Showing 15001 words to 18000 words out of 25373 words
Chapter 6 - KARSHEN ZALUNCI COMPLETE BOOK BY SUFI .pdf
duk jinsin miyagun
halittu babu mai ƙarfin damtse da sihirin tsafi tamkar mucijiya kuburul-shamshan.
Waccan zakanya kuwa zai yi amfani da ita a matsayin abin hawa, lokacin ita kaɗai dabbar da
za ta iya jure wahalhalu har ya cimma nasarar isa kogon Garul-musib.
Sa'adda sarki Nadiyar yaga wannan al'amari sai hankalinshi ya dugunzuma ainun kuma ya cika
da matuƙar farin ciki.
Abin da ya sanya shi farin ciki shine ya gano hanyar da zai samu haihuwa.
Abin da ya dugunzuma hankalinshi kuwa shine halarar tsafin shi ta kasa bayyana mashi cewa a
ina ne zai mallaki takobin haɗe da zakanya.
Wata rana sarki Nadiyar na zaune a turakarshi bisa kujera, sanye da riga 'yar shara da
gejeran wando irin na hamshaƙan sarakai, ya ɓaje alƙalumman sihirin shi yana gudanar da
bincike domin ganin irin wainar da ake toyawa a duniya, yana cikin wannan hali ne kawai sai ya
taƙarƙare ya bushe da dariyar farin ciki. Bakomai ne ya sanya sarki Nadiyar wannan dariyar farin ciki ba sai domin wani al'amari da
ya gani a cikin halarar tsafin shi, wannan abu ba komai ba ne face a halin yanzu yana da halin
da iya mallakar takobi tare da zakanya Juraima, kasancewar jaruma Sulairat dake da mallakin
su ta bayyana kuma tana shirin kwabza yaƙi da wata ƙasaitacciyar sarauniya dake mulkin birnin
sin.
Sai dai wani tunani da ya faɗo mashi shine ta ta ya ya zai mallaki abubuwan biyu, shin zai haɗa
kai ne da sarauniya Abidat ko kuwa shi kaɗai zai farki dajin Baitul-Shazwas.
Haka dai ya cigaba da binciken a inda ya gano cewa akwai ɓoyayyen jarumi da zai kawo mashi
cikas wajen cika wannan buri na shi, sai halarar tsafi bata bayyana mashi a ina jarumin yake ba.
Tun daga wannan rana sarki Nadiyar ya fara shirye-shiryen tafiya izuwa dajin
Baitul-Shazwas domin farautar zakanya Juraima da takobin sarkin bokaye.
Ranar da tafiya dajin Baitul-Shazwas tazo tun da duku-dukun safiya sarki Nadiyar ya
kammala shiri tsaf kuma yayi bankwana da dukkan iyalinshi gami da al'ummarshi ya kama abin
hawa tare tawagar rakiya dakaru dubu biyar suka ɗauki hanyar da zata kai su izuwa birnin Sin.
Wannan shi ne abin da ya wakana ga sarki Nadiyar na kasar Madinatul-haiwan.
BABI NA SHA UKU
Al'amarin sarauniya Abidat kuwa lokacin da ta Kaɗaita a cikin turakarta cikin matuƙar
takaicin yadda abokan gabarta suka suɓuce mata, sai ta wanzu tana kai komo a cikin turakar ta
kasa zaune ta kasa tsaye tana juya al'amarin a cikin ran ta.
Tana cikin wannan hali ta iso madubi yake koda ta kalli fuskarta taga yankan da SULAIRAT ta yi
mata bata san sa'adda ta dunƙule hannunta ɗaya ba ta naushi madubin ya tarwatse sannan ta
taƙarƙare ta kurama wawan ihu, tsawon daƙiƙa goma tana cikin wannan hali sannan daga
bisani ta murtuke fuska tamkar an aiko mata da SAƘON MUTUWA. Kwatsam! Sai taji an tura ƙofar shigowa turakar, wani garjejen ƙato mai ƙirar samudawan farko
ne sanye cikin sulken yaƙi ya bayyana gare ta. Sannu a hankali yana takawa da ƙafafuwanshi
har yazamana tazarar dake tsakanin su bata huce taku uku sannan ya zube ƙasa bisa
gwiwoyinshi ya kwashi gaisuwa kanshi a sunkuiye.
