Showing 18001 words to 21000 words out of 25373 words

Chapter 7 - KARSHEN ZALUNCI COMPLETE BOOK BY SUFI .pdf

waɗansu matattu.
Wohoho! Haƙiƙa komai hassadar mutum idan ya ga yadda Waɗannan zaratan mataye ke
ragargazar 'yan maza suna maishe su mataye, dole ne ya jinjina masu ya tabbatar cewa tabbas
sun cika mataye masu kamar maza kuma zaratan mayaƙa.
Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya da rabi ana wannan ɗauki ba daɗi.
Nan fa ƙura ta turnuƙe sararin samaniya tamkar hadari ya gangamo, ƙarar karafniyar ƙarafa,
ihu da kururuwar mazaje haɗe da haniniyar dawakai suka cika dodon kunne.
Haƙiƙa a wannan rana dakarun sarauniya Abidat suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa
ganin tamkar ta ba.
Ana cikin wannan karon batta ne sarauniya Abidat ta kaiwa Sulairat wani wawan sara da
takobinta a kafaɗa da nufin tsinke mata wuya.
Cikin wani irin baƙin zafin nama Sulairat ta wurƙila da zillewa harin gami da mayar da martani,
koda Abidat ta sanya takobin da nufin karewa take ta karya gida biyu ta faɗi ƙas.
Kafin ta yi wani yunƙuri Sulairat ta dunƙule hannunta ɗaya ta kirɓa mata wawan naushi a fuska,
saboda ƙarfin naushin sai da Abidat ta yi sama ta sauka daga kan dokin ta tayi katantanwa sau
biyu sannan ta faɗi ƙasa amma sai ta miƙe tsaye zumbur!
Tana mai gyara tsayuwarta, koda ta sanya hannunta ta shafa kumatunta nan take taga jini a
inda Sulairat ta naushe ta ɗin.
Koda ganin hakan sai sarauniya Abidat ta cika matuƙar baƙin ciki, kawai sai ta taƙarƙare ta
kwarara wawan ihu ta zare sabbin makamai biyu a jikinta ta sake afkawa Sulairat a karo na
biyu, suka ruguntsume da sabon artabu.
Abu kamar wasa sai gashi dukkanin makaman yaƙin Abidat sun karairaye sun faɗi ƙasa.
Abin da bata sani ba shine har abada babu wani makami da zai iya yin tasiri akan takobin
Saiful-imfal, bisa wannan dalili ya sanya makamanta suka lalace.
Nan fa taurarin biyu suka ja da baya suna haki da zufa, suna hararar juna tamkar waɗansu
zakaru saboda yadda suka bawa hammata iska.
Ita zakanya Juraima sai ta dinga buga ƙafarta ɗaya a ƙasa tana gurnani domin shirin
kar-ta-kwana.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga sararin samaniya ta yi
duhu dunɗum! Tamkar dare biyu ne ya haɗu waje guda, sannu a hankali sai aka hango
waɗansu irin halittu marasa adadi na ketowa daga cikin gajimare suna sauka a bisa turba, duk
sa'adda ɗayansu ya saukan sai ƙasa ta amsa, ya yin da halittun suka kammala sauka sai suka
yiwa dajin ƙawanya.
Nan fa dawakai suka firgice suka kama haniniyar suna zubar da mahayansu suna nausa cikin
daji bisa arba da suka yi da halittun.
Su dai halittun suna matuƙar muni, kwarjini daban tsoro. Baki ɗayan su suna shirye cikin
gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini, hannayensu ɗauke da miyagun makamai.

Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su Sulairat Abidat da tawagar halittun.
Daga can nesa kaɗan sai aka jiyo ƙarar takun sawayen dawakai haɗe da haniniyar su, ƙura ta
turnuƙe sararin samaniya, sannu a hankali sai aka hango tawagar mayaƙa guda biyu
mabanbanta sun durfafi sansanin.
Lokacin da yazamana tazarar dake tsakani bata huce kamu ashirin ba, sai dukkanin su suka yi
turjiya suka tsaya cak!
Sa'adda zakanya Juraima taga abin da ke faru na bayyanar waɗannan baƙin rundunoni
uku sai kawai ta yi wani gurnani. Ashe Sulairat ta fahimci abin da take nufi don haka sai kawai
ta murza wannan sarƙar tsafi dake wuyanta.
Nan take su duka jama'arsu suka ɓace ɓat! Daga filin artabun tamkar ba su taɓa wanzuwa ba.
Cikin matuƙar takaici da baƙin ciki sarauniya Abidat ta taƙarƙare ta kurma wawan ihu a karo na
biyu tamkar baza ta daina ba.

