Showing 6001 words to 9000 words out of 25373 words

Chapter 3 - KARSHEN ZALUNCI COMPLETE BOOK BY SUFI .pdf

kan dokin
sai ta ci gaba da mirginawa a ƙasa ya yin da ta isa daf da ramin ta ga inda za ta afka sai kawai
ta taƙarƙare ta kwarara wawan ihu take numfashinta ya ɗauke. Sa'adda taswirar ta zo dai-dai nan akan madubin tsafin sarauniya Abidat sai ta bushe da
dariyar farin ciki, ta mayar da madubin izuwa cikin aljihunta sannan ta sake miƙewa tsaye tsam!
Daga kan karagar mulkin ta ta durfafi wata ƙofa da za ta sada ta da gidan sarautar dakaru na
take mata baya. Nan take sauran jama'a suka miƙe daga wajen zamansu suka fice daga fadar suna masu
faɗar albarkacin bakunansu bisa wannan tsantsar zalunci da Abidat ta yiwa Sarki Urwat da
talakawansuhi, wasu har suna
rokon abin bautarsu da ya a kawo KARSHEN ZALUNCIn Sarauniya Abidat.
Lokacin da Suhaimat matar
Margayi Sarki Urwat ta faɗa izuwa cikin wannan rami mai zurfi cikin halin suma sai igiyar ruwa
ta ci gaba da tafiya da ita, sai da gari ya waye sannan igiyar ruwan ta kawo gaɓar tekun, kusa
da wani daji ma'abocin tarin bishiyu da duwatsu da ƙoramu, kuma ya tara kayayyakin ni'ima,
waɗansu irin kyawawan tsuntsaye na shawagi a sama suna fitar da sauti mai daɗin sauraro. Ya yin da hasken rana ya fito sosai sai Suhaimat ta farka daga dogon suman da ta yi tana
mai jan dogon gwauron numfashi, kuma ta buɗe idanuwanta ta miƙe zaune koda ta ga a inda
take hawayen baƙin ciki suka zubo daga idanuwanta.
A sannan ne ta ji yunwa da kishirwa sun addabeta kuma raunikan da ke jikinta
suna yi mata raɗaɗi da zugi, don haka sai ta miƙe tsaye da ƙyar ta shiga izuwa dajin domin ta
samu abin da za ta yi kalaci.
Daga wannan rana Suhaimat ta kasance a cikin dajin ba ta da abokan ɗebe mata kewa
face tsuntsaye, a duk sa'adda ta tuna maigidanta marigayi Sarki Urwat da jama'ar birnin su sai
ta fashe da kukan baƙin ciki.
Amma da zarar ta tuna cewa tana ɗauke da juna biyu sai ta cika da matuƙar farin ciki domin ta
san cewa za ta haifi abin da zai dawo mata da farin cikinta kuma ya kawo KARSHEN
ZALUNCIn Sarauniya Abidat Sa'adda Suhaimat ta fahimci cewa juna biyunta ya cika wata tara.
A koda yaushe naƙuda za ta iya kamata ta haife abin da ke cikinta, sai ta yanke shawarar ta ci
gaba da tafiya domin ta samu wani birni a gaba da za ta haife abinda take ɗauke da shi.

