Showing 15001 words to 18000 words out of 18096 words

Chapter 6 - FATAUCIN BAYI Book Complete Book Written by Mansur Usman Sufi .pdf

05 Aug 2025

553

wajen,
jim kaɗan da fara aiwatar da hakan sai ga wata makeken murfi ya bayyana a wajen da aka yi
shi da zallar baƙin ƙarfe.
Cikin baƙin zafin nama Mazabir ya sanya hannayenshi biyu ya buɗe murfin, sai ga
wata matattakala da zata shiga izuwa ƙarƙashin ƙasa, nan fa su Najwas suka cika da matuƙar
mamaki maral-musaltuwa.
Mazabir ya juya ya dubi Najwas da mutum dubu uku daga cikin yaranshi ya ce "duka za ku ajiye
dawakan ku anan mu shiga izuwa wannan ƙofa, sannan ya dubi sauran yaran ya ce "Ku kuma
ku tsaya anan ku jira har mu fito daga wannan ƙofa ina jan kunnenku da ku kiyayi saɓawa
umarni na. Gama faɗin hakan ke da wuya sai Mazabir ya shiga cikin wannan kofa yana mai taka
matattakalar. Najwas, kilimat, 'yan matan uku da dakaru suka mara mashi baya, suna masu
kunna kai cikin Kofar, tafiyar daƙiƙa latalin kacal aka yi aka iso ƙarshen matattakalar. Nan take
aka yi arba da wata ƙatuwar ƙofa Mazabir ya matsa daf da ita ya ƙwanƙwasa sau biyu. Daga can sai wata 'yar siririyar taga ta buɗe a saman ƙofar wani badakare mai turɓunanniyar
fuska ya leƙo da kanshi ya buɗi baki da nufin ya ce wani abu sai Mazabir ya cire hular ƙarfen
dake kanshi,
Koda badakaren ya yi arba da fuskar Mazabir sai ya sakar mashi wani ƙeƙashasshen murmushi
da ya ƙara wa fuskarshi muni cikin wata irin kakkausar murya ya ce mai kama da haushi kare ya
ce "barka da zuwa ya shugabana".
Badakaren ya mayar da kanshi ciki, jim kaɗan sai aka ji ƙarar zare sakatun kofar, zuwa can
sai ta buɗe.
Mazabir, Najwas, kilimat, yan mata uku wato Shamirat, Luwaisat, Zulfirat da dakaru dubu uku
suka kunna kai izuwa ciki aka cigaba da tafiya, duk inda suka huce sai kaga dakaru na zube
kasa suna kwasar gaisuwa ga Mazabir.
Nan fa su Najwas suka cika da matuƙar mamaki da al'ajabi, bisa ganin yadda Mazabir
ya tsara wannan hanya ta cikin ƙarƙashin ƙasa domin kawai yana shirya hanyar da zai bi wajen
ɗaukar fansa akan sarki Uhaisu.
Haka dai aka cigaba da wannan tafiya har ya zamana an kawo ƙarshen wannan hanya an tarar
da wata ƙofa.
Cikin hanzari waɗansu ZARATAN MAYAƘA suka buɗe ƙofar aka fita izuwa waje.
Ya yin da aka fito nan take aka tsinci kai a cikin birnin Darul-kashmal, kuma a kayi arba
da kurkukun Mautul-shammar.
Mazabir ya yi gyaran murya umh! Sannan ya dubi Najwas ya ce "yanzu ga shi mun iso
kurkukun Mautul-shammar, ya zama wajibi mu zage damtse wajen yaƙar dakarun kurkukun, mu
ceci rayuwar al'ummar su Nabihat, mu koma izuwa sansanin mu domin mu sake sabon shirin
yaƙi a gobe.

