Showing 12001 words to 15000 words out of 25373 words

Chapter 5 - KARSHEN ZALUNCI COMPLETE BOOK BY SUFI .pdf

izuwa birnin Sin.


BABI NA GOMA

A can brinin Sin kuwa, washegari tunda duku-dukun safiya fadar Sarauniya Abidat ta cika
ta batse da jama'a maza da mata yara da manya, duk inda mutum ya kalla kawunan bil'adama
ne rututu babu masaka tsinke tamkar dandazon kiyasai.
Abin tambaya anan shi ne ko me ya sanya jama'ar barin gidajensu suka halarci wannan fada
tunda duku-dukun safiya haka?.
Ba komai ne ya sanya hakan ba sai domin a yau ne sarauniya Abidat za ta yankewa baiwa
Sunaifa da bawa Himlas hukuncin kisa ta hanyar sare masu wuya.
Bisa wani BOYAYYEN AL'AMARI da ta gano a cikin halarar tsafinta a daren jiya, abinda ta gano
din kuwa shi ne.
Ba wani abu bane ya sanya bawa Himlas yake wannan murmushi a jiya a lokacin da suke tafiya
a cikin kasuwa ba har ya dai na jan keken dokin da take kai ba face arba da ya yi da Sulairat,
har suka kamu da soyayyar junansu.
Abin da zai ƙara tabbatar maka da hakan shi ne idan ka yi duba izuwa ga waɗansu manyan
diraku da ke tsakiyar fadar, za ka yi arba da bawa Himlas da baiwa Sunaila ɗaure cikin sasari
na baƙin ƙarfe hannu da ƙafa.
Fiye da tsawon rabin sa'a jama'a na cece-kuce kowa na faɗin albarkacin bakinshi bisa jinkirin
fitowar Sarauniya Abidat.
Ana cikin wannan hali ne sai aka jiyo bushin algaita haɗe da bugun tambura daga cikin gidan
sarauta alamar ga Sarauniya Abidat nan tana gab da bayyana.
Jim kaɗan sai ga Sarauniya Abidat tare da muƙarrabanta sun kunno kai izuwa cikin fadar
waɗansu gabza-gabzan samudawa dakaru ma'abota baƙaƙen tufafi na take masu baya, a
wannan lokaci sarauniya Abidat tana sanye da shuɗiyar alkyabba mai ratsin ruwan zinare da ta
kama jikinta, surorinta suka bayyana ainun kanta sanye da kambu na sarauta fuskarta a
murtuke babu annuri.

Kai tsaye ta huce izuwa inda karagar mulkinta take ta taka matattakalar fadar ta juya tana
mai fuskantar jama'a, nan take fadar ta yi tsit tamkar mutuwa ta gifta.
Sarauniya Abidat ta sake murtuke fuska tamkar an aiko mata da SAƘON MUTUWA ta buɗi baki
cikin kakkausar murya sannan ta ce, "Ya ku jama'ar wannan fada tawa mai albarka ku yi sani
cewa, ba komai ne ya sanya na taraku anan ba sai domin ku ganewa idanuwanku irin hukuncin
da zan yankewa bawa Himlas da baiwa Sunaila bisa mummunan laifin da Himlas ya aikata
mani na kin bayyana min abokiyar gaba ta Sulairat 'yar marigayi sarki Urwat na birnin
Nurul-Kusuf a lokacin da yake jan keken doki na a cikin kasuwa."
Sa'adda sarauniya Abidat ta zo dai-dai nan a jawabinta sai fadar ta kaure da cece-kuce
kowa na faɗin albarkacin bakinshi.
Zukatansu cike da matuƙar takaici gami da baƙin ciki bisa hukuncin da Abidat za ta zartarwar
bawa Hilmas da Sunaifa.
Ya yin da Sarauniya Abidat ta ga fadar ta kaure da hayaniya sai kawai ta daga hannunta sama,
jama'a suka yi shiru, sannan ta ci gaba da cewa.
"Sanin kanku ne cewa a iya tsawon rayuwata ba a taɓa aikata mani laifi mafi muni da ya huce
wanda Himlas ya aikata min ba, saboda haka a yanzu zan zartar masu da hukuncin kisa ta
hanyar sare masu wuya."
Koda gama faɗin hakan sai sarauniya Abidat ta koma kan karagarta ta hakimce, kawai sai
wani basamuden ƙato ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanshi mai tsawo da kaifin
tsiya, ya durfafi inda Himlas da Sunaifa ke ɗaure, yana huci tamkar zai ci babu ya yin da ya isa
daf da inda suke sai kawai ya daga takobin domin ya datse wuyan bawa Himlas, a dai-dai
lokacin da baiwa Sunila tare da wasu daga cikin jama'ar fadar suka fara zubar da hawaye
saboda tausayi.