BABI NA SHA BIYAR


Kaico! Haƙiƙa a wannan rana sarauniya Abidat tayi matuƙar baƙin ciki da bata taɓa yin
tamkar shi ba, kuma ta kunyata a idanun talakawanta.
Tsawon daƙiƙa goma tana cikin wannan hali sai daga bisani ne ta tsuke bakinta kuma ta
turɓune fuska tamkar an aiko mata da SAƘON MUTUWA.
Ta dubi sarkin yaƙi a lokacin da ya so daf! Da ita ta dube shi ta ce "ya kai dirkar birnin Sin yanzu
gashi a karo na biyu na sake yin rashin nasara, sai dai hakan ba zai sanya gwiwata tayi sanyi
ba, zamu yada sansani a nan har izuwa lokacin da za mu sake yin nazari game da kai farmaki
ga abokan gaba." Koda jin wannan batu daga bakin Abidat sai sarkin yaƙi Hunaifu ya risina ya ce "zancen ki dutse
ya sarauniya mai duniya, amma wani hanzari ba gudu ba, shin Waɗannan tawagar sarakai da
halittu mene ne manufar su na zuwa nan.
Shin sun zo ne domin farautar zakanya Juraima da Sulairat ko kuwa domin mallakar takobin
Saiful-imfal?
Sa'adda Abidat ta ji wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai tayi shiru tana mai zurfafa cikin
kogin tunani daga bisani ya dube shi ta ce "haƙiƙa maganarka akwai ƙanshin gaskiya a ciki, ai
gamu ga su za muga abin da zai turewa buzu naɗi. Domin kuwa ba zamu lamunci kura da shan
bugu gardi da ƙwace kuɗi ba. Yanzu sai kayi umarni ayi maza a kafa tantuna, tun da rana ta fara zafi ainun, akwai buƙatar
mayaƙanmu su samu ƙwarin jikin da za su cigaba da kai farmaki."
Da jin wannan furuci sai sarkin yaƙi ya ce"an gama ranki shi daɗe.
Cikin hanzari ya juya da baya tare da umartar dakaru su fara aikin kafa tantunan, kafin
shuɗewar daƙiƙa hamsin sun kammala dukkan jama'a sun shiga ciki.
Al'amarin waɗannan halittu da suka sauka a wajen kuwa, ya yin da suka ga cewa su jaruma
Sulairat sun ɓacewa su sarauniya Abidat kuma su Abidat sun kafa sansani, sai suma suka
janye izuwa gefe guda nesa kaɗan da inda suke suka yada na su sansanin a bisa kan waɗansu
dawatsu. Haka al'amarin ya kasance ga sauran tawagar sarakunan biyu inda kowannen su yaja gefe
guda nesa da ɗan uwanshi ya yada sansani.

