Showing 3001 words to 6000 words out of 29267 words
Chapter 2 - Masarautarmu Book 3 Complete Hausa Novel By Sumayya Takori Kabara .pdf
gaya mata na cewa tana matukar adawa da auren, ba kuma
don komai ba sai don kishinta da Fulani Bilkisu.
Ya Gumsu hakimce cikin royal chair ta babban falon ta, kuyangi na yi mata firfita da maficin
gashin dawisu. Wasu na tausa mata kafafu, wasu na zubo kirari amma duka basu ishe ta kallo
ba sai kumburi take kamar zata fashe. Ta daga ido tana kallon Yaa Maira da ke warware
lafiyayyar laffayar jikinta don ta ji dadin hutawa, sun sha zaman mota daga Biu zuwa Askira.
Take gayawa Yaa Gumsu. Ya Gumsu ta harare ta sosai, sannan a hassale ta ce.
To da ki ka kwaso bataliyar yayanki ku ka zo kuka cika min gida me ku ka zo yi? Wa ya
gayyato ku? Na ayya gayyar sodi?”
Dariya Yaa Maira ta yi, ta ce,
Allah ya taimaki Gumsun Gari, mu ai ba sai an gayyace mu ba. Su Murjanatu ma duk suna
hanya.
Ya Gumsu ta kara shaka sosai, amma ta ja bakinta ta yi shiru sabida kuyangin da ke
zazzaune wasu a tsaitsaye, zuciyar ta na tafasa. Ta kara ganewa Mai Askira bai dauki auren
nan da ya daura da sauki ba tunda har da kan sa yake gayyatar yayan sa abinda bai taba yi ba.
Allah kadai yasan iya gayyatar da yayi da irin hamshaqan sarakunan da ya gayyato akan auren
nan. Bata kara magana ba sabida kunar zuci. Kallo daya Yaa Maira ta yi wa kuyangin da ke
wurin duk suka mike suka bar falon, suna masu yi mata kirari irin wanda suke yi wa diyan Ya
Gumsu.
A tashi lafiya Yaa Mairar gida,
A gana lafiya uwar marayun Askira,
A fito lafiya cikin alheri Yaa Maira uwar diyan Yaa Gumsun Askira bakidaya..
Daidai kafafun ta Yaa Maira ta zauna suke kara gaisawa a nitse, gaisuwa irin ta Da da
mahaifi, Yaa Gumsu na kokarin hadiye fushin ta, yaran duk sun bazama cikin gida, kowa ya tafi
wurin saanninsa yadda suka saba in sun zo gidan. Yaa Maira ta ce da mahaifiyar ta cikin sanyin
murya. Sai muka ji abin alheri Yaa Gumsu, da ma zaman Yarima da mace daya ai ba yi ba ne,
Yarima fa, Yariman Askira Mai jiran gado! Balle wadda ba ta fito daga jinsinmu ba balle addinin
mu.
Na yi farin ciki kwarai da gaske don dama ni auren nan na farko na Yarima bai kwanta min ba
ko kadan, babu wani biki na alaadunmu da muka yi sabida abin kunya ne ma mu fito mu fadi ga
wadda ya aura a cikin masarautun da ke zagaye da mu.
Sai kuma ku yo gayya a auren shegiya mara asali? Tukunna ma kin san da wa ya daura
masa auren da kike wannan giringidishin?
Subhanallah, Yaa Gumsu tofar da miyan bakinki tun kafin malaiku su rubuta. Saadatu ba
shegiya ba ce, diyar Bilkisu ce ta cikinta
Tayi aure ta haife ta da mijin ta na fari kafin ta auri Askirama..!.
A razane Yaa Gumsu ta dago ta dubi diyar ta Yaa Maira. Sai Yaa Maira ta yi amfani da
wannan damar data samu wajen luguiguita zuciyar ta.
Tiryan-tiryan ta soma bai wa Ya Gumsu labarin Bilkisu da yadda ta haifi Saade, sak yadda
mahaifin su ya bata labari, ta kare da labarta mata Bilkisu ta boye musu Saade yarta ce sabida
ba ta son gori musamman daga ita Yaa Gumsu in ta ji cewa ba a budurwa Mai Askira ya aure ta
ba ta kade har ganyen ta da gori. Karshen maganar da Ya Maira ta fada shi ya kara sanyayar
da jikin Ya Gumsu.
Dangin mahaifinta na hanya, wan mahaifinta uwa daya uba daya Alhaji Kyari Babagana, na
tabbata kin san wannan sunan, don kuwa shi ne yake bai wa Bulama fatun da yake kai wa
kasar Italiya. (Bulama kani ne ga ya Gumsu, wanda suke sanaa daya da Alhaji Kyari). Ita ma Ya
Maira Askirama ne ya gaya mata hakan. A binciken da yasa aka yi masa akan asalin mahaifin
Saade.