SHIN WANNAN BASAMUDEN ƘATON YANA SARE WUYAN BAWA HIMLAS DA BAIWA
SUNAILA?

SHIN YAUSHE NE SULAIRAT ZA TA ƊAUKO TAKOBIN SAIFUL-IMFAL DAKE CIKIN
DAJIN BAITUL SHAZWAS?

YAUSHE NE ZA TA SHIGO HAR CIKIN BIRNIN SIN DOMIN TA ƊAUKI FANSA AKAN
SARAUNIYA ABIDAT?

A WANE HALI ZA TA KASANCE NA KAMUWA DA MATUKAR SOYAYYAR BAWA
HIMLAS?

Mu haɗu a ƘARSHEN ZAMUNCI littafi na uku domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.
Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.
Mansur Usman Sufi

ƘARSHEN ZALUNCI
Littafi na uku
Rubuta Labari
MANSUR USMAN SUFI
Sarkin Marubutan Yaƙi
08137237071



BABI NA SHA ƊAYA


Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu masifaffun kibbau sun soke
badakaren a idanuwanshi ya kurma wawan ihu ya zube ƙasa yana shure-shure take jikinshi ya
sandare ya sheƙa barzahu.
Cikin hanzari mutane suka waiga bayansu domin su ga wane ne ya harbo kibbau ɗin.
Ai kuwa koda suka yi tozali da ko mene ne sai suka yi turus! Bakomai suka gani ya ba su
mamaki ba face wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa.
Budurwar takasance mai matsakaicin kaurin jiki ba doguwa ba ce ba gajera ba. Tana da
dara-daran idanuwa farare ƙal! Masu haske tamkar tacecciyar madarar shanu, hancinta dogo
mai lankwasa a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓanshi suka kasance jajur,
wuyanta dogo mai kyawu tamkar na barewa, ƙirjinta a cike yake kuma a tsaye ƙyam basu
ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda saboda kyawun su, cikinta a shafe yake tamkar bata
taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake ta gaba daga baya kuma ya yi tudu ainun ta yadda
koda kofin lemu aka ɗora akai zai zauna daram, tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi masu ɗaukar
hankali, babban abin da ya ƙara tona asirin kyawunta shine dogon gashin kanta baƙi siɗik mai
ƙyalli ya zuba har izuwa kan kwankwasonta.
Wohoho! Haƙiƙa wannan budurwa ta cika maƙura a kyawu, domin babu wani ɗa namiji mai
hankali da zai yi arba da ita face ya kamu da matuƙar ƙaunar ta. Tana sanye cikin ƙayatattun
tufafi na fatun dabbobi tun daga ƙasa har sama, a gadon bayan ta tana rataye da wani kwari,
hannunta riƙe da baka, kuma tana zaune ne akan wata ƙatuwar zakanya. Wata ba ce wannan kyakkyawar budurwa ba face jaruma Sulairat yar Marigayi sarki urwat
tare da zakanya Juraima.
Sa'adda sarauniya Abidat tayi arba da ita sai ta miƙe tsaye zumbur daga kan karagarta
fuskantarta a murtuke babu annuri tamkar an aiko mata da WASIƘAR MUTUWA, Nan fa aka
fara kallon-kallo tsakanin su, cikin tsantsar ƙiyayyar juna, inda a ɓangaren guda kuma Sulairat
ke satar kallon masoyinta bawa HIMLAS. Tsawon daƙiƙa hamsin ana cikin wannan hali. Daga can Abidat ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, a lokaci guda kuma ta turɓune
fuska tamkar ta buɗi baki cikin kakkausar murya ta ce "lale marhaban da zuwan manyan
abokanan gabata, haƙiƙa wannan rana ce mai ɗumbin tarihi a gare ni, domin gashi dukkanin
abokan hamayya sun taru a waje guda. Na rantse da ƙabarin kakana sarki Zaujatul-ashiƙ ba zan ƙyale ɗayan su a raye ba".
Koda gama faɗin hakan ta zare wata sharɓeɓiyar takobin a gadon bayanta ta dako tsalle a
sama tamkar an harbo ta daga cikin baka, ta durfafi inda Sulairat take.

