Showing 12001 words to 15000 words out of 18096 words
Chapter 5 - FATAUCIN BAYI Book Complete Book Written by Mansur Usman Sufi .pdf
Yesiran kuwa sun cigaba da kaiwa juna miyagun
hare-hare da niyar hallaka juna,
Idan Yesiran ya kaiwa Lazimat sara da addarshi, idan ta kare harin sai ta durkushe ƙasa saboda
bambancin ƙarfin a bayyane yake,
Ana cikin wannan yaƙi ne Yesiran ya shammaci Lazimat ya yanke ta da addarshi a kwiɓin
cinyarta ta dama jini ya yi tsartuwa. Lazimat ta ƙwalla ƙara sakamakon zafi da raɗaɗin da ta ji.
Sannan ta mayar da martani cikin gwanin ta, nan take ta yanki Yesiran a damtsen cinyarshi ta
hagu jini ya kwaranya. Haka su ka cigaba da wannan ɗauki ba daɗi ya zamana cewa sun yiwa junan su rauni
fiye da biyar dukkanin su jiri na ɗibar su suka kife a ƙasa magashiyan, ma'ana dai an yi RAGAS
tsakanin su
A dai-dai wannan lokaci ne Nabihat suka samu nasarar hallaka gaba ɗaya dakarun dake fadar,
ya yin da Nabihat ta hango halin da Lazimat ke ciki sai ta ruga izuwa inda take kwance ta ɗauke
ta ta goyata a gadon bayanta, sannan ta kama ingarmar doki ta haye 'yan matan fursunonin
suka yi koyi da ita, suka sakar masu linzami suka sukwane su a guje suna masu ficewa daga
fadar. A dai-dai wannan lokaci ne mafarauci Najwas da matarshi kilimat suka dako wawan tsalle daga
kan ruwan cikin sarki Uhaisu suka dira a can gefe, cikin wani irin baƙin zafin nama suka kama
dawakai suka haye suka rufawa su Nabihat baya suka fice daga fadar.
Lokacin da mafarauci Najwas suka samu nasarar tserar da rayuwar su jaruma Nabihat
daga fadar sarki Uhaisu, sai suka wanzu suna ratsa layuka da unguwannin birnin har suka
samu nasarar ficewa daga birnin baki ɗaya, suka nausa izuwa cikin daji suna tsala azababban
gudu a bisa dawakansu.
Tafiyar daƙiƙa arba'in kacal suka yi suka iso wata mararrabar hanya guda biyu a dajin, hanyar ta
farko ta gangara ne izuwa wani waje mai ɗauke da kwazazzabai, ta biyun kuwa ta durfafi wata
sahara.
Ya yin da aka ga waɗannan hanyoyi biyu sai aka ja linzamin dawakai aka tsaya cak! da tafiya,
mafarauci Najwas ya buɗi baki ya yi gyaran murya ya dubi jaruma Nabihat cikin alamun matuƙar
damuwa ya ce "ya ku wadannan jarumai yanzu ga shi mun iso mararrabar hanya shin yanzu
wacce ya kamata mu bi? Koda jin wannan tambaya sai kowa ya yi shiru aka rasa wanda zai ce kala,
sai daga bisani ne jaruma Nabihat ta buɗi baki cikin damuwa ta ce "waccan hanya mai ɗauke
da sahara babu alkairi a cikinta, domin ba za mu damu ruwan sha, da 'ya'yan itace da zamu yi
kalaci ba.
Ita kuwa mai ɗauke da kwazazzabai dole ne a samu halittu masu cutar wa a cikin ta ba, amma
dole ita za mu bi''.
Koda jin wannan batu daga bakin Nabihat sai kowa ya na'am da hakan, aka sakarwa
dawakai linzami aka cigaba da tafiya, ana cikin wannan tafiya ne aka iso wani waje mai tattare
da duhuwa a dajin, kwatsam! Sai aka ga ganyayyakin bishiyun motsawa,
alamun dake nuni da wani abu mai rai na shirin bayyana.
kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu irin mutane bila-adadin suna fitowa daga
duhuwar bishiyun suna masu yiwa su Najwas ƙawanya.