A sannan sarauniya Abidat ta juya cikin ƙasaita da baƙar izza ta dube shi da kyawawan
idanuwanta masu haske da kwarjini, sannan ta buɗi baki cikin murya mai tattare da fushi ta ce "
ya kai dirkar birnin Sin kayi sani cewa bakomai ne ya sanya na kira ka nan ba sai domin kafi
kowa sanin abin da ya faru da ni a fada na suɓucewar abokan gabata. Ba'a taɓa keta mutumcina da ƙasƙanta darajata tamkar yau ba.
Saboda haka ina so ka shirya tawagar mayaƙa da baka taɓa tsara tamkar ta ba, gami da
abin guzuri da masu hidima domin ba zan dawo gida ba face na kawar da abokan gabata kuma
na mallaki takobin Saiful-imfal, ina so asubar fari ta yi mana a gaɓar shiga dajin
Baitul-Shazwas." Koda jin wannan batu daga bakin Abidat sai sarkin yaƙi ya buɗe bakin ladabi ya ce "an gama ya
sarauniyar kyawawa hadari malafar duniya. Kece guguwar ajali mai share TAWAGAR MAYAƘA,
GAWURTACCIYA kike uwar hatsabiban duniya. KAIFIN TAKOBI kike mai raba tsakanin
masoya, ANNOBA ƊARI kike duk wanda ya tono ki zai baƙunci barzahu. Kasaitaccen daji kike
babu mai yi miki ƙyaure sai mahaukacin kafinta. MURUCIN KAN DUTSE kike baki fito ba sai da
kika shirya. DAMISA ƘI SABO kike ki fyaɗe na gida ki fyaɗe na daji".
Lokacin da sarkin yaƙi ya zo nan a kirarin da yake yiwa sarauniya Abidat nan take taji wata
irin BAƘAR IZZA da ƙasaita ta cika kwanyarta. Ta dube shi ta ce "ya kai Hunaifu maza ɗago da
kan ka ka dube ni haƙiƙa ka cancanta ka kalli sura a matsayin tukwicin wannan kirari naka".
Koda jin wannan batu sai sarkin yaƙi Hunaifu ya buɗi baki cikin ladabi ya ce ya shugabata ba
zan iya duban kyakkyawar surarki a matsayina na bawanki ba. Sai dai ina tsoron saɓa
umarninki."
Koda ya zo nan a zancen shi sai ya ɗaga kan shi ya ƙurawa Abidat idanu yana kallon surarta ko
ƙiftawa ba ya yi tamkar wanda ruhinshi ya fita daga gangar jikinshi.
A wannan lokaci sarauniya Abidat tana sanye ne da wata ƙasaitacciyar alkyabba mai
shara-shara gaba ɗaya surar jikinta ta bayyana, tun daga wuyanta har ƙirjinta a bayyane suke,
har kana iya ganin tsinin kan ƙirjin tamkar idan aka tsoka ne su da yatsa koda harshe zasu fito
waje, cinyoyinta har zuwa kwankwason ta sai sheƙi suke suna ɗaukar hankali. Tun da sarkin yaƙi yazo duniya bai taɓa ganin wata 'ya mace mai kyawun sura tamkar
sarauniya Abidat ba.
Koda Abidat ta fahimci cewa idan har ba ta suturta jikinta ba sarkin yaƙi ba zai dawo da
hankalin shi sai kawai ta juya mashi baya, a sannanne ya dawo hayyacin shi yana mai sauke
numfashi.
Cikin matuƙar shauƙi sarkin yaƙi ya buɗi baki muryar shi na rawa ya ce cikin ladabi "ya
shugabata na rantse da wannan kyawun sura da zati naki farautar su jaruma Sulairat zai zamo
tamkar kawar da yunwar cikina."
Da jin wannan batu sai Abidat ta yi murmushi da ya ƙarawa tona asirin kyawunta har fararen
haƙoranta suka bayyana cikin zazzaƙar murya mai ɗimauta zuciyar duk wani ɗa namiji ta ce
"je ka abin ka ya kai garkuwar birnin Sin."
Koda jin hakan sai sarkin yaƙi ya juya ya fice daga turakar.
***
Bokanya Zulaima ta ƙurawa tukunyar tsafin dake gabanta idanu ko ƙiftawa bata yi, kwatsam
sai taswirar wata runduna guda biyu mabanbanta ta bayyana, runduna ta farko bisa jagorancin
wata kyakkyawar budurwa ce ma'abociyar sarauta, runduna ta biyu kuwa bisa jagorancin wani
namijin sadauki ne ma'abocin tarin shekaru. Baki ɗaya tawagar biyu suna tafiya ne cikin hanzari a cikin ƙasaitattun dazuka.