Ya Gumsu da ke ba ta son nuna karayarta, sai ta hau mitar rashin dalili.
Ban da munafurci me ye na boye mana cewa yarta ce? Ina ruwanmu don ta taba aure? Gori
yana tsiro a goshi ne? Duk wata harka ta kishiya sai kin samu dunkulallen munafurci a ciki.
Ashe ma a bazawara ta zo shi ne ta bi ta juye kan tsoho, kinibabbiya, haba! Ni fa in ce wannan
so da Askirama ke wa yarinyar nan da walakin, ashe agola diyar mowa ce, to muna jira mu ga
wan baban yarinyar da idanunmu don mu tabbatar ba shegiyar bace.
Kuma shi Yareema shi ke nan ba zai auri yar sarauta ba, auren misali sai dai ya gani a wurin
tsararrakin sa? Alhalin ba gata aka fi shi ba? Daga jinsin yahudawa da masu kanan ido sai jinin
talakka agola a matsayinsa na Yarima mai jiran gadon Askira?
Ya Maira ta yi kasa da murya ta ce.
Yaa Gumsu, gara talaka, agola tushen musulunci tashin musulunci a kan tubabben da aka ce
daga kwalba ta ke yi a bar, sallar ma ta daina. Ki gode wa rahmar Allah Ya Gumsu alheri
Askirama ke nufinmu da shi. Yariman ai ba wankakke ba ne kin fi kowa sani. 'Yar Bilkisu aka
cutada auren Yarima ba Yarima ba. Ni tun ganina da yarinyar na farko na san za ta zame mana wani jigo cikin zuriar mu. Tana da
charisma mai yawa. Tana da wisdom bayyananne. Allah ne bai taba kai hankali na kan Yarima
ba, musamman da ya zo ya yi auren sa daga baya. Amma na yi zaton Ashgar zaa bai wa, sai
dai lalurar sa ba za ta bari ya yi aure ba, Jiki na ya dade da bani hakan cewa bazata wuce mazan gidan nan ba koda ba daga dakin
nan ba.
Yaa Gumsu Ta kyabe baki tace Mairam ki fita ido na in rufe, na bi wisdom da gudu na tattake
babu takalmi a kafata me yasa baa baiwa dakin Yaa Kirjiloma ba? Uban wa yace miki Ashgar
bazai iya aure ba? Sai Yarima na dana dora dukkan buri akan sa da yayan da zai haifa? Kawai
sai kuka ya kwace mata. Yaa Maira ta rasa yadda zata yi da Yaa Gumsu, duk dabarar ta ta kare. Haka ta yi ta tausar
Ya Gumsu tana nuna mata muhimmancin wannan aure ga mutuncin Yarima da rayuwarsa, da
alkhairin da ta ke hangowa a cikinsa na kimtsuwar Yarima.
Yaa Gumsu baki da masaniyar cewa har yanzu Yarima Sageer bai bar bin mata a garin Abuja
ba? In baki sani ba ki sani, in kuma kin sani ki tuna.
Ko jikin ta ya yi sanyi dai ba ta nuna ba, Ya Gumsu akwai Ki-Fadi, ko ma me ye ba za ta so
hada jini da Bilkisu ba gara dan kowa a kan nata. Da ta rasa hujjar kamawa sai ta ce da Yaa
Maira.
Shi ke nan kuma shi ba zai yi aure irin na gidansu ba? Ba zai yi auren martaba (auren
sarauta) ba sabida ubansa na auren uwarta?
Yaa Maira ta sake kwantar da murya, Allah ya taimaki Gumsun Askira, ai akwai sauran
damarmaki. Yarima na da gurbin wasu matan biyu bayan Saadatu, ki ka sani ko duka ya auri
yayan masarautu a sauran guraben yadda kike masa shaawa?
A nan ne Ya Gumsu ta yi ajiyar zuciya, don shaf bacin rai ya sa ta manta da hakan, yayi
zabin sa ya yi zabin mahaifin sa dole nan gaba kadan ya yi nata zabin. Ta ce,
Yanzu ki ka yi magana Mairam, daga yau zan fara binciken yayan babban gida wa Yarima.
Ba zai yiwu a ce duka aurarrakinsa babu zabina a ciki ba.
