Showing 3001 words to 6000 words out of 18096 words
Chapter 2 - FATAUCIN BAYI Book Complete Book Written by Mansur Usman Sufi .pdf
sai ya yi arba da masu dafa
abincin kwance suna sharar barci babu tufafi a tare da su.
Cikin matuƙar fushi gami da tashin hankali ya zare takobinshi ya ruga izuwa waje yana
mai ƙwallawa sauran dakarun kira.
Al'amarin da ya janyo hankalin sadauki Sharkar kenan ya zare takobinshi da nufin
dakawa dakarun tsawa.
A dai-dai wannan lokaci ne hodar banjun da su Nabihat suka zuba a cikin abincin ta fara
bugar da dakarun suna ɓingirewa kasa suna sharar barci.
Kafin Sharkar da Hushaibu su farga fiye da rabin dakarun dake cikin jirgin ruwan sun kamu da
barci mai nauyin gaske, cikin matuƙar kaɗuwa gami da tashin hankali sadauki Sharkar ya
cigaba da falfala azababban gudu, yana mai kurma wawan ihu
Nan fa sauran dakarun da ba su kai ga cin abincin ba suka firgice suka ɗauko
makaman yaƙin suka dinga fitowa daga kowace kusurwa a jirgin.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga su jaruma Nabihat da sauran 'yan matan
fursunonin sun yo fitar burgu daga maɓuyar su suna, suka yi ɗauki izuwa kan dakarun suna ihu
da kururuwa mai firgitarwa.
Koda ganin hakan sai dakarun suka yi ɗauki kansu suna ihu da kururuwa mai firgita
DANDAZON MAYAƘA a filin daga.
Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan zaratan 'yan mata su ashirin
kacal! Suka tunkari ɗaruruwan dakarun dole ne ya cika da mamaki kuma ya jinjina masu ya
tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA, mata masu kamar maza.
Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro daban
al'ajabi.
Nan fa gaba ɗaya jirgin ruwan ya yamutse da ƙarar haɗuwar makaman yaƙi, gami da ihu da
kururuwar mazaje.
Nanfa Nabihat da 'yan matan fursunonin suka wanzu suna kaiwa dakarun sara da suka
cikin matuƙar zafin nama tamkar jikkunan ba su kasance na jini da tsoka ba.
Cikin abin da bai gaza daƙiƙa arba'in ya zamana cewa sun samu nasarar hallaka fiye da mutum
hamsin na dakarun sun rauna ta fiye da ɗari biyu.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin dakarun kenan kuma ya fusata su ainun, bisa
ganin cewa a matsayin su na GWARAZAN MAYAƘA, amma a ce 'yan mata sun zame masu
alaƙaƙai kuma GOBARAR ANNOBA.
Nan fa dakarun suka ZAGE DAMTSE wajen kaiwa su Nabihat miyagun hare-hare.
Ana cikin wannan artabu ne wani garjejen sadauki, ya kaiwa wata daga cikin 'yan
matan wani wawan sara, da nufin tsinke mata wuya amma budurwa ta sunkuiya cikin zafin
nama, takobin sadauki ta sari iska. Kafin ya sake mayar da martani, budurwar ta cire wata
siriyar wuƙa a damtsenta s caka mashi a maƙogaranshi, sannan ta sanya ƙafarta ɗaya ta daki
ƙirjin shi da dukkan ƙarfin ta.
Saboda da matuƙar ƙarfin dukan sai da ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya ya
faɗa cikin tekun yana mai tsandara ihu.
Kawai sai budurwar ta sake afkawa cikin dakarun ta ci-gaba da saran su.
Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne SADAUKi Sharkar ya samu nasarar make Nabihat ta faɗi
ƙasa, magashiyan nunfashin ta na fita daƙyar, kawai sai ya sanya hannunshi ya damƙo wuyanta
ya tattare dukkanin karfinshi da nufin karya wuyan Nabihat.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga Nabihat ta dunƙule hannayen ta biyu ta
girɓawa sharkar naushi a fuska.
Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da ya yi katantanwa a sama sau uku, sannan ya kife a ƙasa,
yana mai tsandara ihu sakamakon zafi da zugin da ya ji, haƙorinshi guda ɗaya ya yi fitar burgu
daga cikin bakinshi jini ya yi tsartuwa.
Amma saboda karfin zuciya gami da juriya irin ta manyan GWARAZAN JIYA sai ya miƙe
tsaye zumbur yana mai goge jinin dake bakinshi yana mai gyara tsayuwa.
