Showing 9001 words to 12000 words out of 18096 words

Chapter 4 - FATAUCIN BAYI Book Complete Book Written by Mansur Usman Sufi .pdf

05 Aug 2025

557

ta miƙe tsaye da nufin ta mayar da martani amma sai ya damƙe ta da
hannunshi ɗaya ya matse ta ya shiga yi mata lugudan naushi a fuska nan take fuskarta ta
kumbura, tayi kaca-kaca da jini da majina kuma numfashinta na fita samas-sama.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai ya ji ta ƙwalla ƙara ta suɓuce daga hannunshi sannan ta
gabza mashi naushi a idonshi ɗaya.
Take ya fashe wani koren ruwa gami da jini ya dunga kwaranya da ga ciki, nan fa shugaban ya
dunga ihu da kururuwar neman taimako, kafin ya sake wani yunƙuri matar mafaraucin ta cire
wata 'yar karamar wuƙa ta caka mashi a maƙogaronshi, nan take ya faɗi kasa rikica! Yana
shure-shuren mutuwa kafin wani lokaci ya sheƙa barzahu. A dai-dai wannan lokaci ne mai gidanta ya rugo izuwa wajen, koda ya yi arba da
gawarwakin birran sai kawai ya rungume matarshi cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa bisa
ganin cewa tana raye bata mutu ba.

Sai daga can ne ya janye jikinshi daga na ta, a lokacinne ya lura cewa ta samu manyan
raunika, sai kawai ya ɗauke ta ya shiga da ita izuwa cikin gida cikin matuƙar tashin hankali.
Lokacin da ya isa sai ya shimfiɗe ta a bisa wani gadon na musamman dake cikin turakarshi ya
shiga bata taimakon gaggawa,to ta hanyar sanya mata magani a raunikan ta, inda jini ya taru ya
gasa mata da ruwan ɗumi.
Har a wannan lokaci yarinya Lazimat ba ta farfaɗo ba tana kwance tana sharar barci
sakamakon maganin barci da aka bata.
Ana cikin wannan hali ne sai kawai ya ga uwargidanta shi ta buɗe idanuwanta tana mai yi masa
wani murmushin karfin hali, cikin tattausan murya ta buɗi baki ta ce "ya uban 'ya'yana shin
mene ne ya sanya zaka saka kan ka a damuwa bayan cewa mun samu abin da zai share mana
hawaye, kuma gani a raye ban mutu ba? Mai gidan nata ya dube ta cikin tsantsar tausayi da so da ƙauna ya ce "zancen ki haƙƙun ya
abar kaunata, amma ina so kiyi sani cewa tsananin kaunar da nake yi miki ne ta tayar min da
hankali.
Koda jin wannan batu sai su duka biyun suka bushe da yar karamar dariyar murna suna yiwa
junan su wani irin kallo mai tattare da tsananin begen juna
Sai aka shafe kwanaki uku mafaraucin yana jinyar matar shi da yarinya lazimat.
A wata rana matar mafaraucin na bawa yarinya lazyimat horan yaƙi, bayan ta kammala bata
horan yaƙin sai ta ta ja hannunta izuwa kan wani faffaɗan dutse suka zauna tare a kan shi,
sannan ta sanya hannayenta biyu ta ɗora a kan kafaɗunta dube ta cikin nutsuwa ta yi gyaran
murya ta ce "ya ke wannan yarinya shin mene ne sunan ki da labarin rayuwar ki?. Koda jin wannan tambaya daga bakin matar sai hawaye suka kwaranyo daga idanun
Lazimat tana mai fashewa da kuka mai tsuma zuciya.
Al'amarin da ya yi matuƙar bata mamaki kenan kuma ya dugunzuma hankalinta dube ta ta ce
"shin ina dalilin wannan kuka naki?
Ki sani cewa sanar da ni labarin ki shi ne zai bamu damar taimaka wa rayuwar ki.
Da jin haka sai Lazimat ta share hawayen dake fuskarta ta buɗi baki daƙyar ta ce "da farko ni
suna Zalimat bintu Haiman mahaifina ya kasance GWARZON DUNIYA mai tarwatsa maza a filin
daga,
Bisa wannan dalili ne ya sanya jama'ar birninmu ke matuƙar kaunar shi domin yana bayar da
gagarumar gudummawa wajen kare martabar birninmu daga harin bazato.
Daga wannan ne lazimat ta kwashe labarin farmakin da sarki Uhaisu ya kai birnin su bisa
jagorancin shugaba Yesiran,dama abin da ya faru tsakaninta da dakarun jirgin ruwan da ya
ɗauko su a saman tekun Baharul-sawara, daaga farko har ƙarshe ta zayyane mata.
Sa'adda da yarinya lazimat tazo nan a labarin ta sai ta sake fashewa da wani
matsanancin kuka mai ban tausayi ,
Saboda matuƙar tausayi da matar mafaraucin ta ji bata san lokacin da hawaye ya zubo mata ba
ta rungume ta a kirjinta su duka biyun suka fashe da matsanancin kuka, sai da suka ɗauki
tsawon lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani ta janye jikinta daga na Lazimat suka
fuskanci juna. Idanu sharkab da hawaye ta dube ta ce "ya ke Lazimat haƙiƙa sarki Uhaisu baƙaramin
AZZALUMI ba ne, tun da ya raba ki da iyayen ki dangi da yan uwanki ya mayar dake marainiya.