Koda taswirar tazo nan sai bokanya Zulaima ta nuna tukunyar da hannu taswirar ta ɓace ɓat!
Sannan ta dawo da duban ta izuwa ga ifritu Shammar da ƙwala-ƙwalan idanuwanta da suka
ƙarawa fuskarta muni cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ta ce "ya kai sarkin
matasan ifritai na duniya kayi sani cewa haƙiƙa abun nan da masu iya magana ke faɗa ya faru
gare mu wato, "kowa ya daɗe zai ga daɗau, kuma a bari ya huce shine kawo rabon wani"
Amma dai ai masu iya maganar sun ce sa'a tafi sammako. Kuma duk mai nema yana tare da
samu.
Takobin Saiful-imfal da na shafe tsawon shekaru ɗari huɗu ina jiran bayyanar ta yanzu lokaci ya
yi. A halin yanzu takobin tana tare da wata jaruma yar baiwa mai suna Sulairat, raba Sulairat da
takobin abu ne mai matuƙar wahalar gaske domin wata zakanya dake gadin takobin ba za ta
taɓa bari wani mahaluki ya kasance ta ba. Babban abin damuwar shine babu wani mahaluki da zai iya sarrafa takobin Saiful-imfal face ya
mallaki wata sarƙar sihiri dake rataye a wuyan jaruma Sulairat.
Bincike ya tabbatar min da cewa manyan sarakunan duniya biyu sun fito domin farautar
zakanya Juraima da takobin Saiful-imfal.
Wannan ita ce damar mu ta ƙarshe da zamu ɗauke takobin ta kowacce fuska.
Haƙiƙa burina ya kusa cika na mulkar duniya baki ɗaya domin cigaba da shimfiɗa baƙin
mulkina.
A halin ruhikan sarakunan duniya guda dubu shida dake aijye a cikin akwatin siddibaru sun
kammala tsumuwa da sihirin tsafina, a ranar da zan mallaki takobin Saiful-imfal dukkan ruhukan
za su shiga jikina, wannan shine zai bani damar shafe miliyoyin shekaru a duniya, domin sai na
rayu adadin shekarun da kowanne ruhi zai yi a duniya. Ya kai sarkin matasan ifritan duniya kayi sani cewa sai na sanya duniya a cikin musiba da
annobar da bata taɓa gani ba. Zan shafe duk wani addini dake doron ƙasa.
Lokacin da bokanya Zulaima yazo dai-dai nan a zancenta sai sarkin matasan ifritai ya dube ta
cikin ladabi ya ce "tsafi ya taimake ki ya uwar bokayen duniya uwa ma bada mama, yanzu
batare da ɓata lokaci ba gaba ɗaya rundunar afritai za su bayyana a gare mu wacce ba ki taɓa
ganin tamkar ta ba. Da yardar tsafi abin dogaro sai kin cimma nasara."
Koda jin wannan batu daga bakin ifritu Shammar sai bokanya Zulaima ta taƙarƙare ta bushe da
dariyar mugunta mai kama da haniniyar doki, al'amarin da ya sanya baki ɗaya kogon dutsen ya
kama girgiza tamkar zai tsaye.
Take ifritu Shammar ya ɓace ɓat! Daga kogon tamkar bai taɓa bayyana ba.
Ita dai bokanya Zulaima ta kasance gawurtacciyar matsafi da tayi shura a cikin bokaye har
masu bincike da hasashe na duniya ke yi mata laƙabi da uwar matsafa,
Babban burin Zulaima shine ta mulki duniya baki ɗaya, bisa binciken da ta yi ne ta gano cewa
dole sai ta mallaki ruhikan sarakunan duniya guda dubu shida ta tsafe su sun shiga jikinta, bisa
wannan dalili ya sanya ta dinga farautar sarakunan tana hallaka su ta ƙarfin sihiri.
Wannan shi ne abin da ya wakana tsakanin uwar bokayen duniya bokanya Zulaima tare da
sarkin matasan ifritai na duniya.
