Showing 6001 words to 9000 words out of 18096 words

Chapter 3 - FATAUCIN BAYI Book Complete Book Written by Mansur Usman Sufi .pdf

05 Aug 2025

558

da sarki Uhaisu a tsaye tsam! fuskarshi a murtuke babu annuri tamkar
an watsa mashi garwashin wuta a kan ta, kuma idanuwanshi sun kaɗa sunyi jajur.
Sai suka yi turus! Kowa ya kasa isa izuwa inda yake,
cikin matuƙar fushi sarki Uhaisu ya ƙwallawa wani badakare kira mai suna Hushaibu.
Kafin ya gama rufe bakinshi Hushaibu ya bayyana a gare shi ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa
jikinshi na ƙyarma saboda tsananin tsoro.
Cikin matuƙar fushi sarki Uhaisu ya dakawa kuyangin dake yi mashi hidima tsawa da su fice
daga cikin lambu, sannan ya mayar da uban shi ga Hushaibu cikin kakkausar murya ya sune
shi ya ce "ya kai Hushaibu ka yi sani cewa bakomai ne ya sanya na kira ka nan ba sai domin
ina son ka hanzarta kira min sadauki Yasiran''. Muryar Hushaibu na rawa ya ce "An gama ya shugabana, yana gama faɗin hakan sai ya
miƙe tsaye ya fice daga cikin lambun da sauri.
Jim kaɗan sai ga Yesiran ya bayyana gareshi, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya
kasance SADAUKIN SADAUKAI, mai tarwatsa maza a filin daga.
Sarki ya dubi Yesiran ya ce "ya kai Yasiran ka yi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin
ina so ka tafi izuwa wani birni dake iyaka da tekun Baharul-sawara, ana kiran birnin da suna
DARUL-IMFAL
ina so gaba daya mazajen birnin su zamo matattu, sannan ka kawo min matayensu da
dukiyoyin su cikin ƙoshin lafiya,
sai dai ina son kayi sani cewa kuɓucewar ɗaya daga fursunonin dai-dai yake da rasa rayuwar
ka baki ɗaya''.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Uhaisu sai Yesiran ya ce "ya shugabana ai
wannan aiki abu mai sauƙi a gare ni tamkar kurɓar ruwa, na rantse da ƙarfi mulkin ka sai na
kawo maka matayen birnin DARUL-IMFAL cikin ƙoshin lafiya'';
Koda jin wannan batu daga bakin Yesiran sai Uhaisu ya cika da matuƙar farin ciki
maral-musaltuwa.
Kafin sarki Uhaisu ya sake furta wani abu Yesiran ya miƙe tsaye zumbur ya fice daga lambun.
Kamar yadda sadauki Yesiran ya yiwa sarki Sarki Uhaisu alƙawari haka al'amarin ya
kasance, a in da yana fita ya ɗebi dakarun yaƙi guda dubu hamsin, suka durfafi hanyar da za ta
sada su da birnin DARUL-IMFAL bisa wani makeken jiragen ruwa.
Da la'asar sakaliya, sadauki Yesiran da rundunar mayaƙanshi, suka iso gaɓar tekun
Baharul-sawara sakamakon hango kofar birnin DARUL-IMFAL da su kayi.
A wannan lokaci jama'ar birnin DARUL-IMFAL na gudanar da ayyukan su na yau da
kullum cikin walwala da jin daɗi, hakan ya faru ne sakamakon saukar ruwan sama a daren jiya.
Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ji ihu da kururuwar dakaru masu tsaron ƙofar
gari, kafin ka ce me, gari ya hargitse da guje-gujen jama'a gami da ifice-ifice, yara da manya
mata da maza,
Nan take dakarun sadauki Yesiran suka afkawa jama'ar birnin da masifaffan yaƙi, nan fa mazaje
suka dunga yin MUTUWAR JARUMTA, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, ƙarar karafniyar
ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje gami da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne.

