Showing 1 words to 3000 words out of 31306 words
*í ½í°„WALIJAAMí ½í°„*
_Maman teddyí ¾í·¸_
_page 1_2_
_Da sunan allah mai rahma mai jink'ai" dukkan godiya ya tabbata ga allah uban gijin talikai Allah
ina rokan ka yanda na fara wannan littafi lafiya allah kabani ikon kammala shi lafiya ameen ._
_*Wannan littafin tun daga farkon shi har karshen WALIJAAM sadaukar ne ga dukanin
fulanií ½í°„*_
Alheri writers asso.í ½í³š
******
"Wani irin iska ne yake tashi daga sararin samaniya ,wanda in badon yanayin da ake ciki na
Rani ba da tabbas ka alamta cewa wannan goguwar ruwan sama ne yake dab da tsinkewa.
Wata yar budurwan bafullatana ce na hango wacce a shekaru bazata haura 13 ba tana sanye
da kayan ta na sak'i ,da ka gane ta kaga bafullatana ta usul ,sanye take da kayan fulani farar
sake da akayi masa ado da blue din abawa hannun ta dauke da dan madaidaicin sanda ,wanda
yayi dai dai da tsawon wannan yarinyar bafullatanan .
Gyefe guda ta juya da idanun ta tana mai bin shanayen ta da kallo , wanda suke garke guda
,don yawon su ya 6aci dai dai yawon garken shanaye amma duka ita ce mai kula dasu a
wannan asararen dajin . Babu kowa daga ita sai dabbobinta . Ganin irin goguwar da sanyayyar
iskan dake kadawa ne yasa ta bin sararin samaniya da kallo tana kallon yanayin faduwar rana
,wanda ganin yanayin sanyin da rana yayi yasa ta fahimtar cewa lokacin komawan ta Rugar su
tayi .
Nufar shanayen tayi hadi da masu magana ta harshen fulani hadi da fara kadasu da sandar ta
,su kuma shanayen suna yin gaba tana mai biye a bayansu a haka har suka fara ficewa daga
wannan dajin .
Tafiya ce sukayi ta mai tsawo kamin su fara shiga cikin rugar su ta Surbajo . Nan na fara hango
bukka dai_dai bakaman bukkan sauran rugar fulani ba , don idan ka wuce bukka daya sao kayi
dan dogon tafiya kamin ka kara saduwa da wani bukkan .
Nikam Maman teddy nace rugar SURBAJO kenan , rugar surbajo ya samu wannan suna ne
daga wurin Makotan wannan ruga ,wanda yawon yammatan wannan ruga yasa ake kirar su da
sunan Rugar surbajo . Yara tun suna da kankantan shekaru basa wuce shekara 7 ko 8 ake
aurar dasu ,sai idan sun yi girma akai su dakunan maxajen su ,bikin al'adar su kadai sukeyi
masu wato shad'i.
Hakan yasa wannan ruga da akwai yara kanana sosai ga yammata ,amma ko wacce ka gani
da Auren ta ,idan kuma babu karama ce wadda bata shekara shida ba tom da akwai wanda
yake rikon ta . A takaice dai duk yarinyar da ka gani indai takai shekara 8 tom tana da miji a
wannan ruga .
Rugar surbajo rugace da ta tara fulani ,wanda ba mazauna ba ,idan suka tafi kiwon cirani sai
sufi shekara goma biyar basu waiwayo rigar surbajo ba . Idan kaga Budurwa ta waiwayo rugar
surbajo tarewan tane yayi daga nan sao ayi bikin shadi a kaiki Garken mijinki .
Duk wacce baayi bikin tarewar taba to tana tafiya yawon cirani wato kiwo da shanayen ta amma
su yammatan da suke da Aure shekara daya ce sukeyi wasu ma basa kaiwa suke dawowa
rugar su ,a gansu suna yan kwanaki suke kara komawa...wannan dai shine kadan daga cikin
Al'adan wannan Ruga . Bari mucigaba da labari WALIJAAM ,komai xamuji daga gaba .
