Showing 21001 words to 24000 words out of 25373 words
Chapter 8 - KARSHEN ZALUNCI COMPLETE BOOK BY SUFI .pdf
ta
zubar da gawarwakinsu kwance cikin jini.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai Husnat ta yi godiya ga Ubangiji bisa baiwar da ya yi
mata, cikin hanzari ta durfafi inda taguwarta take ta ciro salkar ruwa ta wanke jinin da ya ɓata
tufafinta ta haɗe da takobinta. Sannan bugi ƙasa tayi taimama kasancewar bata da tabbacin
ruwan da take ɗauke da shi zai ishe ta har ta fice daga cikin wannan sahara, bayan ta kammala
sai ta shiga gabatar da sallah ba tare da fuskantar alƙilaba, kasancewar a sahara ba a iya gane
ina ne gabas da yamma a lokacin da rana ta take, kuma addinin musulunci ya amince mutum
ya yi sallah a duk halin da ya tsinci kanshi a ciki.
Bayan ta kammala gabatar da bautar Ubangiji ne sai kawai ta miƙe tsaye ta kama linzamin
taguwarta ta haye sannan ta cigaba da tafiya tana sassarfa, domin ta na so ta fice daga cikin
saharar kar dare ya riske ta a ciki.
Haka dai ta cigaba da wannan tafiya, kwanaki na bin kwanaki mako na bin mako, har ya
zamana Husnat ta shafe tsawon mako uku tana tafiya.
Cikin taimakon Ubangiji da addu'o'in da take karantawa ta ba haɗu da wasu miyagun halittu
masu cutarwa ba ko 'yanfashi da makami.
Wannan shi ne abin da ya wakana ga gimbiya Husnat ma'abociyar addinin musulunci da ta
fito farautar 'yar uwarta Hasinat domin hanata mallakar takobin Saiful-imfal da za ta yi don
hallaka mahaifinsu sarki Shaibat tare da azabtar da al'ummar Musulmi.
BABI NA SHA BAKWAI
Lokacin da sarakuna gami da matsafa haɗe da manyan bokayen duniya su huɗu suka yada
sansani a agaɓar shiga dajin Baitul-Shazwas domin dakon su jaruma Sulairat ma'abociyar
zakanya. Sai suka shafe tsawon sa'a bakwai ba tare da sun ji wani motsi ko labari akan su
Sulairat ba har duhun magariba ya kawo kai, lokacin da dare ya tsala sai sarauniya Abidat ta
karanta ɗalasiman tsafi ta rikiɗa izuwa wata kyakkyawar tsuntsuwa ta fice daga tantinta kai
tsaye ta durfafi sansanin su sarki Nadiyar tana tafiya cikin hanzari.
Lokacin da iso inda wani faffaɗan dutse yake kwatsam sai ta hango waɗansu tsuntsayen masu
kama da ita sak tamkar an tsaga kara sun sauka a bisa kan dutsen, koda ganin hakan sai ta
saki fuka-fukanta tayi ƙasa luuuh! Ta sauka a bisa dutsen, aka shiga yin kallon-kallo tsakanin ta
da sauran tsuntsayen. Daga can sai tsuntsayen suka rikiɗa izuwa, sarauniya abidat, bokanya zulaima, Damzaru
da sarki Nadiyar.
Nan take gwarazan duniyar huɗu suka shiga kallon juna cikin mugun tanadi, tsawon daƙiƙa
arba'in ana cikin wannan hali sai daga bisani ne sarauniya abidat ta katse shirun da ya wanzu
tsakanin su ta hanyar buɗe baki ta ce "ya ku manyan sarakuna da kasuwar buƙata ta kawo ku
nan ku yi sani cewa, baki ɗayanmu nan manufa ɗaya ta tara mu shi ne mallakar zakanya
juraima da takobin Saiful-imfal, dole ne mu yi abin nan da masu iya magana ke cewa "a rashin
uwa akan akan yi uwar ɗauki, wajibi ne mu ajiye kasuwar buƙata mu fuskanci abun hari, ma'ana
mu tabbatar mun mallaki zakanya juraima da takobi, kuma mu hallaka waɗanda zasu hana mu
cimma burin mu jaruma Sulairat da tawagarta".