Kaico! Haƙiƙa yaƙi abin tausayi ne in da a ce mutum zai ga yadda dakarun Yesiran ke
hallaka mazajen birnin ba ji ba gani, dole ne ya zubar da hawayen tausayi domin hatta ƙananan
yara maza kashewa suke yi, koda kuwa jariri ne sabuwar haihuwa ba su ƙyale ba.
Kasancewar masu iya magana na cewa SARKIN YAWA yafi SARKIN KARFI sai ya
zamana dakarun Yesiran sun kashe gaba ɗaya mazajen birni ɗayan su bai tsira da rayuwar shi
ba. Nan fa ƙananan yara da mata suka dunga rusa kuka mai matuƙar ban tausayi da narkar da
zuciya, wasu na kuka ne bisa rasa mazajensu, wasu 'ya'yensu, wasu 'yan uwansu. Bayan sadauki Yasiran ya kashe sarkin dake mulkin birnin wani dattijo mai suna Sha'aran
sai ya yi umarni aka kwashe baki ɗaya dukiyar dake birnin, aka sanya matayen birnin da suka
rage a raye sasari na baƙin karfe, bayan an fice daga birnin sai waɗansu dakaru suka bankawa
gidadanjiin birnin wuta, take aka nufi gaɓar teku aka sanya ɗora dukkanin jama'ar a bisa
wannan makeken jirgin ruwa.
Lokacin da aka ɗora su jama'ar a bisa jirgin ruwan suka hango yadda birninsu ke ci da
wuta, kuma an mayar da da yawa daga cikin su zaurawan yara kuwa sun zamo marayu.
Sai suka fashe da matsanancin kukan takaici da baƙin ciki.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba sadauki Yesiran ya yi umarni aka tuƙa jirgin ruwan a aka
cigaba da tafiya zuciyarshi cike da matuƙar farin ciki da samun wannan nasara.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya sarki Uhaisu ya farauto su jaruma Nabihat daga birnin
DARUL-IMFAL dake iyaka da tekun Baharul-sawara.


BABI NA UKU


Al'amarin shugaba Yesiran kuwa, lokacin da ya gabatar da su Nabihat da sauran jama'ar
birninsu gami da dukiyar ganima a gaban sarki Uhaisu sai sarki ya dube shi a lokacin da yake
durƙushe a gaban shi ya buɗi baki cikin alfahari da BAƘAR IZZA ya ce
''ya kai Yesiran haƙiƙa kayi aiki mai kyau yadda na buƙata saboda ina mai tabbatar maka da
cewa zaka samu gwaggwaɓan kaso daga cikin ganimar dukiyar da aka farauto. Yanzu abin da
nake ya kamata ayi shine a tafi da dukkanin fursunonin izuwa kurkuku a ajiye su a ɓangaren
BAUTAR MUTUWA". Koda yarima Zafiyar da ya kafa idanuwanshi akan jarumai jaruma Nabihat dake cikin halin
suma, ya ji wannan batu daga bakin mahaifinshi sai ya yi caraf ya tari numfashin shi ya ce "ya
abbana ina neman alfarma a gare ka da abar fursunonin a hannuna har izuwa lokacin da za'a
yanke hukunci akan su." Da jin wannan batu daga bakin yarima sai sarki ya juya ya dube shi yana mai fahimtar wani abu
akan fuskarshi, sannan ya yi tattaunawar murmushi a gare shi ya ce "ya abin alfaharina kuma
muradin zuciyata kayi sani cewa babu wani abu da zaka nema a gare ni face na baka shi koda
kuwa raina ne, amma akwai buƙatar ka ba ni lokaci na yi nazari, domin bisa binciken da na
gudanar ya tabbatar min da cewa a cikin jama'ar za a samu wanda zai kawo ƙarshen mulki na".
Sa'adda yarima ya ji wannan batu daga bakin sarki sai ya gyaɗa kai cikin alamun matuƙar
damuwa, domin wannanne karo na farko a rayuwarshi da ya ji ya kamu da matuƙar tausayin
bayin da mahaifinshi ke farautowa.