Sai da ta shafe tsawon kwanaki huɗu tana tafiya a ranar kwana na biyar ne lokacin da rana ta
take ta yi tsananin zafi Suhaimat ta iso wani kasaitaccen birni tun da ta shiga birnin ta kama
kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni a iya tsawon rayuwarta bata taɓa
ganin birnin da ya ƙawatu kamarshi ba, tana mai tambayar kanta a cikin ranta tana cewa shin
wannan wane birni ne na shigo? Kuma a wace nahiyar nake.
Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenan, kawai ta ci gaba da tafiya a cikin birnin,
tana cikin tafiya ne ta zo giftawa ta cikin kasuwa sai ta ji waɗansu dattawa guda biyu suna hira a
tsakanin su a inda ɗayan ya dubi ɗan uwanshi ya ce, "Shin wai kuwa ka ji labarin abin da ya
faru da Sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf da jama'ashi na kisan wulakancin da Sarauniya
Abidat ta yi masu."
Ɗayan ya ce, "Kwarai kuwa na samu labari kuma na jinjina al'amarin matuƙa, fatana shi ne a
samu wani GWARZON ƘARNI da zai kawo maka KARSHEN ZALUNCIN wannan sarauniya
tamu."
Sa'adda Suhaimat ta ji abin da dattawan ke tattaunawa a kai sai zuciyarta ta kama tafarfasa
tamkar za ta ƙone ta ji ta tsani sarauniya Abidat fiye da komai a rayuwarta.
Kuma a sannanne ta fahimci wannan birni da ta shigo shi ne birnin Sin tana tana cikin wannan
hali wani tunani ya faɗo mata, tunanin kuwa shi ne ya zama wajibi ki fice daga wannan birnin
matsawar kina bukatar ki haife abin da ke cikinki, domin da dazarar Abidat ta ganki ba za ta bar
ki a raye ba. Koda Suhaimat ta zo nan a tunaninta sai kawai ta ci gaba da tafiya da sauri domin ta fice
daga birnin baki ɗaya.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya dakaru Sarauniya Abidat ke farautar wannan mata wato
Suhaimat matar marigayi Sarki Urwat na birnin Nurul-Kusuf.

SHIN SUHAIMAT DA JARIRIYARTA NA TSIRA DAGA SHARRIN DAKARUN SARAUNIYA
ABIDAT!
WACE IRIN ƊAUKAKA
JARIRIYAR SUHAIMAT ZA TA SAMU A DUNIYA?
SHIN INA LABARIN ƊAN DATTIJO SAFWAN WANDA
SARAUNIYA ABIDAT TA BAYAR DA RENONSHI GA BAIWA SUNAILA?
WANE IRIN AZABABBEN YAƘI ZA A YI TSAKANIN DAKARUN SARAUNIYA ABIDAT DA
WANNAN ZAKANYA?

Mu hadu a KARSHEN ZALUNCI 2 na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.



BABI NA BIYAR

Sa'adda aka ci gaba da kallon-kallon tsakanin dakarun ke biye da Suhaimat matar
marigayi sarki Urwat da wannan zakanya.
Sai da aka shafe tsawon daƙiƙa talatin a na wannan kallo-kallo daga can sai dakarun suka zare
makamansu suka zaburi dawakan su izuwa inda zakanyar take suna aihu da kururuwa mai
firgitarwa.