Koda jin wannan batu daga bakin Mazabir sai Najwas ya gyaɗa kai, sannan ya zare wata
sharbebiyar takobi daga cikin kuben ta ya durfafi ƙofar kurkukun. Mafarauci Najwas, Kilimat,
Nabihat, Shamirat, Luwaisat, Zulfirat da dakaru dubu uku suka yi koyi da shi suka zare
makamansu suka rufa mashi baya. Lokacin da ya zamana saura kamar taku goma tsakanin su da kurkukun, su Najwas suka
yi arba da dakarun dake tsaron kurkukun sai suka firgice ainun, su dai waɗannan dakarun sun
kasance zabga-zabga tamkar samudawan farko, suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar
yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, hannayensu ɗauke da waɗansu miyagun makamai, suna
ta kai komo tamkar za su ci babu.
Mazabir ya ɗaga takobinshi sama yana mai yiwa dakarunshi wata inkiya, kawai sai
dakarun suka zaro kibiya suka saka a cikin bakansu suka ja suka ɗame sannan suka harba su
izuwa dakarun dake saman ganuwar ƙofar kurkukun.
Nan take suka hallaka fiye da rabin dakarun, kuma fitilun dake wajen suka ɗauke, wajen ya yi
duhu dunɗum!
Ta yadda mutum ba zai iya hango wanda ke nesa da shi ba, a dai-dai wannan lokaci ne su
Najwas suka ƙarasa ƙofar kurkukun suka hallaka dakarun ta hanyar yi masu kisan sunƙuru,
suka murɗe masu wuya ba tare da dakarun dake cikin kurkukun sun ji ihun su ko wani sautin
ƙara ba. Kafin cikar rabin sa'a sun hallaka dakarun sun ɓalle ƙofar kurkukun ta ƙarfin tsiya suka
kunna kai ciki.
Ya yin da dakarun kurkukun suka yi arba da su Najwas sai suka zare makaman su suna ihu da
kururuwa mai firgitarwa suka rugo izuwa kan su. Ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi
mai matuƙar muni da ban tsoro.
Ɓangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama
JUTIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance.
Ana fara wannan arbu ne dakarun suka fahimci cewa tabbas yau sun haɗu da gamon su, domin
su Najwas sun wanzu suna aika rayukansu barzahu babu sassauci. Duk inda Mazabir, Kilimat,
Najwas, Nabihat, Zulfirat, Shamirat da Luwaisat suka sanya a gaba sai dai ka ga dakarun na
zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar auduga. Nan fa sassan jikkunan bil'adama suka dunga shawagi a sararin samaniya suna zubowa
ƙasa, jini yana kwarara, feshi gami da tsartuwa tamkar an balle ƙorama.
Wohoho! Haƙiƙa MANYAN JARUMAI sune waɗanda suka saba yin KARO DA MAZA
komai tsakanin yawan su, kuma su ne waɗanda TSANANI DA UKUBA basa saka su gudu a
FAGEN GUMURZU sai dai su yi MUTUWAR JARUMTA.
Sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ana wannan ɗauki ba daɗi tsakanin su Mazabir da dakarun
kurkukun.
Ya zamana cewa su Najwas sun kashe kaso bakwai bisa goma na dakarun, amma su dakarun
ba su samu damar kashe ɗaya daga cikin su Nabihat ba sai raunika da suka samu.
Duk da cewar dakarun sun firgita da irin mugun kisan da su Nabihat ke yi masu amma sai
suka cigaba da kai sara da suka saboda naci da taurin kan tsiya.
Koda shugaban 'yan fashi Mazabir ya ga cewa tabbas idan aka cigaba da wannan yaƙi a haka
wankin hula zai kai su dare, sai kawai suka ci-gaba da yaƙar dakarun suna masu ƙutsa kai
izuwa ɓangare BAUTAR MUTUWA
in da aka ajiye jama'ar su Nabihat.

A wannan lokaci gaba ɗaya fursunonin kurkukun suna sharar barci ba su san abin da
ke faruwa ba.
Koda suka jiyo kurkukun ya hautsine sai su ka dunga fitowa daga cikin ɗakunan su.