Suna saman suka kaiwa juna sara a kafaɗa.
Cikin matuƙar zafin nama suka sanya takubbansu suka kare harin tartsatsi wuta ya tashi gami
da ƙara, sannan suka sauka ƙasa bisa diga-digansu take suka ruguntsume da azababban yaƙi,
ita kuwa zakanya Juraima sai ta afkawa dakarun fadar da ciwo da yakushi.
Jaruman biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA
DA BAJINTA ta gaban kwatance.
Wohoho! Haƙiƙa idan gwani da gwani suka haɗu a filin fama dole artabu ya zamto abin sha'awa
da tashin hankali.
Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce ranar bikin BABBAR GIWA babu wanda ke
fitowa ya taka rawa face JARUMAN DUNIYA.
Komai hassadar mutum idan yaga yadda jaruman ke yin artabun cikin gwaninta dole ya jinjina
masu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA.
A ɓangaren zakanya Juraima kuwa duk inda ta sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa
ƙasa matattu waɗansu magashiyan.
Nan fa fadar ta kaure da guje-guje da ifice-ificen jama'a kowa ya shiga gudun ceton rai.
Sannu-sannu sai ga shi GWARAZAN MAYAKAN sun shafe tsawon daƙiƙa ɗari biyu suna bawa
hammata iska, suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin matuƙar zafin nama
JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance tamkar ifritai.
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaure wa jama'a kai kenan kuma ya ba su mamaki suka ce a cikin
ransu "haƙiƙa yau sarauniya Abidat ta ɗebo ruwan dafa kanta, kuma ta ɗebo ruwan dafa kanta,
domin a iya tarihi ba su taɓa ganin jarumin da ya yi GABA DA GABA da sarauniya Abidat na
tsawon wannan lokaci ba ba tare da ta kawar da shi ba, wannan fa shi ake cewa ɗan hakin da
ka raina shi ke tsoka ne maka idanu.
A ɓangare guda kuma a ran su suna cewa yau abidat ta sayi ajalinta da kuɗin ta. Kuma mucijin
da ta kashe bata sare kanshi ba. Ma'ana ta kashe Sarki urwat ga 'yarshi ta zame mata ciwon
idanu.
Duk sa'adda ɗayansu ya kaiwa abokin gwaminshi hari idan ya zille sai kaga duk abin da takobin
ta sauka a kai sai ya yi bindiga ya tarwatse koda kuwa gini ne, nan fa manyan giwayen suka
hargitsa fadar baki ɗaya, kuma suka tashi duk halittar dake ciki, a ɓangaren zakanya Juraima
kuwa ta zame wa dakarun sarauniya Abidat ANNOBA ƊARI kuma ƙadangaren bakin tulu sun
rasa yadda za su yi da ita, duk inda ta sanya gaba sai dai kaga zaratan mazaje na zubewa ƙasa
matattu, waɗansu cikin mawuyacin hali.
Nan fa fadar ta kaure da ihun mazaje gami da ƙarar karafniyar ƙarafa.
Ana cikin wannan hali ne jaruma Sulairat ta fahimci cewa idan aka ci gaba da wannan
artabu a haka gine-ginen dake rushewa za su iya raunata bawa HIMLAS da baiwa SUNAILA.
Koda gama tunanin hakan sai ta dako tsalle daga inda take ta dira a daf da inda bawa HIMLAS
da baiwa SUNAILA suke cikin zafin nama ta sanya takobi ta sare sasarin dake jikinsu, sannan
ta sake dako tsalle ta dira akan zakanya Juraima, kawai sai juraima ta dako sufa izuwa inda su
Himlas suke suka haye gadon bayanta sannan ta durfafi ƙofar fita daga fadar. Amma sai sarauniya Abidat ta dako tsalle sama ta sha gaban su ta kaiwa SUNAILA sari da
takobin ta, cikin zafin nama ta sanya takobi ta kare saran sannan ya mayar da martani, duk da
ƙoƙarin da abidat ta yi na kare harin sai da takobin sunaila ta tsarga kumatunta kaɗan jini ya yi
tsartuwa.