Koda ganin hakan sai zakanyar ta sake dako wawan tsalle a karo na biyu ta dira a tsakiyar
dakarun, tana gurnani mai ban tsoro.
Nan take aka ruguntsume da azababben yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro gami da ban
al'ajabi.
Wohoho! Tabbas mai ƙarfi sai Allan ya isa ana fara wannan artabu ne wani abin al'ajabi
ya fara gudana, domin halitta guda ɗaya jal ta addabi mutum dubu biyu ta zame masu alaƙaƙai
sun rasa yadda za su yi da ita.
A duk sa'adda dakarun suka kaiwa zakanyar hari sai ka ga ta wurƙita haɗe da zamewa ta
zillewa saran kafin badakaren ya sake ɗaga takobinshi, zakanyar ta dako tsalle sama ta sanya
farantata ta tsire mashi idanu ruwan cikin ya tsiyaye take ya sulale ƙasa daga kan dokinshi yana
mai kurma wawan ihu a wasu lokutan idan ta bangaji badakare a kirjinta take badakare da
dokinshi za su make 'yan uwansa dakaru fiye da goma sun zube a ƙasa matattu, kai wasu
lokutan ma idan ta daki badakare a wuya sai ka ji ya karye ya yi ƙara ruƙus!! Ƙas! Ya faɗi
matacce ko shurawa bai yi ba.
Haƙiƙa waɗannan dakaru suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa ganin irin shi ba, domin
kafin cikar rabin sa'a zakanyar ta kashe fiye da rabin su.
Babban abin da ya dugunzuma hankalin dakarun kuma ya fusata su shine. Gashi dai ƙiri-ƙiri
suna saran zakanyar da makaman su amma sun kasa koda kwarzanar jikinta, nan fa dakarun
suka fusata ainun suka zage damtse suna kaiwa zakanyar miyagun hare- hare.
Nan fa karafniyar ƙarafa da ihun mazaje, haniniyar dawakai haɗe da gurnanin zakanyar ya cika
dajin baki ɗaya. Ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin turmutsutsu,
kofatunsu na kartar kasa.
Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce idan wuya ta kai wuya sai ka ga
ZARATAN MAYAƘA suna neman cika wandunansu da iska domin TSIRA DA RAYUKAnsu.
Hakanne kuwa ya faru ga sauran 'yan tsirarun dakarun domin koda suka ga cewa a kowanne
lokaci za su iya baƙuntar barzahu sai suka cika wandunansu da iska da nufin tserewa.
Amma sai zakanyar ta dinga ƙure masu gudu tana turmushe su suna faɗuwa ƙasa matattu,
kafin wani lokaci ta zubar da gawarwakinsu a ƙasa.
Koda samun wannan nasara sai zakanyar ta yi girgiza sannan durfafi inda Suhaimat ke
kwance tare da jaririyar ta, koda ta ga halin da Suhaimat ke ciki sai ta ruga izuwa bakin wata
ƙorama ta guntso ruwa a baki sannan ta dawo inda take ta fesa mata ruwan a kan fuskarta.
Faruwar hakan ke da wuya sai Suhaimat ta ja dogon gwauron numfashi gami da ajiyar zuciya,
idanuwanta suka buɗe tarwai, kuma ta miƙe zaune ya yin da ta yi arba da wannan zakanya sai
ta razana ta ja da baya tana mai ɗaukar jaririyarta ta ƙanƙame ta a kirji.
Koda ganin halin da Suhaimat ta shiga sai zakanyar ta juya ta ruga izuwa cikin wannan
kogon dutse da ke cikin dajin.
Cikin matuƙar farin ciki Suhaimat ta miƙe tsaye ta matsa izuwa inda wannan ƙorama take ta
yiwa jaririyarta wanka itama ta tsaftace ƙazantar dake jikinta, sannan ta dawo izuwa ƙarƙashin
wata bishiya, ta zauna ta shiga shayar da jaririyarta tare da shafa gashin kanta zuciyarta cike da
matuƙar farin ciki. Kuma ta shiga tambayar kanta a cikin ranta tana cewa shin wane ne ya kashe waɗancan
dakaru, ko kuwa wannan zakanyar ce?.

Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenan, a cikin wannan hali ne zakanyar ta dawo
izuwa gare ta, bakinta riƙe da waɗansu ƙunshin ciyayi ta ajiye a gaban ta a wannan karon bisa
mamaki sai Suhaimat ta ji ko kaɗan ba ta tsora ta da ganin zakanyar ba.
Ba tare da fargabar komai ba Suhaimat ta ɗauki ta shiga warware ƙunshin, ai kuwa sai ta
ga ashe nau'ikan kayan marmari ne a ciki, dangin su ayaba da inibi kawai ta shiga ci har sai da
ta ƙoshi sannan ta fasa kwakwa ta shanye ruwanta zakanyar na tsaye a gefen ta tamkar mai
jiran umarni, a sannan ne ta lura cewa a jikin zakanyar akwai alamun jini take ta fahimci cewa ita ce ta
hallaka waɗannan dakaru domin ta ceci rayuwarta da jaririyarta.