Ina so ki kwantar da hankalin ki domin ni da mai gidana mun yi miki alƙawarin sai mun ɗauko
miki fansa akan sarki Uhaisu, kuma sai mun ceto sauran jama'ar ku ina so ki ɗauke mu tamkar
iyayenki";
Koda jin wannan batu sai Lazimat ta cika da matuƙar farin ciki ta dube ta ce "ya ummina
ba ki sanar da ni sunanki da na abbana ba da ma labarin ta ku rayuwar?
Da jin wannan tambaya sai matar mafaraucin ta yi murmushi mai taushi a gare ta ta ce "mai
gidana ana kiranshi da suna Najwas ibnu Naufal, ni kuwa ana yi min laƙabi da Kilimat bintu
kurbas, ya 'yata ki yi sani cewa a halin yanzu ba zan ba ki labarin rayuwar mu ba, kasancewar
na ki labarin ya yi min fami a zuciyata, amma na yi miki alƙawarin zan ba ki anan gaba". Koda Kilimat bintu kurbas ta zo nan a zancen ta sai suka hango mafarauci Najwas ya dawo
daga farauta, cikin matuƙar farin ciki suka miƙe tsaye suka je suka tarbe shi,
Kilimat ta riƙe mashi dabbar da ita kuwa yarinya Lazimat sai ta karɓi salkar ruwa da jakar dake
rataye a gadon bayanshi suka dunguma izuwa cikin gida.
Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya lazimat bayan ta samu lafiya a hannun
mafarauci Najwas da uwar gidanshi.