Koda jin wannan jawabi daga bakin sarauniya abidat sai sarakunan suka yi shiru suna dogon
nazari, daga can bokanya Zulaima ta bushe da yar ƙaramar dariya mai kama da kukan jaki
sannan daga bisani ta turmuke fuska, cikin kakkausar murya kai kama da haushin kare ta bude
baki ta ce "haƙiƙa wannan shawara ce mai kyau, amma wani hanzari ba gudu ba, shin yanzu
idan mun kawar da su Sulairat mun mallaki zakanya da takobin Saiful-imfal shin a cikin mu
wane ne zai iya haƙura ya ƙyalewa ɗan uwanshi ya mallaki Saiful-imfal? To amma dai masu iya
magana na cewa sai an gwada akan san na kwarai, ga fili ga mai doki"
Sa'adda bokanya Zulaima tazo dai-dai nan azancen ta sai kawai tayi murmushi mai tattare
da mugun tanadi da baƙin tuggu.
Shi kuwa sarki Nadiyar abin da ya faɗo mashi a rai shine taya ya zai samu nasarar mallakar
zakanya juraima da takobin cikin sirri ba tare da kowa ya farga ba.
Wani ɓangaren a zuciyarshi ya ce da shi ya zama wajibi ka canja tunanin ka a game da wannan
yarjejeniya, tunda sanin kanka ne cewa gaba ɗayanku yaudara ce a tattare da kowanensu,
burin kowanne ya ci amanar ɗan uwanshi, saboda haka shawara a gare ka ita ce a lokacin da
sauran abokan gabar suka yunƙura wajen hallaka su Sulairat kai kuma kayi ƙoƙari wajen ceton
rayuwarsu tare da basu goyon baya.
Hakan zai sanya su aminta da kai har su baka goyon baya su taimaka maka wajen cimma
buƙatar ka ta samun ruwan ƙaramar shajarul-shifa domin samun haihuwa.
Sa'adda sarki Nadiyar yazo dai-dai nan a tunanin shi sai ya yi murmushin farin ciki.
Daga wannan furuci ne sarakunan suka sake rikiɗa izuwa tsuntsayen suka kaɗa fuka-fukansu,
kowannensu ya nufi sansanin shi.
A can dajin baitul-shazwas kuwa, al'amarin su sulairat tun sa'adda suka kammala fafatawa
artabu da su sarauniya Abidat, sai suka kasance cikin shirin ko ta kwana, lokacin da dare ya
tsala sai suka hallara a cikin kogon dutse.
Bawa Hilwas ya katse shirun da ya wanzu a tsakanin su ta hanyar buɗar baki ya yi gyaran
murya, ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya ce "ya 'yan uwa abokan share hawaye ku yi sani
cewa haƙiƙa abun da ya faru a yau a filin yaƙi ya tabbatar mana da cewa sai mun sake tanadi,
domin masu iya magana na cewa na zaune bai ga gari ba, kuma komai sammakon ka wani a
hanya ya kwana. Idan a yau mun yi artabu da sarauniya Abidat kaɗai to ku sani cewa a gobe
zamu yi fito-na-fito ne da tawagar sarakuna biyar.
Kar mu manta cewa sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi, kuma alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba.
Dole a yauzu mu canja tunanin mu da nazari akan tunkarar gumurzun gobe".
Sa'adda bawa Hilwas ya zo nan a zancen shi sai kowa ya shiga damuwa ainun aka yi shiru
tsawon daƙiƙa talatin babu wanda ya ce ƙala.
Sai daga bisani ne Sulairat ta yi gyaran murya ta ce "haƙiƙa zancen ka dutse ya kai Hilwas,
wani abu da baka sani ba shine dukkan sabbin tawagar sarakunan da suka bayyana ba komai
ne ya kawo su ba face, buƙatar mallakar takobin saiful-imfal da zakanya,
Sai dai abin da suka manta shine masu iya magana na cewa "kifi na ganin ka mai jar koma"
babu wani a cikin su da isa ya sarrafa takobin saiful-imfal koda ya mallake ta face yana tare da
sarƙar tsafi, domin matuƙar ya ce zai sarrafa ta take takobin za ta hallaka shi.
Bisa dogon nazari da nayi akwai yiwuwar a gobe sarakunan za su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin su
kawar damu, daga baya a tsakanin su sai su san abin yi"
Lokacin da Sulairat tazo nan a azancen ta sai kowa ya jinjina kai yana mai yuya al'amarin a ran
shi.