Ba wasu ba ne waɗannan tawaga biyu face, ayarin sarki Nadiyar na kasar
Madinatul-haiwan, da ya fito farautar zakanya Juraima da takobin Saiful-imfal, domin cika burin
shi na samo maganin da zai bawa ɗaya daga cikin matanshi ta samu haihuwa.
Tawaga ta biyu kuwa tana bisa jagorancin sarki Damzaru ibn Gauras na birnin
Salsalul-mahabba dake yamma maso arewacin duniya a gaɓar tekun nil.
Shi dai sarki Damzaru ya kasance matashin saurayi kyakkyawa, da masu hasashe suka
tabbatar cewa a duka nahiyar babu namiji kyakkyawa tamkar shi, GWARZON ƘARNI mai
tarwatsa dandazon mayaƙa a filin daga, ya shahara ainun a fagen ilimin tsafi gami da tarin
dukiya dangin lu'ulu'u da dinare. A rayuwar sarki Nadiyar bai taɓa soyayya ballantana aure, 'ya'yan manyan sarakai da attajiran
duniya sun rasa rayukansu bisa kamuwa da ciwon soyayyar shi.
Bakomai ne ya sanya sarki Damzaru bai taɓa ƙarɓar soyayyar wata 'ya mace ba ko batun aure
ba sai domin wata lalura dake damun shi.
A jikinshi yana ɗauke da halittar mace da namiji, tun ranar da aka haife shi bokaye suka
tabbatar da cewa idan har likitoci suka yi masa aiki domin cire al'auran mace a tare da shi to fa
za a rashi baki ɗaya. Kuma bokayen ba su gano inda wane magani zai magance lalurar ta shi
ba. Tun daga wannan lokaci dare da rana sarki Damzaru bashi da aiki face gudanar da bincike bisa
halarar tsafin shi domin ya gano maganin lalurar shi amma bai taɓa samun wani bayani ba.
Al'amarin da yake matuƙar jefa shi a cikin damuwa kenan har takai yana zubar da hawayen
baƙin ciki.
Wata rana yana zaune a turakarshi bisa kan ƙasaitacciyar tujera yana gudanar da bincike bisa
halarar tsafin shi kwatsam! Sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar farin ciki tamkar na zai daina,
Al'amarin da yayi matuƙar bawa kuyangi da dakarun tsaro mamaki kenan domin yau tsawon
shekaru goma rabon da aji sarki Damzaru ya yi wanan dariya.
Abin da basu sani ba shine bakomai ne ya sanya sarki Damzaru wannan dariyar farin ciki
ba sai domin ya gano maganin da zai sha ya warware mashi lalurar shi.
Bakomai ne maganin ba face wata saiwar itaciya da ake kira da Shajarul-shifa'a dake ajiye a
dajin fatalwa. Zai jiƙa saiwar Shajarul-shifa'a sannan ya sha ruwanta, da zarar aiwatar da
hakan halittar 'ya mace dake tare dashi zata fita ya dawo cikekken namiji,
Asalin Shajarul-shifa'a ta tsiro ne daga cikin tukunyar tsafin wani shu'umin boka da ya rayu a
dajin fatalwa, saboda bishiyar na ɗauke da waɗansu muhimman ɗalasiman tsafi da a halin
yanzu babu wani matsafi da yake da irin su a duniya.
Sannan muhimmin abin da sarki Damzaru ya gano shine burin shi ba zai taɓa cika ba na samun
saiwar Shajarul-shifa'a face ya mallaki takobin Saiful-imfal wacce da ita ne kaɗai zai iya yaƙar
halittun dake rayuwa a jikin bishiyar.
Su dai halittun sun kasance masu kama da tsuntsun batoyi, suna ɗauke da fuka-fukai irin
jemage, bakunansu suna kaifi fiye da na takobi, duk abin da suka yanka da shi koda ƙarfe ne
sai sun raba shi gida biyu, tsananin zafin naman su ya huce tunanin bil'adama.
Sai da sarki Damzaru ya shafe tsawon daƙiƙa goma yana wannan dariyar farin ciki, sannan ya
tsagaita, nan take ya fito daga turakarshi ya dinga ɗibar dinare yana rabawa talakawa, al'amarin
da yayi matuƙar ɗaure jama'a kai kenan suka ce a cikin ransu shin ko mene ne ya sanya sarki
Damzaru sannan farin ciki haka? Ko kuma ya samu abokiyar rayuwarshi ne. Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan kawai suka zuba idanu.

Kashe gari tunda asubar fari sarki ya kammala shirin fita farautar takobin Saiful-imfal, bayan
aiwatar da hakan sai ya yi bankwana da talakawan shi suna masu yi masa fatan samun nasara
kasantuwarshi adali mai tausayin jama'arshi.
Wannan shine dalilin da ya sanya sarki Damzaru ya fito farautar takobin Saiful-imfal.