BABI NA HUƊU

Ƙasaitacciyar turaka ce da aka ƙawatata da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin
rayuwar duniya, gaba ɗaya tana shimfiɗe da wani irin kilishi mai matuƙar taushi,wanda idan
mutum ya taka shi sai ya ji tamakar kafafuwanshi za su shige ciki, ku san dukkanin abin da ke
turakar an sana'anta shi ne da zallar ƙarfen jauhari da yaƙutu, waɗansu irin fitilu masu matuƙar
haske sun ƙara fito da kyawun tuarakar.
Kai tsaya wa musalta tsaruwa da kawatuwar turakar ya huce hankali sai dai abin da idanu suka
gani kawai.
A wannan lokaci dare ya tsala babu abin da kunne ke ji face kukan gyare gami da haushi
karnuka tsilli-tsilli,i' idan mai kallo ya kai duban shi a tsakiyar turakar zai yi arba da wani mutum
sanye da riga 'yar shara da wando irin na hamshaƙan sarakai yana kai komo tamkar wanda ya
yiwa sarki ƙarya. Ba wani ba ne face sarki Uhaisu, a wannan lokacin bakomai ne ya hana Uhaisu barci ba
face tunanin buƙatar da ɗanshi yarima Zafiyar ya nema a wajen shi, ta ya amince mashi ya
zamo mai kula dasu jaruma Nabihat.
An ya kuwa yarima ba saboda zuciyarshi ta kamu da soyayyar Nabihat ba ne yasanya ya ce a
ba shi ikon kulawa da su ɗin ba? Yanzu idan har ya yi ganganci soyayya mai ƙarfi ta ƙullu
tsakanin su ta ya ya zai iya zartar da hukuncin kisa akan su Nabihat tun da halarar tsafi ta
bayyana mashi cewa sune za su kawo ƙarshen MULKIN ZALUNCIn shi daga doran ƙasa. Sa'adda sarki Uhaisu ya zo nan a tunanin shi sai hankalin shi ya dugunzuma fiye da ko
yaushe.
Yana Cikin wannan hali ne wani tunani ya faɗo mashi wanda ya sanya shi farin ciki.
Tunanin kuwa shi ne ai ya umarci sadauki Yesiran akan ya kai su Nabihat izuwa ɓangaren
BAUTAR MUTUWA dake kurkukun, tabbas yunwa ce zata zamo ajalin su.
Koda ya zo nan a tunanin sai ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa.

Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Uhaisu bayan ya baro fada, ya kaɗaita a cikin
turakarshi.
Kashe gari tun da duku-dukun safiya kafin hudowar rana aka fito dasu jaruma Nabihat
daga cikin ɗakunan da aka kulle su a ɓangaren BAUTAR MUTUWA, dake cikin kurkukun
Mautul- shammar, aka rarraba masu aikin farfasa duwatsu, da yake yanayin garin ana cikin
wunturu, nan take tsananin sanyi ya addabi ƙananan yara da tsofaffi, saboda ba sa sanye pda
tufafi masu nauyi,
Sai da suka wuni cur suna aiki sannan dakaru suka sake mayar da su izuwa cikin ɗakunan su
ba tare da an bawa ɗayan su koda loma ɗaya ta abinci ba.
Tun da duku-dukun safiya fadar sarki Uhaisu ta cika ta batse da jama'ar gari gami da
fadawa, bayan kowa ya hallara ne sai sarki ya miƙe tsaye daga kan karagar shi ta mulki ya
fuskanci jama'a ya buɗi baki cikin tunƙaho da baƙar uzza ya ce "ya ku jama'ar wannan fada mai
albarka ku yi sani cewa ba komai ya sanya na tara ku anan ba sai domin sai ku ganewa da
idanuwanku yadda zan yanke wa jama'ar birnin DARUL-IMFAL hukunci, domin a cikin su ne
za a samu tsageran da zai kawo ƙarshen mulkina, ina so hukuncin ya zamo darasi ga duk wani
mai ƙarar kwana irin su";
Koda gama faɗin hakan ya koma kan karagarshi ya zauna, take fadar ta kaure da ce kuce kowa
na faɗin albarkacin bakinshi.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka hango shugaba Yesiran ya tuso ƙeyar su
jaruma Nabihat sanye cikin sasari na baƙin ƙarfe, dakaru na take masa baya sun Kunno kai
cikin fadar, sai da Yesiran da fursunonin ashirin suka iso izuwa wani dogon tudu,sannan ya
zube ƙasa ya kwashi gaisuwa ga sarki, kana ya miƙe tsaye ya juya ya yi wani badakare inkiya
ta wutsiyar idanu.
Kawai sai badakaren ya tusa ƙeyar jaruma Nabihat izuwa kan wannan gayayyen tudu mai
matattakala ta hau ta tsaya kuma ya ɗaure idanuwan ta wani baƙin ƙyalle.
Daga can sai wani badakare ya ratso daga cikin dakarun fadar ya fito waje yana taka
tafka-tafkan ƙafafuwanshi. Badakaren ya kasance garjejen kato mai ƙirar samudawan farko,
yana da manyan damatsa ya tara kwanji, cikinshi runtumeme ne tamkar an kifa ƙwarya, kallo
ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa zuciyarshi a ƙeƙashe take da tsantsar zalunci. Kai tsaye ya durfafi inda jaruma Nabihat take yana mai zare wata sharbebiyar takobi a
cikin kubenta, yana wani irin huci tamkar kububuwa ya ɗaga takobin sama domin ya datse mata
wuya.
Kafin KAIFIN TAKOBIN ya ratsa wuyan Nabihat
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu kyawawan jarumai biyu mace da namiji
da gami da wata yarinya 'yar kimanin shekaru goma sha biyu sun kutso izuwa cikin fadar shirye
cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensi rike da miyagun makamai, ba wasu ba ne waɗannan
jarumai ba face mafarauci Najwas da uwargidanshi Kilimat tare da yarinya Lazimat. Har dakarun dake fadar sun yunƙura za su afka masu a kacame da azababban yaƙi sai
sarki Uhaisu ya daka mssu tsawa su ka ja da baya, cikin matuƙar fushi ya miƙe tsaye zumbur!
Daga kan karagar mulkinshi yana mai zare takobinshi gami da kwarara uban ihu, sannan ya
dako wawan tsalle daga inda yake tsaye tamkar an harbo shi daga cikin baka, Yana saman ya kaiwa mafarauci Najwas wawan sara da nufin tsinke mashi wuya.
Cikin ƙwarewa gami da zafin nama Najwas ya sanya takobinshi ya kare harin,
Uhaisu ya dira bisa turba aka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro.