Suhaimt tayi gyaran murya a karo na farko ta ce "tabbas dukkan maganganun ku suna kan
tsari, kuma a halin yanzu hankalin duniya yana kan takobin saiful-imfal da zakanya juraima, duk
da cewa matuƙar yawan abokan gaba bamu da tabbacin zamu samu nasara akan su, amma
kar mu manta cewa yaƙi ɗan zanba ne, Dole a gobe mu yi amfani da tuggun yaƙi ba iya na
takobi ba,
Shawarar da zan bamu ita ce me zai hana a gobe mu tura iya zakanya juraima da takobi a
gaɓar shiga daji, mu sai mu ɓuya a cikin duhuwa mu hangi yadda yaƙi zai ɓarke tsakanin
sarakunan, zasu yi ta kashe junan su inda daga ƙarshe dole wani ya yi nasara a cikin su ya
mallaki takobi da zakanya. Shi kuma koda ya mallaka sun tashi a banza domin dole ne takobin ta dawo hannun
Sulairat.
Wannan wata mafita a gare mu bayan baƙin artabu, kun san masu iya magana na cewa "gida
biyu maganin gobara".
Sa'adda Suhaimat mahaifiyar Sulairat tazo nan a zancen ta sai kowa ya cika da farin ciki bisa jin
wannan kyakkyawar shawara, daga wannan kowa ya koma can gefe inda shimfiɗar shi ta ke ya
kwanta domin huce gajiyar dake tattare da shi.
Amma koda su Sulairat ta zo hucewa ta gaban Himlas sai da ta jefe shi da wani ƙayataccen
murmushi mai tattare da tsantsar so da ƙauna, shima ya mayar mata da martanin murmushin.
Wannan shi ne abin da ya wakana a
dajin baitul-shazwas.
BABI NA SHA TAKWAS
Kashe gari tun da duku-dukun safiya, su bokanya Zulaima da sauran tawagar sarakunan
suka yi sahu-sahu a gaɓar shiga dajin baitul-shazwas, domin tsumayen fitowar tawagar su
jaruma Sulairat,
Sai dai wani abu da ya ɗaurewa tawagar kai shine babu su ga sarki nadiyar da dakarunshi.
Shin ina sarki nadiyar da ya shiga? Shin ya koma izuwa birnin shi ne ko kuwa ya canja wani
tunanin domin cin amanar su.
Amsar da tawagar da suka kasa bawa kan su kenan.
Duk da cewa a daren jiya sun samu ƙari a cikin tawagarsu wato gimbiya Hasinat 'yar uwa ga
gimbiya Husnat
ma'abociyar addinin musulunci.
Tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali ba tare da anji motsin komai ba,
Daga can sai aka ji ganyayyakin bishiyun dajin suna motsawa alamun dake nuni da cewa wani
abu mai rai yana shirin bayyana a wajen.
Zuwa can sai aka hango Jaruma Sulairat, bawa Himlas, Suhaimat, baiwa Sunaila tare da wasu
baƙin jarumai biyu da suka rufe fuskokinsu da baƙin yanki, idanuwansu kaɗai ake gani. Baki
ɗayansu suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro kana gani
kasan fitowar yau cike take da mugun tanadi, kuma fitowa ce ta ko a mutu ko ayi rai. Ba wasu ba ne baƙin jaruman da suka bayyana ba face.
Jaruma Husnat yar uwa ga gimbiya Hasinat tare da sarki nadiyar, nan fa aka fara
kallon-kallo tsakanin duka ɓangarorin ashe abin da su su sarauniya Abidat ba su sani ba shine
a daren jiya Jaruma Husnat ta samu shiga dajin baitul-shazwas kuma ta bayyanawa su Sulairat
abin da ke tafe da ita. Kuma a halin yanzu baki ɗayansu sun ƙarɓi addinin Musulunci. Wannan dalili ya sanya aka ajiye zakanya juraima da takobi a cikin daji kasancewar abubuwa
ne na shiri.