BABI NA SHA HUƊU
A can dajin Baitul-Shazwas kuwa kamar yadda bawa Himlas ya tsara haka al'amarin ya
kasance wato a daren wannan rana suka kammala sanya dukkan tarkuna a dajin cikin
kyakkyawa shiri, ta yadda komai kallon ƙurillar mutum ba zai iya gane an sanya abubuwa masu
cutarwa a dajin ba. Kashe gari tun da duku-dukun safiya aka hango ƙura ta turnuƙe sararin samaniya tamkar hadari
zai gangamo a kece da ruwa. Koda ganin hakan sai kowa ya miƙe ya kimtsa jikin shi, Sulairat
shigar kayan fata tayi tun daga ƙasa har sama a gadon bayanta tana rataye da wata
rantsattsiyar kwari da baka, a gwiɓin cinyarta kuwa tana ɗauke da takobin Saiful-imfal wacce a
daren jiya zakanya Juraima ta yi mata jagora izuwa inda takobin take ta ɗauko, a wuyanta kuwa
tana rataye da sarƙar tsafinta kuma ta raba gashin kanta gida biyu ya zuba akan kafaɗunta.
Shigar ta yi matuƙar yi mata kyawu da kwarjini, bawa Himlas da Sunaila tare da Suhaimat
shigar tufafi iri ɗaya suka yi sak gaba ɗaya sun rufe fuskokinsu da baƙin yanki idanuwansu
kaɗai ake gani.
Cikin hanzari kowanne ya tsaya a matsayar shi kamar yadda aka tsara.
Sulairat ta tsaya a ɓangaren gabas tana zaune bisa kan zakanya Juraima, Suhaimat a yamma,
Himlas kudu sai Sunaila a yamma.
Tsawon daƙiƙa ɗari aka shafe a cikin wannan hali sai daga bisani ne duhun dake sararin
samaniya ya ye sai aka jiyo ƙarar takun sawaye haɗe da haniniyar dawakai ta cika dajin baki
ɗaya.
A can bakin gaɓar shigowa dajin Baitul-Shazwas kuwa sarauniya Abidat tare da tawagar ta
na ƙara kusantar dajin, lokacin da ya rage saura taku arba'in tsakanin su da dajin sai Abidat ta
ɗaga hannunta sama aka tsaya can! A wannan lokaci Abidat tana sanye cikin baƙin sulken yaƙi
tun daga ƙasa har sama kanta sanye da hular ƙarfe a gadon bayanta tana rataye da wata
rantsattsiyar takobi a cikin kubenta, sanye a jikinta akwai makaman yaƙi fiye da guda ashirin,
kaico! Haƙiƙa babu wani gwarzo da zai yi arba da Abidat a cikin wannan hali face ya razana
domin shigar da tayi, shiga ce ta tawagar mutuwa.
A gefen hannunta na dama sarkin yaƙi ne cikin shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
Abidat ta ƙarewa dajin kallo tana nazarin shi zuwa can sai ta dubi sarkin yaƙi ta ce "ya dirkar
birnin Sin kana ganin cewa su Sulairat ba su san da zuwan mu ba, ko kuwa wani tanadi suka yi
mana domin su yi mana mamayar bazato?
Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaƙi ya dube ta cikin ladabi ya ce "ya shugabata haƙiƙa
abokan gabarmu sun shirya wani tuggu domin su mamaye mu, na tabbata cewa suna cikin
wannan daji domin babu wani waje da zamu ɓuya da huce nan, sannan koda a ce ba su san da
zuwan mu ba ai bayyanar mu ta zo masu domin hakan dole mu fara kai farmaki na somin taɓi." Koda jin wannan batu sai sarauniya Abidat ta ce "zancen ka dutse ya kai dirkar birnin Sin dole
ayi hakan, sannan kasancewar ba ni da ikon shiga dajin Baitul-Shazwas dole ne mu tura
dakarun mu su kai hari da yadda dole su Sulairat za su fito mu yi GABA DA GABA da su."
Ya yin da sarauniya tazo nan a zancen ta sai sarkin yaƙi Hunaifu ya risina kawai sai ya yiwa
waɗansu dakaru mutum dubu inkiya ta wutsiyar idanu, tamkar dakarun sun fahimci abin da
yake nufi sai kawai suka sanya hannayensu suka ciro kibbau daga cikin kwarinsu suka tsoma
su a cikin wani kuttu mai ɗauke da guba, kana suka sanya a cikin bakansu suka ja suka ɗame
sannan suka harba. A lokaci guda kibban suka tafi cikin matsanancin gudu suka durfafi dajin,
duk inda suka sauka sai wuta ta kama koda korran tsirrai ne sai wutar ya ƙonamu. Nan fa
hayaƙi ya turnuƙe dajin wuta ta kama ci ganga-ganga.