A dai-dai lokacin da Nabihat ta miƙe tsaye zumbur, aka sake sabon kallon kallo, sannan
suka sake afkawa junan da yaƙi, ana fara wannan arbu ne Nabihat ta shammaci Sharkar ta
gabza mashi naushi a kirjinshi da kafafuwanta biyu, saboda ƙarfin naushin sai da ya yi sama ta
tamkar an janye shi da ƙungiya sannan ya faɗa izuwa tekun Baharul-sawara. Koda samun wannan gagarumar nasara sai jaruma Nabihat ta ruga izuwa inda 'yan
uwanta suke ta kai masu ɗauki su ka cigaba da ragargazar dakarun.Cikin kankanin lokaci suka
hallaka su baki ɗaya.
Kawa sai Nabihat ta umarci 'yan mata uku da su tuƙa jirgin ruwan a cigaba da tafiya
Cikin matuƙar kaɗuwa ɗaya daga cikin fursunonin ta dubi Nabihat cikin tashin hankali ta ce '' ya
ke Nabihat ta ya ya zamu cigaba da tafiya bayan cewa yarinya Lazimat na cikin wannan teku,
kuma bamu da tabbacin a wane hali take ciki tana raye ne ko ta mutu.
Koda jin wannan batu daga bakin Sharimat sai idanun Nabihat su ka ciko da ƙwalla, ta
dube ta ta ce "ya ke Shamirat tabbas a yanzu ba ni da tabbacin yarinya Lazimat na raye, shin
yanzu zamu tsaya neman ta ne? Ko kuwa zamu cigaba da tuƙa wannan jirgin ruwa domin ceto
daruruwan jama'armu da suka haɗar da yara ƙanana da mata gami da tsofaffi,'? Ina so ki
kwantar da hankalinki idan har yarinya Lazimat na raye zamu sake saduwa da ita".
Koda jin wannan batu daga bakin Nabihat sai Shamirat ta gyaɗa kai cikin alamun
matuƙar damuwa ta matsa kusa da 'yan uwanta, suka shiga tuƙa jirgin ruwan domin koma
izuwa birnin su.
A dai-dai wannan lokaci ne shugaba Yasiran ya taso daga ƙarƙashin tekun fuskarshi a
murtuke babu annuri, tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta, gundulmin hannunshi da
Lazimat ta sare mashi na zubar da jini.
Sa'adda jaruma Nabihat ta cigaba da jagorantar sauran 'yan uwanta fursunoni, a bisa
jirgin ruwan dake tafiya akan tekun Baharul-sawara, domin gudun TSIRA DAGA HAKA.
Sai suka shafe tsawon sa'a biyu suna tafiya babu sassauci.
Lokacin da ya zamana an shafe sa'a ɗaya ana tafiyar sai jaruma Nabihat ta yi umarni aka
shiga ɗakin sirri dake ƙarƙashin jirgin ruwan, aka ɗauka gurasar gami taceccen ruwan inabi, aka
shiga rarrabawa jama'arsu domin kowa ya kimtsa cikinshi.
Ana cikin wannan hali ne
kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka hango waɗansu tawagar jiragen ruwa kimanin guda
ashirin, sun bayyana a saman tekun a kowa ce kusurwa, wato gabas, yamma, kudu da Arewa,
Cikin matukar kaɗuwa gami da tashin hankali Nabihat ta yi umarni aka tsayar da tafiya,
kawai sai 'yan matan suka ruga izuwa wani ɓangare a jirgin suka ɗebo makaman yaƙi, sannan
suka ruga izuwa tsakiyar birnin suna masu gyara tsayuwar su zukatansu cike da matuƙar firgici.
Ya yin da ya zamana cewa jiragen ruwan sun matso daf juna, sai Nabihat ta sake
ɗimauce wa, su dai jiragen ruwan suna ɗauke ne da waɗansu irin zaratan dakaru masu ƙirar
samudawan farko, suna sanye cikin sulken yaƙi na baƙin ƙarfe, ɗauke da miyagun MAKAMAN
ƘARE DANGI. Kaico! Haƙiƙa waɗannan dakaru sun kasance masu ban tsoro, domin babu halitta da za
ta yi arba da su face ta yi nadamar wanzuwar ta a doran ƙasa.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su Nabihat da tawagar dakarun.
Tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali, a lokacin ne su Nabihat suka hango shugaba
Yasiran a ɗaya daga cikin jiragen ruwan, shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannunshi ɗaya
ɗauke da wata sharbebiyar takobi, ɗayan kuwa da ya yi dungulmi ya naɗe shi da wani farin
ƙyalle, fuskarshi a murtuke babu annuri har gyatsune take saboda matuƙar fushi. Al'marin da ya yi matuƙar ba su mamaki kenan, suka tambayi kansu a cikin ransu suna
masu cewa, ya aka yi Yasiran ya rayu shin ina yarinya Lazimat take tana raye ne ko kuwa ta
mutu?