Koda gama wannan tattaunawa sai shugaba Yesiran ya huce kai tsaye izuwa hanyar da za
ta sada su da kurkukun birnin, koda isowar su sai masu gadin suka wangame makekiyar ƙofar
shiga, suna masu risinawa ga shugaba a gare shi.
Daga ciki kurkukun ya kasance tafkeke tamkar gari guda, katangun shi sun kasance masu
matuƙar tsawo da aka yi su da zallar duwatsun wuta masu ƙwarin gaske.
Duk inda mutum ya kai duban shi a ciki bayi ne maza da mata, yara da manya na ta
gudanar da ayyukan bauta nau'i daban-daban, waɗansu na aikin farfasa duwatsun wuta da
manyan gudumun ƙarfe, wasu na ɗinka kayan adon dawakai da tufafin sarauta.
Koda shigowar shugaba Yesiran cikin kurkukun sai gaba ɗaya bayin su ka dunga a jiye
aiyukan su suna zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa a gare shi, cikin hanzari shugaban dake
kula da kurkukun ya karɓi su jaruma Nabihat ya yi umarni aka rarraba jama'ar su a cikin
waɗansu ɗakunan na musamman. Koda jama'ar dake wajen suka ga cewa an shigar da su jaruma Nabihat izuwa ɓangaren
da ake yiwa laƙabi da BAUTAR MUTUWA, sai suka cika da matuƙar tausayin su. Domin kuwa
duk wanda aka shiga da shi izuwa ɗakin BAUTAR MUTUWA baya fitowa a raye sai daigawar
shi. Sa'adda jama'ar su Nabihat suka tsinci kansu a cikin ɗakunan sai suka fashe da kukan
baƙin ciki mai matuƙar tsuma zuciya.
Wannan shine abin da ya faru da su Jaruma Nabihat ya yin da aka isa da su izuwa
kurkuku.

Al'amarin wannan yarinya fursuna da ta fafata yaƙi da shugaba Yesiran a ƙarƙashin tekun
Baharul-sawara kuwa, bayan ta samu nasarar datse nashi hannunshi ɗaya, shi kuma ya samu
nasarar yi mata miyagun raunuka, ɗaya a gadon bayanta na biyu a cinya na ukun kuwa a
damtsen ta na hagu. Saboda yawan jinin dake zuba a jikinta take numfashinshi ya ɗauke, kuma ta taso izuwa saman
tekun igiyar ruwa ta cigaba da tafiya da ita, har ta kawo ta izuwa gaɓar tekun ta ɓangaren
yamma maso kudu.
A dai-dai wannan lokaci ne wani mafarauci da matarshi suka nufo gaɓar tekun ɗauke da
bahon ɗibar ruwa.
Sa'adda suka yi arba da ita kwance babu alamun rai a tare da ita ga manyan raunika a jikinta
sai suka yi turus! cikin kaɗuwa suka matsa inda take.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba suka ajiye bahon ruwan dake hannunsu, mafaraucin ya
ɗauki yarinyar ya saɓa ta a kafaɗarshi.
Cikin hanzari suka juya suka durfafi hanyar da zata sada su da dajin da suka fito.
Tafiyar daƙiƙa latalin kacal suka yi suka iso wani gida a dajin. Gidan an gina shi ne da zallar
duwatsun wuta, kai tsaye suka kunna kai izuwa gidan.
Daga ciki gidan ya kasance mai kyawun tsari yana ɗauke da ɗakuna guda biyu da makewayi
ɗaya sai wani madaidaicin fili da aka kafa turken dabbobi wata saniya guda ɗaya fara sol tana
cin ciyawa a cikin wani bawon kaba.
Cikin hanzari matar mafaraucin ta shimfiɗe yarinya Lazimat a bisa wani madaidaicin
gado da aka yi shi da zallar itace aka shimfiɗe shi da kilishi mai taushi, bayan ta kwantar da ita
sai ta shiga danna ƙirjinta cikin matuƙar tashin hankali.