Daga can sai ɓangarorin suka tunkari juna, yayin da ya rage saura taku goma tsakani sai
kowannen su yaja ya tsaya, aka sake sabon kallon-kallo na tsawon daƙiƙa arba'in, daga can sai
Husnat ta dubi 'yar uwarta Hasinat tayi gyaran murya ta ce "yake yar uwata kuma gudan jinina
kiyi sani cewa ban zo nan domin na yaƙe ki ba sai domin na yi miki nasiha ki tuba zuwa ga
Ubangiji ki dawo zuwa addinin Musulunci".
Koda jin wannan batu daga bakin Husnat sai 'yar uwarta Hasinat ta taƙarƙare ta bushe da
dariyar mugunta, daga can ta turɓune fuska tamkar an aiko mata da saƙon mutuwa ta ce
"wannan nasihar ta ki abbanmu ya yi dubunta amma bai sanya koda kwarzane na imani ya
ɗarsu a raina ba. Ina mai tabbatar miki da cewa sai na cimma burina na mallakar takobin
saiful-imfal domin ɗaukar fansa akan abbanmu saboda haka ki shirya ga maza nan bisa kan ki".
Koda gama faɗin hakan sai ta miƙa hannunta a gadon bayanta ta zare wata sharɓeɓiyar
takobi a cikin kubenta, sannan ta ruga da gudu izuwa kan 'yar uwarta tana ihu da kururuwa mai
firgitarwa.
Koda ganin hakan sai Husnat ta zare takobin dake damtsenta ta tare ta gami da ƙwala kabbara
da ƙarfi.
Sa'adda tawagar sarakunan duniya suka ga abin da ya ke faruwa sai suka yi ɗauki kan su
Sulairat.
Sarauniya Abidat ta tari Sulairat, bawa Himlas ya tari sarki Damzaru, Baiwa Sunaila ta tari
bokanya Zulaima, Suhaimat, sarki Nadiyar da dakarunshi suka tari tawagar sarkin matasan
ifritai na duniya, da dakarun sarki Damzaru.
Lokacin da ɓangarorin biyu suka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai
matuƙar muni, ban tsoro da ban al'ajabi gami da tashin hankali.
Wohoho! Haƙiƙa yaƙi KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka sha gwagwarmaya a
GUMURZUN SHEKARA DUBU.
Haƙiƙa ranar bikin farar kaza balbela ba abar gayya ba ce, idan manyan giwaye suka fito fagen
artabu dole ne yaƙi ya zamto tashin hankali kuma ban tsoro.
Nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne,
ƙura ta turnuƙe sararin samaniya tamkar hadari ya gangamo, za'a kece da matsanancin ruwan
sama.
Husnat da Hasinat suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA
DA BAJINTA ta gaban kwatance, duk sa'adda makamansu suka haɗu da juna sai kaga
tartsatsin wuta ya tashi. Wani abu da zai ɗaurewa mutum kai kuma ya bashi mamaki shine
yadda salo da dubarun yaƙin 'yan uwan yakasance iri ɗaya sak. Amma a ɓangaren manyan giwaye kuwa wato Jaruma Sulairat 'yar baiwa da sarauniya
Abidat, tuni labari ya sha banbam, domin gaba ɗaya sun zamto taurari ababan haskakawa a
filin yaƙin, domin komai hassadar mutum idan ya ga yadda suke artabun dole ne ya jinjina masu
ya tabbatar da cewa sun cika mata masu kamar maza, masu ƙarfi na Allah ya isa. A ɓangaren Bawa Himlas da sarki Damzaru an yi kunnen doki babu rinjaye ga kowanne
abokin gwami. Ma'ana anyi kare jini biri jini,
Sai dai ana samun asarar rayuka tsakanin dakarun sarki Nadiyar da tawagar muridai haɗi da na
sarki Damzaru,
Yazamana cewa duk inda mutum ya kai dubanshi sai dai ya ga Suhaimat da Sunaila na bazar
da dakaru a ƙasa tamkar suna sassabe a gonar auduga.
Nan fa waje ya cika da mutuwar mazaje, ƙarar karafniyar makaman yaƙi haɗe da hargowa
da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne, duwatsu suna dinga karo da juna suna yin bindiga
suna tarwatsewa, dawakai suka dinga dudufniya suna haniniya kofatunsu na kartar ƙasa suna
tayar da ƙura, wasu na zubar da mahayansu suna nausawa cikin daji saboda matuƙar firgici. Wohoho! Haƙiƙa duk wanda ya iya ya huta, komai hassadar mutum idan yaga yadda Zaratan
matan biyu ke ragargazar yaran ifritu da sauran abokan gaba dole ya jinjina masu ya tabbatar
cewa sun cika GWARAZAN JIYA masu ƙarfi na Allah ya isa.