Sa'adda su mafarauci Najwas su ka yi arba da mutanen sai suka raza ainun, domin a
iya tsawon rayuwar su ba su taɓa ganin dakaru masu kwarjini tamkar su ba.
Su dai mutane sun kasance girɗa-girɗa masu ƙirar samudawan farko, suna shirye cikin
gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro,
fusakunsu a murtuke suke tamkar ba su taɓa dariya ba, hannayensu rike da makamai dangin
gatari, majaujawa, al'amudi da takobi.
Haƙiƙa waɗannan dakaru sun cika ababan tsoro.
Domin ƙaramin jarumi ba zai iya haɗa idanu da su ba face JARUMIN ƘWARAI mai dakakkiyar
zuciya, a hankali mayaƙan su ka cigaba da matsowa kusa da su Najwas sai da ya rage saura
kamar taku goma sannan su ka ja suka tsaya cak!
Sannan suka dare gida biyu suka buɗe wata 'yar siririyar hanya a tsakiyar su,
Jim kaɗan sai ga wani garjejen ƙato ya da nunka sauran dakarun girma da kwarjini gami da cika
idanu.
Idununshi ɗaya a makance yake ya jirkice ya zama fari gaba ɗaya. Ya fito gaban dakarun yana
mai tako lafka-lafkan kafafuwanshi.
Sannan ya ja ya tsaya cak yana mai ƙarewa su Najwas kallo, kawai sai ya bushe da dariyar
mugunta sannan daga bisani kuma ya murtuke fuska tamkar an ai ko mashi da WASIƘAR
MUTUWA ya shaƙi iska da manyan ƙofofin hancinshi masu kamar da mazirari ya busar, sannan
ya buɗe tafkeken bakinshi mai kama ƙofar gari cikin wata irin kakkausar murya ya ce " shin
wane rashin sani ne yasa ku shigowa wannan daji, shin ba ku da labarin cewa nan ce fadar
sarkin ɓarayi na wannan nahiya baki ɗaya.
Kuma alamu sun nuna cewa ku ba fatake ba ne bakwa ɗauke da wani abu da ya danganci
dukiya ko da za a amfana da shi, hakan ya tabbatar min da cewa kenan ɗayan ku ba zai tsira
da rayuwarshi ba''.
Koda jin wannan batu daga bakin shugaban dakarun sai mafarauci Najwas ya tari
numfashinshi yana mai daka mashi tsawa cikin ƙarfin hali ya dube shi ya ce ''shin wane ne kai a
jerin JARUMAN DUNIYA da har za ka kira kanka da shugaban 'yan fashin wannan nahiya, ka
sani cewa kawar da mu ba abu ne mai sauƙi ba''. Da jin wannan batu daga bakin Najwas sai badakaren ya fusata ainun ya dakawa mashi
tsawa wacce ta firgita dukkan wata halitta dake wajen, sannan daga bisani ya murtuke fuska
tamkar an aiko mashi da WASIƘAR MUTUWA ya dubi Najwas ya ce "tabɗijan! Wai yanzu a
duniyar nan har an samu jarumin da zai tsaya a gaba na yana faɗa min baƙaƙen maganganu,
ya kai wannan jarumi tabbas ka sayi ajalinka da kuɗinka, Amma kafin hakan zan sanar da kai
ko ni wane ne kamar yadda ka buƙata.
Suna na Mazabir ibn Sharr shugaban 'yan fashin wannan nahiya baki ɗaya.
Koda gama faɗin hakan sai sadauki Mazabir ya shammaci mafarauci Najwas ya gabza masa
wawan naushi a fuska,
take Najwas ya sulalo ƙasa daga kan dokinshi yana mai aman jini.
Al'amarin da ya harzuƙa zuciyar kilimat da su jaruma Nabihat kenan suka zare makaman su
domin su afkawa sadauki Mazabir.
Amma sai suka ga Najwas ya daga masu hannu yana mai nuna cewa su dakata.