Tsawon daƙiƙa ɗari ana cikin wannan hali al'amarin da ya fusata sarkin yaƙi Hunaifu kenan ya
fara wasi-wasi ya fara tunanin shin ko su Sulairat sun yi nisa a cikin dajin.
Kawai sai ya dakawa dakaru dubu uku tsawa da ke nuna ba su umarni suka afka cikin dajin.
Cikin hanzari dakarun suka zaburi dawakansu suka durfafi dajin.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani ya fi dare duhu kuma tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka
inda ace waɗannan dakaru sun san abin da zai faru da ba su gangancin kutsa kai ba.
Lokacin da suka isa ciki nan take suka fara faɗawa tarkuna suna hallaka tare da dawakansu.
Nan fa ihu da kururuwar mazaje ta cika dajin baki ɗaya
Sa'adda sarauniya Abidat taga yadda dakarunta ke yin mutuwar wulaƙanci sai takaici da baƙin
ciki suka turnuƙe ta ta ji tamkar ta kunna kai izuwa cikin dajin amma da ta nuna babu halin
hakan sai ta haƙura,
Kafin shuɗewar daƙiƙa hamsin fiye da mutum dubu na dakarun sun baƙunci barzahu, cikin
hanzari sarkin yaƙi Hunaifu ya yi umarni a ja da baya, kamar taku goma sannan aka tsaya cak
aka yi cirko-cirko.
Sai da ƙura ta lafa sannan aka jiyo ihu da gurnanin zakanya Juraima daga can sai ga su sun
ratso ta duhuwar bishiyun sun bayyana a fili.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu cikin matuƙar ƙiyayyar juna da mugun
tanadi.
Daga can dukkan ɓangarorin biyu suka yunƙura izuwa kan juna gami da falfalwa da
azababban gudu, suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA, lokacin da ya rage
saura kamar taku shida tsakani sai sarauniya abidat ta dako wawan tsalle daga kan dokinta tun
a sama ta zare takobinta ta kaiwa Sunaila wawan sara. Cikin baƙin zafin nama irin na GAWURTACCIYA ta zare takobin Saiful-imfal ta kare harin, koda
takubban suka haɗu da juna nan take aka kwantsama wata tsawa gami da walƙiya marar daɗin
sauraro wacce ta sanya bishiyu karairayewa suna haɗu izuwa kan mayaƙa da dama suka faɗi
ƙasa matattu. Sannan Abidat ta sauka ƙasa cikin gwaninta bisa diga-diganta.
A dai-dai lokacin ne bawa Himlas ya tari sarkin yaƙi Hunaifu, baiwa Sunaila da Suhaimat kuwa
suka kutsa izuwa cikin abokan gaba.
A lokaci guda duka ɓangarorin suka haɗu da juna aka ruguntsume da azababban yaƙi mai
matuƙar kwarjini muni daban tsoro,
Kaico! Haƙiƙa duk wanda bai ziyarci filin yaƙi ba to bai ga maƙurar tashin hankali ba. Domin yaƙi
shine ke sanyawa a rasa rai, dukiya, da mutunci baki ɗaya.
Wohoho! Idan gwani ya haɗu da gani a filin fama dole yaƙi ya zamo gwanin sha'awa da tashin
hankali.
A ɓangaren manyan giwaye biyu Sarauniya Abidat da jaruma Sulairat kuwa gaba ɗaya sun
ɗauki hankalin duk wata halitta dake filin yaƙin, domin kuwa suna artabun ne cikin gwaninta da
ƙwarewa tamkar na'ura ce ke sarrafa su, jikkunansu ba su kasance na jini da tsoka ba, ita kuwa
zakanya Juraima aiki biyu yake tana kaiwa sarauniya abidat hari tare da farmakar dakaru tana
yi masu ɓarna.
A ɓangaren Bawa Himlas da sarkin yaƙi Hunaifu kuwa sun wanzu suna kaiwa juna hare-haren
cikin JURIYA DA BAJINTA irin ta 'yan MAZAN JIYA, duk sa'adda takubbansu suka haɗu da juna
sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara marar daɗin saurare.
Suhaimat da Sunaila kuwa duk inda suka sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa
magashiyan