BABI NA SHIDA

Dukkanin abin da ya wakana tsakanin Suhaimat, zakanya da dakarun sarauniya Abidat.
Abidat ta gani a cikin madubin tsafin ta tun daga farko har ƙarshe. Koda ganin wannan
al'amari sai takaici da baƙin ciki suka turnuƙe ta ta ji tamkar ta kurma wawan ihu.
Ba komai ne ya sanya ta wannan baƙin ciki ba, sai domin ta tabbatar da cewa a halin yanzu
Suhaimat da jaririyarta sun tsira daga sharrinta.
Babban abin da ya dugunzuma hankalin ta kuma ya jefata cikin damuwa ainun shi ne wani
al'amari da ta gani a cikin madubin tsafin ta.
Ta gano cewar wannan jaririya da Suhaimat ta haifa ita ce za ta kawo KARSHEN
ZALUNCIn ta daga doron ƙasa. Asalin dajin da Suhaimat ta haihu a ciki ya kasance mallakin
wannan zakanya mai tattare da abubuwan al'ajabi ana kiranta da suna Juraima.
Binciken bokaye da MATSAFAN DUNIYA ya tabbatar da cewa dajin Baitul-Shazwas na ɗauke
da wata takobi ta musamman mallakin sarkin bokayen aljanu na duniya Sababul-Ukub, babu
wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai mallaki takobin face ya zamewa duniya ANNOBA
DARI. MANYAN SARAKAI haɗe da matsafa
da JARUMAN DUNIYA sun rasa rayukansu bisa muradin mallakar takobin, domin zakanya
Juraima ba ta barin duk wanda ya raɓi dajin a raye. Bisa dole bokayen suka janye ƙudurinsu na
shiga dajin Baitul Shazwas domin mallakar takobin Saiful-Imfal.
Abinda binciken ya ƙara tabbatar masu shi ne babu wani mahaluki da zai mallaki takobin Saiful
Imfal da zakanya Juraima face wata jariya da za a haifa a dajin na Baitul Shazwas, sai dai ba a
bayyana masu ga nahiyar da za a haifi jaririyar ba.
kuma zakanya juraima na ɗauke rabin sirrikan tsafin sarkin bokaye a jikinta, takobin Saiful-imfal
na ɗauke da sauran.
Tsakanin Sarauniya Abidat da zakanya Juraima akwai gaba mai tsanani tun iyaye da
kakanni, domin mahaifinta da kakanta sun rasa rayukansu ne ta hanyar mallakar
takobin Saiful Imfal, kuma lokacin da mahaifinta yana raye ya gargaɗe ta a kan kar ta kuskura
ta ce za ta shiga dajin Baitul-Shazwas domin ɗaukar fansa.
Nan fa Sarauniya Abidat ta ƙara cika da matuƙar baƙin ciki tana mai tambayar kanta a cikin
ranta tana cewa.

"Hakika na tafka babban kuskure da har na bari Suhaimat ta shiga dajin Baitul-Shazwas yanzu
gashi ta haife abin da ke cikinta yanzu shi kenan ba ni da ikon hallaka Suhaimat da jaririyarta
har sai ranar da ta fito daga dajin Baitul Shazwas."
Daga wannan rana Sarauniya Abidat ta kasance dare da rana bata aiki face gudanar da
bincike a halarar tsafinta, domin ta gano lokacin da Suhaimat za ta fito daga dajin Baitul
Shazwas.
Bayan Suhaimat ta kammala kintsa cikinta da waɗannan kayan marmari sai Zakanya
Juraima ta juya, ta nufi kofar wannan kogon dutse tana mai yiwa Suhaimat nuni da ta biyo
bayanta.
Ba tare da gardamar komai ba Suhaimat ta miƙe tsaye ta bi bayanta tana rungume da
jaririyarta a kirji, da shigarsu cikin kogon dutsen sai ke da wuya sai Suhaimat ta ga kogon ya
gauraye da wani irin haske na ban al'ajabi, sannan yana cike da dukkanin kayan more rayuwa
da ɗan adam zai bukata, kai wani abin ma Suhaimat ba ta taɓa gani ko jin sunan shi ba.
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaure mata kai kenan kuma ya ba ta mamaki ta kama kalle-kalle da
dube-dube.
Ba tare da ta jira wani umarni daga Zakanya Juraima ba sai kawai ta je ta kwantar da
jaririyarta bisa wata shimfiɗa ta lulluɓe ta da mayafi sannan itama ta kwanta domin ta rintsa
amma sai hakan ya gagara, ba komai ne ya haddasa hakan ba, sai domin raunukan da ke
jikinta na yi mata zugi da raɗaɗi kuma inda wannan badakare ya harɓe ta da kibiya yana yi
mata ciwo.
Sai da zakanya Juraima ta kawo mata wani ganyen bishiya ta murza ta sanya a raunukan,
sannan ta kwanta barci ya ɗauke ta.
Wannan shi ne abin da ya faru da Suhaimat matar marigayi sarki Urwat na birnin
Nurul-Kusuf a lokacin da ta tsira daga sharrin sarauniya Abidat ta birnin Sin.