Sannan ya yunƙura ya miƙe tsaye yana gyara tsayuwarshi da riƙon takobin dake hannunshi,
sannan ya furzar da gudan jini daga bakinshi ya dubi Mazabir ya ce "ya kai Mazabir ka yi sani
cewa ni kaɗai zan iya kashe yaranka baki ɗaya ba tare da ka samu nasarar taɓa lafiyar ɗaya
daga cikin 'yan uwana ba''. Koda jin wannan batu daga bakin Najwas sai Mazabir ya bushe da dariyar mugunta ya
dubi Najwas a karo na biyu ya ce "dakyau SARKIN SADAUKAI haƙiƙa ka tabbatar min da cewa
kai GWARZON NAMIJI ne, to ai ga fili ga mai doki, kuma sai an gwada akan san na ƙwarai''.
Koda gama faɗin hakan sai shugaban 'yan fashi Mazabir ya yi wa yaran shi inkiya ta
wutsiyar idanu dake nuna cewa kada su kuskura su yaƙi su jaruma Nabihat.
Take dakarun suka ja da baya suka buɗe masu wani fili, kamar haɗin baki Najwas da Mazabir
suka ruga izuwa kan juna suna ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Lokacin da ya zamana cewa saura taku goma a tsakanin su nan take Najwas ya zamo
ɗan wada a gaban Mazabir, saboda yadda Mazabir ya nunka shi a girma da tsawo. Mazabir ya
zare wani al'amudi a jikinshi.
Ana haɗuwa aka rincaɓe da masifaffan artabu, suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin
matuƙar zafin nama JUTIYA DA BAJINTA ta ban mamaki, sai da aka shafe sa'a ɗaya cur ana
wannan fafatawa amma babu nasara ga ZARATAN MAYAKAn biyu.
Al'amarin da yayi matuƙar ɗaurewa shugaban 'yan fashi Mazabir kai kenan kuma ya ba
shi mamaki, domin fiye da shekaru ashirin suna gudanar da wannan sana'a ta su ta fashi da
makami, amma bai taɓa haɗuwa da jarumi mai zafin nama da juriya tamkar Najwas ba.
Haƙiƙa yau ya gamu da gamon shi.
Sa'adda Mazabir ya zo nan a tunanin shi sai zuciyar shi ta kama tafarfasa tamkar zata
ƙone ta faso ƙirjinshi ta fito waje, sai kawai ya sake zare wani makami a jikinshi mai kama da
lauje mai matuƙar tsawo gami da kaifin tsiya ya cigaba da kaiwa Najwas sara da suka ta ko ina.
Sa'adda kilimat, Nabihat da sauran fursunonin su ka ga yadda shugaban 'yan fashi Mazabir ke
kaiwa Najwas miyagun hare-hare sai hankulan su su ka dugunzuma ainun.
An cikin wannan hali ne Mazabir ya shammaci mafarauci Najwas ya danƙara mashi wani sara
da wannan makami na shi a cinyarshi ta dama, jini yayi tsartuwa Najwas na ƙwalla ƙara
sakamakon zafi zugi da raɗaɗin da ya ji a cinyarshi.
Kafin Najwas ya sake wani yunƙuri Mazabir ya sake kafta mashi wani saran a karo na biyu a
hannunshi jini ya zuba.
Ya yin da Najwas ya ga halin da yake ciki sai ya faɗa izuwa Kogin tunani domin samun mafita.
Koda samun mafitar sai kawai aka ga ya daka tsalle sama tamkar an janye shi da ƙugiya
sannan ya ya sanya ƙotar takobin shi ya daki kan Mazabir da dukkan ƙarfin shi,
saboda ƙarfin dukan sai da Mazabir ya kurma ihu sannan ya runtuma da ƙasa, amma saboda
juriya da nacin tsiya sai ya zumbur ya miƙe tsaye. Cikin gwanin ta Najwas ya kama reshen wata
bishiya a lokacin da ya yi ƙasa zai faɗi, sannan ya yi sufa yana riƙe da reshen ya durfafo inda
Mazabir ya ke ya shammace shi ya sake maka mashi ƙotar takobin a ƙeyarshi Mazabir ya kurma wawan ihu ya faɗi ƙasa da rubda ciki.