Wannan yarinyan Bafullatanan ce duk wani bukka da zata wuce sai ta tsaya da garken ta ta
masu gaisuwa da cewa Ifini jaam kamin ta wuce ,a takaice dai kamin ta isa bukkan su sai da
tadan kara tafiya mai tsawo ,amma ahaka kowa ta gani tsakanin ta dashi Ifini jaam , wanda
kowa cike da fara'a yake ambaton sunan yarinyar da SHATTU , hakan ne ya tabbatar mun da
cewa Wannan ruga ,ruga ce mai hadin kai toh kun kuma san fulani badai hadin kai ba .
Garken ta nufi da shanayen tana kaisu masaukin su ,kamin ta nufi bukkan Mahaifiyarta da ta
tadda bata nan a wajen bukkan .
Bukkan ta kutsa kanta hadi da dan dukawa kadan sannan ta shiga daga ciki ,bata tadda
Oumman nata ba ne hakan ya tabbatar mata da cewan Oumman tata tayi nisa ,komawa tayi
tana rage kayan jikin ta kallabin dake saman kanta hadi da sauke nishin gajiya kamin ta zauna
saman tabarman kaban dake bukkan tana magana ita kadai da cewa " _Aradu hande miwadi
kugal misomi"._
_( wlh yau nayi aiki nagaji ) ._
Hannun ta takai tana jawo kwaryar da tasha nono ta rage na safe kamin ta fita kiwo ,tana fara
sha hankalin ta kwance hadi da lissafin kwanakin da ya rage mata ta tafi ciranin kiwon su da
suka saba .da kuma dogon zongon da suke dauka ,duk da a wannan Karon Shatun ita kadai ce
xata tafi ba tare da Oumman nata ba .
" Ni uwar teddy na shirya tsaf don kayatar daku a dadadan littafina mai suna a sama kar ku bari
ayi baku...wannan dandano ne daga cikin wannan littafin nawa ta Walijaam ,yanayin sharhin ku
comment yanayin yanda xana rinka yin update í ½í±Œ .
********
Zaune na hangota a gaban mirrow dake makale a bangon dakin nata ,wanda ya kasance ciki
daya ne . Amma kayatuwar dakin ba'a mgn ,ka rantse da Allah dakin wata sabuwar Amarya ce
".
Fatima!!
Naji ankirawo sunan wannan budurwan da ashekaru baxata haura 24 ba a haihuwa . Ba tare da
ta amsa kirar ba ne naga ta cigaba da bin la66an ta da lipstick tana jagayewa hadi da gyara
zaman Zak'o_zak'on Eye lashes din idon ta .
Bin ta da kallo nake hadi da kare mata kallo sosai ,a takaice dai Ita din ba tsayine da ita ba can
gajera ce ,amma batayi kasa sosai ba . Sanye take cikin damammun english wear riga da
wando wanda suka dameta matuka na kuma kurewa . Komai na surar jikin ta a bayya ne suke .
Saman kanta kuwa gashin kari ne wato atachment mai dauke da kalon kayan jikin ta Wato light
pink . Glass ta daura a saman fuskan ta mai dauke da colourn pink wanda girman shi ya
mamaye rabin fuskan ta . Takalmi ta saka cover sai daga gaba ya bude blue wannan kuma
kalon jeans din wandon jikin ta ne wato blue . Karamar jakarta ta dauka da wayar ta kirar iphone
tana taunan swingum ta fito daga dakin nata .
Wani irin girgixa nayi da ganin irin gidan da wannan diya take ,dakin nata ka rantse da Allah a
gidan wani hamshakin yake ,amma dana fito wajen dakin na biyo bayan ta sai nagan ni a filin
tsakar gidan su . Da flour din arxiki babu .
Wata dattijuwar mata ce naga ta fito tana kare maawa diyar nata kallo ,hadi da dan girgixa kai
wanda da kagani kasan shigar ta bai mata ba . Fatima tom gyara mayafin don Allah ,ina kirar ki
baki amsa mun ba sai da kika gama abun da kikeyi sannan zaki fito .