Kafin Abidat tayi wani yunƙuri, Cikin wani irin baƙin zafin nama Juraima ta daka wawan tsalle ta
tsallake Abidat da dakarunta dira a ƙofar fadar ta falfalwa da azababban gudu cikin matuƙar
takaici da baƙin ciki dakarun sarauniya suka rufa masu baya, amma kaico! Koda suka fita sai
suka tarar wayam babu kowa, cikin matuƙar takaici suka suka ja suka tsaya, abin da ba su sani
na shine jaruma sunaila ta sanya wannan sarƙar sihiri, bisa wannan dalilin ya sanya
idanuwansu basu iya ganin su.
Koda labarin ɓacewar su bawa HIMLAS ya zo wa sarauniya Abidat sai kawai ta ɗauko madubin
tsafinta a cikin aljihunta ta shafe shi da hannunta na hagu tana mai karanto waɗansu ɗalasiman
tsafi, domin ta gudanar da bincike akan su, amma sai madubin ya yi bindiga ya tarwatse.
Cikin matuƙar takaici ta ƙarƙare kurma wawan ihu da karaɗe fadar baki ɗaya kuma ya amsa
kuwwa izuwa gidan sarauta.
Tsawon daƙiƙa talatin tana cikin wannan hali sai daga bisani ne ta tsuke bakinta sannan ta
durfafi ƙofar da zata fitar da ita daga fada ta kai ta izuwa gidan sarauta, fuskarta a murtuke babu
annuri tamkar an watsa mata garwashin wuta a kai, cikin hanzari dakaru suka rufa mata baya.

BABI NA SHA BIYU

Al'amarin su jaruma Sulairat kuwa sa'adda ta ceci rayuwar su bawa HIMLAS suka cigaba da
gudu a bisa kan zakanya Juraima sai suka shafe tsawon sa'a ɗaya suna tafiya, sannan suka iso
dajin Baitul-Shazwas, tun daga nesa Suhaimat ta hango su koda ta ga su uku a maimakon
'yarta kaɗai sai ta cika da matuƙar mamaki, sannu a hankali suka iso gare ta bakin Kogon
dutsensu.
Bawa Himlas ne ya fara sakkowa daga kan zakanya Juraima sannan Sunaila, Sulairat ce a
ƙarshe.
Cikin matuƙar farin ciki Suhaimat ta tare su tana mai yi masu lale marhaban, fuskarta cike da
annuri tamkar ta haɗu da 'yan uwanta na jini.
Kai tsaye ta jagorance su har izuwa cikin kogon dutse ta zaunar da su, sannan ta kawo
masu abin kalaci da ruwan sha.
Da yake Sunaila da hilwas suna cikin matuƙar galabaita da yunwa nan fa suka shiga cin abincin
hannu baka hannu kwarya, ita kuwa Sulairat sai ta dinga satar kallon Hilwas a fakaice.
Bayan sun kammala ne sun samu nutsuwa nan take Sulairat ta kwashe labarin abin da ya
faru da ita a daren jiya ta yi mafarki bawa Himlas da Sunaila na cikin mawuyacin hali bisa
wannan dalili ya sanya ta ziyarci birnin sin domin ceton rayuwar su.
Kuma ta bata Labarin irin gwagwarmayar da ta sha kafin ta ceto rayuwar su bawa Himlas tun
daga farko har ƙarshe.
Sa'adda Suhaimat taji wannan batu daga bakin 'yarta Sulairat sai ta cika da matuƙar tausayin su
Sunaila, kuma hankalinta ya dugunzuma ainun.
Abu na farko da ya dugunzuma hankalinta shine haƙiƙa ceto rayuwar su bawa Himlas tamkar
siyan ajalinsu ne da kuɗin su domin zai kasance dare da rana sarauniya Abidat na farautar
rayuwar su. Sannan a halin yanzu shin Sulairat ta samu gagarumin ƙarfin da za ta iya GABA
DA GABA da sarauniya Abidat har ta FANSAR RAYUKAN jama'ar birninsu da mahaifinta. Kawai ta ɗago da kanta ta dubi Sunaila da Hilwas ta ce "haƙiƙa labarin ku akwai taɓa zuciya,
kuma ni da 'yata Sulairat zamu zauna tare daku cikin amana, har kawo lokacin da zamu ɗauki
fansa akan AZZALUMA sarauniya Abidat.