Yaa Maira ta ce, Oh ni ya su. Amma Ya Gumsu ki bari ki ga kamun ludayin zaman nasu
tukunna, kafin ki nema masa sabon aure. Yarima kodayake basarake to bature ne na gani
kashe ni. Ba zai so da kuruciyarsa a cika masa gida da mata ba. Ki yi hakuri ki daga masa kafa
zuwa wani lokacin. Haka ta yi ta lallashin Ya Gumsu cikin kwantar da kai da lalama, kodayake da ma cikin
yayanta kakaf Yaa Maira ce kadai ta iya tafiyar da ita cikin hikima duk taurin kanta. Ko dai ba ta
sauko duka ba, to Yaa Maira ta yi nasarar dakushe kiyayyarta da auren kashi talatin cikin dari.
Tunda ta ji Saade ba shegiya ba ce sannan yar Fulani ce ta cikinta ba yar riko ba kamar yadda
suke tsammani. Kuma ta ji cewa dangin ubanta za su bayyana kansu.
Wannan ne kadai ya sassauta zuciyar Ya Gumsu har ta yarda ta amince musu su je su
shirya biki nasu na aladar masarautar Askira. Amma ita tana nan sassan ta ko waje bazata leka
ba.
Don farin ciki Ya Maira a take ta hau buga wa kannenta mata da maza waya ta ce duk su
hadu yau a Unguwar Fulani Bilkisu kan shirin bikin Yareema bayan sallar isha’.
Kafin lokacin Mairam-Murjanatu ta iso. Ko hutawa ba ta yi ba suka dinga firfitowa daga
sassan iyayensu mata zuwa na Fulani Bilkisu.
Da ma kuma tun da yamma Yaa Maira ta aika wa da Fanna sakon zuwan nasu. Fanna kuma
ta gaya wa uwargijiyarta. Don haka ba su zauna ba tun lokacin suke dafe-dafen abinci na
alfarma domin saukar su Yaa Maira da sauran yayan Askirama maza.
Humaira ce kadai ta ki zuwa don ta shiga matukar damuwa da wannan auren da aka daura.
Fulani Hibbani kuma ta ce ta raba kanta da wahala, fadan da ya fi karfin ka ka maida shi wasa,
ta fita batun Fulani Bilkisu da yarta, don sun gama da ubanta saidai wani sarkin ba shi ba, in
kuma ta ki ji ita ce a wahale. Saade da ma ba ta yarda ta bar dakinta a bude tun daga lokacin da suka yi magana da
Fulani a kan aurenta da Yareema, ita kanta Fulanin haushi take bata yanzu don ta lura ta gama
mika wuya ga auren sabida son da take wa mijin ta Askirama, kuma bata dauki shirin sa da
wasa ba, ko don bata san waye Dr. Sageer ba? Ko kuma bata dauki hakan da muhimmanci ba?
Aisha Sultana bazata yi masa karya ba da ta ce hes committing adultery kuma SAI YA BARI
ITAMA ZATA BAR GIYA, wannan ne gidan da Fulani ta amince a kai ta kuma cikin mutanen da
take mata fatan rayuwa ta har abada?
Ita kuma Fulanin kamar ta san tunanin da take yi sai ta fita sabgarta, shirye-shiryenta ta ke
kain da nain, ta ce cikin ran ta,
Allah shine mai shirya bawa bani da tsumi banida dabara sai abinda Allah ya shiryawa
rayuwar ki Sa'ade. In kun tafi Abujar ku karata can, ni biki ne a gaba na. dama ai tare kuka zo,
don kun koma tare matsayin miji da mata yanzu babu laifi.
To yau ma tana jin su suna maganar kabakin abincin da za a shirya wa su Yaa Maira ita da
kuyangin ta wadanda a nan za su ci abincin dare, bata dai ji hakikanin me zai kawo su ba
amma taji ana maganar abinci na gani na fada zaayi yayan Askirama gabadayan su, da gudu ta
kara murza key din kofar ta duk da dama a kulle ta ke. Kada ma wani ya shigo in da take. A bar
ta ta ji da damuwar ta ita kadai tunda babu mai taya ta bakin cikin kaddarar da ta same ta.
Karewa ma kowa harkar gaban sa yake yi, dan tausayin ta da Fulani ke ji a farko ta zubar.
Abinci wannan Saade ta daina cinsa sai fruits kawai ta ke sha a firjinta, sai ko fresh milk din
oldenburger gora-gora idan yunwa ta matsa mata.
Yau kwanaki biyu kenan rabon da ta sa Fulani a idonta. Wayarta ta kashe ta don ta san dole
Saidu zai kira ta, ba ta san da wanne baki za ta fara masa bayanin ita matar aure ba ce yanzu,
ta san babu kyau mace ta dinga muamala da wani kuma. Ta ce ita matar Uncle Yarima ce ma ai
yanzu ai abun kunya ne bayan ta gama yi masa homar Yayan ta ne. Saidu-Saidun ta hakika
zata yi kewar sa. Babban tsoron nata shi ne kada Yarima ya kira ta a waya.