Ba tare da tayi duba ga mahaifiyar nata ba ,wanda take ta sharce gumin itacen da suke bata
wahala don fitowan ta kenan daga madafi .
Takawa Fatima tafara hadi da nufar hanyar da zai sada ta da zauren gidan nasu kamin tace "
Mama sauri nakeyi yanxu inaso na leka gidan Hjy Dr Haulah . Tana fadi mata hakan tayi ficewar
ta da sauri hadi da wani irin tafiya wanda Maman nata kawai girgixa kai tayi ,a zuciyarta tana
cewa" tabbas da'alama sojan gidan ne ya dawo ,sai ta kuma ta6e baki hadi da cewa a sarari
iska na wahalar da mai kayan kara .
Inbanda hauka irin naki Fatima inake ina wannan yaro ???. Ai komai yanxu wannan yaron kirkin
me xaiyi dake fatima? Ai... Haba Mama wai me kika dauke mune? . Wani irin mgn ce wannan
shi Umar Farouq din ba mutum bane ,kodon yana soja kuma Mahafin shi shine Jurnalist Bashir
Mahafiyar shi Hjiya Dr Haula?? Shikenan sai kice fatee batakai matsayin da zai kaunace taba ?
Yanda fah kk kallon mu a gida a waje ba haka muke ba . Asma'u ce ta katse mahaifiyar tasu da
sam basa ganin kimarta da girman ta idon su na duniya da kwadayin abun dake cikin ta .
Cigaba da cewa tayi kene kk mawa Liftanal yake ko major ne Umar farouq dai na gidan nake
magana ke kike masa kallon mutumin kirki ,amma fasadin da yake a bayan kasa walh gomma
wani mazinacin dashi don bambancin su kadan ne! . Kawai don mahaifin sa ne da ya zama mai
zafi da jajircewa akan Omar wlh da mazinaci yafishi tafka abun arxiki .
Subhanallahi!!
Futucin da ya fito daga bakin Mama kenan ta fadi da sauri jin irin wannan kalamina Asma'u .
Wannan wacce irin mgna ce Asma'u?. Toh wlh ni koya ma dai yake wannan yaron yafi mun ku
,tun da har yanada wanda yake tsawatar masa ya tsawatu ba irin ku ba yan kanku ...Kullum dai
ina maku fatan shiriya mtswww mama ta karke maganan tana mai jan dogon tsaki hadi da wuce
Asma'au da ta kasance Yaya ce Wurin fatima .
Ta6e baki Asma'u tayi ba tare da ta damu da damuwar mahaifiyar nata ba sai ma cewa tayi
",tom idan bamuyi gayu mun fita ba ,so kk mu zauna kullum bamu da abun ci sai tuwo ??
Tuwon bama ta masara ba aa ta dawa?? Ina ?! Wlh ni har kunyar kawo samari na nake
wannan gidan jar kasan ,duk yanda nake flexcing wai azo ace nan ne gidan mahaifina ai abun
da kunya ina xan iya ,shiyasa muke haduwa a waje baazo ba bare ma wannan gida yakorar
mun Alhjazai da samari . Gwamma mu fita mu saka sutura cikin rufin asiri a cigabada mana
kallon silent ajebourters...
********
A hankali Shattu ta dago ido tana kallon mahaifiyar nata kamin cike da damuwan tafiyar da
zatayi ta bar umman nata ta ce" Oumma kinsan gobe xan tafi kiwo xanyi tafiya mai tsawo kamin
na dawo rugar surbajo ,ina bukatan addu'ar ki ,kin san da Yagwalgwal xamu tafi......
Tom Shattu allah yakaiku inda xaku lfy ,ku dawo lfy a kullum addu'a na kenan gareki ,sai dai
banason kiyi dadewa kar ki wuce Watanni bakwai baki dawo ba duk inda ko xaki je .
Murmushi shattun tayi wanda har sai da gyefe da gyefen kuncinta suka lo6a kamin tace tom
Oumma inshaallh baxan wuce ba.
"Yowa diyar Albarka Allah yy mawa rayuwar ki Albarka ya karemun ke daga dukkan wani sharri
Amin".
