilkisu,ta ce,
Amma Saadatu ba ta kyauta ba, an gaya mata miji wasa ne? Bari in je in samu Fulani zuwa
anjima a shirya muku ganawa ta musamman, don in anka shiga hidimar bikin nan ba za ku
samu ko ganin juna ba.
Tana kashe wayar ta nufi unguwar Fulani Bilkisu.
A falon ta tadda ta tare da mutane, nan ta nemi kebewa da Fulani, suka dan yi magana
kuskus, Fulani ta kama baki cikin mamaki.
Ashe Saade ba ta kunna wayar ba? Na rasa me ke damun yarinyar nan???
Yaa Maira ta ce, Ki bi ta a hankali dai, Saadatu na bukatar lallashi har zuciyarta ta samu
nutsuwa da auren, kada ki manta baku nemi shawarar ta ko amincewar ta ba, don haka lallashi
ne naku ba tursasawa ba, shi ma Yarima gajen hakuri ne irin nasa, ina ce tare za su koma
Abujan? Fulani ba ta saurari Yaa Maira ba ta nufi dakin Saade cikin fushi.
Ita da Hanne ta same su tana ware sitturunta masu kyau kala-kala daga wardrove tana bai
wa Hanne. Suna yi suna hira. Gabadaya ta manta da damuwar da take ciki sabida zuwan
Hanne.
Ashe ba ki kunna wayarki ba Saa?
Fulani ta fada daga bakin kofa. Tana kokarin hadiyefushin ta.
Saade ta turo baki gaba irin na shagwababbun yaya, Babu caji ne, amma yanzu zan saka
daman.

Ya yi kyau!.
In ji Fulani, sannan ta juya ta bar dakin cikin fushi.
Dakinta ta koma ta dauko wani dandatsetsen leshi cotton mara nauyi kalar maroon da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login