Shi kuwa mafaraucin sai ya fice daga ɗakin, jim kaɗan sai ga shi ya dawo ɗauke da
tafashasshen ruwan zafi gami da tacecciyar madarar shanu, a ɗayan hannunshi kuwa yana
ɗauke da wata jakar fata, kawai sai ya shiga ɗauko waɗansu magunguna a cikin jakar ya na
haɗa su a cikin wani akushi mai ɗauke da ruwa. Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya Lazimat bata farfaɗo daga dogon suman da tayi ba.
Sai daga bisani ne ta buɗe idanuwanta tana mai jan gwaron numfashi, nan fa suka cika da
matuƙar farin ciki bisa ginin farfaɗowarta, ba tare da wani ɓata lokaci ba matar ta shiga sanya
mata magani a raunikan ta.
Bayan ta kammala ne sai ta tashe ta zaune ta shiga bata wannan madarar shanu a baki tana
kurɓa, sai da tasha ta ƙoshi sannan ta bata waɗannan magunguna da maigidanta ya haɗa a
cikin wannan akushi.
Kana daga bisani mafaraucin ya dubi matarshi fuskarshi cike da annuri gami da tsantsar so
da kauna ya ce "ya uwar 'ya'yana ina mai ba Ni farin ciki, kiyi sani cewa ina ji a jikina wannan
yarinya da muka tsinta za ta maye mana gurbin da raɗaɗin 'yarmu da muka rasa.
Kuma na ji a jikina cewa za ta zamto silar da zamu ɗauki fansa akan sarki Uhaisu".
Koda jin wannan batu daga bakin mai gidannata sai ta cika da matuƙar farin ciki ta ce
"maganar ka haƙƙun ya abin bege na tabbas alamun nasara sun fara bayyana a gare mu";
Mafaraucin ya ce "yanzu zan ɗan shiga izuwa daji, domin na farauto mana abin da zamu yi
kalaci sai ki kula da ita har naje na dawo".
Yana gama faɗin hakan sai kawai ya miƙe tsaye ya fice daga ɗakin ya na mai waigen
matarshi suna jifan juna da tsantsar so da ƙauna, yana fita ya sake kunna kai izuwa cikin daji .
Jim kaɗan bayan shuɗewar waɗansu daƙiƙu matar mafaraucin na zaune a gaban Lazimat ta
ƙura mata idanu sai kawai ta jiyo ƙarar takun sawaye gami da gurnani mai matuƙar ban tsoro,
ya cika dajin baki ɗaya.
Koda jin hakan sai kawai ta ɗauko wata takobi a gefen gadonta ta miƙe tsaye zumbur
ta ruga izuwa ƙofar gidan, ai kuwa tana fita sai tayi arba da waɗansu irin ayarin gabza-gabzan
birrai su kimanin guda ɗari biyu.
Birran sun kasance masu matuƙar tsawo, girma, kwarjini gami da muni, a hannayensu na ɗauke
da wani irin sungumi mai waɗansu irin tsinika a jikin shi tamkar zarto,
Wannan shi ne abin da ya faru da mafarauci da matarshi da suka tsinci yarinya Lazimat.
Kallo ne ya wakana tsakanin kilimat matar wannan mafarauci da ayarin gwaggwan birran na
ɗan wani lokaci.
Daga can sai birran su kayi wani mahaukacin gurnani mai matuƙar ban tsoro mai ɗimauta
duk wata halitta numfashi, bishiyu suka dunga rangaji suna karairayewa suna faɗuwa kasa.
Wani daga cikin birran wanda alama shi ne shugaban su ya daka masu wata tsawa dake nuna
cewa su afkawa matar, ai kuwa sai su ka yi ɗauki kanta suna masu daga makamansu suna ihu
da kururuwa mai firgitarwa.
Shi kuwa shugaban birran sai ya samu wani ɗan faffaɗan dutse ya zauna a a kai yana
mai harɗe kafafuwanshi yana mai zuba idanu domin ya ga yadda artabun zai wakana.
Koda ganin hakan sai uwar gidan mafaraucin ta ɗaga takobinta sama sannan ta ruga izuwa kan
birran tana ihu da kururuwa mai firgitarwa ta far masu da sara da suka, su kuwa suka shiga kai
mata duka da bugu da sungumin su cikin wani irin zafin nama, duk sa'adda takobinta ta sari
jikkunan birran sai ta ji kamar dutse ta sara domin ko gezau ba su yi