" Oumma ina Abba yake yakamata muyi sallama kamin mu tafi rabona da ganin shi tun jiya...
Ai kin san yana can rumfar da yake sana'ar aa .
A hankali Shattun ta mike daga tsaye hadi da cewa "Umma bari na leka rumfar Abba na gaida
shi ba lalalli mu hadu ba gobe ,bari na tafi yanxu nasan mutane sunyi masa sauki yanxu.
Abunka ga fulani da kuma ita Shattun da take ganin ita din yarinya ce karama a haka ba mayafi
daga ita sai sandarta da yake wurin ta tun yarinta kafanta babu ko takalmi ta bar garken nasu
don nufar inda Mahaifin nata ke Bada magani . Don Mahaifin ta wato Malam Bukar Shaharren
malami ne a wannan ruga tasu ,sosai yake bada taimakon maganin sa ta gargajiya ,yana bada
magani ta fanni dabam dabam ...shiyasa mutane ta koina suke zuwa wannan ruga ta Surbajo .
Kullum baka ganin sa ba tare da jaama'a ba .
Itakan ta Shattun sai tayi kwana biyu uku basu hadu ba!!
Tom mu tare a page na gaba na WALIJAAM.
_*Masoyan taurari uku nasan tambayoyin dake tare daku duka , mun dakata da yin taurari sai a
zongo na gaba zuwa march haka ,nima naso na dakata da wannan littafi nawa ta WALIJAAM
,tom amma duba ga masoyan labarin da kuma korafin ku akan cewa nayi maku saboda wasun
ku da suka fara biyan wannan labari nawa , hakan yasani kar6ar korafi akan xan saki wannan
littafi nawa ,a taurari na gaba zan sakar maku da sabon littafina wanda shima nasan xaku so shi
kaman yanda kuka nuna kaunar ku a wannan littafin WALIJAAM...*_
_Tom bari na dakata haka na fada maku hanyar da zaku biya kudin littafin WALIJAAM ,don
nasan shine tambayar ku ._
_Littafin walijaam idan kina bukatar turo da kudin shi..._
_NORMAL GROUP 200_
_VIP PAYMENT 500_
Ga masu bukatar biyan wannan littafi Zaku na iya mgn ta wannan whatsap link din í ½í±‡í ¼í¿»
https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1
Yan nijer zaku iya tura katin Airtel ta wannan number í ½í±‡í ¼í¿»
+22797780373
*Ina godiya gareku masoyana sosai naji dadin kaunar da kuke kan nuna mun a wannan littafi na
WALIJAAMí ½í°„*
*í ½í°„WALIJAAMí ½í°„*
_Maman teddyí ¾í·¸_
_Page 3_4_
_"Da sunan Allah mai rahama mai jinkai ,dukan godiya ya tabbata ga Allah ubangijin talikai
,Allah yanda na fara wannan littafi na WALIJAAM lfy ,allah ka bani iko kammala shi lafiya
Ameen ._
*Wannan littafi tun daga farkon shi har karshen WALIJAAM Sadaukarwa ne ga duk kan
fulanií ½í°„*
*ALHERI WRITERS ASSO.í ½í³š*
_Masu bukatar sayan wannan littafin WALIJAAM zasu na iya magana da marubuciyar ta
whatsap link din nan_
https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1
" Cikin Rugar tasu Shattu ta fara nufa don isa garken da Mahaifin nata yake don tayi masa
sallama na tafiyar su safiyar gobe". Tun daga nesa ta hango rumfar Abban nata damkam da
nutane ,hakan yasata juyawa da sauri tana nufar can nesa inda Babu mai hangota ,abunka ga
kunya ta fulani . Bazata iya kutsa kanta wurun wannan mutane ba! " miyiddima Shattu surbajo". Jin muryar wanda batayi tsammani ne ba yasata lumshe idon tayi
tana sakin masa sanyayyar murmushi ba tare da ta juyo ta kalle shi ba ,don tabbas ta shaida
shi ko bata gansa ba ,wannan sunan kadai da yasaba ce mata a ko yaushe ya wadatar da ita .