Amma wani hanzari ba gudu ba, dole ne a kodayaushe mu kasance cikin shiri domin a kowane
lokaci Abidat da dakarunta za su iya kawo mana FARMAKIN BAZATO"
Koda jin wannan batu daga Suhaimat sai Hilwas da Sunaila suka cika da matuƙar farin ciki
maral-musaltuwa.
Hilwas ya buɗi baki ya yi gyaran murya sannan ya fara magana a karo na farko ya ce "haƙiƙa
nayi matuƙar farin ciki yadda kuka ƙarɓe mu kuma kuma bamu mafaka tare da ceton rayuwar
mu, bamu da wani abu da zamu iya biyan ku. Ina mai yi maku alkawari ni da ummina cewa ba
za mu ci amanar ku ba. Sannan game da batun sarin bazato da Abidat zata iya kawo mana ina da wasu shawarwari da
idan muka bi su za su cimma nasara.
Da farko a yau zamu kafa dukkan tarkuna a sama bishiyu da duk wata hanya ta shigowa
wannan daji,
Sannan zamu kasu gida huɗu kusa da juna ta yadda zamu dinga samun bayanan juna,
Sannan dole ne mu yi amfani da makamai biyu Kwari da baka da wani daban domin kai hari ta
nesa kafin yin karon batta da abokan gaba."
Sa'adda bawa HIMLAS yazo dai-dai nan a zancen shi sai kowa ya cika da matuƙar farin
ciki maral-musaltuwa, domin ya kawo shawara mai kyau.


BABI NA SHA BIYU


A gabar tekun Baharul-Aswad dake yamma maso kudancin duniya an yi wata babbar ƙasa
da ake kira da suna Madinatul-haiwan.
Kasar Madinatul-haiwan ta bunƙasa a noma kiwo da ƙarfin tattalin arziki, daɗin daɗawa kuma
sun tara zaratan mayaƙa masu juriya a filin daga.
Sarkin dake mulkin birnin yakasance GWARZON MAYAƘI mai tarwatsa dandazon mayaƙa a
filin fama, mashahurin attajiri ne kuma gawurtaccen matsafi na kiran shi da Nadiyar ibn shaiban.
Sarki Nadiyar ya shara a kaf nahiyar a jerin sarakunan dake makwabtaka da shi bisa ƙasaitar
sa ne ya sanya sarakunan dake shakkar shi, domin ya zame masu ciwon idanu" kuma
ƙadangaren bakin tulu".
Sarki Nadiyar yana da matan aure guda bakwai. Gaba ɗaya matan sun kasance 'ya'yan 'ysn
majalisar sarki bakwai, baki ɗaya 'yan majalissar sun kasance wakilan ƙabilu bakwai mafiya
yawa a ƙasar.
Domin haka kowacce ƙabilar tana matuƙar kwaɗayin ace jinin ƙabilarsu ta samu juna biyu ga
sarki Nadiyar, sai dai duk cikin su babu wacce ta taɓa samun rabo, sarki ya gudanar da bincike
sai shirun masaƙi domin ya gano mene ne ya sanya ya kasa samun magani amma sai halarar
tsafin shi ta bayyana mashi cewa ba zai taɓa samun haihuwa ba face ya mallaki abubuwa guda
biyu masu matuƙar wahalar gaske waɗanda neman su dai-dai yake da neman jaki mai ƙaho.
Abu na farko shine wata takobi mai abubuwan al'ajabi, mallakin sarkin bokaye.
Na biyu shine wata zakanya mai abubuwan al'ajabi dake ake kira da suna Juraima.
Waccan takobi zai yi amfani da ita wajen kashe wata mucijiya dake zaune a kogon Garul-musib,
wacce da ake yiwa laƙabi da kuburul-shamshan wato uwar mucijan duniya, bayan ya kashe

mucijiyar zai samu damar shiga wata ƙorama har ya ɗebo ruwanta ya kawo ɗaya daga cikin
matanshi ta sha ruwan sannan zai samu magaji.
Binciken bokaye da masu hasashe ya tabbatar da cewa a halin yanzu a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login