A dai-dai lokacin da Najwas ya dira a gadon bayanshi ya riƙe hannayenshi ya banƙara su ta
baya.
Nan fa Mazabir ya shiga ƙoƙarin ƙwacewa daga hannun Najwas amma sai abu ya gagara
ya ci-gaba da kurma wawan ihu domin ji yake tamkar najwas zai ɓalla masjid hannaye.
Tabbas in da a ce mutum ya na tsaye a wannan waje ya ga irin bajintar da Najwas ya yi dole ne
ya jinjina mashi, bisa ganin yadda ya danne garjejen basamuden ƙato ya hana shi rawar gaban
hantsi,
Ya yin da Mazabir ya ga cewa Najwas yana yunƙurin yanka mashi wuya ta baya da wata 'yar
siririyar wuƙa, sai ya buɗi baki cikin matuƙar galabaita ya ce "ina roƙon ka ya kai wannan jarumi
da kar ka kashe ni na yarda cewa kai shugaba na ne kuma duk abin da kake so shi za'a yi nayi
maka rantsuwa da rayuwa ta. Koda jin wannan batu daga bakin Mazabir sai Najwas ya ce "bazan yarda da abin da
ka faɗa ba har sai ka umarci yaranka da su zubar da makamansu.
Da jin hakan sai Mazabir ya ɗaga kanshi kaɗan yana daga kwancen a lokacin da idanuwanshi
suka kaɗa suka yi jajur tamkar garwashin wuta, cikin kakkausar murya ya dubi yaranshi ya ce
"na umarce ku da ku zubar da makamanku''.
Koda jin wannan batu daga bakin shugaba Mazabir sai gaba ɗaya 'yan fashin suka
ajiye makaman su suka durƙusa a ƙasa bisa gwiwoyin su suna masu yin MUBAYA'A.
Ya yin da Najwas ya ga cewa dukkanin 'yan fashin sun miƙa wuya sai ya tashi daga kan gadon
bayan Mazabir ya na mai duban kilimat da su Nabihat yana mai yi masu murmushin samun
nasara.
Da ya ke a wannan lokaci duhun magariba ya fara kawo kai sai Mazabir ya umarci
yaranshi suka sanyawa Najwas magani a raunukan sa, da yarinya Lazimat dake cikin
mawuyacin hali sakamakon artabun da ta fafata da shugaba Yesiran a can fadar sarki Uhaisu.
Duk wani abu da su Najwas suke buƙata 'yan fashin ke kawo masu hatta abin kalaci da
taceccen ruwan sha.
Shi kuma shugaban 'yan fashi Mazabir sai ya shiga aikin nemo manyan itace aka haɗa su
Najwas tafkeken ɗaki domin su shiga ciki su huta, sannan ya rarraba 'yaran a kowacce kusurwa
a dajin domin tabbatar da cikakken tsaro, shi kuma sai ya tsaya a ƙofar ɗakin da su Najwas ke
ciki ya shiga yin rangadi, hannunshi riƙe da wata sharbebiyar Adda, ɗayan kuwa riƙe da wutar
ice domin haskawa. Yana cikin wannan hali ne sai ya hango mafarauci Najwas ya tawo gare
shi.
Koda ya iso daf da shi sai Mazabir ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa.
Najwas ya dube shi a nutse sannan ya yi gyaran murya ya ce "shin wane azzzalumin sarki ne
ake kiran shi da suna Uhaisu?
Koda jin wannan tambaya daga bakin Najwas sai fuskar Mazabir ta murtuke tamkar an aiko
mashi da WASIƘAR MUTUWA, ya dubi Najwas ya ce "ya shugabana ai wannan sarki da ka
ambata babban abokin gabar mu ne, babu aminci ko yarda tsakanin mu da shi face yaƙi''.