Yayin da suka ga cewa su jaruma Nabihat ne ke yaƙar dakaru, sai suka shiga make dakarun ta
hanyar amfani da itace da gudumun da suke amfani da su wajen farfasa duwatsu domin dai
taimakon su Nabihat.
Da wannan dama su Mazabir suka samu nasarar fito da jama'ar Nabihat.
Lokacin da aka zo fitowa sai dakarun Mazabir yi kuri suka saka su a tsakiya su kayi masu
ƙawanya domin kada wani abu ya taɓa lafiyar su.
Haka dai aka cigaba da wannan yaƙi fursunonin sun taimaki su Nabihat har aka samu isa inda
wannan ƙofa, take suka shige izuwa cikin wannan ƙofa tekun mai ɗauke da siririyar hanya ta
cikin karkashin kasa.
Lokacin da aka fito izuwa inda aka bar sauran dakaru da dawakai, sai Mazabir ya yi
umarni aka ɗora jama'ar su Nabihat akan dawakan dakaru aka sake nausawa izuwa cikin daji
cikin matuƙar farin ciki maras musaltuwa.
Kashe gari tun da duku-dukun safiya su jarumi Najwas suka kammala shiri tsaf
A wannan karon dakaru dubu huɗu aka ɗauka sannan aka ƙara samu waɗansu gwarazan 'yan
mata mutum shida daga cikin jama'ar su Nabihat da aka ceto suma suka shiga sahun MAYAƘA
Wato jaruma AMATULLAH, KHADIJAH, SAFNA, jaruma FATIMAH, Basadaukiya TEEMERH, da
KHADIJAH bintu Yahya, Jaruma Nabihat tayi matuƙar mamakin yadda akayi sunayen yan
uwannata ya canja zuwa masu daɗi haka.
Amma sai ɗaya daga cikin su wacce ta kasance kyakyawa ta gaban kwatance mai suna
AMATULLAH ta bayyana mata cewa
Sunayen nasu sun sauya ne sakamakon sun karɓi addinin Musulunci a hannun wani fursuna da
ake yiwa laƙabi da sheik ABDULLAH IBN ZAID.
Bisa wannan dalili ne ya sanya sunayen na su suka canja.
Tun a daren jiya jaruma Nabihat da gaba ɗaya fursunonin jama'arta har Mazabir da
dakarunshi suka ƙarbi addinin Musulunci suka bayar da gaskiya da Ubangijin talikai.
A wannan lokaci inda ace mutum zai ga irin shigar da jaruma Nabihat da sauran 'yan
matan su kayi dole abin ya burge shi gwanin ban sha'awa.
Shigar fararen tufafi na sulken ƙarfe su kayi tun daga ƙasa har sama, sun rufe fusakunsu da
koren rawani, idanuwansu kaɗai ake gani, hatta dawakan da suka hau ingarmu ne farare sol! Ita
kam yarinya Lazimat shiga tayi cikin ayarin ta na rataye da kwari da bakanta.
Bayan an kammala yin kalaci sai aka ɗauki hanya aka durfafi zuwa birnin Darul-kashmal
qka wanzu ana ratsa duhuwar bishiyu da kwazazzabai haɗe da sarƙaƙiya a bisa dawakai cikin
matsanancin gudu na keta sa'a,
tafiyar sa'a ɗaya kacal aka yi aka iso ƙofar birnin.
Tamkar sarki Uhaisu jira yake su iso tuni ya gama shirin yaƙi tsaf.
Koda tsayuwar su jaruma Nabihat a wajen sai aka ga Ƙofar birnin ta buɗe sai ga dakaru
na tuttuɗowa wasu a bisa dawakai, giwaye, raƙuma wasu a ƙafa.
Tsamanin yawan su ya huce misali, duk inda mutum ya kalla makaman yaƙinsu ne birjik.
Bayan dakarun sun yi sahu-sahu a filin daga.