***

Budurwa ce kyakkyawa ta gaban kwatance sanye da fararen tufafi masu yalwa tun daga
ƙasa har sama. ta rufe fuskarta da baƙin rawani idanuwanta kaɗai ake gani a gadon bayanta
tana rataye da wata sharɓeɓiyar takobi a cikin kubenta tana zaune bisa farar taguwa.
Tafiya take cikin hanzari a cikin wani ƙasaitaccen daji mai ɗauke da sahara.
Sai da shafe tsawon zango biyu tana tafiya babu sassauci, tana cikin wannan hali ne kwatsam
sai ta hango ƙura ta turnuƙe a can nesa kaɗan da inda take, koda ganin hakan sai taja linzamin
taguwarta ta tsaya cak!
Sannu a hankali ƙurar tana Kusanto inda take har yazamana tazarar dake tsakanin su bata
huce kamu goma ba.
Lokacin da ƙurar ta lafa sai ga waɗansu irin karen daji uku masu matukar girma da
kwarjini, sai gurnani suke sun durfafo inda take wani yawu mai yauƙi yana dalala daga
bakunansu. Su dai waɗannan karnuka sun kasance na sahara masu cinyin naman bil'adama,
yau tsawon kwanaki huɗu ba su komai ba, domin haka suna cikin tsananin buƙata, bisa ɗabi'ar
kurayen suna jiyo ƙamshin bil'adama a tsawon nisan rabin zango.
Lokacin da kyakkyawar budurwar ta hango karnukan sun durfafo inda take cikin mugun
nufizsai kawai ta dako wawan tsalle daga kan taguwarta ta dira bisa diga-diganta gami da zare
takobinta suka shiga yin kallon-kallo.
Daga can kawai ta ruga izuwa gare su domin tarar juna tana mai furta waɗansu kalamai da ita
kaɗai ta san me take nufi.
Sa'adda suka haɗu da juna sai suka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban
tsoro.
Abin tambaya anan shine daga ina wannan kyakkyawar budurwa take kuma ina ta dosa?
Amsar hakan kuwa shine :-
Sarki Shaibat ibnu Abbas yakasance dattijo ma'abocin haiba da SADAUKANTAKA da
tarin duniya, mutum ne shi mai son addini da kyautata al'ummarshi, baya nuna bambanci a
wajen hukunci tsakanin talaka da attajiri, bisa hakan ya sanya al'ummarshi ke matuƙar tausayin
shi, hakan ya samo asali ne kasancewar shi ma'abocin addinin Musulunci. Yana da matan aure ɗaya da ta haifa mashi 'ya'ya biyu.
Gimbiya Husnat da Hasinat, an haife su tagwaye masu matuƙar kama da juna tamkar an tsaga
kara, sun tashi cikin gata da kulawar mahaifin su.
Wata rana kwatsam! Sai aka wayi gari matar sarki Shaibat tare gimbiya Hasinat sun ɓace an
neme su an rasa, nan fa hankalin sarki da jama'a ya dugunzuma ainun aka shiga bincike saƙo
da lungu amma tsawon kwanaki biyu babu labarin su, wani abu da ya ɗaurewa al'umma kai
shine babu wani sahihin labari da aka samu na dakarun sumame. Lokacin da sarki Shaibat ya tsananta da bincike sai ya fahimci cewa tabbas anyi aiki da
sihiri a sace gimbiya da mahaifiyarta.