BABI NA BAKWAI

Al'amarin baiwa Sunaila kuwa tun sa'adda sarauniya Abidat ta bata renon jaririn dattijon
Safwan, sai ya zamana cewa dare da rana tana bawa jaririn kulawa, kuma suka shaƙu da juna
ainun ya yi wayo sai Sunaila ta sanya masa suna Himlas, ma'ana ma'abocin hikima da
abubuwan al'ajabi, domin tun yana da shekaru huɗu ta fahimci cewa yana tattare da kaifin
basira da jarumtaka.
Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba sai gashi Himlas ya girma ya zama
cikakken saurayi.
Nan fa ya zamana cewa ya zama zarra a tsakanin sauran 'yan uwanshi bayi, a wasu
lokutan idan suna ba wa juna horon yaƙi suka yi masa rubdugu amma sai ka ga ya tarwatsa su
ta karfin tsiya.
Wata rana Himlas ya dawo daga farauta yana zaune tare da baiwa Sunaila a cikin ɗaki sai
ya lura cewa tana cikin damuwa.
Don haka sai ya dube ta ya ce "Ya Ummina shin mene ne dalilin wannan damuwa ta ki?"
Koda jin wannan tambaya sai baiwa Sunaila ta yi murmushi a gare shi, mai tattare da takaici
sannan ta sanya hannayen ta biyu ta dafa kafaɗunshi ta dube shi cikin alamun tsananin
damuwa ta ce.

"Ya ɗana abin alfaharina ki yi sani cewa ba komai ne ya sanya ni a cikin wannan damuwa ba sai
domin na san cewa duk daren daɗewa ɓoyayyen sirrin da na daɗe ina ɓoye maka zai fito fili
ƙarara."
Koda jin wannan batu sai idanun Himlas suka zazzaro cikin tsoro ya kama sa cikin alamun
rashin fahimta ya dubi Sunaila ya ce. "Ya Ummina ban fahimci abin da kike nufi ba, shin wane
sirri ne ki ke son bayyana mani."
Sunaila tayi ajiyar zuciya sannan ta kawo gwauron numfashi, ta ajiye kana ta yi gyaran murya ta
ce, "ya ɗana ka yi sani cewa a yau ne zan bayyana maka sirrin da na daɗe ina ɓoye maka, ya
farin ciki na ka yi sani cewa kamar yadda kake tsammani cewa ni ce mahaifiyarka to ba ni ce na
haife ka ba." Nan take Sunaila ta kwahse labarin kaf abin da ya faru tsakanin dattijo Safwan da
Sarauniya Abidat da irin mugun kisan gillar da ta yiwa mahaifinsa tun daga farko har ƙarshe ta
zayyanewa bawa Himlas.
Sa'adda baiwa Sunaila ta zo dai-dai nan a labarinta sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya
shima Himlas bai san sa'adda ya fashe da kukan ba, yana mai rungume ta yana mai cewa "ba
zan taɓa canja ki ba har abada ke ce Ummina."
Inda ace mutum yana wannan waje lokacin da wannan al'amari ke faruwa dole ne ya kamu da
tsananin tausayin Sunaila da bawa Himlas.
Sai da suka ɗauki wani lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani Sunaila ta janye jikinta
daga na Himlas ta dube shi a lokacin da hawaye ke ci gaba da kwaranya daga idanunta ta ce.
"Ya ɗana ka yi sani cewa ba komai ne ya sanya na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login