Nanfa sarkin matasan ifritai ya ɗinauce bisa ganin yadda Suhaimat da Sunaila suka zame masu
gagarabadau kuma ƙadangaren bakin tulu.
Kaico! Haƙiƙa yaƙi shine mabuɗin dukkan wata musiba a doron ƙasa, domin yaƙi shine ke
haddasa asarar rayuka, dukiya, fari da JUYIN SARAUTA.
Haƙiƙa wanda bai san shi shine yake fatan zuwan shi shine yake fatan zuwan shi.
Abin da sarakunan kafuran ba su sani ba shine bakomai ne ya sanya su Sulairat ke samun
galaba akansu ba sai domin addu'o'i da suke karantawa.
A wannan rana sai da aka shafe tsawon sa'a biyu da daƙiƙa arba'in ana wannan ɗauki ba daɗi.
Haƙiƙa Ubangiji ya nuna ikon shi a wannan rana domin ya kunyata maƙiya Addinin Allah,
Baiwa Sunaila ta samu nasarar hallaka bokanya Zulaima ta hanyar karya mata wuya ta jefar da
gawarta a ƙas.
Shi kuwa sarki Damzaru ya miƙa wuya ga bawa Himlas bisa ganin cewa zai iya rasa rayuwar
shi, zai tashi a tutar babu.
Kamar yadda ya wakana tsakanin Damzaru da bawa Himlas haka al'amarin ya kasance
tsakanin sarauniya Abidat da Jaruma Sulairat domin sai da Sulairat ta samu nasarar kai ta ƙasa
sau babu adadi amma bata hallaka ta ba.
Lokacin da Abidat ta fahimci cewa kowanne lokaci zata iya rasa rayuwarta, nan take ta miƙa
wuya. Domin dai ina amfanin baɗi ba rai,
A ɓangaren gimbiya Hasinat da 'yar uwarta Hasinat kuwa sun yiwa juna ƙananun raunika, kuma
Hasinat ta miƙa wuya tayi nadamar abin da tayi.
Sai dai sarkin yaƙinta ya rasa rayuwarshi.
Wohoho! Haƙiƙa a wannan rana Ubangiji ya nuna ikon shi akan bayinshi ya kunya kafurai
maƙiya addinin shi.
Cikin matuƙar farin ciki Jaruma Husnat ta karanta kalmar shahada baki ɗayansu suka amsa,
faruwar hakan ke da wuya nan take sarki Damzaru yaji yanayin jikinshi ya canja, koda ya duba
sai ya ga cewa halittar mata maza dake tare da shi ta bar shi, yanzu yana ɗauke da cikakkiyar
halitta ta kowanne ɗa namiji lafiyayye. Nan fa ya cika da matuƙar farin ciki maral musaltuwa, ya ji ya ƙara imani da Ubangijin gaskiya.
Kafin ya bar filin yaƙin sai da Jaruma Husnat ta fito da takobin saiful-imfal ta lalata shirin dake
jikinta ta hanyar karanta ayatul-kursiyyu ta tofa, ita kuwa zakanya juraima koda aka tofa mata
ayatul-kursiyyun nan take wani baƙin aljani ya fito daga jikinta ya kama da wuta ta ƙone ƙurmus,
ashe duk abin da take gudanarwa wannan aljani ke sarrafa ta hanyar amfani da sarƙar tsafi. Haƙiƙa a wannan rana babu wanda ya kai Sulairat da mahaifiyarta matuƙar farin ciki bisa ganin
cewa suna kawo ƘARSHEN ZALUNCI a doron ƙasa baki ɗaya.
Da yake akwai sauran sa'o'i kafin faɗuwar rana sai aka ɗunguma izuwa birnin Sin, aka kafa
tutar musulunci dukkan al'umma suka yi mubaya'a bisa jin abin da ya faru da sarauniya Abidat.
Sai da Jaruma Husnat ta shafe tsawon mako guda tana koyar da dukkan al'umma yadda ake
gudanar da ibadar Ubangiji, sai da aka aika da wasikar gayyata izuwa ga sarki Shaibat