kuma babban abokin gabar shi ne ya aikata haka sarki Marwatu, kuma ya yi hakanne domin
shirya mashi baƙin tuggu na shafe birnin sa da addinin musulunci a doron ƙasa.
Asali tsarkin sarki Marwatu da Shaibat sun kasance ba a ga maciji da juna, kuma gaba ce
data samo asali tun iyaye da kakanni.
Amma rana tsaka sarki Marwatu ya yi mubaya'a aka yi sulhu, aka cigaba da hulɗar kasuwanci
da auratayya tsakani, yazamana cewa wasu daga cikin al'ummar sarki Marwatu na barin bautar
gumaka su karɓar addinin musulunci, batare da sun fuskanci wata tsangwama ko hukunci ba.
Lokacin da alaƙa ta yi ƙarfi sosai sai sarki Marwatu ya aikewa da sarki Shaibat cewa babbar
'yarshi gimbiya maulut ta kamu da matuƙar ƙaunarshi kuma ta na so ta aure shi.
Lokacin da wannan labari ya riske shi sai ya kasa zaune ya kasa tsaye, yana nazari akan
wannan al'amari inda daga ƙarshe ya yanke shawarar amince domin wata ƙila idan ya aure ta
hakan zai janyo hankalinta da na mahaifinta zuwa addinin musulunci.
Bisa wannan dalili ya sanya sarki Marwatu ya auri gimbiya maulut har ta haifa masa 'yan biyu
mata gimbiya Husnat da Hasinat.
Abin da sarki Shaibat bai sani ba shine a daren ranar da matarshi ta haihu sarki Marwatu ya
bayyana a turakarta cikin alƙalumman sihiri ya shayar da jaririyar Hasinat tsufin tsafi, bayan ya
ɓace ɓat daga turakar ne da daƙiƙa goma aka haifo Husnat.
Bisa wannan dalili ne ya sanya gimbiya Husnat ta taso da son ibada da addini saɓanin 'yar
uwarta Hasinat.
Sirrin da aka ɓoyewa sarki Shaibat shine an aura mashi gimbiya maulut domin ayi amfani da
ita wajen cin amanar shi da ganin bayanshi.
A halin yanzu 'yarshi gimbiya Hasinat babu wanda ta tsana a duniya fiye da shi.
Wani abin takaici da sarki Shaibat ya samu labari shine, a halin yanzu sarki Murwatu ya tura
gimbiya Hasinat izuwa dajin Baitul-Shazwas domin ta mallako takobin Saiful-imfal wacce da
zarar ta mallaki takobin zata shigo har birnin Niyaƙul-kabir ta hallaka shi.
Daga wannan lokaci za ta cigaba da azabtar da dukkan Musulmi a faɗin duniya.
Lokacin da sarki Shaibat ya samu wannan bayani sai hankalinshi ya dugunzuma ainun ya
kasa zaune ya kasa tsaye, bisa wannan dalili ya sanya ya yi ganawar sirri da manyan
hakimanshi, inda daga ƙarshe suka yanke shawarar a tura 'yar uwarta Husnat domin ta hana ta
cimma burinta na mallakar takobin Saiful-imfal domin ta hallaka mahaifinsu. Wannan shi ne dalilin da ya sanya wannan kyakkyawar budurwa ta fito farautar 'yar uwarta
Hasinat, kuma take so ta isa dajin Baitul-Shazwas.


BABI NA SHA SHIDA

Lokacin da waɗannan masifaffun karnuka da gimbiya Husnat suka ruguntsume da
azababban yaƙi a tsakiyar sahara. Sai suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin
matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance.
Karnukan suka wanzu suna kai Husnat yakushi ya cizo cikin wani baƙin zafin nama da ya huce
tunanin bil'adama, ita kuwa ta wanzu tana kare hare-haren gami da zillewa cikin gwaninta da
ƙwarewar yaƙi.

Wohoho! Haƙiƙa duk wanda ya iya ya huta, komai hassadar mutum idan yaga yadda Husnat ke
kaucewa hare-haren karnukan tare da mayar da martani cikin baƙin zafin nama JURIYA DA
BAJINTA sai mutum ya yi tsammanin ko wata na'ura ce ke sarrafa ta.
Sai da suka shafe tsawon rabin sa'a suna kaiwa juna hare-hare cikin baƙin zafin nama,
babu alamun nasara ga kowanne ɓangare.
Al'amarin da ya fusata dukkan ɓangarorin biyu kenan kuma ya fusata su ainun.
Abin da ya fusata karnukan shine a iya tsawon wanzuwar su a dajin basu taɓa haɗuwa da
halitta mai matuƙar zafin nama da nacin tsakiya tamkar Husnat ba.
Ita kuwa abin da ya fusata ta shine lokacin da gudanar da ibadar Ubangiji ya yi gashi ta kasa
nasarar koda ƙwarzanar jikin ɗaya daga cikin karnukan,
tana cikin wannan hali ne wani tunani ya faɗo mata, tunanin kuwa shine haƙiƙa bakomai ne ya
sanya ta gaza samun nasara akan abokan gwanin ta ba sai saboda da ta shagala da neman
taimakon Ubangijin musulunci.
Koda ta zo nan a tunaninta sai kawai ta buɗe baki ta kwala kabbara da ƙarfi tare da ɗaga
takobinta ta kai sara, bisa sa'a sai KAIFIN TAKOBINTA ya ratsa wuyan ɗaya daga cikin
karnukan, kanshi ya yi fitar burgu jini ya yi tsartuwa gami da feshin, gangar jikin ta faɗi ƙasa
rikici! Kafin sauran karnukan su yi wani yunƙuri Husnat ta sanya takobinta ta datse masu wuya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login