Al'amarin da ya yi matuƙar dugunzuma hankalin ta kenan, yazamana ta canza salon
fadan ta a in da ta dunga saran su gami amfani da hannunta ɗayan tana gabza masu naushi da
bugu da dukkan ƙarfin ta.
Gaskiyar masu iya magana da suka ce "Idan kiɗa ya canja dole ne rawa ma ta canja, nan fa ya
zamana cewa ta fara samun galaba akan birran, domin duk wanda ta gabza masu naushin sai
ka ji ya tsandara ihu ya ya faɗi ƙasa yif!.
Koda ta fahimci cewa ƘARFIN DAMTSE ya fi tasiri akan su sai kawai ta yi jifa da takobinta ta
shiga amfani da hannayenta duka biyun gami da kafafu wajen kai farmaki. Duk in da ta sanya a
gaba sai dai kaga gawarwakin birran na zube kasa matattu.
Wohoho! Tabbas ƙarfi da jarumtaka ba a siyan su da kuɗi face baiwa daga Allah,
Komai tsakanin hassadar mutum idan ya ga yadda kilimat ke ragargazar birran dole ne ya
jinjina mata ya san cewa ta ciri tuta a cikin jerin manyan JARUMAN DUNIYA.
Nan fa kururuwa gami da hargagin su ya cika dajin baki ɗaya, jini ya dunga tsartuwa
yana kwaranya a kasa, haƙiƙa waɗannan birrai suna ganin tashin hankalin da basu taɓa ganin
irin shi ba.
Domin ta zame mssu alaƙaƙai, kuma ƙadangaren bakin tulu, cikin abin da bai gaza daƙiƙa ɗari
biyu ba ta kashe fiye da kaso biyu bisa uku na birran.
Sa'adda shugaban birran ya ga irin muguwar ɓarnar da matar mafaraucin ke yi mashi sai
ya cika da matuƙar mamaki kuma ya fusata ainun, domin fiye da shekaru ashirin suna zaune a
wannan daji ba su taɓa ganin bil'adama da ya yi masu hasara kamar haka ba.
Nan take zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone, kawai sai ya taƙarƙare ya kurma
wawan ihu da sanya bishiyu suka dunga ƙarye suna faɗuwa ƙasa, duwatsu suna karo da juna
su na yin bindiga,
kawai sai sauran birran da ke yaƙin suka zubar da makaman su suka ruga izuwa bayan bishiyu
su ka ɓuya
A lokaci guda shugaban ya tsuke bakinshi sannan ya dako wawan tsalle daga inda yake
zaune ya durfafi inda take, ya yin da ya isa gare ta nan take ta zamto 'yar mitsitsiya tamkar an
ajiye ɓera a gaban giwa, saboda matuƙar tsawo da girman shi.
Kafin ta yi wani yunƙuri shugaban ya shammace ta ya gabza mata wawan naushi a fuska da
hannunshi ɗaya.
Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da tayi katantanwa a sama sau uku sannan ta faɗo
ƙasa tim! A matuƙar galabai ce,
cikin ƙarfin hali ta yunƙura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login