Da jin wannan batu sai Najwas ya kwashe labarin da yarinya Lazimat ta ba su, da kuma
abin da ya faru da su a fadar sarki Uhaisu lokacin da suka ceto su jaruma Nabihat tun daga
farko har ƙarshe ya zayyanewa Mazabir.
Sa'adda Mazabir ya ji wannan batu daga bakin Najwas sai ya cika da matuƙar mamaki ya
yi ajiyar zuciya ya ce "ya shugabana haƙiƙa ka zo mani da labarin da muka daɗe muna jira,
wato hanyar da zamu bi wajen ɗaukar fansa akan sarki Uhaisu.
Ya shugabana tun da dai yanzu babban burin ku shine kawar da sarki Uhaisu, tabbas zama bai
same mu yanzu zan haɗa dakarun yaƙi domin kai FARMAKIN BAZATO izuwa kurkukun Uhaisu
domin mu ceto sauran fursunoni 'yan uwan su Nabihat.
Za mu bar yarinya Lazimat da 'yan uwanta biyu su kula da lafiyar ta, sauran dakarun mu za su
yi gadin su, ka sani cewa babu abin da zai same ta a wannan daji.
Koda kuwa dakarun sarki Uhaisu ne domin akwai iyaka tsakanin mu dasu, haƙiƙa na san duk
wata hanya da za mubi wajen shiga kurkukun ba tare da mun sha wata wahala ba, da zarar sun
ceto fursunonin, sai kuma mu fara shirin yaƙi domin kuwa dole ne sarki Uhaisu ya kawo mana
FARMAKIN BAZATO''. Sa'adda Najwas ya ji wannan batu daga bakin Mazabir sai Najwas ya cika da matuƙar
farin ciki maral-musaltuwa.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba Najwas ya juya ya shige izuwa cikin wannan ɗaki na
su, shi kuwa Mazabir sai ya ƙwallawa wani badakare kira mai suna Hidairu.
Hidairu ya bayyana a gare shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa, Mazabir ya
dube shi ya ce "ya kai Hidairu ayi maza a shirya mana dakarun yaƙi mutum dubu biyar domin
zamu kai wata mamayar bazato";
Koda jin wannan umarni sai barde Hidairu ya ce "an gama ya shugabana". Yana
gama faɗin hakan ya miƙe tsaye zumbur ya ruga izuwa wani ɓangare a dajin, jim kaɗan sai ga
shi ya dawo tare da waɗansu ZARATAN MAYAƘA shirye cikin gagarumar shigar yaƙi
hannayensu riƙe da miyagun makamai suna zaune a bisa dawakai fusakunsu rufe ruf da
hulunan ƙarfe.
A dai-dai wannan lokaci ne mafarauci Najwas tare da matarshi Kilimat, jaruma Nabihat
da mutum uku daga cikin waɗannan 'yan matan fursunonin shirye cikin shigar yaƙi mai matuƙar
kwarjini da ban tsoro suka durfafo wajen.
Koda ganin hakan sai wani barde dake tsaye a can gefe guda hannunshi riƙe da takobi,
ya janyo wani ingarmar doki ya kawowa su Najwas da Mazabir suka kama suka haye.
Cikin hanzari Najwas da Mazabir suka sakarwa dawakansu linzami suka shige gaba,
Kilimat, jaruma Nabihat da 'yan mata uku suka mara masu baya dakaru a ƙarshe, aka fara tsala
azababban gudu na keta sa'a ana ratsa duhuwar bishiyu gami da ƙoramu da kwazazzabai.
Da yake a wannan lokaci dare ya tsala akwai matuƙar duhu, sai wa su daga cikin dakarun suka
kunna fitilar ice suka riƙe a hannayensu.
Lokacin da aka iso wani waje mai tattare da waɗansu duwatsu 'yan madaidaita sai Mazabir ya
ja linzamin dokinshi ya tsaya ya kama ya sakko ƙasa, take kowa ya yi koyi da shi aka tsayar da
tafiya.
Mazabir ya tsugunna ƙasa ya sanya hannayenshi ya ɗauke waɗansu duwatsu dake wajen ya
shiga kwashe ƙasar