Murmushi ta kuma saki wanda sai da gyefe da gyefe na kuncin ta ya lo6a kamin cike da
sanyayyar muryar ta a hankali tace masa " miyidda kayejo Hard'o '
". Murmushi wannan bafullacen yayi hadi da takowa zuwa inda Shattun take har a lokacin idon
ta a lumshe yake taki budesu ,wai ala dole kunya takeji .
Da gaske kikeyi shattu?? Bude idon ki ki fadi mun gsky kina sona kina kuma son na zama miji a
gareki??.
Murmushi tayi a wannan karon taffan hannun ta tasa tana rufe fuskar nata baki d'aya tana
darawa siririn hushiryar ta sao da ya bayyana .
Ina jinki surbajo ". Hard'o ne yayi maganan yana mai juyo da fuskar shi inda Shattun take. Daga
masa kai tayi ,wanda hakan yasa Hardo sakin dariyar farin ciki ,don shi a rayuwar sa ta duniya
babu wata diya mace da yakeso kaman ransa irin shattun . Amma Shattu mai yasa kika ki
amincewa a wannan karon Ayi bikin mu na shad'i mu xama cikakkun ma'aurata?. Jin yanda yayi
mgnan hadi da karke mgnan cike da jin ba dadi ne yasa ta sauke taffan hannun ta daga saman
fuskan ta ,a sanyaye cike da harshen fulatanci ta cigaba da ce masa" aa Hard'o daga wannan
ciranin da xan tafi ,baxan kara komawa ba ,ina dawowa xa'ayi mana shad'i . Kasan da
yagwalgwal xamu tafi kuma baxan dade ba ,kajirani kaima nasan xakayi tafiya wuri mai nisa
idan....kamin ta karake ne ya katseta da cewa" Shikenan Surbajo ta ,a ko ina kikaje ki rikemun
amanan kanki ki kula mun da kanki sosai .
Murmushi shattun tayi kamin tace " muje xan koma Garken mu ,wurin abba nazo ,kuma yanxu
yana da mutane sosai . Murmushi yayi kana a tare suka juya hadi da nufar Cikin rugar don ba
bukkan tasu hardo yy da ita ba kaman yanda tace . Hanyar dandalin matasan fulanin ya nufa
da ita ,inda maza da mata sukayi sansani ,wasu na xaman gulma wasu kuma suna sana'ar
sayar da nono .
******
Dr Kina nufin wannan shine result din ,da gaske ke kenan ina dauke da junan biyun 100%í ½í²— ?.
Tayi mgnan tana bin Dr Hajar da kallo . Murmushi Dr Hajar tayi kamin tace kwarai da gske
Salmah kina dauke da juna biyun hubbyn ki a halin yanxu ,ba karya kika fadi masa ba . Hmmm
nisawa Salma tayi wanda amaimakon naga farin ciki sai akasin hakan na gani domun kuwa
kwallah ne ke diga daga saman kuncin ta . Taune la66an ta tayi kamin ta musguta tana facing
din Aminiyar nata sannan ta fara cewa " Ada baya nayi fatan naganni da cikin wannan bawan
Allah ,anaawa tunanin idan na sanar masa komai namu zaizo karshe zai aureni dole ,amma kin
san meye ? , na sanar masa tunkan na samu wannan tabbacin daga gareki ,sai cemun yayi bai
san wannan mgnan ba ,ba dan shi ne ba dana ne. Ke Hajar a takaice korar kare yayimun cike
da cin mutumci yasa masu tsoron sa suka fataattake ni". Wai yau ni.....kawai sai ta rushe da
wani irin kuka mai ban tausayi da ta6a zuciya .
Nisawa Hajar tayi hadi da dafa Kafadan Salma kamin a hankali ta sauke space din dake saman
fuskan ta sannan ta fara da cewa " wai ban gane ba shi dai wai shidin ne yace hakan ? Kice duk
abun da muke tunani ya xamto shirme da hauka ? Ta6dijam . Abun da Hajar tace kenan tana
mai karkada kafa hadi da son tunano