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kawunansu kenan.
Kawai sai Nabihat su ka hango dakaru masu tarin yawa suna dako tsalle daga inda suke suna
sauka akan jirgin da suke suna shawagi a sama tamkar tsuntsaye, suna ihu da kururuwa mai
firgitarwa.
Koda ganin hakan sai Nabihat ta ɗaga takobinta sama cikin ƙarfin hali gami da ƙarfafawa
sauran 'yan matan gwiwa ta falfala da gudu izuwa kan dakarun.
Ya yin da 'yan matan suka ga haka sai suka yi koyi da ita, suna masu mara mata baya.
Tabbas shi ƙarfi a zuciya yake ba wai a girman jiki ba, domin idan ba haka ba taya ya
mutum ashirin za su za su tunkari ɗaruruwa.
Amma dai masu iya magana na cewa shi bala'i kafin ya zo ne ake neman mafita, amma idan
yazo babu abin da ya rage face a karɓe shi hannu biyu.
In da a ce mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan dubban dakarun suka
yunƙura kan su jaruma Nabihat, sai ya yi zaton DANDAZON zakuna ne suka farwa barewa
guda ɗaya jal, saboda matuƙar kwarjinin su.
Ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi mai matuƙar firgici da ban tsoro.
Ƙarar haɗuwar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne.
Ana fara wannan artabu ne su jaruma Nabihat suka fara gane cewa sun haɗu da gamon su.
Domin kuwa koda ba'a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza, kuma ruwa ba sa'an
kwando ba ne. Domin a zahiri dakarun sun ninka su a ƘARFIN DAMTSE gami da zafin nama
nesa ba kusa ba.
Sai da aka shafe sa'a ɗaya da daƙiƙa ɗari biyu ana wannan baƙin artabu, kasancewar
masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN ƘARFI sai ya zamana
dakarun sun yi masu miyagun raunuka suna zubar da jini, bisa hakan ya sanya suka faɗi ƙasa
a sune.
Koda samun wannan gagarumar nasara sai dakarun suka sake ɗaure fursunonin da
waɗansu irin murtuka-murtukan sarƙoƙi.
Koda aiwatar da hakan sai waɗansu dakaru na musamman suka shiga tuƙa jirgin ruwan aka
cigaba da tafiya, sauran jiragen tawagar guda ashirin suka mara masu baya.
Tafiyar sa'a uku kacal suka yi aka iso izuwa gaɓar tekun, take dakarun suka fito da su
Nabihat daga jirgin ruwan, nesa kaɗan da inda aka sauka wani ƙasaitaccen birni mai dogayen
gine gine, masu tsari da kyawu.
Kallo ɗaya za ka yiwa birnin ka fahimci cewa an kashe dukiya mai tarin yawa wajen ƙawata shi.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka tusa ƙeyar fursunonin izuwa birnin su su Nabihat kuwa
sai aka ɗora su
a bisa kan keken doki.
Nan fa tsananin wahala ya sanya sauran jama'ar su Nabihat suka dunga yanke jiki suna
faɗuwa ƙasa, sakamakon matuƙar zafin rana amma a haka dakarun suka cigaba da jan su a
ƙasa.
Komai rashin tausayin mutum idan ya yi arba da halin da ƙananan yara da mata ke ciki dole ne
ya zubar da hawayen tausayi.
Domin wasu lokutan idan mutum ya faɗi ƙasa sai dakarun su zabga mashi wata
murtukekiyar bulala, take inda ya daka ɗin zai fashe jini ya yi tsartuwa.
Tun kafin a iso kofar birnin waɗansu girɗa-girɗan dakaru suka wangame makekiyar kofar birnin,
suna zuwa suka kunna kai izuwa ciki.
Daga ciki birnin ya kasance tafkeke na gaban kwatance, gaba ɗaya gine-ginen shi an yi su
ne bisa tsari mai ban sha'awa, duk inda mutum ya kalla jama'a ne rututu na kai komo suna
gudanar da ayyukan su na yau da kullum, haka dai su shugaba Yasiran suka ci-gaba da tafiya a
cikin birnin, duk inda jama'a suka hango su sai ka ga sun dare sun buɗa masu hanya. Kai tsaye aka shiga izuwa fadar birnin wacce ta kasance ƙasaitacciya da aka ƙawata da
nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, kai tsayawa musalta tsaruwa da
ƙawatuwar fadar zai iya zama ƙauyanci sai dai abin da idanu suka gani kawai.
A wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a maza, mata yara da manya tare da yan majalisa.