Tuna sunansa kadai fadar mata da gaba yake yi. Duk wata kyakkyawar alaka da ke
tsakaninsu a baya daga yanzu ta yanke ta. Karatun ma in dai ba hostel zaa maida ita ba ta
hakura ta yafe shi har abada. Tana nan kusa da uwarta da kanwarta, a rayuwa wannan shi ne
babban kwanciyar hankalinta wato ta gan ta tsakanin Fulani da Zarah. Bayan ita ma Zaran ko za ta wuni tana buga mata kofa ba za ta bude ba sai Fulani ta zo ta
kore ta a wurin.
Wajejen karfe takwas suka fara shigowa mazansu da matansu iyalin Mai Askira. Yaa Maira
ce karshen shigowa har da bawan Allah Ashgar wanda bai san me ake yi ba shi dai an kira shi
kuma ya zo.
Babban falon saukar bakin Fulani na musamman aka bude musu, kuyangin Fulani sai shige
da fice suke suna shirya abinci na alfarma. Sai hirarrakinsu ke tashi cikin kasaita da taushin
murya kamar ba magana ke tashi a falon ba sabida yadda suke yin ta cikin nutsuwa da salama.
Sassan Fulani Bilkisu ya game da kamshin turaruka na alfarma, wannan na wane wannan. Ya
kuma cakude da na wuta irin nasu na barebarin usli, ga sanyi da rabar iya kwandishan na ratsa
su.
Ba jimawa Fulanin Askirama ta shigo cikin falon, as usual cikin kwalliya ta alfarma, ta fi
kowacce iya tsara kwalliya cikin matan Mai Askira kamar yadda duk ta fi su kuruciya da daukar
ido. Da faraa sosai wadda ta fiddo hakoran Makkanta na danyen gold guda biyu ta ke musu
barka da zuwa. Ta dubi Mairam-Murjanatu cikin jin dadi ta ce, Har da mutanen Istanbul? Lallai kuna ji da wannan yar kanwa taku, ga shi ta shige daki ta
rufe balle ku gaisa.
Ya Maira ta ce, Kyale Saadatu kin ji? Kunya ce irin ta Baggara, me ake da amaryar da babu
kunya? We really appreciate, muna nan tare har abada ai.
Mairam Murjanatu ta muskuta cikin lallausar royal chair three seater da take zaune a kai, ta
ce,
Shin wane shiri ki ka yi Fulani game da biki ki gaya mana mu ji?
Fulani ta yi dan murmushi ta ce, Ban shirya komai ba. Na bar muku wuka da nama, ku ne
Yayyenta kuma surukanta. Ni ina gefe yar kallo ce.
Yaa Maira ta ce, To madallah da wannan girma da anka ba mu, mu kuma za mu shirya
mashahurin biki na alada, wanda za a dade baa manta a masarautar nan ba. Za mu huce na
auren farko da ba mu samu yi ba.
Daga nan Fulani ta yi umarni a zo a yi serving dinsu abinci.
Sun dade suna tsare-tsare da shirye-shiryen yadda abubuwa za su gudana a junansu, bayan
sun gama cin abinci. Fulani ba ta saka musu baki sai dai ta raka da eh ko aah.
Yaa Maira ta dubi kannenta su Murjanatu ta ce.
“Kamar yadda kuka riga kuka sani a aladar bikin gidan nan za mu fara da sakun lalle ranar
laraba, alhamis za mu yi nakiya, jumaa wushe-wushe, ranar asabar ake daurin aure, to tunda
an riga an daura ba shiri, to a ranar ne za mu yi kelatul (wanke kai da kitso na amarya), sannan
mu yi Biji Ginata (ana shimfida tabarmi ne a ranar a ajiye amarya ana kida ana wakoki bayan an
yi mata kwalliyar masarauta.
Ranar lahadi za mu yi kaulu na amarya da ango da safe (kaulu shi ne, zaa ajiye miyar yauki a
gaban amarya bayan an mata kitso da kwalliya, Baaba za su goyo amarya (sisters din
Maimartaba su ne Baaba) su kai ta wajen Kaulu, yan uwa da iyaye su dinga dibar wannan
miyar yaukin suna shafa mata. Da daya da daya kowa zai zo yana shafa mata yana ajiye wa
amarya kyauta, wasu har gold suke badawa, wasu iphone ko mota ya danganta da mukamin
mutum a masarautar, wasu kuma kyautar kudade suke yi, kaulu kenan.
Da yammacin lahadi kuma za mu yi ‘dubdo’, wato wunin biki a gidan amarya bayan an kai ta
ranar asabar da