Koda ganin hakan sai yarinyar Lazimat ta ruga izuwa inda su jaruma Nabihat suke ta sanya
takobi ta sare sarƙoƙin da aks ɗaure su.
Nan fa Nabihat da sauran 'yan matan su sha tara suka rungume yarinya Lazimat suna
masu fashewa da kukan farin ciki.
Suna cikin wannan hali ne suka hango shugaba Yesiran da dakarun shi sun ya rugo izuwa kan
su, koda ganin hakan sai suka yi wuf suka juya suka fuskance su aka yi karon battar ƙarfe aka
kacame da azababban yaƙi.
Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin mafarauci Najwas da sarki Uhaisu, su
jaruma Nabihat da shugaba Yesiran da dakarun shi.
Sai karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne,
Najwas da kilimat suka wanzu suna kare hare-haren da Sarki Uhaisu gami da mayar da
martani.
Wohoho! Haƙiƙa wanda ya iya ya huta, kuma faɗan gwani da gwani daɗin kallo gare shi,in da
ace mutum ya na tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan ZARATAN MAYAƘA uku ke kaiwa
juna hare hare domin hallaka juna dole ne ya jinjina masu ya kira su da JARUMAN DUNIYA.
Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya da daƙiƙa ɗari da arba'in ana wannan fafatawa amma ɗayan
su bai samu nasarar yiwa abokin gwamin shi koda kwarzane ba.
A zahiri ga wanda yake kallon artabun zai lura sarki Uhaisu ya ninka su jarumi Najwas a
ƘARFIN DAMTSE, sai dai su nuna mashi ƙwarewar yaƙi.
Al'amarin da ya fusata sarki Uhaisu kenan kuma ya cika da matuƙar mamaki, domin a
tarihin jarumtakar shi tai taɓa yin GABA DA GABA da wani jarumi ba face ya kai shi ƙasa, abin
tambaya ana shi ne ya aka yi ya kasa samun nasara akan su? Shin wai su waye ma waɗannan
jarumai Kuma daga ina su ka fito? Amsar tambayoyin da ya kasa bawa kanshi kenan, kawai sai ya ja da baya sannan ya yi
kururuwa ya sa ke afkawa masu yana mai canza salon faɗan shi.
Ashe Najwas da Kilimat sun lura da abin da sarki Uhaisu ya yi, don haka su ma sai su ka
koyi da shi suka canza salon artabun nasu.
Wohoho! Gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya sauya dole ne rawa ta sauya salo.
Nan fa yaz' zamana su sarki Uhaisu sun lalata dukkanin makaman yaƙinsu, sun zubar da su
aƙas sun shiga amfani da tsagwaron ƘARFIN DAMTSE suna kaiwa juna naushi da bugu hannu
da ƙafa.
Nan fa labari ya sha bamban domin a yanzu Najwas da kilimat basa iya kare naushin
Uhaisu. Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne sarki Uhaisu ya shammace su gabza masu wawan
naushi a fuska a lokacin da suka dako tsalle sama, take su kayi saman tamkar an janye su da
ƙugiya, sannan su ka rikito ƙasa hancinsu na yoyon jini. A ɓangaren su jaruma Nabihat kuwa ba haka al'amarin yake ba, domin kuwa sun
zamewa shugaba Yesiran alaƙaƙai ya rasa yadda zai su da su, duk inda su ka sanya a gaba sai
dai kaga MAZAJE na zubewa ƙasa matattu tamakar ana sassabe a gonar auduga.
A ɓangaren yarinya Lazimat kuwa, ta zamo tamkar shaiɗaniya a tsakiyar dakarun, ta wanzu
tana aika rayukansu barzahu ta hanyar amfani da KWARI DA BAKAnta,
Ya zamana cewa duk hare-haren da ake kawo mata tana kare wa, tare da mayar da martani
cikin zafin nama na ban al'ajabi, ta wanzu wajen ragargazar dakarun, a cikin wannan hali ne sai
ta hango shugaba Yesiran ya rugo izuwa inda take hannunshi riƙe wata zabgegiyar adda mai
baki biyu,