Sai aka hango sarki Uhaisu ya saki linzamin dokinshi ya durfafo inda suke, yana sanye cikin
gagarumar shigar yaƙi ta baƙin sulke mai matuƙar kwarjini da ban tsoro tamkar wani ifritu.

A gefen hannunshi na hagu kuwa shugaba Yesiran ne shirye cikin gagarumar shigar yaƙi,
a dama kuwa yarima Shaiban ne cikin shigar yaƙi.
Lokacin da ya zamana cewa tazarar da ke tsakanin su bata huce taku goma sha biyu ba
sai kowa ya ja linzamin dokinshi ya tsaya cak! Aka shiga yin kallon-kallo tsakanin ɓangarorin
biyu,
Sa'adda shugaba Yesiran ya yi arba da yarinya Lazimat sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar
zata ƙone ya na mai duban dungulmi hannunshi ɗaya da ta sake mashi .
Shi kuwa yarima Shaiban ya shagaltu da kallon kyakkyawar surar jaruma Nabihat,
tsakanin ƙaunar ta na ƙara ruruwa a zuciyarshi, har sai da Nabihat ta galla mashi harara sannan
ya kawar da kanshi.
Sarki Uhaisu da shugaban 'yan fashi Mazabir da Najwas haɗe da kilimat kuwa, wani irin
kallo su ke wa junan su mai cike da matuƙar ƙiyayyar da mugun tanadi.
Sarki Uhaisu ya ce a cikin zuciyarshi "ya aka yi sadauki Mazabir ya haɗa kai da abokan gaba
ta? Shin dama har yanzu mazabir na raye bai mutu ba?
Lallai babu tantama shi ne ya jagoranci rundunar mayaƙa a daren jiya suka ce ci rayuwar
jama'ar su Nabihat
Sa'adda Sarki Uhaisu ya zo nan a tunanin shi sai takaici gami da baƙin ciki suka turnuƙe
zuciyarshi.
Daga can ne sai sarki Uhaisu ya zare takobinshi ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu
sannan ya ruga izuwa kan su Najwas.
Koda ganin hakan sai Najwas da Mazabir suka sakarwa dawakansu linzami suka yunƙura kan
shi. Shugaba Yesiran ya durfafi yarinya Lazimat, ana haɗuwa sai aka ruguntsume da
azababban yaƙi suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JUTIYA
DA BAJINTA. Sa'adda dakarun ɓangarorin biyu suka ga cewa shuwagabannin su sun kacame da yaƙi,
sai kowanne su ya yi kukan kura ya afkawa abokin gabar shi aka yamutse da masifaffan yaƙi.
Koda ganin hakan sai jaruma AMATULLAH, KHADIJAH bintu Muhammad, SAFNA,
jaruma FATIMAH bintu Yahya da Basadaukiya TEEMERH suka ƙwala kabbara da ƙarfi suka
zare takubbansu suka kutsa izuwa cikin dakarun kafirai aka cigaba da artabu.
Wohoho! Haƙiƙa wannan rana ƙasa ta jiƙu da jinin bil'adam, kaico! Tabbas yaƙi abin
tashin hankali da ban tsoro wanda bai san shi ba shi ne yake fatan zuwan shi
Duk inda su jaruma SAFNA suka sa a gaba sai dai ka ga dakarun arna na zubewa ƙasa
matattu.
Wani sadauki mai ƙarfi na Allah ya isa ya kaiwa jaruma AMATULLAH wani wawan sara da
takobin shi, cikin baƙin zafin nama AMATULLAH ta sunkuiya takobin sadaukin ta sari iska,
Kafin ya sake dawo da martani AMATULLAH ta kafta mashi wani sara a wuya take ta tsinke
jijiyar wuyanshi ya faɗi ƙasa yana shure-shuren mutuwa.
Jaruma FATIMAH kuwa ta zamto tamkar shaiɗaniya a tsakanin mayaƙan sarki Uhaisu,
Khadijat kuwa da ƙarfin damtsen ta take ragargazar dakarun babu sassauci.