Zaune a bisa wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'anta ta da ƙarfen jauhari
aka yi mata feshin da ruwan zinare.
Wani garjejen mutum ne mai kimanin shekaru talatin da ɗoriya, yana sanye cikin tufafin alfarma
irin na hamshaƙan sarakai, kanshi sanye da KAMBUN SARAUTA.
Kallo ɗaya zaka yiwa mutumin ka ji baka marmarin sake haɗa idanu dashi, saboda
matuƙar munin fuskarshi tamkar murmushi bai taɓa wanzu akan ta ba.
Ba wani bane wannan mutum ba face sarki Uhaisu ibn Falluz.
A gefen hannunshi na dama bisa wata ƙasaitacciyar kujera wani kyakkyawan saurayi ne
ma'abocin kwarjini da haiba, ya caɓa ado irin hamshaƙin BASARAKE, babban abin da ya ƙara
tona asirin kyawun shi shine saje da gemunshi da suka kasance baƙaƙe siɗik.
Ba wani ba ne kyakkyawan saurayin ba face yarima Zafiyar ibnu Uhaisu, wanda ya kasance ɗa
guda ɗaya tilo ga sarki Uhaisu.
Sarki Uhaisu ibn Falluz ya kasance GWARZON DUNIYA a fagen jarumtaka gami da
sanin ilimin tsafi, daɗin daɗawa kuma ya kasance AZZALUMI na gaban kwatance.
Tun yana da shekara goma sha biyar ya hau bisa karagar mulki, duk da yana da ƙarancin
shekaru amma sai jama'a suka ga yana gudanar da sha'anin mulki cikin tsari fiye da na
mahaifinshi marigayi sarki Falluz.
Lokacin da sarki Uhaisu ya cika shekaru ashirin a bisa kan gadon sarauta, sai ya zamana
cewa ya fara kai mamayar bazato izuwa ƙauyuka da biranen dake maƙwabtaka da shi, ana
farauto mashi bayi gami dukiya mai tarin yawa.
Cikin ƙanƙanin lokaci Uhaisu ya zama mashahurin attajiri da babu tamkar shi a nahiyar.
Da wannan dukiya da ya tara yake siyo manyan sadaukai daga sassan duniya domin su
taimaka mashi wajen FATAUCIN BAYI.
Shin mene ne dalilin da ya sanya su jaruma Nabihat suka baro birninsu har aka farauto
su a cikin wannan jirgin ruwan?
Amsar hakan kuwa shi ne kamar haka:-
BABI NA BIYU
Wata rana daga cikin ranakun da sarki Uhaisu ke kai FARMAKIN BAZATO izuwa birane
da ƙauyuka domin FATAUCIN BAYI.
Yana zaune a cikin lambun shaƙatawar shi sanye da riga 'yar shara irin ta hamshaƙan sarakai,
waɗansu irin tsala-tsalan kyawawan kuyangi na shayar da shi taceccen ruwan inibi da barasa a
bisa waɗansu kofuna na zinare, a gefe guda kuwa waɗansu kuyangi ne sanye da tufafi mai
bayyana tsiraicinsu. Babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da su face hankalinshi ya tashi.
Su na yiwa sarki Uhaisu tausa tamkar wani jariri, shi kuwa yana kallon korayen tsirrai
gami da waɗansu irin tsuntsaye dake shawagi a wajen, su suna fitar da wani irin sautin kuka
mai daɗin saurare.
Zuciyarshi cike da matuƙar farin ciki, yana cikin wannan hali ne kawai sai ya ɗauko madubin
tsafinshi ya shafe shi da hannunshi na hagu ya fara gudanar da bincike bisa halarar tsafin shi.
Kamar yadda a duk sa'adda zai kai farmakin yana gudanar da bincike ne domin ya gano
birnin da zai kai aiwatar da hakan,
Tsawon daƙiƙa hamsin yana gudanar da binciken sannan ya gano wani baƙon birni dake iyaka
da tekun Baharul-sawara wato birnin DARUL-IMFAL,
Abin da ya firgita shi a binciken shi ne, tabbas a wannan birni ne za a samu mahalukin da zai
kawo ƙarshen mulkin zaluncin shi a doran ƙasa.
Kooda ganin hakan sai sarki Uhaisu ya miƙe tsaye zumbur yana mai kurma wawan ihu,
ihun na shi ya firgita kuyangin dake yi mashi hidima, gami da tsuntsayen dake lambun suka
tashi sama furrrr!. Al'amarin da ya janyo hankulann dakarun dake gidan sarautar kenan suka
rugo izuwa lambun ɗauke da makamai.
Amma koda suka yi arba