Koda ganin hakan sai tayi wata katantanwa a tsakiyar dakarun tayi fanka tana mai dukan
ƙafafuwansu, a lokaci guda suka zube a ƙasa magashiyan suna aman jini,
sannan ta gyara tsayuwar ta tana mai jiran isowar shi,
Ya yin da rage saura taku goma tsakanin su sai shugaba Yesiran ya ja ya tsaya aka yi
kallon-kallo na wani lokaci.
Yesiran ya jijjiga addar dake hannunshi sannan ya duba ɗayan da ya zama dungulmi,
take abubuwan da suka faru tsakanin shi da yarinya Lazimat a ƙarƙashin tekun Baharul-sawara,
ya dunga dawo masa a cikin kwanyarshi.
Daga can sai hawayen baƙin ciki su ka kwaranyo daga idanuwan shi, kawai sai ya
taƙarƙare ya kwarara ihu ya afkawa Lazimat da dukkanin ƙarfin shi suka garƙame da masifaffan
yaƙi.
Lokacin da su mafarauci Najwas suka fahimci cewa wankin hula zai kai su dare, idan aka
cigaba da wannan yaƙi a haka za'a iya yin ragas ko ayi kare jini biri jini.
Sai su ka zurfafa izuwa cikin kogin tunani domin samun mafita. Koda samun mafitar sai suka ja
da baya sannan suka rugo da gudu suka haɗa ƙarfin su waje guda suka gabzawa sarki Uhaisu
wawan naushi a fuska da hannayensu biyu,
saboda ƙarfin naushin sai da sarki Uhaisu ya tuntsira baya har sau uku ya kife a ƙasa yana
aman jini, sannan suka shiga da naushi.
Nan fa Uhaisu ya dunga kwarara wawan ihu sakamakon naushin dake ratsa sassan ƙasusuwan
jikinshi, fuskarshi duk ta daddauje jini na zuba.
A ɓangaren Lazimat da shugaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login