A ɓangaren yarinya Lazimat da shugaba Yesiran kuwa sun wanzu suna kaiwa juna
miyagun hare-hare cikin JURIYA DA BAJINTA gami da baƙin zafin nama tamkar za su cinye
junan su.
A ɓangaren manyan GWARAZAN SADAUKAI, sarki Uhaisu, Mafarauci Najwas da
shugaban 'yan fashi Mazabir kuwa. Tuni labarin ya sha banbam, domin kuwa sai da suka lalata

gaba ɗaya makaman yaƙinsu suka yi jifa da su suka dira ƙasa daga kan dawakansu bisa turba
suka shiga kaiwa juna naushi da bugu cikin juriya da nacin tsiya.
Nan fa ya zamana cewa idan Najwas da Mazabir suka nushi Sarki Uhaisu sai su ji
tamakar buhun hatsi suka daka domin ko gezau ba ya yi sai ƙura ce kawai ke tashi.
Idan kuwa Sarki Uhaisu ne ya naushi ɗaya daga cikin su sai kaga ya yi sama tamkar an janye
shi da ƙugiya sannan ya faɗo kasa tim!
Nan fa yazamana cewa Uhaisu ya tara masu jini kuma ba sa iya mayar da martani sai
dai ƙoƙarin kare kai, sa'adda su Najwas suka fahimci halin da suke ciki sai kawai su shiga
neman Ubangijin musulunci
a cikin zukatansu, ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai suka fara samun nasara akan Uhaisu
ya zamana cewa suna haɗa ƙarfin su waje guda su gabza mashi naushi. Kafin cikar rabin sa'a
sunyi mashi jina-jina ya zamana cewa ya faɗi ƙasa daƙyar yake numfashi yana kakarin
mutuwa. Kawai sai Mazabir ya yi wuf ya zare wata sharɓeɓiyar takobi a jikin wani badakare ya
datse wuyan Sarki Uhaisu.
Kaico! Inda a ce mutum ya na wannan waje lokacin da Sarki Uhaisu ya yi irin wannan mutuwar
ta wulakanci dole ne ya yi farin ciki ya yiwa Allah godiya bisa ganin mutuwar AZZALUMI.
A dai-dai lokacin ne yarinya Lazimat ta samu nasarar hallaka shugaba Yesiran ta hanyar
soka mashi kibiya a kan ƙahon zuciyarshi ya yi mutuwar banza.
Sa'adda dakarun marigayi Uhaisu suka yi arba da gawar jagoran su sai suka zubar da
makamansu suka miƙa wuya.
A wannan rana aka shiga izuwa birnin Darul-kashmal aka musuluntar da gaba ɗaya
jama'ar birnin, aka fito da dukkan fursunonin dake kurkukun, aka karya gumaka da ababan
bauta.
Tsawon kwani uku aka shafe kowa ya yi jinyar raunin dake jikinshi. Sannan aka ɗora yarima
Shaiban abisa karagar mulki, bayan an ɗaura auren shi da da Jaruma Nabihat da Jaruma
Zulfirat.
Najwas kuwa ya zamo angon 'yan mata uku wato
Khadijah, Luwaisat da Shamirat, kuma yazamo waziri ga yarima Shaiban.
Mafarauci Najwas kuwa ya zamo shugaban majalisar dokokin birnin Darul-kashmal.
Sheikh ABDULLAH IBN zayyad yazamo jagoran harkar addinin musulunci da amsa
fatawa na birnin.
Yarinya Lazimat kuwa ta zamo wacce zata gaji sarkin yaƙin birnin wato shugaba Yesiran.
Tun daga wannan rana aka kawo ƙarshen FATAUCIN BAYI a nahiyar baki ɗaya addinin
Musulunci ya mamaye ko ina, sarakunan dake nahiyar da kansu suke zuwa su miƙa wuya su
karɓi addinin Musulunci, saboda mulkin adalci da yarima Shaiban ke gudanarwa saboda
HASKEN MUSULMI.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login